Uncategorized

Shin ko da gaske ne Uwar gidan shugaban ƙasar Najeriya A’isha Buhari nada ciki

 Sabbin Hotunan Uwargidan Shugaban Najeriya A’isha Buhari na ƙara rura wutar jita-jitar cewa wai A’isha Buhari tana da ciki, inda ‘yan Najeriya ke tunanin ko da gaske tana da cikin ko a’a. 

A ɓangare ɗaya kuma cikin hotunan da jaridar Peoples Gazette ta gani, A’isha Buhari tare da mijinta, shugaban kasa Muhamadu Buhari, suna tare da jami’an tsaro, ɗaya daga cikinsu dauke da jakunkuna.  Uwar gidan na sanye da lace mai launin rawaya da bakar shawl da ke lulluɓe da abin da ya zama kamar na jariri.

A’isha Buhari mai shekaru 50 ta ɗora hannunta na dama a hankali.  Wani hoto ya nuna ma’auratan suna zaune a cikin jirgin sama. 

 Wani zuzzurfan bincike da aka yi akan Mrs Buhari ya nuna cewa fuskar A’isha ta kukkumburo irin ta mace mai juna biyu.

Hoto na uku ya nuna ma’auratan akan matakalar jirgin, da alamun jinjirin ciki a tare da ita. A yayin da uwargidan shugaban kasar take sauka a hankali.  

Za Ku Iya Karanta 

✓ Maryam Yahaya bata jin magana wallahi – Datti Assalafy

✓ Tsohuwar Matar Adam A. Zango ta sake dawowa Kannywood Bayan shekaru 13

 Gwamna Aminu Tambuwal ya bada umurnin kamo mawakin da ya waƙe shugaban ‘yan bindiga Bello Turji

✓ Shatu Garba daga Kano ta lashe gasar sarauniyar kyau ta Nijeriya

Ga kadan daga cikin maganganun yan Nigeria da suke yi akan A’isha Buhari.

“Aisha Buhari tana da ciki ko abin da ke cikinta,” in ji wani mai amfani da shafin Twitter @Promise. 

 Shi ma wani mai amfani da shafin Twitter, @Solowizzy ya yi tsokaci a kan hotunan, inda ya ce, “Yan Najeriya me ku ke tunani kan wadannan hotuna?  Babu shakka Aisha Buhari tana da ciki.”

 A wani sako mai ban dariya da wani shima ya wallafa a shafinsa na Twitter, @Alamin97296003 ya taya Buhari mai shekaru 79 murna kan “kwazonsa”.  “Aisha Buhari tana da ciki.  Baba Buhari mai aiki tukuru,” inji mai amfani da Twitter.  

Idan har da gaske tana da ciki, Mrs Buhari, wacce ta riga ta zama kaka, za ta kasance matar shugaban kasa ta farko da take da juna biyu a lokacin da mijinta ke kan mulki, kuma mai yiwuwa ita ce ta fara haihuwa a fadar shugaban kasa.  

Shugaban Buhari dai nashan caccaka daga al’ummar Nigeria biyo bayan taɓarɓarewar tsaro da musamman yankin Arewacin Najeriya yake fuskanta, kuma shugaban ya kasa yin komai akan lamarin. An dauki hotunan ne biyo bayan isowar ma’auratan farko daga kasar Turkiyya.

Back to top button