Uncategorized

AlhamduLillahi Anyi sulhu tsakanin Naziru Sarkin Waƙa da Abubakar Maishadda.

 

Alhamdu Lillahi an samu daidaito tsakanin Naziru Sarkin waƙa da Abubakar Maishadda a yau da yammacin nan na ranar Litinin.

Biyo bayan kace-na-ce da yan kannywood ɗin nan suka dinga yi, haɗi da tonon Silili da suka dunga yi wa kansu daga ƙarshe dai sun karɓi batun yin sulhun hannun bibbiyu.

Naziru sarkin waka ya saki wani bidiyo a shafinsa na Instagram inda yake kara jadadda maganar Mama gaskiya ce, har ma ya kara da cewa wasu yan matan Film din ma, sai suna bada kansu kafin a yarda a saka su a film. Wannan maganar tashi zamu iya cewa ita ce ta kara hura wutar rigimar. 

Nuhu Abdullahi ya ce da zamu fito muyi magana da mutuncinku ya zube. Shi ma wannan maganar tasa ta jawo ka-ce-na-ce. 

Wasu kuma irinsu Ali Artwork sun goyi bayan maganar Sarkin Waka duk da kuwa ya soki wasu daga cikin.

         KARANTA WASU LABARAN

Ana ci gaba da tona wa yan kannywood asiri akan fitar da BBC Hausa suka yi da Ladi Cima

Cikin ƙunar rai Jaruma Nafisat Abdullahi ta mayar wa da Naziru Sarkin waƙa raddi.

Asirin wasu daga cikin daractotin kannywood ya tonu 

Sauran jarumai da dama sun yi magana cikin ruwan sanyi domin kwantar da hankali abokan aikinsu, sun yi matukar kokari wurin ganin sun kashe wutar da ke cigaba da huruwa. Kamar irin su Tijjani Asase da kuma Sabir Abdul. Musbahu M Ahmed wanda yaya ne ga Sarkin waka, jan kunnen Yan Film yayi kan su guji furta maganganun da zasu jawo rigima.

Sai dai daga ƙarshe zamu iya cewa anyi wa tufkar hanci domin an shawo kan lamarin biyo bayan shiga maganar da Kamal S. Alƙali, Mubarak A. Kabba da kuma yayan Naziru Sarkin Waƙa wato Musbahu M. Ahmad suka shiga cikin lamarin.

Kamar yadda Abubakar Maishadda ya wallafa a shafin sa na Facebook ya rubuta 

LONG LIVE KANNYWOOD ❤️❤️❤️

@kamalalkali2 

@sarkin_wakar_san_kano 

@misbahu_m_ahmad_ 

@mubarakabba3

Back to top button