Uncategorized

Yadda za ki saka mijinki farin ciki

 

Da yawa daga cikin mazajen da ke karo aure na karo shi ne ba tare da son ransu ba, zan iya cewa kashi 30% ne ke karo aure da radin kansu amman sauran matayensu ne ke jawo masu su kara auren ta hanyar rashin kulawa ko kazanta da dai sauransu abubuwa.

Dalilin rubutu wannan kasidar tawa shi ne Yadda za ki hana mijinki karo aure ba tare da kinje wajen wani boka ko Malam ba.

Kadan daga cikin abubuwan da za ki yi wa mijinki ki saka shi farin ciki har ya manta da wata kishiya su ne kamar haka;

  1. Abu na farko da ya zama wajibi a gareki shi ne biyayya, ki nuna masa cewa yana gaba da ke don haka duk abin da ya sa ki babu gardama kawai ki yi muddin bai ci karo da abin da aka yi hani ba.
  2. Na biyu yana da kyau ki giya masa baya dari bisa dari a duk abin da ki ka ga nasara ne a rayuwarsa, kina mai jaddada masa ai nasarar sa taki ce. Idan da dama ma ki taimaka masa da Addu’a ko kudi a duk lokacin da ya ke buƙata, kin nuna masa kin fishi damuwa a lokacin da ya shiga matsala, sannan ki nuna kin fishi farin ciki a lokacin da ya samu nasara.
  3. Ki yawaita tura masa saƙonnin soyayya masu ratsa zuciya da sanyayata a lokacin da ya ke kasuwa ko wurin aiki, domin hakan zai sanya shi farin ciki da annushuwa ba kaɗan ba.
  4. Ba ko wanne namiji bane yake iya tuna ranar zagayowar haihuwarsa, ko kuma ranar da aka daura muku aure da sauran makamantan wadanda abubuwan, to yana da kyau ke ya kasance kina tuna irin wadannan ranaku kuma kina ba shi kyauta idan ranar ta zagayo.
  5. Idan ki ka fahimci mijinki yana da yawan sha’awa, to kiyi ƙoƙari ki dinga biya masa buƙatar akai-akai ba sai kinga yana nema ba, ko baya buƙata ke ki nuna masa kina buƙata. Hakan zai sa ya ji sam baya tunanin karo maki wata.
  6. Abu mafi mahimmanci ga mace shi ne ki zamo mai so da yawan kwalliya, yana da kyau ki zamto wadda bata da ƙazanta ko kadan, domin namiji ba ya son mace kazama koda kuwa shi kazamin ne.
  7. Ki dinga girka ma shi abin da yafi so, kuma idan ya zo ci kar ki kuskura ya ci da kansa, ki bashi da kanki hakan na ƙara danƙon soyayya.
  8. Kin dinga nuna masa a zahiri tabbas kina son sa, da kuma yawaita faɗa masa yadda ki ke son sa. Kada ki bari ko da wasa wata a waje ta fiki nuna wa mijinki kulawa, hakan ba ƙaramin hatsari ba ne ga rayuwar aurenki.
  9. Idan mijinki ya ɓata maki rai, kada ki haushi da zage-zage, ki bi shi a hankali ki sanar masa. Hakan zai sa jikinsa ya yi sanyi ya gane kuskurensa.

Tura zuwa 

Back to top button