Sirrin Rike Miji

Ya Ya Launin Jinin Al’ada Yake Da Kuma Launinsa

*JININ AL’ADA………..*

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

*FUTOWA TA 👉04*

*YA YA LAUNIN JININ AL’ADA YAKE DA KUMA SIFFARSA❓*

An shardanta ga jinin Al’ada dole ya kasance cikin daya daga cikin Wadannan launikan sune kamar haka:

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

1- BAQI :  Jinin Al’ada baqi ne mai kauri kuma yana warin najasa saboda fadin manzan Allah (saw) da yake cewa “JININ AL’ADA JININE BAQI KUMA ANA GANE SHI” bukhari da Muslim.

Karanta>>> Amfanin Zogale Guda 18 A Jikin Dan adam

2- JA : Domin shine asalin launin jini.

Karanta>>> Yadda Zaki Haɗa Ingantaccen Maganin Ciwon Sanyi (Infection)

3- FATSI-FATSI : shi ne abun da mace ta ke gani kamar ruwan magunya yana kar kata zuwa fatsi-fatsi.

Karanta>>> Dalillai 4 Da Suke Sawa Nonon Mace Zuwa Ba Tare Da Ta Tsufa Ba.

4- BAQI-BAQI : Shi ne tsaka tsaki tsakanin fari da baqi zaki gansa kamar ruwan datti.

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

Wadannan sune nau’ikan jini da mata suke gani hakan baya nunawa cewa suna tabbata akan hali guda daya ako wane lokaci mace zata iya ganin canji daga yadda take ta koma wani ban garen na daban misali tana ganin baqi ako da yaushe sai ta ga fatsi- fatsi wannan ba wani abu bane don taga hakan.
Amma ganin da mace zata yi na BAQI-BAQI ko FATSI-FATSI baya kasance wa Al’ada sai idan ya zo alokacin kwanakin Al’adar saboda hadisin Ummu Adiyya (RA) take cewa “Mun kasance bama lissafa BAQI-BAQI ko FATSI-FATSI bayan munyi tsarki a matsayin wani abu”. Kenan idan mace tagani ba lokacin Al’ada babu komai atare da ita.

*MU HADU A FUTOWA TA 👉 5*

Karanta>>> Daga Wacce Shekara Mace Take Fara Jinin Al’ada.

Back to top button