MARUBUCI: Nasir S. Nasir Gwangwazokat! Ne a duniyar rubutu. Bana tantama ko shakkar alƙaminsa, gwani ne na yankan shakku. fikira da ƙwarewarsa sun tallafawa shirin wajen fuzgar zukatan masu kallo
UMARNI: Malam Aminu Saura, gwani ne da ya ƙware a harkar ba da umarni. Ya nuna gwaninta wajen sarrafa taurari tare da aje kowanne a gurbinsa.
KAMFANI: Saira Movies.
TAURARI:
Sarkin Waƙa
Lukman
Rukayya
Ummi
Baba Rabiu
Sa’a
Bello
Atete
Kabir
Talatuwa
Bintalo
Murja
JIGO:
Tsaro da soyayya.
FITA TA FARKO: Salo mai burgewa, kalamai ma su narkar da zuciya. Wa’azantarwa cikin hikima da gwaninta ba tare da jan aya ko hadisi ba. Tabbas an tsuma mana zuciya da kalamai masu tausasawa.
KARANTA:
✓ Hukuncin Abincin Kirsimeti Ga Musulmi Fita ta farko
✓ Gwamnatin Tarayya zata dauki karin Matasa 400,000 aikin N-Power
✓ Kano State School Of Nurses and Midwife Enterance Examination 2021/2022
✓ Rahama Sadau Da Shatu Garba Mata biyu da suka fi shan ce-ce-ku-ce a shafin sada zumunta
FITA TA HUƊU: Hmm! Ziyarar Lukman da Ummi a gidan su Sumayya, ta zo da kalamai na bazata. Shin gaskiya ce ko abun kunya? Domin dai Ummi ta saki baki da yawa.
FITA TA ƘARSHE: Ta zo da abin da muka dade cikin lissafinmu. Wato haduwar Baba Rabiu da Presido.
1. Kalaman Umma a tataunawar su da Atete da Rukayya sun yi tsauri, kamar ta so ta sauka daga hanya.
2. An ɗaukko hanyar warware dukkan matsalolin shirin ciki hikima.
3. An sauya mana Sumayya cikin hikima. Tabbas ƙwaƙwalwa ta yi aiki.
Ƙorafi: Ma su kallo har da ni, muna kuka da tallan da ke janye yawan lokutan kafin fara shirin da kuma a cikinsa. Musamman ma na e-naira ɗin nan da kuma na Kano. Ya kamata a duba gaskiya.
Akwai sauran kallo a labarin nan!
Mubarak Abubakar Saulawa
Kada na cika ku da surutu ku Danna bulun rubutun da aka saka Play Video ko kuma hoton dake ƙasa.