Novel Document

Karshen Wahala Novel Document

Description/Story:

Karshen Wahala! Novel Document

Written By Aisha A. Muh’d 

 

Description

Yanayin unguwar irin unguwar masu hannu da shuni ce gwamna road a garin kd,family d’in gdn gaba d’aya suna xaune a k’ayataccen falon su hira sosae suke da kagan su kasan happy family ne ….

 

Alhaji sa’eed haruna kenan da matar shi hajia maimuna sai yaran su safah itace babba sai nauwarah da k’aramin su saleem,su kadai Allah ya basu don sun ma fitar da ran sake haihuwa tun da saleem ya kai 7yr’s da haihuwa, suna matuk’ar kaunar ‘ya’yan su sosae ana cikin hira caraf nauwarah tayi magana cikin shagwaba take cewa

 

” _Abba gaskia ina son idan na kammala secondary schl malaysia nake son ka sama min university_”

 

Dariya abban yayi irin ta manya sannan yace

” _nauwarah ‘yar gidan Abba kada Ki damu Insha Allah xan cika miki wannan burin ke dai Allah yasa muna raye ki kwantar da hankali ki_”

 

Cikin tsananin murna tace

” _Ameeen my abba na_”

 

Har ta bud’e baki xata sake magana safah ta watsa mata harara kamar idon ta ya fad’o tace

 

” _tabbb Lallai yarinyar ae yanda nayi karatu a 9ja ke ma hka xakayi ba inda xaki je_”

 

Turo baki tayi cike da shagwaba tace ” _uhm kaji aunty safah da wani xance kuma bayan ynx agaban Ki abba ya amince min koh abb?_”

 

” _k’warai da gaske nauwarah ta haske mai kyau hasken idaniya ta da ixinin Allah xaki je ke dai ki dage da karatu kmr yanda na san ki_”

 

Wani tsalle ta buga tana ihun murna yayin da safah ta xumburi baki cike da haushi tace

 

” _dallah malama kin dame mu da ihu idan baki shiru ba ynx na tashi na bubbuge bakin ki_”

 

Murgud’a mata d’an k’aramin bakin ta tayi cike da tsiwa tace

 

” _kaji mu da aunty safah nan ina ruwan ki da ihu ba Naga dai murna nake_”

 

Axuciye safah ta tashi tayo kanta aikuwa da gudu ta b’uya a bayan ammin ta tana mata gwalo abba da saleem da ammi dariya kawai suke yi musu hannu tasa xata fisgo ta da sauri ammi ta tare tana cewa

 

” _a’a safah yi hak’uri ki kyale ta kinsan yarinya ce kuma naga ae murna take_”

 

” _amma dai ammi Kina kallo gwalo take yi min_”

 

Da sauri ammi ta juya bayan ta ae kuwa taga nauwarah gwalo take mata cikin fad’a ammi tace

 

” _bana son hka nauwarah baki ga yayar Ki bace ji nake d’axu kika gama bibbige min saleem don ya tab’a miki phone d’in ki_”

 

” _tohh ammi na dai na yi mata_”

Ta fad’a kamar xata fashe da kuka murmishin mugun ta safah ta saki tare da cewa

 

” _yarinya xaki xo ki same ni ne_”

Idon ammi ta faka ta Murgud’a mata baki yanda take Murgud’a bakin da ka gani kasan ta riga ta saba da hkan….

 

 

Ko _10 mints_ ba’a yi ba na hango nauwarah kusa da safah tana wani marairaice fuska tare da langab’e kai alamar tana son wani abu safah tana kallon ta ta gefen ido kamar xata tuntsire da dariya hka take ji dakyar ta iya danne dariyar bata kula ta ba ta Kalli inda saleem yake tace

 

” _saleem dauko min maltina a frige mai sauk’in sanyi_”

 

Ae Kafin ta rufe bakin ta da gudu nauwarah ta nufi frige ta d’auko mata maltina ta Mik’o mata hararar ta safah tayi tare da cewa

 

” _na ambaci sunan ki ne ae Naga saleem na aika_”

Murgud’a mata baki tayi cikin k’uluwa safah tace ” _au Murgud’a min baki kike_”

 

Da sauri nauwarah ta dafe bakin ta cikin marairaicewa tace

” _hba aunty safah na mance ne I’m so sorry baxan k’ara ba ki karb’a kisha Kinsan baxan ji dad’i ba Idan baki karb’a ba plsss_”

 

Gaba d’aya falon aka kyalkyale da dariya ita kuma sai wani lalangab’e kai take da yake safah tana masifar son kanwar ta bata son abin da xai b’ata mata rai yasa ta karb’a ae kuwa ta rungume ta tana dariya ba wanda bai yi dariya ba a wajen…..

 

Tana shan maltina nauwarah cikin K’aramar murya tace ” _Aunty safah yaushe xaki kaimu shopping ne gaskia kayan kwalliya na sun kusa k’are wa_”

Harara ta xabga mata kafin tace

 

” _baxa ajeba sai ki nemi driver ya kai ki_”

 

” _Kaiiii aunty baxa ki kai ni ba don Allah ki taimaka plsss_”

 

Abba ne yace ” _aunty safah ayi hak’uri akai ta mana_”

 

Hannu tasa ta dungure mata gaba d’aya aka tuntsire da dariya kafin tace ” _kinci darajar abba yarinya_”

 

Cike da d’oki da murna tace” _xaki kai ni my cwt sister?_”

 

” _xan kai Ki Insha Allah gobe ‘yar cwt k’anwata_”

 

Murmishi tayi har dimple d’in ta ya lotsa tayi kissing d’in ta a kumatu tare da fad’in

” _thank you so much my aunty safah_”

 

Saleem yace ” _har dani xa’a je koh aunty safah?_”

Harara nauwarah ta xabga mishi tare da cewa ” _baxa’a da kai ba yaro_”

 

B’ata rai yayi tare da cunkushe fuska kamar xai fashe da kuka da sauri ammi tace ” _kada ma kayi kuka dole aje da kai_”

 

Xumbura baki nauwarah tayi tare da tashi ta nufi bedroom…….

Karshen Wahala Complete Novel Document Txt

File Name   Katshen Wahala… Hausa Novel Doc.
Title   Karshe Wahala Complete
Author    Aisha A Muhd
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    17/07/2024
File Size    200KB
Format Size    TXT
Book Price    Free
Phone No    Nil
Download Karshen Wahala Complete Novel Document By Aisha A Muh’d 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button