Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 53 Complete Novel
*ASM Bk2053*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
………..kasa jurewa tay a hankali ta maida idonta k’asa shima maida nashi yay ya lumshe bayan wani lokaci ta d’ago ta sake kallon shi har lokacin bai bud’e idanun nashi ba hakanan sai taji wani iri don kallon da ta ga yana yi mata ba kalan wanda yake mata bane a kwanakin baya kafin hakan ta faru, maida idon tay tana kallon gaban ta cikin ran ta tana k’ara tariyo abubuwan da suka faru gaban ta ne ya fad’i tunowa da jinin data gani nan ta fara kokonton anya cikin bai fita ba kuwa lokaci guda ta yanke ta san ma zai yi wuya in yana nan, wani iri taji damuwa ta bayyana kan fuskar ta sai kuma ta hau yin tunanin halin da gwaggo da Hajiya suke ciki tana haka taji fitsari ya matseta ta fara kokarin yunk’urawa ta tashi dama an riga an cire mata k’arin jinin da aka saka mata na farko a can gefe ta hango gyalenta dama yana jikinta aka zo da ita Saboda rolling d’in shi tay sai bayan an kawo ta d’akin ya kwance, bayan ta yafa gyalen saman kanta zuro k’afafun ta tay a hankali ta saukko daga saman gadon wani irin fayau taji ta kwata kwata ba k’arfi a jikinta ga juwa na niyyar kwasar ta ba shiri ta koma ta zauna tasa tafin hannun ta guda ta dafe forehead d’inta duk Haisam na kallonta don tunda ta fara k’ok’arin saukkowa ya bud’e ido jin mutsu mutsun da take, bin ta yay da kallo ba tare da ta sani ba can ya yunk’ura ya tashi tsaye walking slowly ya nufe ta duk bata sani ba har saida taji k’amshin shi jikin shi ya cika mata hanci sannan ta d’ago da fuskar ta da d’an sauri idanunta suka sauka a cikin nashi wani irin bugu kirjinta yay ta kafe shi da ido had’i da d’an motsa baki kamar zata ce wani abu amman ta kasa furta komae Slowly taji cool voice d’in shi ya furta “Let me Help” ya mik’a mata hannu duk tayi tsuru tsuru kamar mara gaskiya ta kai hannu a d’arare ta kama santalelen hannun nashi jajir dashi ga taushi kai kace ba hannun babban namiji ba don kuwa banda yanayin halittar fata shi kan shi hannun yana shan tsadaddun mayukan gyara masu saka taushi, bayan ta mik’e tsaye zame hannun na shi yay ya zagaya dashi ya tallabo Shoulders d’in ta suka fara tafiya fuskarta a k’asa gaban ta naci gaba bugawa har suka isa bakin kopar toilet d’in sannan ya dakata ya zame hannun nashi ta d’an kalle shi sai taji yace “Can u….or I should call Nurse?” d’an girgiza kai tay a hankali tace zata iya shiru bai ce komae ba ta juyar da fuskarta ta tura ta shige ta maido k’opar, toilet d’in tsaf kai kace bana asibiti ba duk da ba bathtub amman har heater ta ruwan zafi akwai da shower, butar data gani wadda gwaggo tasa Amadu ya kawo ta d’auka ta tari ruwan zafi daidai yadda zafin zai mata, lokacin data tattare rigarta gabanta ne ya fad’i ganin cinyoyinta jage jage da jini bata yi mamakin rashin ganin pant d’in data sa ba don tasan a ina take zai yuwu an cire shi ne, jiki a mace ta duk’a ta fara yin fitsarin bayan ta gama tay amfani da ruwan wurin wanke k’asan nata sosae bayan ta gama ta mik’e tsaye da k’yar, tunanin yakamata tay wanka ta shiga yi don tasan duk jini ne a jikin rigar don ma tana bak’a saidae bata san kuma ko akwai wasu kayan da zata canza ba, matsawa tay ta jingina da bango tay shiru sam ta kasa karantar yanayin da ta ga fuskar Haisam don sai take ganin kaman yana d’aure fuska, tana ta tsaye ta rasa mike mata dad’i gashi bata san ya zata yi ba tana son yin wanka amman bata san ko akwae kaya ba kuma sai take ta jin fargabar fita tana haka taji an yi knocking kopar har saida kirjinta ya d’an buga damm da sauri ta kai ido kan kopar k’ara knocking d’in akai ta nufi kopar cikin rashin k’arfin jiki tasa hannu a hankali ta bud’e tay arba da Fuskar shi, bin shi tay da ido ya mik’o mata abun hannun shi wanda towel ne da soap dish ta kai hannu ta amsa murya k’asa k’asa tace mashi ta gode bai ce komai ba ya juya itama ta koma ciki, yana bata kayan waje ya nufa yaje yay ma Nurse Magana kan azo a gyara mata bed har ya dawo bata fito ba ya zauna kan kujera yana nan aka zo aka gyara gadon aka canza Bedsheet can ya tuna da Magungunan da Dr Habeeb ya tura pharmacy don yace akwae yuwuwar ba sai an yi mata wankin ciki ba don yana tunanin komae ya fito sakamakon jinin da ya zuba sosae zuwa washe gari za’ai mata scanning don a tabbatar mik’ewa yay ya tafi ya amso, bayan ta gama wankan tsaye tay ta kasa fita da towel d’in jikinta wanda iyakar shi tsakiyar cinyoyin ta, tana ta tsayuwa gashi jiki ba kwari can dae ta nufi kopar saida tay d’an jimm kafin hannu na rawa ta kama handle d’in ta bud’e sai dae tana sa kai taga d’akin wayam ba kowa wani sanyi taji ta shiga ta nufi gadon da taga an gyara mata shi zaunawa tay tana ta yan kalle kalle ta hango jakar kayanta a gaban drawer d’in gadon ta tashi ta d’aukko ta a gefen gadon ta d’aurata ta bud’e, hannu ta kai tana d’an d’aga kayan kafin ta fiddo wata doguwar rigar material ta aje gefe ta ciro pant da pad data gani suma ta aje tunanin ko ta koma toilet tasa kayan ta shiga yi wata zuciyar ta raya mata tunda ita kadae ce ta sa anan mana k’ilan har ta gama bai shigo ba, yin wannan tunanin yasa da sauri ta bud’e pad d’in ta ciro wadda zatai amfani da ita tasa a jikin pant d’in bayan ta gama ta saukko daga saman gadon ta zura pant d’in tana kokarin sanyawa taji an turo kopar aikuwa da sauri ta d’ago ta kalli kopar ba tare da ta ankare ba kuma towel d’in ya kwance Saboda d’agowar da tayi ba shiri nan take boobs d’in ta suka bayyana duk ta dabarbarce don kuwa idon shi na akanta ganin haka yasa da sauri ya koma yaja mata kopar, ta d’ago da towel d’in da sauri had’i da dafe k’irji tana kallon kopar kafin a kasalance ta duk’a taci gaba da sakawa bayan ta gama ta zura doguwar rigar ta fiddo hula ta saka ta zuge jakar har ta koma ta zauna sai kuma ta mik’e ta d’auki towel d’in da ledar da ta ciro pad da yan takardun ta nufi toilet da ganin yadda take tafiyar jikinta sam ba kwari, bayan ta dawo still bai shigo ba ta koma bakin gadon ta zauna tana facing kopar tama rasa tunanin da zatayi tay zuru sai kikkafta ido take tana haka ya turo kopar da yar sallama ya shigo suka had’a ido a hankali ta amsa kafin ta maida idonta k’asa da sauri ta fara d’an wasa da yatsun ta, wurin gadon ya nufa a saman yar drawer d’in gefe ya d’aura ledar drugs d’in ya juyo ya d’an kalle ta kan ta a k’asa kaman yana son cewa wani abu ji tay a jikinta ita yake kallo ta d’an d’ago a hankali suka had’a ido taji yace “How are u feeling?” a sanyaye tace “Alhamdulillah da Sauk’i” shiru bai ce komae ba can taji yace “are u done with this?” jin tambayar yasa ta kai idon ta kan jakar kayan da ke gefen ta kafin ta kalle shi ta d’aga kai alamar eh ta gama amfani da ita hannu ya kai ya d’auke ta ya maida ita inda take da, duk’awa yay wurin kayan Abincin ya d’auki plate da spoon sai bottle water ya mik’e ya nufi window d’in d’akin bayan ya zuge net d’in jiki ya fara d’auraye su Fatuu nata kallon shi har ya gama ya rufe ruwan tana ganin zai juyo ta maida idonta k’asa ya dawo ya tsugunna gaban basket d’in Warmers masu d’auke da abincin ya fara bud’ewa, Faten dankalin ya zuba ya saka spoon d’in kafin ya mik’e ya kai mata ta mik’a hannu ta amsa nan ma saida ta furta mashi ta gode bai ce komae ba ya juya tabi shi da kallo, rufe warmer d’in yay ya koma kan kujerar ya zauna had’i da jingina bayan shi ya d’an d’age kan shi, gaba d’aya jikinta ya mutu Saboda canjin da ta gani a tattare da shi da k’yar ta d’auki spoon d’in ta fara ci duk yadda Abincin yay mata kyau a fuska sam ta kasa jin dad’in shi a baki hakanan dae take ci kad’an kad’an saida taci kaman rabi sannan ta tashi zata maida wurin kayan Abincin lokacin ya sauke fuskar idanun shi suka sauka a kan ta wani kallo ya jefa mata ta sadda kanta k’asa cike da bada umarni taji yace mata ta cinye shi duka d’agowa tay ta kalle shi still kallon dae yake mata jiki a sa6ule ta koma ta zauna don sai taga kaman ma hararar ta yake, ba yadda ta iya haka ta dingi turawa ba don tana jin dad’in shi ba har ta samu ta cinye tana niyyar mik’ewa taga ya taso yazo gabanta, amsar plate d’in yay ya maida ya k’ara d’aukar wani yaje ya wanko shi bayan ya dawo ya zuba mata farfesun yan cikin shima ya mik’a mata ta amsa yanzu bata ce mashi ta goden ba saidae ta d’an kalle shi, bayan ya juya plate d’in da ta 6ata ya d’aukka yaje ya wanko shi ya maido, kujerar ya koma ya zauna ya k’ara d’age kan kaman d’azu, sosae farfesun yay mata dad’i saidae damuwa ta hana taci shi sosae don gani take kaman dai da gaske fushin yake, bayan ta d’an sha kawai sai ta aje spoon d’in tsam ta mik’e zata aje shima sai gashi ya sake juyowa ya kalleta nan take tay pause tana kallon shi fuska a yamutse daga inda yake taji yace “Eat it up!” d’an yamutsa fuska tay cikin rawar murya tace “na k’oshi” shiru bai ce komae ba idon shi akanta itama ta kasa motsawa balle ta aje can ya mik’e ya nufo ta yazo daga gabanta ya tsaya suna facing juna abu ta rink’a had’iya ta sak’a d’ayan hannun da bada shi ta ruk’e plate d’in ba gefen wuyanta tana d’an sosa wurin kasa jure kallon shi tay ta maida idon t k’asa, hannu taga ya mik’o ya amshi plate d’in ta kalle shi da kai yay mata alamar ta zauna ta koma gefen gadon kawae sai gani tay shima ya zauna a gefenta ya fara d’ibowa zai bata ta yamutsa fuska idanunta har sun ciko tace mashi ta k’oshi wani kallo ya wurga mata ba shiri ta bud’e bakin ya zuba mata ta fara taunawa tana kikkafta ido, haka yaci gaba da bata har ta dai ta saki Fuska taci gaba da ci tana yi tana satar kallon shi wani lokacin su had’a ido sai tay saurin janye idon ga k’amshin shi da ya gama cikata, saida ta cinye shi duka sannan ya mik’e ya maida plate d’in ya d’aukko mata ruwa bayan ya bud’e mata ya mik’a mata ta amsa tasha da d’an yawa sannan ta cire robar daga bakinta ta mik’a mashi ya amsa ya rufe, ledar fruit ya bud’e suma ya zuba a plate d’in ya mik’a mata k’in amsa tay ya wani d’aure fuska kawae sai ta saka mashi kuka still yay yana kallon ta komi yay mata na kuka shida ko tanka mata bai yi ba cike da shagwa6a duk da ita ba da niyyar shagwabar take yi ba nature d’in ta ne haka taci gaba da yamutsa fuska tana d’an ta6e baki kalan yadda take kuka tun yarinta tana ta faman kikkafta ido kwalla na gangaro mata shi dai kallon ta kawai yake ga abu ta barshi dashi a hannu sigh yay ya d’age gira yace mata “na buge ki ne?” da sauri ta girgiza mashi kai alamar a’a ya sake cewa “to wannan d’in na miye?” yay mata nuni da k’wallan dake zubawa da ido shiru tay ta sadda kanta k’asa har saida yace ba magana yake mata bane sannan ta d’ago tana d’an share kwallan cikin muryar kuka tace “ba komae” shiru bai ce komae ba sai ya koma gefen ta inda ya tashi ya sake zaunawa ya d’aukko 6ararrar ayaba zai bata tana ta goge kwalla ba tare data kalle shi ba hakan yasa bata san yana mik’o mata ba saida taji yace “FATUU” damm k’irjinta ya buga a ranta ta maimaita sunan daya kira ta dashi don tunda yasan sunanta bai ta6a kiran ta da hakan ba sai yau nan take jikinta yay lakwas tamkar an watsa ma kaza gishiri a sa6ule ta kai idon ta gare shi taga ayabar da yake mik’o mata a hankali ta bud’e baki ta d’an gutsira ta fara taunawa, haka yaci gaba da bata har saida ta shanye komae ya maida plate d’in ya d’aukko ledan magungunan daya aje da ruwa ya sake zaunawa suma ya shiga 6aro mata yana mik’a mata tana sha da ruwan har ta gama dama bata gudun magani allura ce wani lokacin ake fama da ita shima kafin ta girma haka yanzu saidae in za’a yi mata ta cije baki da runtse ido, bayan ya maida komae duk plates d’in ya wanko su ya bud’e warmer d’in ya zuba Abincin don shima yunwa yake ji bayan ya saka spoon ya nufi kujera tana ta bin shi da ido har ya zauna a nutse ya soma ci, Allah sarki true love sai kawae taji tausayin shi ya kamata ta shiga tunanin k’ilan ma ya dad’e bai ci Abincin ba tunda hakanan ma tasan ba ci yake sosae ba, tana ta zaune tana kallon duk wani motsi da yake wurin cin Abincin kama daga kai cokalin ya d’ebo zuwa kai wa bakin shi saida ya d’an d’auki lokaci da farawa tukunna ba tare data ankare ba taga ya juyo sun had’a ido duk sai ta kame kanta sum sum kaman munafuka ta haye gadon ta kwanta had’i da juya mashi baya, cigaba da cin Abincin yay har ya gama ya tashi ya d’ebo farfesun bada yawa ba shima ya sha da ya gama ya je ya wanke abun da 6ata ya d’auki bottle water ya koma kan kujeran ya bud’e yasha da d’an yawa bayan ya gama ya rufe murfin ya ajeta a gefe ya maida bayan shi jikin kujerar ya kai idon shi kan Fatuu data duk’unk’une wuri d’aya ya d’an d’auki lokaci yana kallon ta kafin ya janye idon ya kai hannu ya d’auki wayar shi ya fara latsawa can kuma ya aje ya mik’e bargon daya shimfid’a ya d’auka ya nufeta yana zuwa bakin gadon ya bud’e shi ya lullu6a mata lokacin idon ta biyu tay ma bango tsuru taji ya rufa mata, lumshe ido tay yana daga abunda ke k’ara mata k’aunar Haisam wato sanin yakamata don kuwa kaman yasan sanyi take ji kuma ta rasa yadda zata sanar mashi, yana gama rufa mata wayar shi ta fara ringing ya nufi inda take bayan ya zauna ya kai hannu ya daukko sunan daya sa ma Fanan ya bayyana akan Screen yasan su can gari ya waye, picking yay ya kara ta a kunne tun kafin tace wani abu yace mata “Good Morning” cikin sigar shagwa6a ta amsa mashi ta tambaye shi ya akai bai yi bacci ba yace mata yayi farkawa yay da bud’ar bakinta sai cewa tay wai ba dae yana soyayya da wata bane ta waya d’an guntun murmushi yay yace mata ai da taji yana waya ko tace ai wai ko chat fuska a sake yace mata yana wani aiki ne tace mashi Ok, tambayar shi tay mai jiki yace mata ya samu sauk’i sosae shima ta tambayi na shi yace ya warke cike da shagwa6a tace “so when are u coming back, serious am missing my husband ina daurewa ne kawae” d’an murmushin da ta ji sautin shi yay kawae tace “seems like u’r not missing me babe” sigh yay yace waya fad’i mata tace gashi nan ta fad’a mashi tayi missing nashi but bai nuna shima yana nata ba, yana murmushi yace ai abunda ta sani ne dole yayi so ba sai ya fad’a ba, d’an murmushi tay tace tama manta waye mijin nata, tambayarta yay waye shi tana yar dariya tace wanda magana ke ma wuya d’an Murmushin gefe yay kawae,
“I asked when are coming back baka fad’a man ba” shiru ya d’an yi kafin yace mata ya kusa yanzu yana Katsina ne da alamun mamaki ta tambayi mi yaje yi Katsina kuma yace ya rako Hajiya ne sai kuma wani aiki ya rike shi a shagwa6e tace to yanzu har sai yaushe kenan yana murmushi yace “Don’t worry I will come back soon” da sauri tace “not soon babe soonest in ba haka ba zan zo ne nan” yar dariya yay har hak’oran sa suka d’an bayyana yace mata aikin nata fa tace shima ai yana aikin ko yace ai shi yana da strong reason Dad d’in shi ke bai lafiya,
“But tun kafin ya fara ciwo ka taho ai” yace ai wannan ya nemi permission ne sai kuma ya k’ara nema yanzu Saboda ciwon kuma ko daga nan zai iya yin wani aikin tace itama sai ta nema ai tana da babban dalili tunda wurin mijinta zata zo yace banda wanda aka bata taje Germany tana yar dariya tace zata k’ara nema ne kaman yadda shima yay, nan yace mata kar ta damu zai dawo bada dad’ewa ba tace Ok, suna cikin wayan ta tambaye shi Zarah har saida ya d’aga ido ya kallo Fatuu kafin ya bata amsa da tana lafiya tace ai ta yada ita ko waya ta manta last da sukai itace ma ke mata magana ta WhatsApp wani lokacin sigh yay yace mata tasan yanayin karatun da take may be bata samun isashshen time ne tace hakane Allah ya bada sa’a slowly ya amsa da Ameen, tun dae yana wayan a zaune har ta kai ya d’an kishin gida ya aje wayan a hannun kujera yasa speaker saidae ya rage volume dama baida juriyar ya kafa waya a kunne yay tayi, duk wannan abun idon Fatuu biyu ta ji tun lokacin da ya fara yin wayan saidae kwata kwata bata jin mi yake fad’a don dama bai d’aga murya ko a waya balle kuma da yake da Sweetheart d’in shi yake wayar, duk da Fatuu bata gane da ita bane amman ran ta ya bata itace, runtse idonta tay ta shiga jefa ma kan ta tambayoyin da bata da amsar su, tambayar farko wadda tafi d’aure mata kai itace yanda akai Ya Haisam ya aureta ba kamar data ji gwaggo tace dalilin fasa aurenta da Khalid kenan wanda ita dae tasan tun bayan data je ruga sau d’aya ma su kai waya da shi har sai bayan da suka dawo nan ta ayyana ashe ranar da sukai Vedio call da yace zai ga fushin da take dashi ita matar shi ce, tsananin mamaki ne ya cika ta sai kuma ta d’an yi murmushi, tambaya ta biyu data sake jefa ma kanta itace ya matsayin auren yake tunda ba wanda ya bayyana mata har sai yanzu da Al’amarin nan ya faru shin auren zai d’ore ko kuwa ba zai d’ore ba don ta fahimci kamar ba don hakan aka yi shi ba, gashi kamar yana fushi da ita kuma tasan don abunda ya faru ne ga maganganun data je ta fad’a mashi har tak’i d’aga wayar shi wanda tasan da ta d’aga kiran nashi da hakan bai faru ba, tambaya ta k’arshe da har saida gaban ta ya fad’i sosae itace yanzu in auren zai d’ore ne ya Aunty Fanan zata ji anya zata amince da ita matsayin KISHIYA tunda ta tabbatar itama ba ta san da auren ba kaman yadda ko Hajiya bata sani ba wata zuciyar ta raya mata ga dangin su kuma suma ba lalle ma su amince ba, wani irin sanyi jikinta yay ta raya ita dama ta dad’e da fahimtar Ya Haisam ya fi k’arfinta ba iya samun shi zatai matsayin miji ba hakanan zuciyarta ke azabtar da ita da son shi duk kuwa yadda taso ta cire shi abun ya gagara duk aje a dawo son shi na nan mak’ale a zuciyar, wasu siraran hawaye ne suka fara gangaro mata masu d’umi taci gaba da tunane tunane a haka bacci ya d’auketa, shima tuni sukai sallama da Fanan d’in ya nuna mata bacci yake ji, gaba d’aya kwanciyar bata mashi dad’i dama d’azun harda k’arin da bargo ne ya samu har bacci ya d’auke shi yanzu kuwa ji yake ya takura ga kayan jikin shi daya kwanta dasu su kan su a takure yake da su don bai saba kwana da kaya ba bai ma tunanin ya ta6a kwana da kaya haka, hakanan dae ya d’aure yana ta faman gyara kwanciya akai akai, bai fesa maganin daya gani a cikin basket d’in ba don ba sauro a d’akin tunda akwae Ac ga kuma fanka sannan windows d’in akwae Net, sai can dare ya raba ya samu bacci ya d’auke shi,
A kan kunnan shi aka fara kiran farko na sallar Asuba hakan yasa ya tashi zaune ya kai idon shi kan Fatuu dake ta bacci, d’auke idon yay ya shiga tunanin yadda zai yi salla don bai using wani toilet ba wanda ya saba amfani ba balle kuma na Asibiti gashi bai yuwuwa yace zai tafi gida ya barta can yay deciding ya shiga na cikin d’akin kawae ya mik’e ya nufi toilet d’in, after few minutes ya fito harda Alwala yayo ya koma wurin kujeran ya ciro prayer mat dake jikin ta ya shimfid’a ya kabbara raka’atanil fajr bayan ya sallame zaune yay yana tasbih ta hanyar yin amfani da wayar shi har lokacin salla yayi sannan ya mik’e saida yay d’an jimm yana kallon gadon sai kuma ya juya ya tafi, har aka gama sallar ya dawo bata farka ba ya koma kan kujerar ya zauna ya bud’e wayar shi ya fara yin Azkar bayan ya gama ya ajiye wayar ya d’an zamo jikin shi daga kan Sofa d’in ya d’age kai had’i da lumshe ido yana haka yaji motsin ta slowly ya sauke kan ya kai idon shi kan gadon lokacin ta tashi zaune suna had’a ido tay saurin maida kanta k’asa,
“Do u need anything?” taji cool voice d’in shi yana tambaya daga inda yake d’agowa tay ta kalle shi a sanyaye tace toilet zata je d’an shiru yay sai kuma yace “Do u need Help?” Girgiza mashi kai tay alamar a’a bai ce komae ba ta fara kokarin saukkowa daga kan gadon, ba laifi taji k’arfin jikin ba kaman jiya ba idon shi a kan ta har ta shige cikin toilet d’in, bata d’au lokaci ba ta fito idon ta a k’asa ta nufi gadon ta zauna a gefe kan ta a sadde, pad da pant take son ta d’auka don ta canza amman ta kasa d’auka tana haka taji yace “U need to take bath” da sauri ta d’ago ta kalle shi suka had’a ido kaman yar k’adangaruwa ta d’aga mashi kai sai kuma murya na rawa ta gaishe da shi ya amsa had’i da tambayar jikin ta tace da Sauk’i sosae ya d’aga mata kai kawae ya janye idon shi daga kallon ta har yanzu dae canjin da ta gani a fuskar tashi yana nan, mik’ewa tay ta nufi inda jakar kayan take ta duk’a bayan ta bud’e ta d’auki abunda take buk’ata ta rufe jakar ta mik’e tana rungume da su ta nufi Toilet d’in still kallon ya bita dashi har ta shige, saida ta gama kimtsawa a ciki sannan ta fito bata gan shi a cikin d’akin ba saidae attender dake Mopping sarkin tsafta har yaje ya kira azo a goge suna had’a ido da matar Fatun ta gaishe da ita tana murmushi ta amsa tay mata ya jiki tace da Sauk’i ta nufi gadon ta haye ita kuma bayan ta gama har kujerar ta kakka6e ta nufi cikin toilet d’in don ta gyara shi tana shiga sai gata ta fito ruk’e da dustbin ta yi hanyar fita, saida aka gama gyara d’akin fess sannan ya shigo lokacin Fatuu na zaune ta jingina da kan gadon ta bishi da ido har ya zauna sannan ta janye idon, tsit kake ji sai kace ba mutane a d’akin ko kuma kurame ne a ciki bayan d’an wani lokaci ya fara tunanin ya samo mata wani abu ta ci sai dai kuma yasan yayi safiya da yawa ko ya fita ba lalle ya samo wani abu ba hakan yasa shi tunanin ya bari garin ya d’an k’ara wayewa, suna ta zaune can ta d’an saci kallon shi karaf suka had’a ido kasa janyewa tay shima kallon nata yake kawai sai ji tay yace “kina jin yunwa ne?” tambayar ma saida taso ta d’an bata dariya amman ba halin yi da sauri ta girgiza mashi kai alamar a’a sai kuma kamar mara gaskiya ta zame ta kwanta ta juya mashi baya don ta fahimci Saboda kallon data yi mashi ne yasa shi yi mata tambayar bin bayan ta yay da kallo can kuma ya d’age kan had’i da lumshe ido, karfe bakwae saura yan mintuna aka kwankwasa kopar ya sauke kan ya kai idon shi kan kopar saida aka k’ara knocking d’in sannan yace a shigo kopan a bud’e take aka turo Amadu ne ya fara shigowa yana ruk’e da basket mai d’auke da kayan abinci gwaggo na biye da shi itama tana ruk’e da wasu kayan harda bucket da kujera yar tsugunno ta roba yana ganin su ya mik’e tsaye fuskar shi a sake yake kallon su suka nufo ciki suma duk suna yi mashi murmushi, a gefen gadon ya aje basket d’in gwaggo dake gefe da murmushi tace “Sannu d’ana Haisam ya kwanan Asibiti” d’an murmushi yay yace mata Alhamdulillah had’i da gaishe da ita bayan ta amsa tace “Amman dae nasan baka samu yin bacci ba kwanan Asibiti akwae takura gashi ba’a shirya mashi ba” still murmushin yake yace mata yayi bacci yar dariya tay tace ya dae fad’a ne Amadu ya gaishe dashi yayi mashi ya mai jiki ya amsa, ganin yayi tsaye tace mashi yay zaman shi zata zauna a gefen gadon ya koma yace ma Amadu yazo ya zauna itama gwaggo ta zauna idonta akan Fatuu dake ta bacci ta lullu6e tana son ta tambayi ko ta farka amman ta kasa Saboda kunya can dae ta kalle shi tana murmushi tace “ya mai jikin?” Kallonta yay calmly ya furta “da Sauk’i sosae tun jiyan around 11 ta farka yanzu bata dad’e data koma ba” wani sanyi gwaggo taji cikin ranta Amadu ma har saida yay d’an murmushin jin dad’i gwaggon tace Allah ya k’ara lafiya duk suka amsa da Amin shiru ta biyo baya, bayan d’an wani lokaci gwaggo tace ma Haisam ko a had’a mashi breakfast taga safiya ce sosae bata san ko zai ci ba yace mata a’a tace to ko tea ne a had’a mashi ya gasa cikin shi fuska a sake yace mata ba zai iya sha ba bai wanke baki ba tana murmushi ta jinjina kai kawai don ta san shi sarkin tsafta ne da gaske ba zai iya cin ba, Shiru suka k’ara yi Amadu na latsa waya ita kuma gwaggo kanta a k’asa tana yi tana d’an juyawa ta kalli Fatuu can ta juya ta kalli Haisam daya had’e hannuwan shi ya kifa goshin shi tace “d’ana Haisam Don Allah ka tashi kaje gida ko ka samu ka huta sosae” slowly ya d’ago ya d’an kalleta suka had’a ido sai kuma ya kawar da idon bai ce mata komae ba dae hakan yasa ta k’ara ce mashi yaje ba wani abu ai tunda gasu sun zo, a hankali ya furta to tare da yin godiya ya mik’e bayan ya d’auki wayar shi sukai sallama ya nufi kopa ya fita,
“Bawan Allah ni tausayi ma ya bani da gani bai samu isashshen bacci ba” Amadu ne yay Maganar gwaggo tace “taya zai samu yin isashshen bacci a nan duk da dai kamawa take amman nasan da wuya in ya ta6a jinyar wani haka suda suka saba kai mara lafiya K’asar waje shiyasa wllh ban so ya kwana ba don dole zai takura to ba yadda zan yi da Hajiya” shiru Amadu yay can ta mik’e ta cire hijabin jikinta ta d’auki bucket d’in da kujerar ta nufi toilet, bayan ta shiga fess ta gan shi dama niyyarta in yana buk’atar gyara sai ta gyara anan taga rigar Fatuu data cire jiya da undi ta d’aukko su ta saka acikin bucket d’in don ta wanke, Amadu na zaune ruk’e da wayar yana lallatsawa kaman daga sama yaji muryar Fatuu ta kira sunan shi da sauri ya d’aga kai ya kalli gadon suka had’a ido da ita ta tashi zaune gaba d’aya hankalin shi na akan wayar har baiji motsin tashin ta ba, mik’ewa yay ya nufi gadon yana washe baki ya zauna a gefe itama murmushi take mashi cike da farin ciki yace “Sannu kin tashi?” Kai ta d’aga mashi a sanyaye ta tambayi yaushe ya zo yace basu dad’e ba harda gwaggo tana cikin toilet ta d’aga mashi kai ya tambayi ya jikin nata tace da Sauk’i sosae yanayin fuskar shi ne ya canza “ashe haka abu ya faru ni ban sani ba koda nazo lokacin baki farka ba saida muka koma gida da daddare gwaggo ke sanar dani” shiru tay ta zuba mashi ido can yaji tace “Kawu Amadu miyasa baka ta6a fad’a man zancen auren ba duk da kasan ni ban 6oye maka abu” yadda tay Maganar kaman zatai kuka shima yanayin fuskar tashi ne ya sauya zuwa yanayin damuwa ya kai hannu ya kamo hannunta guda yace “ba hakanan na k’i fad’a maki ba gwaggo ce ta hana tace kar in sake inyi maki Maganar shine dalili” d’an ta6e baki tay kwallan da suka taru suka zubo sharr da sauri ya kai hannu yana goge mata yana bata hak’uri had’i da nuna mata komi ya faru haka Allah ya k’addara suna haka gwaggo ta bud’e kopar toilet d’in ta fito…………
….
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.