Uncategorized

Zaharaddeen Sani zaiyi shara’a da wani alkali dake da zama a magajin gari ta Jahar kaduna kan cin zarafin sa da yake zargi Alkalin yayi.

 Mun samu kwafin wata takardar koke da jarumi zaharadden ya aika dan neman kotu ta bi masa hakkin sa, kan abin da ya kira cin zarafi da kaskanci da tauye masa hakkin sa na mutuntaka da wani Alkali yayi a kotun sa, kan wata shara’a ta cikin gida da aka kai kotun Alkalin yayi amfani da karfin ikon sa ya kaskanta zahraddeen sanin a bainar jama’a.

Lauyoyin Zahraddeen Sani sun shigar da korafe korafe guda goma a kotun daukaka kara, kan mai shara’ar mai suna Malam Falalu Khadi na kotun shari’a dake magajin gari a kaduna, inda suke tuhumar sa da abubuwa kamar haka.

1. A ranar 2 zuwa uku ga watan 3, an kai wanda muke karewa kara kotun mai shara’ar dake zama a magajin gari kan wani sabani da ya faru na cikin gida wanda an riga da an sulhunta sabanin tun kafin ranar zaman shara’ar

2. Duk da wanda ya kai karar ya amince da ya janye gami da dakatar da shara’ar amma mai nshara’ar ya nemi sai ancigaba da shara’ar gaminda barazana ga wanda muke karewa da cewar zai kulle shi ba abinda zai faru.

3. Ayiyin da aka zauna shara’ar bisa ga umarnin Alƙalin Mai shara’ar ya kyari Zaharadden kamar karamin yaro gami da zagi da cin zarafinnsa da kiran sa da sunaye na kaskanci.

4. duk wannan bai isa ba mai shara’ar ya ci gaba da cin zarfin sa da kaskantashi a bainar jama’a ba tare da la’akari da cewa dukkan bangarorin sun sulhunta kansu kan koma menene ya hadasu, wanda dama rikici ne na cikin gidah ba, wanda har ta kaiga kotu ta umarci Zahradden a cikin kotu da ya baro cikin kantar shi ya durkusa a gaban wanda yayi karar shi ya nemi afuwar shi baya ga haka aka sashi ya kara neman yafiyar wannan akaro na biyu wacce bata daga cikin masu kawo kara a kotun.

5. Wanda muke karewa bai taba raina alkalin ko kotu ko umarnin kotun ba a baya kafin faruwar wannan lamari,

6. baya ga cin zarafin wanda muke karewa da kotun tayi, kotun taki amincewa ya tafi har sai da wani mutum na musamman da kotun ta zaba yazo ya karbi belin sa yadda kasan kotun ofishin yan sanda ne.

7. wanda muke karewa yaji mai- shara’ar bai kyauta masa ba ya keta masa hakkin mutuntaka, ya zage shi wanda abu ne a bayyane ya shigarwa wanda yayi karar ne, wanda hakan yaci karo da kundin tsarin shara’a wanda kowa ya sani a cikin tanade tanade shara’a da suke da tsarin hukunci.

8. Wanda muke karewa sanannen jarumi ne fitacce wanda duniya ta sanshi, kuma ke da tarin masoya

9. Cin zarafin sa da Kotu tayi ya rage masa kima a idon duniya.

10. ya shiga damuwa saboda yadda alkalin ya maida fadan nasa kan wani dalili da shi bai san shi ba, Saboda haka wanda muke karewa ya shigar da wannan korafe korafe ga ofishin ka mai daraja da muradi daya a ransa shine zai samu adalci bisa ga cin zarafin sa da keta masa alfarma da zagi da kiransa da kiransa na kaskanci da mai shara’a na magajin gari a Kaduna yayi.

Wannan shine abinda takardar korafin da lauyoyin zaharaddin sani suka aika ga mai shara’a na kotun shara’a na daukaka kara dake bida roada kaduna da fatan Allah yasa shara’ar tayi aikin ta anan, a bi masa hakkin sa kan cin zarafin da aka yi masa domin kotuma tana karkashin shara’a da doka ne Allah ya kyauta.

Back to top button