Gyaran jiki na mata musamman wanda suke yawan yin aikin gida
Wannan hanya ce da mata za su bi ko amare ko wadanda suka yi auren don gyaran jikinsu. Zai taimaka jikinki ya kasance koda yaushe a cikin laushi musamman hannu.
Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah
Kullum bayan kin gama aiki, ki hada man zaitun da gishiri kadan ki rinka shafawa sau daya ko sau biyu a rana.
Ki hada sugar da butter dai-dai misali ki rinka murzawa a hannunki yayi tsawon misalin mintuna goma.
Karanta>>> Maganin Toilet Infection Da Kuma Rashin Sha’awa Ga Mata
Ki hada gilasirin (glycerin) da turaren miski da lemun zaki ki rinka shafawa a hannunki ko wane dare.
Ki matsa ruwan lemun tsami da man zaitun ki rinka shafawa a hannunki, zai dawwama da taushi.
Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata
Ki samu tumatir kwaya bakwai ki matse ruwan ki hada da man zaitun cokali daya ki rinka shafawa kullum.
Da yawa daga cikin mata ba kowace mace bace tasan cewar idan ta gama wanke-wanke ta samu ruwan dumi ta wanke hannunta sannan ta shafe shi da mai. Duk matar da take hakan batada matsala ta fannin bushewar tafin hannunta.
Karanta>>> Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi
Cikin wadannan abubuwan da muka kawo, duk wanda kika dauka zai miki amfani da yardar Allah.