Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 36 Complete Novel

*typing📲*

🐅 *MATAR DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written and story*
*by*
*Asma’u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)

*WhatsApp me 09065443871*

*BOOK ONE*⬇️
*97 to 98*

 

*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 200👌👇👇👇*

*ASMA’U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*

*OR*

*ASMA’U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*

*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*

https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

 

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

𝐔𝐩! 𝐔𝐩!! 𝐔𝐩!!! 𝐇𝐮𝐫𝐫𝐲💃💃💃

𝐒𝐀𝐅𝐍𝐀 𝐆𝐑𝐀𝐏𝐇𝐈𝐂𝐒 𝐃𝐄𝐒𝐈𝐆𝐍.
ᴴᴼᴹᴱ ᴼᶠ ᴳᴿᴬᴾᴴᴵᶜ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ
ᵂᴱ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ ᴬᴸᴸ ᴷᴵᴺᴰ ᴼᶠ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ ˢᵁᶜᴴ ᴬˢ:
LOGO* POSTER* BANNER* 3D MOCK UP LOGO* FLYER* STICKER* PRODUCT STICKER* I.V CARD* I.V VIDEO* BIRTHDAY VIDEO FLYER* PHOTO FRAME* REMOVE BACKGROUND* PROFESSIONAL I.V CARD* SAVE THE DATE* EXPLAINER VIDEO* LYRICS VIDEO AND MORE…
*PLEASE CONTACT* 👉 08148318396 *SAFNA GRAPHICS*.

🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

Misalin ƙarfe 1 na dare wayar Junaid ne yake bada sautin ƙira, sau biyu ana ƙira yana katsewa ana uku ne sautin ƙiran ya bugi dodon kunnensa wanda tinin bacci ya yi gaba dashi, a hankali yake wutsil-wutsil da idonsa yakai hannunsa kan drower yana lalumen phone ɗinsa, cikin sa’a ya hannunsa ya sauƙa a kan wayar ya ɗaga ƙiran ba tareda ya duba sunan dake rubuce akan screen ɗin wayar ba,
cikin muryar jin bacci ya ce “Hello..” yana lumshe da ido..

“Hy my king kanata shan baccin ka ni kuma ka barni a airport sai faman ƙiran ka nake..”
tayi maganar ne da yaren french.

a hankali ya buɗe eyes ɗinsa ya duba screen ɗin wayar domin ya tabbatar da wa yake wayar, gani ya yi sunan daya saved ya bayyano wato “Girl” Rumana kenam sunan da yake ƙiranta da shi.
murmushi yayi sannan ya mayar da wayar saitin kunnensa cool voice yace “sorry my girl, yanzun kina airport ne?..”
amsa masa tayi! ba tareda ya ƙara cewa komai ba ya katse ƙiran sannan ya miƙe yana hamma domin ba ƙaramin bacci yake ji ba, idanuwansa duk sun ƙanƙance, kai tsaye toilet ya nufa yayi brush sannan ya watsa ruwa a jikinsa shaf-shaf saboda shi a rayuwarsa inba dole ba baya son fita ba tareda yayi wanka ba komin dare..
can bayan wasu mintina ya fito yana ɗaure da towel a kunkuminsa, ya tsane ruwan jikinsa sannan ya shafa mayukansa masu bala’in ƙamshi, ya nufi werdrobe ɗinsa ya zaro ƙananun ƙaya three-quater da rigarsa marar hannu sai da ya ƙara feshe jikinsa da turare kafin ya ɗauki key ɗin motarsa ya zura phone ɗinsa cikin aljihun wandon ya yi ficewarsa,
yana fita harabar gidan kuwa haske ta ko ina kamar ba dare ba, haka ya shige motarsa, horn ya dinga yi wa maigadi amma shuru baccinsa yayi nisa ganin maigadi bashida niyar tashi yasa Junaid fitowa ya buɗe get ɗin da kansa sannan ya yi ficewarsa da gudun gaske..
(wata ƙil baiyi addu’ar fita daga gida ba ma🤔🤔).

Bayan mintina talatin da ficewar Junaid sai ga Ayush itama ta sauƙo falo, kai tsaye kitchen ta nufa sakamakon yunwar da take ji, bata ci komai ba ta kwanta!
tana shiga kitchen ta haɗa tea ɗinta mai kaurin gaske wanda yasha madara ga ta zabga sugar a ciki, ta fito falo tana kaɗa shayin da spoon,
tana shirin haurawa upstairs ta jiyo shugowar mota , dakatawa tayi ta tsaya cak tana son ganin wanda zai shugo kai ta ɗaga sama tana kallon agogon bangon dake manne ƙarfe 2:00, tana sanye da sleeping dress doguwar riga marar kauri mai hannun best tsayin rigar ya tsaya mata a iya gwiwar ta,
gani tayi an turo ƙofar falo, tana kallon bakin ƙofa ganin Junaid ne ya shugo hannunsa yana riƙe dana wata zankaɗeɗiyar mata fara tas baturiya, gashin kanta dogo mai launin fari, ƙwayar idonta kuwa blue ne irin na turawa, gata doguwa ce duk da ta sanya takalmi mai tsini a ƙafa,

gaban Ayush ne ya faɗi rass, zuciyarta kuwa ya soma bugun 3+3, tsananin tsoron matar ne ya kamata gaba ɗaya tasha ruwan jikinta, a ranta kuwa cewa take “subhanallahi ina tunanin wannan ce Rumana, domin itace naji ta ce isowar cikin dare zatayi kuma bayan haka itace mai yaren french baturiya, tab amma wannan banga wani kyau ba sai farin fata kamar wata zabiyan ga sumar kanta fari A’uzubillah wannan kam….”
ba tareda ta ƙarasa maganar zucin ba taga ana murza zara-zaran yatsu suna bada sautin ƙara a saitin ƙwayar idonta, firgitt tayi tana kallon Rumana wacce ta tsaya a gabanta ta kama kunkumi ta kuma kafa mata blue ɗin eyes ɗinta tace “what are you looking for?..”
shuru tayi Ayush bata ce mata komai ba,
ta ƙara tambayarta “who are you?..”
nan ma Ayush shuru tayi bata ce komai ba,
ran Rumana ne ya yi matuƙar ɓaci ta daka mata wani irin gigitaccen tsawa har saida Ayush ta firgita sosai, batada wata mafita kawai ta fashe da kuka…

Junaid yana tsaye a gefe ganin Rumana zata takura mata yace “please Girl leave her alone..”

Rumana ce ta juyo tana kallonsa da blue eyes ɗinta tace “ok tell me who is her?..”

Junaid shima ɗaure fuska yayi yana kallonta sannan yace “she is my sister..”
Rumana ganin yanda Junaid ya ɗaure fuska ba annuri yasa ta shiga taitayinta, sunkuyar da kai tayi tace “okay..”
suna cikin wannan halin saiga Mommy ta fito tana murtsuka ido alamar daga bacci ta tashi jin hayaniya ne yasa ta fito tana faɗin “wai meyake faruwa ne a wannan daren…”
bata ƙarisa maganar ba suka yi ido huɗu da Rumana, sake baki tayi tana kallonta da farko har ta tsorita sai daga baya kuma ta ɗanyi murmushi tana kallon Junaid tace “ko dai ɗaya daga cikin ƴanmatan ka ne tazo? amma wannan itace Rumana ko? domin naji kace baturiya ce.”
duk wannan maganganun da mommy tayi Rumana ba abunda taji aciki sai dai taji an ambaci sunanta wato Rumana,
kwata-kwata bata fahimtar hausa,
Mommy ƙareta take da kallo gata kuwa tana sanye da kayan sojoji a jikinta irin na ƙasar Australia…

Junaid ne ya yi gyaran murya sannan yace “Mom ga nan Rumana ta samu ƙarasowa sai a duba mata ɗakinda zata zauna..”

Mommy tace “ai duk ɗakunan a gyare suke, har na wanda sauran idan sun zo zasu zauna, yanzu dai ita wannan ga can ɗakinta ta nuna ɗakin da yake ƙasan benin da zai kai ka ɗakin Junaid,
ta ƙarasa maganar tareda jan akwatin ta zata nufi ɗakin dashi,
Rumana tana zaune akan sopa ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tace “babu ɗaki ne a sama?..”
Mommy dai kallon Junaid tayi domin bata san mai ta ce ba domin da yaren french tayi maganar,
Junaid ne ya bata amsa da cewa “babu..”
hannu yayi wa mommy akan takai mata jakar ɗakin da aka tanadar mata,
wuce wa mommy tayi tana jinjina kai, domin akwai magana a bakin mommy tarin-tarin..

Ayush tana tsaye da kofin tea a hannunta ta kasa motsawa sai kallon Junaid take cike da takaici ji take kamar ta rufe shi da duka,
gani tayi Rumana ta katse ta da cewa “am really hungry..” ta ware mata miƙaƙƙun hannunta alamar tana buƙatar kofin shayin..

Ayush miƙa mata kofin tayi kanta a sunkuye domin ba ƙaunar haɗa ido take da ita ba,
tana miƙa mata ta wuce zata haura saman stairs,
Rumana ta dakatar da ita tareda faɗin “come here..” tayi mata alama tazo da hannunta, a tunaninta Ayush bata jin yaren natan,
tana zuwa Rumana ta miƙa mata cup ɗinta tace “bazan iya shan wannan abun ba, ya yi kauri da yawa sannan sugar yayi yawa, go and find me coffee…”

Junaid ne ya buɗi baki zai maimaita wa Ayush abunda Rumana ta faɗa da hausa,
cikin zafin rai Ayush ta ɗaga masa hannu da sauri tace “ba sai ka fassara mun ba…”
tana kaiwa haka ta nufi kitchen,
abunda Rumana ta kasa ganewa kenam amma tasan akwai wani abu a tsakaninsu, just tayi shuru ne kawai amma tasan ba ƙanwarsa bace domin a saninta da shi bashida bros or sis…

Junaid bin bayan Ayush yayi da kallo cike da mamaki “taya Ayush tasan abunda Rumana ta faɗa?…”
yana cikin wannan tunanin sai ga mommy ta fito tana faɗin “Junaid ka kaita ɗakin ni zan wuce bedroom ɗina saboda ina jin bacci sosai, ya kamata kuma ku samu ku kwanta kafin sallar asuba, kunga gobe kunada hidima ba baccin rana…”
Mommy tana kaiwa haka ta wuce ɗakinta,
shima Junaid magana yayi wa Rumana suka nufin ɗakinta, yana kaita ya juya zai fito ta tsayar dashi tace “ina zaka je Beb?..”
yace “Girl i what to sleep..”
tace “ok before seat here and wait for me..” ta kama kafaɗarsa ta zaunar dashi a bakin gado..

a gabansa ta gama cire kakin sojan natan ta sanya sleeping dress sannan tazo yanda yake zaune ta hau saman cinyarsa ta zauna tana fuskantarsa tace “Beb you known i really miss you..” tareda da manna masa kiss a saman goshinsa tana shafar lallausar suman kansa,

Shi dai Junaid sai faman kakkauce wa yake saboda sun sani baya taɓa biye musu, kuma tinda yake da su bai taɓa yadda ya haɗa baki dasu ba, sai dai su gama iskancinsu na shashshafa shi amma bayan hug baya barin a kauce hanya saboda wasu dalilansa na farko su ba musulmai bane sannan shi ba irin mazan nan masu ƙwaɗayin mata ba ne,
mace ta farko daya taɓa sumbatar ta a rayuwarsa itace Ayush, kuma itace kawai yake biye mata suyi romance,

Rumana tana cikin kissing ɗinsa a wuya tana wasa da sumar kansa saiga Ayush ta turo ƙofa ta shugo hannunta riƙe da cup na coffee,
ganin halin da suke ciki ne yasa ta tsaya cak tana kallonsu nan da nan hannunta ya fara rawa, idonta har ya cicciko da ƙwalla tana kallon Junaid wanda shima ita yake kallo, gaba ɗaya ya rasa yanda zaiyi domin shima kansa baiji daɗin hakan ba, bai so ace Ayush ta zo ta sameshi a haka ba,
ita kuma Rumana ganin Ayush a tsaye ta kasa motsawa tace “you will not keep it?…”

Ayush jikinta a sanyaye ta ajiye cup ɗin tana jan ƙafa daƙer zata fice a ɗakin idonta kuwa na kan Junaid, shi ɗinma kallonta yake sun kasa ɗage idanuwansu daga na juna,
Ayush kuka ne yake shirin kuɓuce mata tayi saurin barin ɗakin,
hankalin Junaid ba ƙaramin tashi yayi ba,
ɗaga Rumana yayi daga kansa ya kwantar da ita yana faɗin “ki kwanta ki huta..” kafin tayi magana kuwa har ya bar ɗakin..

Ayush tangal-tangal take zata faɗi tsabar hajijiyan da yake ɗibarta da haka take haura upstairs a hankali gudun kar ta faɗo ƙasi, wani irin hajijiya ne ya fizgeta tayi baya zata faɗo daga saman beni,
ji tayi ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, ƙamshin turarensa ne yake bugan hancinta anan ta ƙara tabbatar da Junaid ne,
lumshe idonta tayi wani irin ciwon kai ne yake damunta, gaba ɗaya ta kasa motsawa duk jikinta ya mutu babu sauran ƙarfi a tattare da ita..

hannu yasa ya ɗago ƙafafuwanta yayi mata ɗaukar luɗa sannan ya ƙarisa haurawa da ita, kai tsaye ɗakinta ya wuce da ita, ya kwantar da ita saman katafaren gadonta,
har zai juya ya tafi saiya kai hannunsa yana taɓa saitin wuyanta yaji jikinta ya hau temporary sosai, har tiririne yake fita daga jikinta tsabar zafin zazzaɓi, a zabure ya tashi yana kallonta har ta fara rawar sanyi da sauri ya fice daga ɗakin yana sauƙa daga downstairs kamar zai dungura kai tsaye ɗakin medicine ya nufa yaje ya ɗauko boxes na pharmacy da gudu ya koma ɗakin Ayush tareda bottle na ruwa,
haurawa saman gado yayi ya ɗagota yana ƙiran sunanta, Yushert! Yushert!! please open your eyes,
a hankali take lumshe ido tana buɗe wa,
maganinnuwa ya ɗuɗɗura mata kafin kace mai ta yunƙura ta amar da duk maganin data sha, tana haki sama-sama ganin maganin da ta sha bai zauna mata ba ya ɗauki allura ya zuƙo ruwan maganin paracetamol ya saita dantsen ta sannan ya caka mata allurar hannunsa na rawa, ita kuwa nan danan gumi har ya yarfo mata tana jan numfashi da ƙarfi,
da sauri ya tashi ya shige cikin toilet ya jiƙo ɗan ƙaramin towel da ruwa yazo ya ɗora mata akan goshi, bayan wasu mintuna bacci yayi awun gaba da ita,
ajiyar zuciya yayi yana sauƙar da numfashi a hankali sai yanzu hankalinsa ya dawo jikinsa da tinin har ya tsorita ganin halin da Ayush ta shiga cikin ƙanƙanin lokaci,

tashi yayi ya zamar da bedsheet ɗin da ta ɓata da amai yakai toilet sannan ya shimfiɗa wani bayan ya ɗagota saman kafaɗarsa, a hankali ya maida ita ya kwantar shima kwanciyar yayi a kusa da ita ya mannata a jikinsa tareda jawo musu mayafi suka rufu domin bazai iya barinta ita kaɗai a wannan halin ba, shima daga baya baccin ya ɗauke shi,
sai kace wasu ma’aurata🤔🤔…

ƙiran Asubar farko akan dodon kunnen Junaid, a hankali yake buɗe eyes ɗinsa, ganin ɗakin yayi haske sosai yasa ya buɗe idonsa gaba ɗaya yana mamakin taya akayi aka kunna hasken ɗakin alhalin a kashe yake, hannu ya kai zai taɓo Ayush yaji gurin wayam da sauri yakai idonsa gurinda take kwance ata gefensa yaga babu kowa, miƙewa yayi ya zauna tareda kallon yanda Ayush take a zaune saman sallaya tana jan carbi alamu sun nuna tayi sallar dare ne, domin yanzu ake ƙiran sallar asuba ma…

a hankali yake motsa bakinsa yace “Yushert..” bata kula shi ba sai ɗagowa tayi ta kalle shi sannan ta kawar da kanta tana kallon gabanta bakinta na motsi alamar tana tasbihi..

tashi yayi ya sauƙa daga kan gadon zai fita a ɗakin har yazo daf da bakin ƙofa yaji tace “meya kawo ka ɗakina?..”

murmushi yayi sannan yace “nazo duba lafiyarki ne, ya jikin nakin?..”
daga nan bata ƙara cewa komai ba ko amsa bata bashi ba ta cigaba da jan carbinta..

ganin ta sharar dashi ne yasa ya girgiza kai sannan ya fice, kai tsaye ɗakinsa ya nufa yana shiga kuwa ya shige toilet ya yo alwala ya fito da sauri ya sauƙa down yayi ficewarsa ya tafi masallaci…

misalin ƙarfe 9 na safe mommy tana zaune a falo tana jiran shugowar Junaid tin fitar Asuba, tana so a fara shirye-shirye tin yanzu kafin a fara yin baƙi duk da tasan sai wajen la’asar a buɗe taron, kuma a cikin gidan za’ayi taron a babban hall wanda sai an buɗe wani ƙatoton get a cikin gidan kafin a shiga fili ne guda duk an mamaye gurin da floor, wajen daman an tanadar da shi ne saboda taro na musamman, an ƙayatar da wajen sosai ga kujeru a jere na musamman, ga wasu ƙayatattun kujeru kuma du a saman yanda manya-manyan baƙi zasu zauna da kuma shi kansa Junaid, ga wasu haske masu ƙayatarwa sai walwali suke suna bada haske kala-kala, duk an mammanna photunan Junaid a jikin bangon an tsara shi shima..

(wannan taron da za’ayi nima ina gayyatar members na group ɗin matar damusa dasu halacci gurin taro amma sai kunada card na gayyata domin tin jiya aka raba wa manya-manyan baƙi idan baku samu ba toh ba shiga gurin taron sai dai a baku labari ko kuma ku kalli video, ni kuma Asmeetah ga kujerar Oga Junaid ga nawa🤪🤪 kuma in baku labari raƙumi da saniyoyi uku za’a yanka..)

Mommy tana zaune a saman sofa saiga Rumana ta fito daga cikin ɗakinta tana sanye da gajeran wando zuwa gwiwarta mai kakin soja da kuma ƙaramin best sai dai ta saka breziya ata ciki kafin ta ɗora best akai, zuwa tayi ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun falo tana faɗin “gud morning mom..”

Mummy da murmushi a fuskarta ta amsa mata dake yanzu da turanci tayi gaisuwar bada french ba..

Mommy tace “ga can kayan breakfast asaman dinning…” tayi mata maganar ne da turanci,
yamutsa fuska tayi sannan tace “where is Junaid?..”

“I don’t known..” mommy ta bada amsa a takaice,
Rumana ta kuma cewa “ok bari yazo muyi breakfast a tare…”
daga nan basu ƙara cewa komai ba.

saiga Ayush ta fito sanye da zureren hijab har ƙasi ta fitar da hannunta waje dake hijabi mai hannu ne..
saida tazo gaban mommy ta durƙusa tana gaisheta,
mommy amsawa tayi da murmushi a fuskarta tace “antashi lafiya my dota?..”
Ayush ta amsa mata tareda miƙewa tsaye har fuskarta yayi fiyau farinta ya ƙara fitowa,
zuwa tayi gaban Rumana ta durƙusa mata sannan itama ta gaisheta,

tana turɓune fuska tareda yamutsa shi daƙer ta buɗe baki ta amsa mata,
dake tana zargin akwai wata alaƙa dake tsakaninta da Junaid tin a daren jiya, Rumana sarkin kishi kenam…

Ayush miƙewa tayi mommy tace “Dota ga can kayan breakfast kije ki karya kinji, nasan kina jin yunwa…”
Ayush ta ɗaga mata kai tareda cewa “toh Momy..”

taje ta zauna a dinning tana zuba fried chicken domin shi take sha’awar ci ta haɗa wannan la’anannen shayinta nan mai masifar kaurin gaske domin tana zuba madara kam bana wasa ba sannan ta zabga sugar,
haka take ci tana ɗibar tea da spoon tana haɗawa da shi,
ba ƙaramin yunwa ta tashi dashi ba,
tana cikin karyawa sai ta jiyo sallamar Junaid ya shugo yana jan trolly ta bayansa kuwa wata zankaɗeɗiyar mace ce domin wannan ta wuce ace mata yarinya,
Ayush dakatar da karyawa tayi tana kallon ikon Allah,

miƙewa mommy tayi tsaye tana faɗin “ina kaje Junaid tinda asuba?..”
bata ƙarasa maganar ba taga mata ta shugo tana bin falon da kallo tareda faɗin “wow nice this parlour is so fantastic..” tana magana da yaren china gashi kuwa tayi zubi da chinoni hatta ƙananon idanuwan da ƙaramin baki,

Junaid ne yace “Adity look at my mom..” ya ƙarasa maganar yana nuna mommy shima da yaren china yayi maganar, sannan ya kalli mom itama yace “mommy ganan Aditi fah ta ƙaraso..”

Mommy yaƙe kawai take tace “eah ai na gani, ganan zubinta kuwa irin na chinoni, wato zaka haifo mun jikoki masu kamanni daban daban kenam, a cikin akwai chinoni da kuma turawa..”

Dariya Junaid yayi sannan yace “ita kuma Angel fa?…”
mommy tace “ai wallahi gwara Angel duk ta fisu kyau, ita wannan ai kamannunta irin namu ne..”

Aditi ce ta katse mommy da cewa “mom you are so beatiful, glad to see you..” ta ƙarasa maganar tareda rungumar mommy,
mommy dai kawai ta biye mata ne tana dariyar yaƙe amma daga Aditi har Rumana ba wacce ta ƙwanta mata a rai..

Rumana tana zaune ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana zabgawa Aditi harara kamar idonta zai faɗo ƙasi saboda tasan itama budurwar Junaid ce,
Adity ganin yanda Rumana take hararar ta yasa ta fusata tayo kanta zata naushe ta Junaid yayi saurin riƙota yana faɗin “don’t allow if not you’ll see what am going to do..”

Adity juyowa tayi tana kallon Junaid da fici-ficin idanuwanta, duk zafin ranta tana shakkar Junaid, ba china ba ko itace sarkin faɗan chinoni ce bazata iya gabzawa da Junaid ba…
turo baki tayi tace “nuna mun ɗakina..” tayi maganar da yaren china cikin sauri-saurin magana,
yana riƙe da hannunta yaja ta suka nufi ɗakin dake kusa dana mommy ɗayan hannun kuma yana riƙe da jakarta suka shige ɗakin…

dogon tsuka Rumana taja sannan ta miƙe ta nufi ɗakinta,
Mommy dai tsayawa tayi tana kallon drama baki a sake,
bata ankara ba tajiyo Ayush tana kwashewa da dariya har da tafa hannayenta, ita abun ma dariya ya bata madadin taji haushi, saboda ba iya mutum ɗaya ya kawo ba sannan ta uku tana tafe bazata ji haushi sosai ba..

kallonta Mommy tayi tace “ke idan wannan ƴar china ta fito zaki ƙwala, kinga irin mazgar da sukeyi a film ko to irinsa zatayi miki..”
zaro ido waje Ayush tayi tace “toh kuwa zanyi mata biyayya yanda ya kamata..” tana kaiwa haka ta cigaba da tura abinci a baki tareda shan kakkaurar tea ɗinta..

(tab da Junaid ya bari fa Adity dukan tsiya zata yi wa Rumana domin ta fita ƙarfi nesa ba kusa ba, duk da gaba ɗayansu sojoji ne)..

bayan Junaid yaja Adity ɗaki zaunar da ita yayi yana mata warning akan baya son yawan faɗa, yana cewa “idan kina son ganin farin cikina to karki nemi kowa da faɗa kinji ko?..”
yana magana ta yaren china.
miƙewa tayi akan gado tayi shame-shame ba tareda tace masa komai ba, ta lumshe ƙananun idanuwanta kamar mai yin bacci..

shima miƙewa yayi saman kanta ya kawo ƙaramin bakinsa saitin kunnenta yace “please my war make everything for easy..”
yayi mata haka ne saboda ya rarrashe ta domin yasan halin Aditi indai baiyi mata magiya ba kafin ta koma saita tayar da ƙaramin yaƙi a cikin gidan nan,

hautsinar dashi tayi gefe tana cewa “impossible duk wanda ya taɓani nima dole na taɓa lafiyar jikinsa, leave me alone i wanna to rest…”
ta ƙara miƙewa a saman gadon ta kuma cewa “ƙarfe nawa za’ayi walimar?…”

miƙewa yayi ya nufi hanyar fita tareda cewa “4 O’clock na yamma, ƴar masifa kawai, kafin ki tafi saina miki dukan tsiya wallahi idan baki maida hankalinki ba…”
daiden zai fita ta wurga masa pillow tana huci tareda faɗin “don’t hot my heart…”
juyowa yayi ya kalleta sannan ya girgiza kai ya yi ficewarsa domin yasan idan ya biye mata zata sha duka ne yanzun nan, daman koda yaushe Junaid da Adity acikin faɗa suke, duk da yana mata dukan tsiya amma hakan bayasa ta daina abunda take yi, wani sa’in ita take nema suyi faɗa tana kawo masa naushi shi kuwa ya tattaka ta a wajen, dake lokacin da yake zuwa aiki ana yawan tura shi ƙasar china anan zasu haɗu suyita faɗa, tana jawowa yayi mata duka, akwai wani sa’in daya taɓa gurɗata a hannu irin nan ta kawo masa naushi shikuwa ya riƙe hannun ya murɗe anan ta gurɗe,
su waɗannan kalar soyayyarsu kenam shine faɗa….

bayan Junaid ya fita falo ya tarar da Ayush ta kammala karyawarta, zuwa yayi daf da ita ya tsaya a gabanta yana faɗin “kin koyi girman kai ko? mai kike taƙama dashi ne? kodan kinga ina biye miki ne shine zakina wani isarki kina rashin mutunci yanda kike so! to ki sauƙe wannan girman kan nakin tin kafin na hukunta ki…”
ya ƙarasa maganar yana kallonta, ita kuma kanta a ƙasi tana wasa da yatsunta,
hannu yakai ya jawota jikinsa yana faɗin “ba magana nake miki ba?..”

ɗagowa tayi da sauri tana kallonsa kamar zatayi kuka tace “to meka ce?..”
“cewa nayi ya jikin nakin?..”

tana baza manya-manyan idanuwanta tana kallonsa a hankali take motsi da ɗan ƙaramin bakinta tace “da sauƙi..” murya a sanyaye, hakan ba ƙaramin jefa shi yayi a cikin wani irin yanayi ba, jikinsa ne yayi wani yarrr tinin yaji wani abu ya ɗigo masa a cikin wandonsa,
bai ƙara cewa komai ba sai matso da fuskarsa da yake yi saitin fuskar Ayush, numfashin su har ya soma gaurayuwa yana shirin haɗe musu baki guri ɗaya,
ji sukayi an harba bindiga bullet ya fita ta window!

tsabar firgici da tsoro a razane Ayush ta ƙwarara ƙara mai razanarwa ta toshe kunnuwanta kanta asaman ƙirjin Junaid nan danan jikinta ya soma kakkarwa,
Junaid rungumarta yayi sosai saboda yasan ba ƙaramin tsoro taji ba, shi kuwa ko a jikinsa bai tsorita ba saboda yasan ɗaya ne daga cikin ƴanmatansa Rumana ko Adity, a hankali ya juyo bayansa domin yaga ko wacece a cikinsu yana bubbugar bayan Ayush alamar rarrashi…

ganin yanda mommy ta fito da gudun gaske ko ɗan ƙwali babu akanta tana salati a ruɗe saboda taji ƙarar bindiga ga kuma ihun Ayush a tunanita an harbeta ne,
sai kuma ga Rumana itama ta fito da sauri tana son ganin meke faruwa..

duk tsayawa sukayi sun yi cirko-cirko danin mutum tsaye yana sanye da baƙaƙen kaya ajikinsa,
wando baƙi da kuma rigar sanyi baƙi masu jikin leda sai sheƙin baƙi kayan suke, da baƙin hula a kansa na sanyi, ga kuma ya rufe fuskar da facemark sannan ya ɗora baƙin glass a ido,
yana sanye da safar hannu baƙi, takalmin ƙafarsa baƙi irin takalmin nan mai safa amma yanada tudu, yana goye da ƙatuwar baƙar jaka a baya, hannu kuma riƙe da ƙaramin bindiga..

Adity ce itama ta fito tana masifar waye ya tasheta a bacci,
tsayawa tayi itama tana kallon mutumin buɗe baki tayi tace “ɓarawo a gidan nan?…”
tayi maganar ne da turanci yanda kowa zai jita,

Rumana ce ta ari bakinta da cewa “ɓarawo kuma da rana?..” itama ta mayar da amsa ta turanci..

Mommy kam ba bakin magana ta tsaya tana kallonsa jikinta har ya fara rawar sanyi, zuciyarta kuwa haka yake bugun 3+3…

har yanzu Ayush kanta yana kife a saman ƙirjin Junaid ta kasa ɗagowa..

Junaid bayan ya ƙareta da kallo shi dai yasan wannan ba namiji bane tayi zubi da mace,
murmushi yasau mai ƙayatarwa sannan yace “you are crazy my Angel….”

jin ya canki sunanta yasa ta motsa, tasa hannu ta cire hular kanta saiga baƙin sumar gashin ta ya wantsilo har gadon bayanta, sannan ta cire glass ɗin idonta saiga dara-dara idanuwanta sun bayyano sun sha kwalli kuwa, ta cire facemark ɗin fuskarta saiga ƙaramin pink lips ɗinta sun fito da ƙayataccen murmushi a fuskarta, tana dariya har fararen haƙoranta suka fito, a hankali take motsa lips ɗinta tace “my Man soyayya ne haka kodai itace kishiyar tawan?..”

shima murmushin ne a saman fuskarsa baice mata komai ba sai ware mata hannu da ya yi alamar taje ta..

da gudu taje gurin shi ya rungumota da ɗayan ɓangaren hannunsa yana bubbuga bayanta a hankali a saitin kunnenta yace “kin tsoritar mun da mata shin kin kyauta mun?…”

dariya tayi tana bugan ƙirjinsa..
ta ɗayan ɓangaren hannunsa kuma Ayush ce itama yake rungume da ita har yanzu bata ɗago da kanta ba,
haka ya haɗa su ya rungumesu a tare…..

mommy ajiyar zuciya tayi ganin ashe Angel ce har hankalinta ya kwanta…

Rumana kam ɗaukar ɗan ƙaramin glass cup tayi ta doka a ƙasi ya dagargaje tana huci ta koma ɗakinta..

Adity kuma idanuwanta fici-fici haka ta dinga fin-fincina su tana son ganin shin meke faruwa ne….

Junaid kuma haka ya haɗe kayuwan Angel da Ayush guri ɗaya asaman faffaɗar ƙirjinsa, shima ya kifar da kansa a tsakiyar kayuwansu …..

 

Domin sauke CikakkenLittafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇

Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document 

 

*KUYI HANZARIN TURO KUDIN KU DOMIN CIGABA DA BOOK TWO*

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*ASMEETAH NOVEL*

Back to top button