LABARINA (Zango na biyar, kashi na Biyar)
Sabon shiri, sabon salo, sabuwar fikira.
Shirin ya yi gamon katar tare da afkawa hannun gwanaye ta fuskar rubutu. Wato irin abin nan da ake ce wa komai na babba, daban ne.
Marubuta 1: Nasir S. Gwangwazo, Yakubu M. Kumo.
Marubuta 2: Siddika Habib, da Sidiya Sidiya.
Labari: Aminu Saira
Ɗaukar nauyi- Sarkin waka
Ba da umarni– Aminu Saira
Kamfani- Saira Movies.
Manyan Taurari:
Sumayya
Lukman
Presido
Ummi
Sarkin waƙa
Baba Dan’audu
Baba Rabiu.
Wani Maigidan Haya Ya Kori ‘Yan Hayansa Saboda Yadda Suke Adddabansu Da Kukan Dadi Idan Suna Jima’i
1. Wacce irin soyayya ce tsakanin Lukman da Ummi?
2. Tawagar juyin juya hali ta kankama a gidan Yari ƙarƙashin Baba Ɗan’audu domin kafa sabuwar gwamnati.
3. Alhaji Dan gaske uba ne yake da dattako, da kowa zai zama kamar shi.
4. Fita ta 2, Ummi ta cire tsoro ta yi abin da ya dace. Kuma dukkan kalamanta suna doro na gaskiya.
5. An kama hanyar kammmala shirin nan, kuma shi ne abu mafi dacewa a wannan gabar domin dai an ci zango. Masu kallo sun fara saduda.
KURA-KURAI:
1. Fita ta hudu (ziyarar Gwamna Gidan Yari) bakiɗaya ban tsinci komai a cikin kalaman Gwamnan ba da kuma dalilin kawo shi.
2. Zuciya da riƙo irin na Maimuna game da Rabiu sun yi tsauri da yawa, duk da cewa ya yi mata laifi. Ya kamata a samu zuciyar musulunci, ” Matar na tuba…“
3. Lukman fa ya gama samun matsala, anya shi ma ba shi da tabin kwakwalwa?
Labarina wata katafariyar makaranta mai ɗauke da manyan darussan rayuwa ababen koyi. Gefe guda kuma akwai raha da barkwanci da kalamai masu sanyawa a dara ko ba a shirya ba. Labarina na cikin manyan shirye-shirye masu dogon zango da ake yayi kuma yake ɗaukar hankalin masu kallo.
Mubarak Abubakar Saulawa
30-9-2022.