Hausa novels

Zakuna Biyar Page 44 By Princess Teema

CRYSTAL PALACE.Ai gagara yin shiru Rimsha ta yi, tana wani irin shessheƙa tamkar zata shiɗe, gwanin ban tausayi. Jawota jikinta Aunty Luna ta yi, ta hau rarrashinta. Baki ɗauke da sallama Ammie ta shigo ta samesu, dama a jikinta ta ji Rimsha na kuka shiyasa ta zo rarrashinta. Karisowa ciki ta yi, suka haɗu da Aunty Luna suka rarasheta sosai, sai da ta yi shiru, sannan Aunty Luna ta ce Ammie su je waje su yi magana. Kwance suka baro Rimsha suka fito, a parlo suka zauna Aunty Luna ta tambayi Ammie me ya sa Rimsha take kuka haka? Dan ita wlh Rimsha ta kwanta mata a rai matuƙa, tana jinta tamkar sister ɗinta na jini watau sister Lisa. Ba ɓoye-ɓoye Ammie ta sanar da Aunty Luna gaskiyar abin dake faruwa. Cike da mamaki Aunty ta ce. “Kan wannan abin ne take irin wannan kuka? Waye shi Aryan ɗin? Ba namiji bane?”. Ammie da tasan waye Aryan ne ta amsa da. “Yayan Harleen ne wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya”…… Shiru Aunty Luna ta ɗan yi, sai kuma ta ce. “Shikenan ina zuwa”. Ta miƙe ta fita, ɗakin Rimsha ta koma, nan ta iskota tana waya da Seraphina, ta ce dan ALLAH Seraphina ta zo gidansu yanzu tana son ganinta.Aikuwa Seraphina kafa sarkin son yawo, sai cewa ta yi gata nan zuwa, amma bata san gidan nasu ba ai. Rimsha ta ce. “Benen dake ɗauke da number 2 shi ne benenmu”……. A lokacin Aryan ya fita, Seraphina ɗin ta yi wanka tana shafa mai.Aikuwa kafa sarkin yawo, a gurguje ta karisa shirinta ta fito, ta danya wani crazy jeans fari tas, daga sama top baki, sai ta ɗaura winter jacket a saman kayan wanda ya zo mata har gwiwa saboda sanyin da ake zubabawa, kafafunta sanye cikin socks, ta sanya ankel boot a kafafunta.Kai ba ɗankwali, ta nufi wajen Madam tana faɗin. “Mom ɗaure mun gashina zan je gidansu Rimsha”. Cike da mamaki Madam ta ce. “Kin faɗawa daddy ne?”. Ɗan zazzare violet eyes ɗinta ta yi, sai kuma ta ce. “Zan kirasa a wata mom, yanzu dai ɗaure mun”. Ba musu Madam ta gyara mata gashin, ta cufke mata a tsakiya game da sake jilar a baya, waɗan nan guntaye na gaban goshin kuma ta ƙara gyara mata su, ta kwantar mata da su da kyau kafin ta feshe gashin da turarukan gashinta. Tana murmushi ta amsa da ta gode, fitowa ta yi ta kira number Aryan, a lokacin ya gama wannan rikici da Lion kan dawo da Rimsha gidan, yana kwance saman sofa, ya tada kai da cinyar guru suna ta yi mashi magana ya yi banza da su. Kiran na shigowa ya ciro wayar, ganin my Cherry yasa ya katse kiran ya kirata. Bugu ɗaya ta ɗauka, cike da zumuɗi ta ce. “Daddy zan je gidansu Rimsha tana kirana”. ……. Ai sai da ya ji wani irin rass, da sauri ya miƙe zaune. Sai kuma ya ɗan nisa tare da cewa. “To ki je, amma kada ki jima”. Ya faɗa mata hakan ne kawai dan kada ta sake zargan wani abu, yanzu idan ya hanata tana iya cewa sai ya bata dalili, dama ga shi ta ce taga yana kama da Faryan, kunga kuwa tsab zata gasgata zarginta.”Love you daddy, shiyasa nike sonka sosai”…….. Ƙasa ya yi da murya sosai, tamkar mai raɗa yana satar kallon Vir da ya tsare shi da ido kafin ya ce. “Love you more Cherry”…… Dik abin da ya faɗa guru na jinsa, amma kamar bai ji ba, shi kuwa Vir baya jinsa amma ya karanci bakinsa tsab, ya gano me ya ce.Dan haka yana katse kiran sai ya ce. “You love who?”…… Hararansa Aryan ya yi game da miƙewa zai bar wajen ba tare da ya yi magana ba. Damko hannunsa Vir ya yi, ya jawosa da karfi har sai da ya faɗo jikinsa, ya damki arabs hair ɗinsa da karfi kafin ya ce. “Kaima sarautar zaka gwada mana ne?”. Ai cikin zafa Aryan ya miƙe ya damko korean hair ɗin Vir, da karfi ya ja yana faɗin. “Dama kwana biyu da ka tafi na huta da sa ido, ka dawo kenan yanzu, zamu fara raba hali”….. Dik cikinsu ba wanda ya kai Vir sa ido kam, ko baya jin me ka faɗa in dai yana ganin bakinsa sai ya san me kace.Kafa ɗaya kan ɗaya guru ya ɗaura yana ganinsu, dan in da sabo sun saba wannan faɗa…… Damke gashin Aryan ɗin shi ma Vir ya sake yi yana faɗin. “Sai ka faɗa mun waye kake cewa I love you, na dai san ba Abba bane, kuma ba su Faryan bane”. Kwace kansa Aryan ya yi yana faɗin. “Ba zan faɗa ba”. Ya wuce ya nufi cikin ɗaki. Miƙewa suka yi a tare suka rufa mashi baya guru ka zolayarsu.Ita kuwa Seraphina wucewa ta yi ta fito. Elevator ta zo shiga kenan sai ga wani matashi dake benen nasu amma sama da gidansu shi ma ya zo shiga zai sauƙa ƙasa. Kura mata idanu ya yi, ita kuma ta tamke fuska tamau. Ta shiga ciki, ta tsaya a gefe shima ya tsaya a gefe, sai satar kallonta yake yi, a tare suka kai hannu zasu danna down, dan dik ƙasa zasu sauƙa.Ɗauke hannunta ta yi, ta barshi ya danna. Har elevator ɗin ta sauƙa kasa bata ɗago ta kalli guy ɗin ba, amma ta rike kamanninsa sosai. Fitowa ta yi bayan elevator ɗin ta buɗe, basu da nisa da benen su Rimsha, can ta nufa tana ɗan waigo guy ɗin, abinku da jinin IRON FIST, a cikin ranta tana jin wannan mutumin bashi da gaskiya, ta ce kwayar idanunsa sak na masu laifi ne, shiyasa da suka sauka take ta faman kallonsa.Tana ganinsa ya nufi wata haɗaɗɗiyar motarsa, ya ja ya nufi main gate na CRYSTAL PALACE ɗin. A cikin ranta ta ce. “Zan ce daddy ya saya mun mota nima”. A fili kuma ta kara tamke fuska ganin dik in da ta wuce sai masu wucewa sun kalleta, sun ga ƴar beauty, ita kuma ta tsani kallo kamar uncle ɗinta Lion.Bene na biyu ta nufa, kai tsaye elevator ɗinsu ta nufa, ta zo dab elevator ɗinsu kenan sai ga wani matashi ya fito daga cikin elevator ɗin. Kallo ɗaya ta yi mashi ta ɗauke kai, shi kuma tin da ya ɗaura ido a kanta har fito daga cikin elevator ɗin ita yake kallo. Wucewa ta yi ta shiga ciki tana ɗan rera wakar da ta saba saurare a wayarta tana kalle-kalle.Elevator ɗin na ƙoƙarin rufe kansa sai taga an sanya hannu daga waje an dakatar da shi. Zubawa masu shigowar ido ta yi, Abba ne da Harleen, sun je shopping na sama basu sani abubuwan da suke so gabaɗaya ba shi ne suka je na ƙasa. Hannun Harleen rike da uban niƙi-niƙin kaya a manyan ledoji. Hannu ta kai zata danna hawa na goma sai taga Abba ya rigata ya danna. Bin Abba da kallo ta yi, sak kamannin fuskan Aryan babu banbanci, har sai da ta ji gabanta ya faɗi, haka ma Harleen yana mugun kama da Aryan, abinku da jini, shi da Abba basa kama can sosai fa, amma jini yasa taga suna kama.Rage tsawonta ta yi, ta ɗan durkutsa kafin ta ce. “Good evening sir”. Ɗago da kallonsa a kanta Abba ya yi, lokaci guda ya ji yarinyar ta mashi, sai ya ji yana buƙatarta a cikin danginsa, kun san gidansa auren haɗi ake yi, kamar yadda ya ga su Aunty Luna a cikin elevator ya je ya nemi aurensu wa ƴaƴansa to ita ma Seraphina ta mashi, sai ya ji yana buƙatar haɗata da Faryan.Dan haka fuska ba yabo ba fallasa ya amsa mata game da ce mata. “What’s your name my daughter?”…… Seraphina baki abin magana tuni ta ce. “Seraphina”. Ta faɗa tana Abba. “Seraphina”. Abba ya maimaita sunan kafin ya ce. “Ina iyayenki suka? Ina ne benenku?”…… Abba ya ga ƴar zai je nemanwa Faryan aurenta….. “Mom ɗina tana gida, daddyna ya fita, amma asalin mammyna ta rasu, asalin daddyna kuma ban san shi ba”. Ta bawa Abba amsa a natse…….. “A wani bene kuke?”. Abba ya sake tambaya. Nan ma ta bashi amsa, sai da ta gama bashi information ɗinta sai kuma ta ce. “Mezaka yi da information ɗina Uncle?”…… “Ki kirani da Abba, zan kawowa iyayenki ziyara ne, zan zo mu ƙullah zumunci, ko baki son zumunci dani?”. Abba ya faɗa. Murmushi ta yi. “Ina son zumunci da kai mana Abba”. Ta bashi amsa……. “Yauwa ina da yaron da baida aure, baida mata ma”. Abba ya faɗa, shi fa Abba tallan yaransa maza ma yake yi, kaman Seraphina ta tambayesa wai yana da yaron da bai da aure, kai Abba duniya.Seraphina kuma da hankali ya yi mata yawa sai ta ce. “Ni ma ai Abba bani da aure”……. Ai da sauri Abba ya riko hannunta, ya samu daidai shi, irin Seraphina yake so dama. Baki Harleen ya saki yana kallon yadda Abba yake tallarsu a titi, wai ina da yaron da bai da mata, this word pain Harleens heart wlh.Aikuwa Harleen bai gama mamakin Abba sai ya ji yana cewa Seraphina. “Kuma kinga yaron nawa da bashi da auren kyakkyawan matashi, ya gama degree ɗinsa na farki da na biyu, nasan ma zai burgeki”……. Takaici tamkar Harleen ya saka ihu, watau haka Abba ya yi je ya yi sallarsa wajen su Aunty Luna kenan? To ga shi yana tallar Faryan ma, yanzu fisabilillahi ya za’ayi Aunty Luna tai mashi kallon daraja tin da tallarsa aka yi mata?……….🤌🏻😂Seraphina ta amsawa Abba da cewa. “Abba kaima ai ka burgeni”….. “Yarona zai burgeki fiye dani, zaki auresa ko?”……… Kai ta ɗan girgiza game da cewa. “A’a Abba, ba zan aure shi ba, daddyna kawai zan aura”….. Daidai lokacin suka isa in da zasu sauƙa, kofar elevator ɗin ta buɗe masu. Da yake Abba ya kalleta yarinya kuma ya ɗauka daddynta mahaifi take nufi, sai bai wani damu ba, ya ce. “Zan zo gidanku In Sha ALLAH”. Da okey ta amsa mashi game da tsayawa a gefe ta hau kiran number Rimsha zata faɗa mata ta iso hawa na goma ɗin. Abba da Harleen suka nufi haɗaɗɗen kofar parlonsu, dama daga wajen elevator ɗin wani hadaɗɗen baranda ne kafin ka isa wajen kofar Khaiza’ans House. Har Abba zai buɗe kofar Main parlo sai kuma ya juyo da kallonsa a kan Seraphina. Cike fa kulawa ya ce. “A nan kema zaki sauƙa ne?”. Kai ta jinjina alamar e, sanin cewa gidansa ne kawai a hawa na gomar yasa ya sake cewa. “Wajen waye kika zo?”.Tana ƙoƙarin kara waya a kunne ta amsa da. “Wajen kawata Rimsha”…… Cikin parlo Harleen ya shige da kayan hannunsa, dan tsab Abba zai iya sanyawa zuciyansa ya buga na tallarsu da yake yi wajen ƴan mata.”Nan ne gidansu Rimsha ai, zo ki shiga”. Abba ya faɗa. Ɗan zazzare mashi idanu ta yi, dai yanzu ta gane dalilin da yasa Abba yake kama da daddyn gentle chaos ɗinta, a cewarta saboda baban Faryan ne, kun san ta faɗa ai Faryan yana kama da daddynta. Kamar zata ce mashi dama uncle Faryan ne ɗanka da bai yi auren ba, sai kuma ta fasa game da kufansa. Suka shige ciki a tare. A parlo Abba ba zauna game da nuna mata sama yana faɗin. “Ki je Rimsha tana sama”…. “Nagode Abba”. Ta faɗa game da hayewa sama tana ɗan murmushi. Shi kuwa Abba ya yi shiru yana tinanin yadda zai je ya gana da iyayenta a nan kurkusa. E kam akwai case, Abba zai je karɓawa Faryan auren Cherry a hannun Aryan. Tana haurawa sama suka yi karo da Ammie, risinawa Seraphina ta yi ta ɗaga mata gaisuwa, fuska a ɗauke da fara’a Ammie ta amsa mata, sai ta ce. “Ban gane ki ba”. Kai ta jinjina. “Seraphina by name, friend ɗin Rimsha, wajenta na zo”. Cike da girmamawa ta faɗa.Da yake dik sun san labarin Seraphina sai Ammie ta ce. “A’a, ai mun san labarin Seraphina, mun sanki a bakinta, shiga ga ɗakinta”. Ta kai karshe game da nuna mata ɗakin. Godiya ta yi tare da wucewa ciki. Bayanta Ammie ta bi da kallo tana yabawa kyan yarinyar, sai ta ji ta kwanta mata a rai, a cikin zuciyarta ta ce ina ma ace rabon Faryan ɗinta ce, ALLAH yasa mallaketa.Sai da Seraphina ta shige cikin ɗakin Rimsha sannan Ammie ta wuce ta sauƙo ƙasa. A lokacin da ta shigo Rimsha ta yi shiru, tana kwance ta tada kai da laps ɗin Aunty Luna dake ta ƙoƙarin kwantar mata da hankali. Tana ganin Seraphina ta miƙe da gudu ta nufeta tana faɗin. “Welcome my girl”. Ta kai karshe game da rungumeta. Rungumota ita ma Seraphina ta yi, Aunty Luna ta zuba masu ido tana kallonsu har suka raba jikin juna, Rimsha ta kamo hannun Seraphina ta isar da ita bakin bed, ta zaunar da ita kafin ta ce. “Seraphina my Aunty, Aunty Luna my best friend”. Cikin girmamawa Seraphina ta ɗagawa Aunty Luna gaisuwa, fuska ɗauke da murmushin nan nasu mai kwantar da hankali Aunty Luna ta amsa mata, lokaci guda Seraphina ta gano Aunty Luna na kama da uncle na school ɗinsu, amma bata yi magana ba. Bayan sun gaisa Aunty Luna ta fita ta basu waje, ai sake rungume juna suka yi kafin su fara gulma. Sai ga Ammie da kanta ta shigowa da Seraphina cima irin nasu na larabawa kala-kala masu daɗi da kamshi. A saman carpet ta shirya mata kafin ya juya ta fita. Saga Rimsha ɗin har Seraphina ɗin babu wacce ta ci abinci rana a cikinsu, dan Seraphina ma in baku manta ba ta je yin wanka ne ta fito ta yi lunch ɗin kenan Rimsha ta kirata, so dik basu yi ba, amma ko da Ammie ta kawo masu abinci basu sauƙa sun ci ba, suka yi zaman gulma.To kafin su kammala gulmar nasu bari mu je wajensu sister Zinta mu dawo, jama’a me kuke tunanin zai faru? Abba ya yaba da Seraphina, Ammie ma haka, ga shi dama Faryan yana so, kun kuwa san idan Abba ya nufi yin abu fa to koma ya za’ayi sai ya yi, me kuke tunanin zai faru? Muje zuwa. ————————🔥WS-HOSPITAL.Around 2 na dare sister Zinta ta farka daga barci, ga mamakinta sai bata ga Dr James a saman bed ɗin ba, miƙewa ta yi zaune taka kalle-kallen gefe, babu shi babu alamarsa. Kasa ta sauƙo tana daka hamma, a tinaninta waje ya fita dan bata ji alamar motsi a toilet ba, sai ta nufi waje. Shiru babu alamar motsin mutane a gidan, ta yi matuƙar mamaki sosai, ɗakin dake kusa da nasu ta shiga. Nan ta isko mutum kwance a saman bed.Har zata juya kuma sai ta fahimci ashe macece kuma sister Maya ce. Ajiyar zuciya ta sauke game da karisawa wajen da sister Maya ke kwance, tattaɓata ta fara yi tana ambatar sunanta. A hankali Maya ta buɗe idanunta, ganin Zinta ce yasa ta miƙe zaune tana faɗin. “Sister lafiya?”. Zinta ta amsa da. “Sis babu kowa fa a gidan nan yanzu, ina suke to?”….. “Ban gane babu kowa a gidan nan ba?”. Ta faɗa tana zare idanu. Shaida mata da kyau sister Zinta ta yi lallai babu kowa a gidan nan, zabura ta yi ta sauƙo ƙasan gadon tana tambayar ina suka je?.Sister Zinta ta ce. “Ke, ki natsu, ina ganin wani abin suka je yi, ko sun je cikin hospital ne? Mu je mu dubasu”….. Na’am da wannan zance Maya ta yi, sai ta haɗe natsuwarta waje guda, ta miƙe suka fice a tare.A bakin gate suka isko guards masu gadin gidan suna zazzaune babu alamar barci a idanunsu, zasu fita guards ɗin ɗaya ya ce. “Ina zaku je Madam?”……. “Cikin hospital”. Sister Zinta ta basu amsa. “Sorry Madam ba’a ce mana zaku fita ba, dan haka ku koma”…… Kallon juna suka yi, sister Maya ta juya da nufin su koma, ita kuma sister Zinta da yanzu ta daina jin tsoro da shakkar kowa tin da ta amarce da Dr James sai cewa ta yi. “To idan na zo fita ka hanani in gani”. Ta faɗa tana riko hannun sister Maya. Miƙewa tsaye guard ɗin ya yi game da cewa. “Sorry Madam, ba’a bamu izinin cewa akwai wacce zata fita mu buɗe mata kofa ba”. ….. Sosai sister Zinta ta tsorata da ya miƙe tsaye, wani kato da shi a murɗe. Amma saboda yanzu bata jin magana sam-sam, bata shakkar kowa bare tsoro sai ta ce. “Wannan kai ya shafa, ni dai hanya zaku bani in wuce ko kuma in buɗe da kaina in wuce”. Rikota sister Maya ta yi tana faɗin. “Sis please ki kyalesu mu koma ciki”….. “Ba zan kyalesu ba sis, sai na je na duba mijina, kika sani ne ko yana tare da sister Lazy!”. Cikin masifa ta faɗa, yanzu ta fara iya harda masifa yarinyar nan, da shiru-shiru abinta.Mamaki ne ya kama Maya ganin yadda take masifar, har da ɗaure fuska tamau. Shi kuwa wannan bodyguard ɗin ya tsaya tsayin daka kan ba zata wuce ba, domin kuwa a bakin aikinsa yake. Da ta matsa mashi ma sai ya yi mata ɗaukar amarya, cak ya dagata, bai direta a ko’ina ba sai a tsakiyar parlonsu, ya juya ya fito. Zata bi bayansa sister Maya da ta shigo yanzu ta riketa tana faɗin ta yi hakuri koma menene ai Dr James ɗin zai dawo, ba sai ta titseye shi ba idan ya dawo, kin aminta ta yi, ta kwace kanta zata sake fita Maya ta riketa tana sake bata hakuri. Shi kuwa bodyguard tini ya koma bakin aikinsa.A daidai wannan lokaci kuma 3D suna tsakiyar hospital ɗin, dan SECTION E a tsakiyar gabaɗaya ginin yake, amma ba zaka taɓa zaton shi ne a tsakiya ba har sai in ka san taswirar ginin da kyau, a yadda aka tsara haka ne, amma jama’ar cikin asibitin suna ganin kamar SECTION E a karshe yake. Da ace sister Zinta ta fito a wannan lokaci, to hakika da zata haɗu da 3D rike da jariran da suka ɗauko daga SECTION D, saboda sun fito zasu shiga SECTION E, a daidai saitin hanyar da zai kaisu gidansu suka tsaya Dr James yana duba wani baby da hancinsa ke bleeding, sun ɗauko five babys kamar yadda suka saba, suna tsaka da tafiya ne Dr James ya ji jini na zuba a hannunsa, shi ne suka tsaya duba menene matsalar, to daidai wannan lokaci su sister Zinta suka so fitowa guard ɗin can ya taresu.Sosai hancin jaririn yake zubar da jini, wannan jaririn ne da sister Maya take ɗauka a lokacin da aka ɗauke mata darling, sai ta maye gurbin darling da shi, to shi suka ɗauka dama. Ganin kamar akwai matsala ne yasa Dr James ya ce su Dr Kamal su yi gaba yana zuwa, bari ya duba babyn, in bashi da lafiya ne sai ya ajiyesa ya ɗauki wani, da safe zasu duba lafiyansa.SECTION D ya dawo da babyn, su kuma suka wuce SECTION E da sauran na hannayensu dake ta faman barci. A saman gadon yaron ya kwantar da shi yana duba lafiyan jikinsa. Jikin yaron ya yi zafi sosai alamar bashi da lafiya, tin da yaga haka sai ya kyalesa, dan na faɗa maku basa amfani da jini mai rauni, idan jariri bashi da lafiya komai na jikinsa yana raunata, so jikinsa ba zai baiwa jininsa wannan sinadarin da suke da buƙata ba, ko sun razana shi sinadarin da suke so ba zai fita ba, sun yi asarar kashesa a banza kenan.Matsawa gaba Dr James ya yi, a gadon wani jariri ya tsaya, yaron idanunsa biyu yana wasa da ƴan kafafu da hannayensa, ya ALLAH, wlh ALLAH ya yi halitta a kan wannan yaro, da shi dana kusa da gadonsa, kamanninsu ɗaya sak, ya rabb, kyawawan gaske ne sosai, jajir da su, ɗayan babyn yana harci, while ɗayan idanunsa biyu.Yaron nan ya haɗu jama’a, idanunsa dara-dara farare kal a waje, kwayar idanunsa sky blue irin mai hasken nan, da yake dare ne ga idanun nasa a buɗe har wani kyalli yake yi, lips ɗinsa dark purple tamkar an sanya purple lipstick, yana ta zaro idanu waje yana wasa abinsa, tamkar a baka shi ka je ka ajiye ka yi ta kallo. Hannu Dr James ya sanya ya ɗauki babyn, ya kalli fuskansa da kyau kafin ya juya ya kalli fuskan babyn dake gadon kusa da wannan, tamkar an tsaga kara a kamanni, dik yadda aka yi da sperm na mutum ɗaya aka kyankyashi yaran, kuma yaran alama ya nuna sperm na ainahin European ne, dan turawa ne yaran, gashin kansu golden brown mai shegen kyau haka.Saɓa shi a saman shoulder Dr James ya yi, dama ɗaya zai ɗauka, su Dr Kamal sun tafi da huɗu. Bayansu ya bi yana ɗan jijjiga baby, dan yana ji an ɗaukesa ya fara ƙoƙarin kuka, da alama yunwa yake ji. A SECTION E ya isko su Dr Kamal suna tsaye da babys a hannu suna jiransa, yana zuwa suka kwantar da yaran a wannan gado na lantarkin. Suka kunna masu shocking ɗin. Take suka fara wani irin jijjiga, ya rabb, wannan baby ya zaro blue eyes ɗinsa waje tamkar kwayar zasu faɗi ƙasa, ya jisa a wani irin duniyar da bai taɓa ji ba, ya gagara gane menene ma a wajen.Ko gezau 3D basu yi ba, suna tsaye har sai da jikin yaran ya saki waɗan nan sinadaran, sannan ne Dr James ya matsa ya kashe shocking ɗin. Ai yana kashewa wannan baby mai blue eyes ɗin ya fashe da wani irin kuka har muryarsa tana wani irin garrrr-garrrr-garrr saboda tashin hankalin da gangar jikinsa ya shiga.Babu tausayu babu imani Dr James ya jefasu cikin ɗayar injin, yana jin yaron nan yana ihu, ko kyan yaron nan bai duba ya ce ya mashi kyau bari ya barshi ba, haka ya dannasu cikin wannan ball ɗin, suka mayar da marfi suka rufe. Suna rufewa kuka ɗaya mai ƙara yaron ya yi daga nan bai sake ba, injuna sun murɗe mashi wuya. Allahumma ajirni fi musibatin.Shiru 3D suka tsaya har lokacin tarar jini da ɓargo game da garin ƙashi da tsoƙa ya yi, suka ɗauki bokitansu suka zo suka tari komai kamar yadda suka saba, sannan suka wuce izuwa freezers room dan adana jinin……… Nasan jama’a kun ƙosa ku ji me suke yi da ɓargo da garin ƙashin babys ɗin ko? Tin da kun ji me suke yi da jini kam. Ni kaina na ƙosa in sanar daku amma a aikace ba’a labarce ba, na ƙosa ku sani dan irin abubuwan da dayawanku kuke amfani da shi ne, amma mu je zuwa, lokaci zai kaimu da ku ji komai!.Bayan sun adana su ɓargon yadda yakamata sai suka nufi SECTION D dan duba dashen da suka yi na eggs and sperms ɗin nan. Kewaye suka fara yi a cikin wajen suna dubawa, komai na tafiya yadda suke so. Sai dai abu ɗaya da basu yi tsammani ba, eggs da suka cire a jikin matattun yaran can sun fi kowani eggs a wajen karfi da kwari, sun fita daban da saura, da alama sun fi lafiya.A cewar Dr James jariran zasu fi kwari da lafiya, da alama zasu samu maƙudan kuɗaɗɗe da su. Fitowa suka yi bayan sun tabbatar da komai lafiya, suka nufi gidansu bayan sun je office ɗinsu sun cire kayan aikata ɓarnar nasu kenan, suka mayar da kayansu. Suna hanyar komawa gida ne Dr Kamal ya ce. “Waɗan nan eggs ɗin suna da karfi sosai”…… Dr James ya ce. “Sosai, nima na lura da hakan”……. Dr Mark ya amsa da. “Ina ganin mu sayar da babys ɗin kawai kada mu yi drugs dasu”.Shiru Dr James ya ɗan yi, sai kuma ya ce. “Dama waɗan nan yadda suke da karfin nan manya ƙasashe zamu sayarwa, dama akwai ƙasar da ta nemi jarirai masu karfi a hannuna dan ta renesu ta mayar da su sojojinta, sai dai su jarirai dubu uku suke so”….. Dr Kamal ya ce. “Suna shirya yaki ta karkashin ƙasa kenan?”. Dr Mark ya amsa da. “Zaka gane masu ne? Ai kasan haka suke, sai su reni jarirai a yadda suke son su kasance, su jefasu hukumar soja dan kawai kasashen duniya su razana da karfin sojansu, kaga yanzu akwai ƙasashen da idan aka ambaci sunansu to sai ka ji ana faɗin sojojinsu tamkar ba mutane ba, basu tsoron mutuwa, yaki kawai suka sani”.Dr Kamal ya amsa da. “To ai dama dole sojojinsu su zamana basa tsoron mutuwa, yaki kawai suka sani, to mutane ne wanda sun taso ba su san komai ba face horon da aka basu, babu uwa, babu uba, babu ƴan uwa, shiyasa zasu iya fito na fito da kowacce ƙasa, basu san daɗin iyaye da ƴan uwa bane, basu san daɗin rai da rayuwa ba, abu ɗaya suka sani shi ne su kashe ko a kashesu”. Jinjina kai Dr Mark ya yi. “Haka ne, dayawan manyan ƙasashe haka suke yi, shiyasa duniya take tsoronsu take tsoron sojojinsu, sojojinsu basu tsoron mutuwa, hasalima basu san me daɗin rayuwa ba bare su ji tsoron mutuwa, ba kana gani dik a wajenmu suke sayan jarirai ba, a renesu su zama sojoji, shekaru 17 zuwa 18 ya isa na renonsu”.Shi dai Dr James ko ƙala bai sake ce masu ba tin da ya ce sayar da yaran zai yi a mayar dasu sojiji tin da eggs ɗin suna da karfi matuƙa, shi saboda yasan komai sai bai shiga hirar ba, su Dr Kamal ne ba komai suka sani ba, amma shi ya jima da sanin cewa manyan ƙasashe basu cika amfani da ƴan kasarsu matsayin sojoji ba, suna sayen jarirai ne su renesu su kuma horar dasu, so yasan komai.A gate ɗinsu suka tsaya suka yi knocking, da sauri wani guard ya zo ya buɗe masu. Ciki suka shiga Dr Kamal and Dr Mark suna cigaba da hiransu.Lokaci guda suka tsaya cak a lokacin da suka shigo parlo. Slowly Dr James ya sauke kallonsa a kan sister Zinta dake zaune saman sofa ta buga uban tagumi tana ruwan hawaye, while sister Maya na rarrashinta.Wucewa Dr Mark ya yi tin da shi bashi da wani business dasu, ya nufi ɗakinsa abinsa. Kallon juna Dr Kamal and Dr James suka yi. A tare suka tako zuwa in da suke, bai yi magana ba, hannun yasa ya ɗauki Zinta cak suka wuce room ɗinsu. Sai faman tirjewa take yi tana faɗin ya saketa ita kam. Bai direta a ko’ina ba sai a saman gadonsun, a lokacin 5 na asuba ta yi. Fashe mashi da sabon kuka ta yi, zama a gefen gadon ya yi tare da jawota jikinsa yana kokarin rarrashinta. Ai tana zuwa jikinsa sai ta ji karnin jini, kun san shi wani shegen abu ne da baya ɓuya dik da suna cire kayansu su sanya na aiki a jikinsu, amma sai ya kama fatansu ƙarnin, bare ma ace jinin ɗan mutum, shiyasa suke yin wanka idan sun gama zaluncin nasu ai.Ta yi mamakin jin karnin jini a jikinsa, amma sai ta kawar da tinanin da cewa. “Ni ka sakeni”……. Saketa ɗin ya yi yana faɗin. “Menene yafaru kike wannan kuka haka? Yaushe kika tashi daga barci?”…….. Tana turo baki ta ce. “Ina ka je? Wajen sister Lazy ko?”. Tana dallah mashi hararar da bata san tana yi ba ta yi maganar.Wani irin dogon ajiyar zuciya ya sauke, shi ya zaci ma wata matsala ce babba, nisawa ya ɗan yi. “Baki ga mu uku muka dawo bane?”…… Tana kallonsa bata yi magana ba….. “Mun je duba babys ɗinku ne basu da lafiya, akwai babyn da hancinsa yake bleeding shi ne muka je basu magani da taimakon gaggawa, ai kinga ma dikkanmu muka fita a tare ko?”. Ajiyar zuciya ta sauke, sai yanzu ta gane dalilin dayasa yake karnin jini, watau babys ɗinsu ba lafiya har da mai bleeding, jinin ya taɓa shi kenan, to yanzu zuciyanta ya yi sanyi. Tafukanta tasa ta rufe fuska tana ɗan murmushi ga hawaye a fuska, wani irin kallon kauna ya bita da shi, har cikin ransa ya ji mugun daɗi ganin tana kishinsa. Dogon hancinta ya ɗan ja game da cewa. “Bari in yi wanka in shirya zuwa office”. Ya faɗa yana miƙewa…. Da sauri ta ce. “My Dr nima zan fita aiki yau, ina son ganin babys ɗinmu”…… Kai ya jinjina mata game da cewa. “Ki shirya to mu fita a tare”. Cike da murna ta tashi, jiya da bata ga jariran nan ba dik ta damu. After some hours. Rike da hannunta suka fito parlo, yana sanya da kayan aikinsa, ita kuma kayan da ya bata shi ta sanya, doguwar riga zuwa gwiwa, ta kamata sosai a in da ta fito mata da shape na jikinta matuƙa. A parlo ya isko su Dr Mark sun shirya, sister Maya ta yi wanka ta nufi sashin gidansu dan shiryawa zuwa aiki. Gaba Dr Kamal and Dr Mark suka yi, Dr James and sister Zinta suka rufa masu baya.Suna shiga sashen asibitin ya saki hannun district Zinta game da cewa. “Jeki wajen babys ɗinku, anjuma ina zuws”………. Tin da suka shigo sauran nurses ɗin suke ta faman kallonsu cike da mamaki. Ita kuwa ko a jikinta, ta matsa ta yi hugging ɗinsa game da sumbatar gefen cheek ɗinsa. Kama nata kumatun ya yi shima ya sumbata kafin su yi sallama ta wuce ta bufi SECTION D.Tana shiga taga ɗakin ya ɗan canza mata, durkutsawa sauran nurses ɗin suka yi suna ɗaga mata gaisuwa, fuska a ɗauke da fara’a ta amsa kafin ta ƙariso ciki, cike da mamaki ta ce. “Sister Nazy meyafaru? Ina sauran babys ɗinmu? Naga sun ragu ne”. Daidai lokacin sister Maya ta shigo, ita ma durkutsawa ƙasa suka yi suka hau gaisheta. Wacce aka kira da Nazy ce ta amsa da. “Aunty Zinta basu ragu ba, dama haka suke”…… Kai Zinta ta shiga girgizawa alamar a’a kafin ta ce. “Ba haka suke ba, gaskiya sun fi haka sosai ma”. Sister Maya da ta shigo yanzu ne ta ce. “Ai dama su 55 ne, na taɓa ƙirgasu a lokacin da muka fara aiki a nan”…… Jama’a ku ce wow, ku tafawa sister Maya!.”Yauwa kin kirgasu ko?”. Sister Zinta ta faɗa. Kai sister Maya ta gyaɗa alamar e kafin ta ce. “Gaskiya an ragesu, ha haka suke ba, waɗan nan ai basu wuci 30 ba a nan”……. “To mu kirgasu mu gani”. Cewar sister Zinta. Na’am suka yi da zancenta, dan haka sai suka fara ƙoƙarin kirga babys ɗin. Suna kirgawa babys 30 ne ciff, kunga daren jiya ma sun ɗauki biyar. Zazzaro idanu sister Zinta ta yi game da cewa. “Sister Nazy ina sauran babys ɗin?”. A kiɗime ta yi maganar. Zazzare idanu dikka nurses ɗin suka fara yi, tsabar babu ƙwaƙwalwa a kansu wai basu san cewa an kwashi yara 25 ba, kuma kullum suna kwana tare da su su tashi da su. Dage mata suka yi a kan lallai su basu san an ɗauki babys ɗin nan ba, su dai kawai suna yi wa yara wanka. Hankalin sister Zinta idan ya yi dubu ne ya tashi, cike da tashin hankali ta ce. “Bari in sanar da Dr James, kila su sun san in da yaran suke”…… Na’am suka yi da zancenta, dik hankalinta ya yi tsananin tashi, tana kiɗime, fitowa ta yi da sauri ta nufi sashin 3D, ita kuma sister Maya ta wuce ta ɗauki ɗan babynta da ta maye gurbin darling da shi wanda yake da rabon kwanaki nan gaba jiya 3D basu niƙa shi ba. Tana ɗaukansa sai ta ji jikinsa da zafi, hakan yasa ta yi gaggawar ɗagowa tana kallon su sister Nazy da suma ita suke kallo, tambayarsu ta yi me ya sami babyn, nan ma idanu suka fara zarewa suma faɗin basu sani ba. Siririn tsaki ta ja game da saɓa babyn a kafaɗa ta fita izuwa office na Dr Kamal dan ta bashi ya duba mata lafiyar yaron.Ita kuwa sister Zinta a kiɗime ta shiga office na Dr James, bata ko bi ta kan office ɗin PA sister Lazy ba, da sauri ta wuce. Tsaye ta iskosa yana ƙoƙarin cire coat ɗin jikinsa ya sanya surgical gown, dan akwai matar da aka kawo daga geferal hospital ɗinsu dake saman WS-HOSPITAL, in baku manta ba ai General hospital ɗin Avaris ce a samansu Dr James, su kuma suna ƙarƙashin ƙasa.To an kawo matar ne zasu cire mata mahaifa, in baku manta ba a farko labarinmu da farkon ganinmu da 3D suna cirewa wata mata mahaifa ne, to ashe daga cikin wannan General hospital ɗin ake shigo masu da matan suke cire masu mahaifa sai a sake fitar da su. Idan mace bata da lafiya, in suka ce tiyata za’ayi mata, bayan anyi mata allura da sunan za’ayi mata tiyatar, in ta yi barci sai su sauketa ƙasa izuwa wajen 3D ta sihirtaccen hanyarsu, 3D kuma su yi mata aiki su cire mata mahaifa, idan sun gama su kaita wannan ɗaki d suke shirya drugs ɗin da suke haurarwa saman nan, fatan kun tuna ɗakin?.Idan suka kaita wannan ɗakin suka ajiye to zasu yi wa babban likitan General hospital ɗin message, shi zai shigo da yaransa su ɗauketa su haurar da ita sama, sai a mayar da ita ɗakin tiyata na General hospital ɗin, su yi kamar su suka yi mata aiki suka cire mata cuta. Wannan mata da kuka gani a farkon labarinsu da 3D suka cire mata mahaifa ma ai daga wannan General hospital na Avaris ɗin ta fito, baiwar ALLAH bata sani ba kawai aka cutar da ita, aka shigo da ita wajen 3D bayan an yi mata alluran barci da sukan za’ayi mata ciyata a cire mata ƙarin mahaifa, shikenan aka kawota 3D suka rabata da mahaifarta.Kun san wani abu? Ko hukuma zata shekara tana binciken General hospital ɗin nan ba zata taɓa samun wani abin zargi ba, ku lura da irin tsarin da aka yi mana, ɓarkar tana ƙarƙashin ƙasa, ko kin ce a wannan asibitin aka cire maki mahaifa wlh ba za’a taɓa yarda ba, saboda babu alamar abin zargi a wajen, ba wanda zai zaci cutarwar tana ƙarƙashin ƙasan hospital ɗin, sai ranar da ALLAH ya yi asirinsu zai tonu ne kawai za’a ga abi da ba’a taɓa tsammata ba.A kiɗime sister Zinta ta ce. “My Dr kazo ka gani babys ɗinmu babu wasu, su 55 ne dama, yanzu kuma saura 30, bamu ga 25 ba”. Tsabar kiɗimewa har haɗewa words ɗinta yake yi….. Wani irin rass Dr James ya ji gabansa ya faɗi, tin da suke babu wata nurses mai kula da babys da ta taɓa kirga adadin yaran da suke kaiwa wannan ɗakin har su gama kwashesu, yau ɗaya an samu haziƙan da suka kirga babys ɗin tin a farko kawosu, lallai kuwa akwai matsala……. Nima na ce matsala kam ba karama bama.*Jama’ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba’ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.*

Back to top button