Zakuna Biyar Page 39 By Princess Teema
CRYSTAL PALACE.Gyara kwanciyarsa Lion ya yi yana tinanin meyasa Aryan yake zuwa wajen yarinyar nan har haka? Shi fa ya ce su bata rayuwa mai kyau ne, amma a nesantata da su, baya son ya buɗe idanu ya ganta a kusa da su ko kaɗan.Kun fahimci wani abu jama’a? Lion ya tsani mata, amma har yanzu zuciyansa da sauranta a kan Seraphina, a yanzu ba wai ya tsaneta kai tsaye bane, ya tsani ta zo kusa da shi ne, dan yasan sai ta zame mashi rauni, Seraphina amana ce a wajensa, domin ya cika wannan amanar yasa bai barta ta ƙare a cikin gidan Dr sun mutu tare ba, bai ceci Dr ba, saboda suna da muguwar gaba a tsakaninsu, but ya ceci Seraphina, ya fita da ita ta window, bayan an kunnawa gidan wuta ya zo ya ɓoyeta cikin jaccuzi.Idan bai yi niyyar cikawa mahaifinta amanar ba zai kyaleta ne a gidan cikin jacuzzin ta mutu, amma saboda ya cika alƙawarin da yayansa ya bar mashi, yana kwance gadon asibiti ya turo jami’an SSO suka zo gidan da daddare a washegarin ranar da abin yafaru, suka shiga suka ɗauketa, baya ga haka in ya so zai iya watsar da amanar da yayansa ya basa a lokacin, amma sai bai yi hakan ba, dan dik duniya bashi da biyun mutane biyun nan, daga Hussainin daddynsa sai Yayan nasa, ko zai yi fushi a kan komai ba zai yi fushi a kan mutane biyun nan ba, dan ya cika amanar gabaɗaya ya ce a bata rayuwa mai daɗi, kada ta nemi komai a rayuwarta ta rasa, ta rayu tamkar ƴar sarki a cikin kingdom, amma kada a bari ta sake ganinsa, kada a bari ta sake zuwa in da yake, ya tsani ganinta Kun san meyasa baya son haɗa inuwa da ita kuma baya son su haɗa inuwa da mata? Domin confirm sai mata sun zame rauninsu, kuma haka ne, in dan ya ɗauki Seraphina suna gida ɗaya, ko baya sonta ya tsaneta a hankali yau da gobe suna haɗuwa sai ya zama cikakken uba a gareta, idan haka ta faru kuma zata zame rauninsa na farko, idan wani abu ya tashi ko shi ba’a iya farmakansa ba ita za’a farmaketa wanda hakan zai raunata shi sosai, tana zuwa school ai, za’a iya cutar da ita ko ta nan, amma kunga yanzu tana rayuwa a gefe, bai saba da ita ba, hasalima bata san shi ba, ko kasheta aka yi ba zai ji zafin komai ba.Tabbas mata raunin maza ne, komai jarumtar namiji idan kunga an kaisa ƙasa to ku duba a tafiyar da aka kaisa ƙasan an haɗa da mace, idan ana son galaba a kan namiji sai da sa hannun mace, haka ALLAH ya yi zuciyar namiji, macece rauninsa. Kuma hakazalika mace tana zama karfin namiji! Dik in kaga namiji ya yi nasara a rayuwa ku duba gefensa akwai mace, shiyasa MANZON ALLAH (SAW) ya umarci maza da su nemi mace ta gari, dan yasan mace itake juya kaso 65 zuwa 70 cikin ɗari na rayuwar namiji, idan ya samu mace ta banza babin wahalar rayuwansa ya buɗe kenan, idan kuma ya samu ta kirki, babin jin daɗinsa ya buɗe kenan, Manzon ALLAH (SAW) baya kuskure, da ya ce ku nemi ta garin kawai ku nema ne, dan mata sai shirin ALLAH!.Da kun san tarihin daddyn Lion hakika da zaku ƙara gasgata me nike faɗe, daddyn Lion yarinman da ya taso cikin gata da tsantsar kulawa, ya bar gida kan ya cewa mahaifinsa sorry, daddyn Lion mutum mai zafin zuciya da taurin rai tamkar zaki, mutumin da ya taso cikin addinin bautar rana, an gwabza yaki da kakasa dan neman ƴanci daga turawan mulkin mallaka, jarumta gadon masarautansu ne, saboda zafin zuciyansa ya gwammaci ya bar gida, ya bar gata da iyayensa kan ya bada hakuri.Ya komo US, ya rayu kaman sarki saboda dukiyan da mahaifiyasa ta basa a lokacin da yake barin gida, daga bisani ya gane yana da baiwa, zai iya abubuwa dayawa, ya tsaya ya jajirce sosai, a tafiyarsa ya haɗu da macen da take iya canza akalan rayuwansa, dik duniya a lokacin idan ya yi fushi ita kaɗai take ce mashi calm down, ta taushesa ya haƙura. Macen da ya so fiye da kansa, macen da ya sanar sirrinsa fiye da ɗan uwansa Hoosain, macen da in ta ɓata rai sai US ta tsaya na ɗan lokaci saboda fushinsa, idan ka taɓata to jini ne zai zuba, da dik wanda ya taɓata baya yafe mashi koma wanene, harta mahaifinta ya taɓa marinta a gabansa kafin su yi aure, kafin mahaifinta ya sauke hannu ya rama mata ɗaya tamkar dubu, daga mari ɗaya sai suma, kai tarihin daddyn Lion abu ne mai tarin darasi, zaku ji complete tarihin ba zan rage komai ba a gaba, dan ni wlh tarihinsa ya fi mun na kowa daɗi da ma’ana a labarin nan, ga tarin ilmantarwa. Mom Lion ta ja shi ya shiga musulunci saboda tana son shi, sun shirya aure, uhm Muhammad Haiza’an, mamallakin HAIZA’AN AIRLINE, mutumin da ya tara dukiyan da yake iya baiwa gwamnatin Amurka da sauran manyan ƙasashe bashi a wannan lokaci, mutumin da in yai magana ko shugaban ƙasa baya ja in ja da shi, mutumin da karfin dukansa ɗaya daidai take dana mutane 20, ya rayu tamkar sarki a fada, ya nunawa mom soyayya fiye da dik mace, ya gatanta rayuwarta da dikkan ahalinta.Family ɗinta dik suna fantamawa da dukiyansa, su je ƙasashen da suke so, ƙaninta sai a ƙasar da yake so yake cin abincin dare, kannenta ba’a magana, sun more fiye da tinani, idan zasu yi birthday su ɗauki jirgin ruwa tampatsetse, a tsakiyar teku ake party ɗinsu, a kashe kuɗi a cashe, dik daddyn Lion bai damu ba, ya sake masu komai, kamfanin jiragen sama yake da shi, kai na ce maku ku jira cikakken tarihinsa, amma daddy ya gatanta mom da ƴan uwanta.Amma me yafaru? Da aka shirya kaisa ƙasa, ba za’a iya tinkararsa ba saboda karfin ikonsa, ko gwamnati tsoronsa take ji, karfin ikonsa ya baiwa CRYSTAL PALACE karfin iko a yau, dalilinsa yasa babu wani jami’in gwamnati da ya isa keta cikin CRYSTAL PALACE bare ya kama wani daga ciki, kuma har yau har gobe gwamnati na shakka da tsoron shiga cikin gidansa, gidan yana nan a rufe sai tarin jami’an dake gadin gidan tamkar akwai ran shugaban ƙasa a ciki, daddy ya sanya tsoro a zuƙatan azzalumai da zaman lafiya ga bayin ALLAH, ba ta yadda za’ayi a same shi bare a kashe shi, dole sai ta hanyar mutum ɗaya! Mom Lion, ita kaɗai take da kusanci da shi fiye da yadda kowa yake da, ya rabb, ta zaɓi matsayin da gwamnati ta kwaɗaita mata fiye da wanda mijinta ya bata, ta zaɓi ta samu karfin iko fiye da wanda ya bata, ta aminta ta sa hannu kan zata fito da shi wajen da babu kowa a kama shi, ya rabb, baya fita sosai, sai dai a zo gida a samesa, amma a wannan rana da tsautsayi ta hau kansa, ta ce sai dai su fita yawo, ya ce ina take son su je, ta kwanta a jikinsa tana kirga mashi in da take son su je.A wannan rana Lion ya zo gidan ganin jaririn ƙaninsa watau Nirash Leo, in baku manta ba Lion yana hannun Hosainin daddy ne. A wannan rana da ya zo bai samu haɗuwa da mom ba, dan tana wanka, shi kuma daddy baya son Lion ya zauna a gidansa saboda wani ɓoyayyen dalili nasa. MENENE WANNAN?.Lion yana son Nirash sosai, ya ɗauki yaron, yai mashi wasa sosai, kafin mom ta fito ya kwantar da shi ya koma. Mom ta yi kwalliyar da tin da take bata taɓa yin isrinsa ba, sai tsokanarta daddy yake yi wai yau ta zama under 13, ta ƙara kyau, har ya ce gaskiya ba zai yarda ba, kafin su fita sai sun ɗan yi chaskale, dan ta yi kyau sosai, da yake ta san me ta shirya, ta yarda, a wannan rana ta bashi kanta na karshe, tin da yake da ita bata taɓa sake mashi jikinta irin wannan rana ba, har yake tambayarta meyasa yau bata mashi kukan yana wahalar da ita ta kame jikinta ba?.Tana munafukin murmushi ta amsa da ai yanzu ta daina bashi wahala wajen saduwa, ta yi alkawarin yi mashi yadda yake so, ya ji matuƙar daɗi, a wajen ya ce ta faɗi me take so ya bata! Buɗar bakinta ta ce kyautar jirgin sama guda ɗaya, a wajen ya ɗauko ɗaya daga cikin takardun jiragen samansa, ya sanya hannu a kan wanda ta zaɓa, ya bata yana ƙara jawota jikinsa, dik bai san me ta shirya mashi ba..Ta karɓa har da godiya, suka sake yin wanka, ta shirya Leo cikin haɗaɗɗun kaya, daddy ya ɗauki Leo a hannunsa yana sumbatar kumatunsa suka fito. Guards zasu rakasu ta ce yau fitar masoya ne, kada wanda ya damesu, hakan yasa daddy ya ce mutum biyu su rakasu, ta yi typing message ta sanar da mutanen can guards biyu ne kawai sukai masu rakiya, sun yi farinciki da jin hakan sosai.Daddy da kansa ya tuƙa mota a wannan rana, motar da bai sake tuƙawa ba kenan a rayuwansa. Mom ta ce daji zasu je, dan yau soyayyarta ce sabo ta motsa, da yake ya yarda da ita fiye da kansa, bai kawo komai a ransa ba, ya ɗauketa suka shiga dajin, bakin teku dan hutawa, yana rike da Leo yana zura mashi harshe a bakin yana tsotsa, suka tsaya a bakin ruwa suna hirar soyayya, ya jawota jikinsa.Unexpected suka ji harbi, an harbi guards ɗinsa guda biyu, da yake a lokacin akwai sa bakin gwamnatin wannan lokaci, sai abin ya tafi cikin tsari, yana bin gwamnatin bashin kuɗi billions of dollars, shi ne kan su biya gara su haɗa baki a kashesa, dalilin kenan da yasa suka yaudari mom da ta haɗa harda yaranta ta kashe dan a rasa magada kuɗin Haiza’an gwamnati ta ci bulus, ita kuma mom da yake kanta dusa ce a ciki, sai ta aminta da su, ta shayar da jaririnta guba, Lion ya gudu, saboda a lokacin da suka kusa kama daddyn Lion ɗin ya yi wa Hoosaininsa message kan ya ɓoye mashi Lion!. A wannan lokaci sun gagara kama daddyn Lion, ya rike mom sun gudu cikin daji, abu ɗaya yasa ya tsaya aka kama shi, watau da ya ga mom ta sanya mashi bindiga a kansa ta ce ya miƙa wuya, ya rabb, gigitar wannan al’amari yasa ya tsaya ya gagara motsawa, macen da yake ƙoƙarin bada ransa ya ceceta ita da ɗansa, amma ita ce ta sanya mashi bindiga a kai take cewa ya miƙa wuya ga miyagu?! Sumar tsaye ya yi, ya dinga kallonta babu kyaftawa, a wannan lokaci WS-HOSPITAL guards suka kewayesa, WS-HOSPITAL su brain ɗinsa suke so, while gwamnati kuma suna son a kashesa dan kada su biya kuɗinsa da suka ci. Haka suka kama shi mom na tsaye, suka ɗaɗɗauresa da igiya, wlh daddy yana tsaye yana kallon cikin idon mom bai motsa ba, ta rigada ta kashesa da ransa, wannan wani irin cin amana ne mai tsananin zafi?. Taya kuke tinanin Lion zai yafe mata? Ko shaiɗan bashi da kalaman da zai sanya zuciyar Lion ya yarda da mace, wlh babu mahaluƙin da ya isa ya sanya shi ya yarda mace tana da kirki, ya taso yana ganin yadda mom da dad ɗinsa suke soyayya sosai tamkar zasu haɗiye juna, amma daga karshe ku duba fa?.Da yake mom tasan daddy na mutuwar son yaransa, sai ta ce a tsayar da shi, kafin a wuce da shi bari ta baiwa Nirash guba a gabansa, so take ta kashesa da heart attack ne kawai……. Azzaluman suka tsaya, ta karɓi guba a hannun ɗaya daga cikin guards na WS-H, ta buɗe kwalbar, tin da uwar daddy sarauniyar Ring Of Power ta haifesa bai taɓa zubar da kwallah ba sai a wannan rana, yana gani ta tsiyaya gubar a marfin kwalbar, ta ɗigawa Nirash dake ta faman wasa a baki, take ya fara lashe baki abinsa. Ya rabb, sai ga hawaye masu tsananin zafi sun fara zuba daga idanun daddy da suka rikiɗe suka yi jajir tamkar wuta, ya ALLAH, ko motsi ya gagara yi, waɗan nan hawaye da suna magana, da sun faɗawa duniya kalamai daga zuciyar daddy wanda zasu firgita duniya! Haka guards na WS-H suka wuce da shi, mom kuma aka dawo da ita gida da nufin gwamnati zata bata muƙami na musamman a gwamnatance. Tana dawowa gida ta kwantar da Nirash a kan gado, ta shirya kayanta, ta ɗauki takardan jirgin da ya mallaka mata, ta fita da gudu ta bar Leo a kan gado, daga nan ta nufi gidan gwamnati, dan tasan Hoosainin daddy ba zai kyaleta ba, in duniya dik gatanta ne sai ya ga karshenta a irin wanan bakar zuciyar tasu.Tana barin gidan sai ga Lion ya shigo, dan a lokacin ya samu labarin dik abin dake faruwa daga bakin Hoosainin daddynsa. Cikin zafa ya hau benensu, yana neman mom ɗinsa, a lokacin bai san da sa hannunta ba, dan lokaci daddy bai faɗa masu ba, sai daga baya ne ya kirasu a waya yake sanar da su har Aryan ya ɗauki kiran.Yana shiga ɗaki ya isko Leo kwance kumfa na fita daga bakinsa, yaron yana fafutukan rai ko mutuwa, ai tuni Lion ya mance da abin da ya kawosa, ya rungumi ƙaninsa da gudu ya fita. Jama’a tarihin daddy akwai taɓa zuciya sosai, ya sha gwagwarmayar rayuwa bawan ALLAHN nan, amma zaku ji komai dallah-dallah a gaba, yanzu tsakure ne, tarihinsa shi ne the most best part a littafin nan!.Kunga a yanzu ko shaiɗan bashi da kalaman da zai zuga Lion ya yarda da mace har ma ya sota, irin wannan zazzafar cin amana mai ƙona zuciya, hmmmm, dan haka kome Lion ya ce da mata ƴan mata ayi hakuri, ba laifinsa bane, muɗin ne muka dinga bashi darasin rayuwa mai tafarfasa bama mai zafi ba, ga Dr ma ta ƙara mashi nata ta hanyar kashe mashi yaya, ai shi Lion hmmmm na dai yi shiru, amma yaga rayuwa!. ————————-🔥Baki a ɗauke da sallama Aryan ya shigo ɗakin, tin daga kan yadda yaga Lion bai amsa mashi sallama ba yasan akwai matsala, ƙarisowa ciki ya yi, ya zauna a gafen bed yana faɗin. “Bro are you okey?”. ….. Zuba mashi idanu kawai Lion ya yi, babu abin da kwakwalwansa yake tariyo mashi face yadda mom and Dr suka ci amanarsa, zuciyansa ta tsananta zafin da yana ji ba zai iya magana ba, in ya buɗe baki zai iya haɗiyar zuciya ne, sai kawai ya bi Aryan da ido, lokaci guda idanun nasa suka rikiɗe suka yi jajir tamkar wuta.Ganin hakan ba karamir girgiza Aryan ya yi ba, matsawa ya yi ya rikosa yana ƙara tambayansa lafiya, shiru bai yi magana ba, sai datse idanun nasa ma da ya yi gabaɗaya kawai. Rungumesa a jikinsa Aryan ya yi, yana ɗan shafa bayansa, sai ya tina a lokacin da suke yara in sun je gidansu Lion, idan suka gwabza faɗa suna huci sai daddy ya ɗauko ruwa ya karanta masu ayatul kursiyu kafa bakwai-bakwai ya basu su sha, take zuciyar take sanyi.Tina hakan yasa ya yunkura zai kwantar da Lion ya miƙe kenan sai gani ya yi an miƙo mashi ruwa, slowly ya ɗago kai, guru ne ya ɗauko ruwan ya tufa mashi ayatul kursiyun, dan in da sabo guru ya saba tofawa Lion da Aryan ayatul kurshiyu a ruwa, yo waɗan nan biyun idan suka fara faɗa tin suna yara ma ai sai da ayoyin ALLAH ake shawo kan zuƙatansu, kuma a da basa taɓa kwana biyu basu gwabza faɗa ba, yanzu da girma ya zo suka rage, amma basu daina ba, sai in ra’ayinsu bai banbanta ba.Karɓar ruwan ya yi game da cewa thanks. Guru ya buɗe mashi marfin, ya saita a bakin Lion yana ɗan shafa wuyansa, da yake Lion ɗin zuciyansa ta ɗauki zafi tamkar an ɗaura dalma a wuta, sai ya ji yana buƙatar ruwa mai sanyi, dan haka ya buɗe baki ya fara karɓa. Tas ya shanye ruwan bai rage komai ba, ajiyar zuciya suka sauƙe.Aryan ya kwantar da shi game da sanya mashi pillow, guru ya matsa ya taɓa gaban goshinsa, babu zafi, kawai zafin zuciya ce. Da haka suka samu barci ya ɗaukesa, sai suka koma parlo suka zauna.Guru ya ce. “Kasan da cewa suna shirin rikita media ɗin Avaris yanzu?”…… Jinjina kai Aryan ya yi. “Yeah, suna shiri ɗaukewa mutane hankali saboda abubuwa biyu dake shirin faruwa, na farko asirinsu kan amfani da tankar mai suna kashe mutane yana gab da tonuwa, na biyu shigo da sabuwar plan na sabuwar dabarar kashe mutane da karɓe masu dukiya da zasu yi”..Guru ya ce. “Suna tafiya da plan A and B ne ai, tin da asirinsu kan tankar mai zai tonu shi ne zasu shigo da plan B, ba zadai su kyale mutanen Avaris su zauna lafiya ba”………. “Ina zasu kyalesu su zauna lafiya tin da sun karɓo kwangila daga turawan yamma, ai sai sun idasa aikinsu, Avaris tana daga cikin ƙasa masu yawan population shiyasa suke son ragesu, sai abin kuma ya zo ya haɗe masu da karfin tattalin arziki da suke da, ai kaga dole su ji a jikinsu”. …..Guru zai yi magana kenan aka fara kiran wayar Lion dake hannun Aryan, fito dawayar ya yi, ta miƙe ya nufi cikin ɗaki, jim kaɗan ya fito hannunsa rike da wayarsa yana karawa a kunne, Abba ne yake kiransa, ya ce maza ya zo ya bashi kuɗi yanzu akwai sayayyar da za’ayi wa amarya Rimsha dan gyaran jiki, Ammie ce ta ce Abba ya kawo kuɗin, shi kuma ya ce Aryan ya kawo, Dr Aryan ne bank ɗinsa.Waje ya nufa yana ce da guru yana zuwa, da safe journey guru ya amsa mashi. Tin da ya fita bai sake dawowa ba sai 12 na dare, ya sallami Abba a kan ya tafi gidansa, dama sun san yana da gida. Abba bai matsa mashi ba, dan shi yasan irin tarbiyar da ta basu, dan haka baya damuwa idan Aryan baya gida.Yana fita ya koma wajen Lion bai je wajen Searaphina ba, dan Lion ne a ransa, ya tafi ya barsa cikin damuwa. Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga cikin ɗakin Lion, zaune ya iskou a balcony suna aiki, Lion da laptop, guru da waya. Ɗan zuba mashi idanu Lion ya yi, yana son yi mashi magana amma har yanzu zuciyansa bata sauƙa ba, he’s not in a good mood, baya jin ma zai iya motsa bakinsa ya yi magana, sai kawai ya bi Aryan da ido.A kusa da shi Aryan ya zauna, cikin sanyin murya ya ce. “How are you feeling now?”. Ya faɗa yana kai hannun jikin Lion ɗin, ya ɗan taɓa forehead ɗinsa, babu zafi, kitson kansa dake watse ya hau tattara mashi kafin ya sake tambayansa meyake damunsa?.Shiru Lion bai tanka ba, a gabaɗaya wannan dare uppan bai furta ba, sun yi juyin duniyar nan yaki ya yi magana, daga karshe ya miƙe ya je ya kwanta, bayan ya kwanta suka bisa ɗaki, Aryan ya dinga lallaɓasa kan ya tashi ya ci abinci, amma ko motsawa bai yi ba, daga karshe ya ja bargo tare da lumshe idanunsa, dik yadda zasu yi sun yi, suka kira Vir suka haɗu, suka dinga mashi magiya, amma Lion yaki ya yi magana, yaƙi ya ci abinci, yaƙi ya kula kowa, tsabar zafin zuciya, a yadda ta kwantan nan haka har barci ya ɗaukesa, shi kaɗai yasan me yake ji, hmmmm ba zasu gane bane.A wannan dare suma dakyar barci ya yi awon gaba da su, dik sun shiga damuwa, har shi Vir ɗin ma, da kyar ya rintsa, Aryan bai leƙa Seraph ba, saboda damuwar da ya shiga.Washegari da asuba suka farka domin zuwa Masallaci, ga mamakinsu sai basu ga Lion a gidan ba, sun ji mamaki sosai, dan sun san baya fitar asuba haka, sai dai in wani meeting ya je kafin ya dawo asuba tai mashi a can, wani meeting ɗin nasu kuma da asuba ake farawa, amma haka kawai baya fitar asuba. TO INA YAJE?Numbersa Aryan ya fara kira, sai dai a kashe take, Aryan ya shiga damuwa sosai, a daddafe suka yi wanka, suka shirya suka tafi masallaci. Bayan sallar asuba suka kira yaransu na SSO, sun tambayesu Lion suka ce bai zo ba, sun kira mr President suka tambayi ko Lion ya ce mashi yana zuwa, nan ma ya ce rabonsa da magana da Lion tin jiya da safe. Kiran masarautar Ring Of Power suka yi, suka kira number grandma, amintattun dake mata hidima ɗaya daga ciki ta ɗauka.Aryan ya tambayi sun samu labarin zuwan Edward ne? Suka ce a’a bai ce zai zo ba. Wasa-wasa dik in da suka san zasu sami Lion sai da suka duba, babu shi babu alamarsa, har karfe biyu na rana, damuwar rashin sanin in da yake ne yasa Aryan bai je wajen Seraphina ba.Around 2:30 na rana Abba ya kira Aryan, ya ce dik abin da yake yi ya bari ya zo yanzu. Dole ya bar komai ya nufi gida. Ga mamakinsa yana shiga gida sai ya isko su Abba dikka a parlon Abba dake sama. One by one ya fara kallon family, a kan Abba ya tsayar da kallonsa, Abban na hakimce saman gado, ya ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya yana rike da scepter ɗinsa, fuskansa a ɗaure tamau yau, babu alamar wasa. Da shigowar Aryan kowa ya ƙara natsuwa tsit, Rimsha na cikin mayafin amare, da alama da gaske Abba sai da ya ɗaura wannan aure.Zaman Aryan ya yi a kan side sofa yana mai da kallonsa a kan Ammie wacce da ka ganta kasan tana cikin tsananin tashin hankali. Shiru ne ya ɗan biyo baya a parlon, can Abba ya katse shirun da cewa. “A yau ina tsananin farincikin wannan al’amari da ya faru, a yau na aurar da ƴaƴana biyu, ALLAH Alhamdulliha”.Shiru suka yi suna kallon Abba, a kan Harleen Abba ya tsayar da kallonsa. “Anjuma da daddare zamu je ɗauko matarka, idan ta zo sai in haɗaku in faɗi abin dake bakina”…… Ya ɗan nisa tare da tsayar da kallonsa a kan Aryan. “A wannan rana irin ta yau, umarni nike baka ba shawara ba! Ga Rimsha nan amana, ita ɗin ba mata bace kawai a gareka, kanwace, ƴar uwace, jininka ce, ka riketa amana tamkar yadda mahaifinta ya rikeka, ya kula da kai, haka zaka riketa”….. Tashin hankali!! Me nike shirin ji? Kirjina sai da ya buga da karfi, nasan kuma naku ya buga da karfi, Aryan kuma, Rimsha matarsa? What?!.Wani irin ɗamke fuska Aryan ya yi, zai yi magana Abba ya rigasa da cewa. “Ban gama magana ba! Ina farincikin sanar da kai yau na mallaka maka sister ɗinka, matarka, jininka, wannan aure da kai aka ɗaura shi ba da Vash ba, sadakinka ka biya da kanka!”…… Babbar magana! E lallai Abba ya cika ɗan duniya, watau sadakinsa da kansa ya biya.Abba ya duba ya ga babu mai iyawa da Rimsha sai Aryan ne, saboda bata jin magana, Aryan ne zai gyara mata zama, shiyasa ya haɗa wannan aure. To amma Aryan ba Uncle ɗinta bane? Kai ni Queen Of Surprise kaina ya ƙulle fa.Miƙewa tsaye Aryan ya yi, in a harsh waye ya ce. “Ni ka aurawa wannan abar? Lallai kuwa ka saya mata tikitin tafiya lahira ne!! Kuma wlh ba zan zauna da ita ba, a yanzu na sak…….”. Tsawar da Abban ya daka mashi ne yasa ya dakatar da maganar. A fusace Abba ya miƙe tsaye, jikinsa har kerma yake yi, ya nuna Aryan da sandar hannunsa, babu wasa a tattare da shi, a fusace ya ce. “Wlh, wlh, wlh, dik ranar da ka saki Rimsha, ba zan taɓa yafe maka ba in bana raye, in kuma ina raye ka sani sai dai kan nemi wani uban ba dai ni Khaiza’an ba, aurenka da ita babu saki, kuma daga yanzu ka ɗauketa ku wuce gidan naka!!”. “Ba zan ɗauketa ba Abba! Lallai ba zan saketa ba kamar yadda ka faɗa, amma kuma ka sani ka jefa rayuwarta cikin uku ba da azaba ne, ba zan taɓa sonta ko in zauna da ita ba!”………. Ammie ce ta miƙe, jikinta na kerma ta ce. “Aryan please ka yi shiru, mahaifinka ne fa!”.A fusace ya kalleta, cikin zafin zuciya ya ce. “Ki mun shiru, ba dake nike magana ba, na tabbata da mahaifiya ce take tsaye a nan ba zata ce in yi shiru ba, ba zata yi shiru tana gani a zalunceni ba, yau da Ummie tana nan babu wanda ya isa ya cutar da rayuwata, amma saboda bake kika haifemu ba shi ne kika zuba ido yai mana abin da yake so, meyasa baki sa anyi har da Faryan ba? Saboda shi ɗanki ne?”………. Shiru Ammie ta yi tana jin zafin kalamansa, amma ta daure saboda tasan yana cikin ɓacin rai ne, da zafi abin da Abba yai masu, sun san babu wanda Aryan ya tsana biyun Rimsha, amma Abba ya haɗa wannan aure, shi ma yasan bai nemi zaman lafiya ba ai.Abba ne ya ce. “Ohk, ni ne na cuceka kenan? Ni Aryan kake faɗawa na cuceka?!”. Cikin faɗa ya faɗa. Mimmiƙewa su Faryan suka yi, Rimsha dai tin lokacin da Abba ya ce da Aryan ga matarka Rimsha, tin daga wannan lokaci da ta ɗaga mayafi ta kwala ihu ɗaya bata sake motsawa, Abba ya jefata cikin balain da yasa numfashinta ɗaukewa ta sume.A fusace Aryan ya ce. “Abba……”. Ammie ce ta yi ƙoƙarin sake dakatar da shi, saboda tasan hali, kuma tasan kome zai ce Abba fa magana ɗaya yake, in dik duniya zasu haɗu babu wanda ya isa ya sanya shi canza magana, ko ana mutuwa, ko wannan magana zata zama silar jefa rayuwar wasu a haɗari to fa ya yi ta ne, babu canji! Dan haka tsayawa ja in ja babu wani abin da zai ƙara masu, gara ta daure ta danni Aryan ɗin kawai. “When I’m talking to my father, I don’t need anyone to interrupt me, just get out of this room now!”. In a harsh way ya faɗa, ya faɗa kuma ba tare da ya kalli fuskar Ammie ba, dan dik da yana cikin fushi yana jin nauyin yi mata magana without respect, dan dik da mahaifiyansa Ummie bata gidan Ammie ta yi iya kokarinta wajen kula da su.Rass gabansu Harleen ya faɗi, tin da suke basu taɓa ganin irin wannan musifa ba, kai Abba baya son zaman lafiya ko kaɗan, in banda neman jafai irin na Abba, a wannan yanyi zaka ce umarni kake bashi bama ka lallaɓa shi ba tin da ka yi son ranka? Mutumin da in ya birkice kai kanka gudunsa kake yi, amma wai umarni yake bashi da ya kula da Rimsha.Nuna Aryan da scepter hannunsa Abba ya yi, a fusace ya ce. “Sai dai ka nemi wani uban ba dai ni Khaiza’an ba muddin ka tsallaka wannan umarni nawa! Babu saki tsakaninka da Rimsha, kuma ka ɗauketa yanzu ku tafi!”. In a harsh way shi ma ya faɗa. Babban magana!. Gidan Abba ya rikice fa.Juyawa da sauri Aryan ya yi, tamkar zai kifa, kamar zai tashi sama ya fice, baya ganin gabansa, kansa na mashi tsananin ciwo, zuciyansa tamkar zai fasa kirjinsa ya fito waje, ga damuwar rashin sanin in da Lion ya tafi, ga wannan bakar labarin wai an aura mashi Rimsha, wai kuma shi ya biya sadaki, innallilahi, da yasa shi za’a aurawa ita wlh ba zai kawo sadakin ba, gaskiya Abba ɗan duniya ne, Harleen kuma an aura mashi Aunty Luna ɗinsa.Baya ganin gabansa sam, bai san time da ya isa benensu Seraphina ba, yana shiga room ɗinta ya nufi bed. Tana zaune tsakiyar gado, tana rike da waya, hawaye ya gama wanke mata fuska, tana ta kiran mumbersa bata shiga, ta damu, ta yi kuka har ta gode ALLAH, burinta ya zo ya faɗa mata waye wanda ya ɗauki wayansa jiya.Tana ganinsa ta miƙe, ta nufosa tana faɗin. “Daddy…..”. Bata iya ƙarisa maganar ba ta dakata sakamakon ganinsa yana tangaɗi tamkar zai faɗi, ga shi ya dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi. Kallon kafafunsa ta yi, ko takalma bai sanya ba, tin daga nan ta goge hawayenta, dan tasan ba lafiya, cikin zafa ta matsa mashi hanya ganin yana ƙoƙarin bugeta tamkar bai ganta ba.Yana zuwa ya faɗa saman bed ɗinta, ya yi kwanciyar ruff da ciki yana ƙara dafe kansa. Ai da gudu ta hayo gadon, ta zo ta ɗago kan nasa, ta ɗaura saman cinyatarta, muryanta na rawa ta fara faɗin. “Daddy baka da lafiya ne? Meyake damunka?”……… Shiru bai iya tanka mata ba. Ƙara ƙanƙamesa ta yi, tana ɗan shafa gashin kansa, cikin taushin murya ta sake cewa. “Daddy ka yi magana please, baka da lafiya ne”. Wani irin dogon ajiyar zuciya ya sauƙe, ya zura hannayensa ta bayanta tighting ɗinta, yana huci mai zafin gaske. Ganin haka yasa ta cigaba da shafa kansa izuwa bayansa, ta fara faɗa mashi kalamai masu daɗi tana son shawo kansa, ya kwanta shiru a jikin nata yana jin kamar zuciyansa na sauƙa a hankali-hankali, ya zo wajen masoyiya ba. Watau Jama’a idan ina hango cakwakiyar dake gaba a littafin nan, Rimsha ta auri uncle Aryan! How? Ba uncle ɗinta bane? Tambayar dake ranku kenan, to kada ku damu, zan warware maku komai. Ya auren nan zata kasance, daddy na son Seraphina, while ita ma tana tsananin sonsa, Rimsha babbar aminiyarta ce, shin ya za’a kaya, daddy zai auri Seraphina a ranar birthday ɗinta, sun zama kishiyoyi da Rimsha, a gaskiya na tausayawa rayuwar Rimsha matuƙa. A yaushe zasu gane uncle ɗin Rimsha shi ne daddyn Seraphina? Ya zasu yi idan suka gane? Dama ba Ammie bace ta haifi Aryan? Wacece Ummie da Aryan ya kira matsayin uwa? Ina kuma take a halin yanzu? Uhm akwai rikici sosai, zamu ga yadda wasan zai kaya, ga dai Rimsha baiwar ALLAH a can ta suma, ALLAH sarki ai dole ki suma baiwar ALLAH, irin wannan tashin hankali, Aryan fa aka aura maki, tab, idan akwai abin da ya fi suma ma yi zaki yi!.To mu leƙa DOL team mu dawo, dan cakwakiyar CRYSTAL PALACE yawa ce da ita, ga Lion ya tafi bamu san in da ta yi ba. Ku karanta littafin Queen Of Surprise taku ta amana babu cawakiya ai kun san ba zai yiwu ba! Yanzu cakwakiyar zata fara mutanen kirki!.————————-🔥DOL.Tafiya suke tsakiyar dokar daji, babu tsoro bare shakka, sun kashe light na hannayensu ma, a cikin duhu suke tafiya……. Zaynish ne ya ce. “Ina da yaƙinin akwai abin da suke shigo da shi, lallai ba iya kaya bane kawai!”.Noor dake jiki dik a mace ne ya amsa da. “Sosaima, ko kaɗan ban yarda da bakin ruwan nan ba”……… Sarai Leo ya fahimci halin da Noor yake a ciki na tsananin feeling, dan ko magana da kyar yake yi, amma bai nuna mashi kamar ya gane ba. Vash dake faman dannar waya suna tafiya ne ya amsa da. “Na fi zargin suna shigo da makamai”. ……. A natse Leo ya ce. “A baya kafin su shahara ne suka shigo da makamai, yanzu ina da tabbacin sun wuce wannan level ɗin, akwai dai abin da suke yi wanda ya saɓawa doka”. Tsalle Noor ya yi, ya haye saman bayan Leo tare da langwaɓar da kansa, yana saƙalo wuyan Leo ɗin yana nishi kaɗan-kaɗan…….. Duka Zaynish ya kai wa Noor ɗin a gadon baya yana faɗin. “Ka dai bi a hankali, kada watarana ta hanaka aiki”………. Kukan shagwaɓa ya saka yana faɗin. “Bro ba ka gansa ba? Wai ina ruwanka dani ne?”. Shi dai Leo cigaba da tafiya ya yi bai tanka masu ba, watau Zaynish ma ya gane halin da Noor ke ciki. ……. “Akwai ruwana da kai mana, dole in saka maka ido kwana biyun nan, dan kada ka biye mace ka lalata mana aiki, yanzu ma jibeka fa? Ka biye mata ko jurar tafiya ba zaka iya yi ba sai an goyaka, dik gaɓɓanka jikinka sun mutu, ga kasala da nauyin wando”……..🤯Wasa-wasa Zaynish mafa ya iya tsiya, baya magana amma idan yana yi da Noor sai kun sha mamaki, sai ma ku zaci bashi bane yai, kuma sai ya yi magana ya fuske tamkar ba shi ya yi ba, bai taɓa murmushi ba bare dariya ko wacce iriyar magana zai faɗa. Vash dai baya tare da su a halin yanzu, yana can yana baiwa aljana hakuri.A shagwaɓe Noor ya ce. “Ni ku kyaleni in ji da ɗaya mana, my Juliet want kill me with her sweet, na samu da kyar na shawo kaina, na danni kaina, na biyoku shi ne zaku takura mun?”. Ya faɗa yana langwaɓar da kansa a gefen wuyan Leo.”Ai zaka iya komawa ka ƙarisar da abin da ka fara, nasan ita ma tana can tana fama da abin da kake mana a nan, dan haka ka koma kawai, kuma dama ni banga amfaninka ba, ko tafiya da kafafunka baka da kuzarin yi, yanzu idan aka farmakemu fa?”. Zaynish ya faɗa yana ƙara kai mashi dundu a gadon baya.A dake Leo ya ce. “Zaysh ka yi na kuɗinka, in ka ƙara sai ka ci wahala a hannuna, babu ruwanka da my pleasure”……. Sumbata Noor ya mannawa Leo a wuya yana faɗin. “This is my brother, love you more heartbeat”. Gyarasa da kyau a bayansa Leo ya yi yana faɗin. “Love you too baby”…. Ƙara rukunkume Leo tightly ya yi yana ɗan sakin shirin murmushi.Shiru Zaysh bai sake yin magana ba, sai dai ya kama kunnen Noor ya murɗa da ɗan karfi. Turo baki Noor ya yi ba tare da ya yi magana ba. Shi kuwa Vash hankali ya yi nisa, ya shiga damuwa sosai ta yadda har zufa yake haɗawa, saboda aljana ta ce zata kashe Manassa a daren yau, ga shi sun barosu a sansani, ya ALLAH.Hannu Noor ya miƙa ya taɓo Vash yana faɗin. “Vash lafiya?”…… A ɗan firgice ya ɗago, nisawa ya ɗan yi tare da cewa. “Akwai matsala bro”…… Dikkansu dawo da hankalinsu a kansa suka yi, cikin sanyin murya Noor ya ce. “Matsalar me?”……… Wayansa Vash ya miƙo mashi kan ya duba ya ga matsalar. Karɓa ya yi, suna cigaba da tafiya farinwata tankar ta fito sosai yanzu, hakan yasa ta ƙara haskaka masu hanya sosai. Fara bin chat ɗin Noor ya yi, wani waje ya yi murmushi, wani waje ya haɗe rai, har dai ya iso kan in da take cewa daren yau zata kashe Manassa, ya duba reply da Vash yai mata, na zunzurutun magiya da ban hakuri, ya damu sosai.Hakan ne ya ɓatawa Noor rai, sai ya ce gaskiya ba zai iya barin Vash a cikin damuwa ba, dan haka zai faɗa mashi gaskiya, miƙa mashi wayan ya yi yana faɗin. “Aljanar zata kashe kanta kenan?”.Cike da mamaki Vash ya ce. “Me kake nufi?”……. “Manassa da ita kake wannan chat ɗin ai, tin ranar na san da haka, na ɗauka zata cigaba da zolayarka irin na masoya ne kawai shiyasa na rufa mata asiri, ban zaci zata jefaka a damuwa ba, tin da haka ne bari in faɗa maka ita ce”. Ina Vash bai yarda ba, sai ya fara girgiza kai alamar kai ba ita bace, a dake Noor ya ce bari in tabbatar maka. Wayansa ya fitar, ya kira number V, bugu ɗaya ta ɗauka, dama ta koma ɗakinsu ta ɗauki wayar. Tana ɗauka ta shagwaɓe murya da cewa. “My Romeo, har yanzu baka dawo ba”. Ai wani sabon feeling ɗinta ya ji, a sanyaya ya ce. “Ina dawowa yanzu, ina son ki mun wani abin ne yanzu”….. Ƙara shagwaɓe murya ta yi wajen cewa. “Me kenan?”……… “Jeki ari wayar Manassa yanzu, kada ki faɗa mata me zaki yi da ita, ki karɓo ki zo cikin tantina ke kaɗai akwai abin da zaki mun da shi”..Da okey ta amsa tare da miƙewa ta fita, jim kaɗan ta dawo game da cewa. “Ga wayar a hannuna”……. Hannu ya miƙa ya karɓi wayar Vash kafin ya sanya wayansa a H-free ta yadda Vash zai ji komai kafin ya kaluɓo number Vash ɗin. “Shi ga contact ki saka wannan number da zan kira maki yanzu”. Da okey ta amsa. A natse ta shiga.Number Vash ya fara kira mata ta fara shigarwa kenan sai ta ce. “Akwai number a wayar, gata ta fito da saving my flower”……. Ɗago idanu ya yi ya kalli Vash kafin ya ce. “Shiga Whatsapp ɗinta ki nemo mun member”. ……. Da sauri ta shiga, sai ta ce. “Number ce a sama, da ita take chat yanzu”. “Okey to shiga kan number ki yi clicking voice, a cikin voice ɗin ki ce I am mrs Noor ya wadatar”……. A natse ta aiwatar da abin da ya ce, bata tambayesa me dalili ba, saboda tasan haka kawai ba zai tsaya wannan dogon magana ba.”Na yi na tura”. Ta faɗa.……. “Okey to goge voice ɗin yazama tamkar ma baki shiga kan chat ɗin ba”. Da okey ta amsa kafin ya aiwatar da abin da ya ce, daga nan ya ce mata. “Je ki mayar mata da wayar, yanzu zan dawo ba jimawa, wait for me don’t sleep”…….. “Okey my Romeo, love you more”…… “Love you too”. Kit ya kashe kiran tare da miƙawa Vash wayansa dan ya duba voice ɗin.A hanzarce ya karɓa, aikuwa yana dubawa ita ce, tabbas ba aljana bace Manassa ce, aikuwa ya ce zai yi mata tsiya shi ma, ba zai bari ta gane ya gane ita ba aljana ba ce, su cigaba da tafiya haka, ranar da zai damketa yana nan zuwa, zata san ta taɓo jinin Champion na IRON FIST, yadda ta dinga bashi wahala yana magiya ba zai kyaleta haka ba.Daidai lokacin suka isa bakin tekun nan amma ta can nesa da tantinsu, wani ɓangare ne da ake sauƙe ƙaya, amma ba ainahin in da ake sauƙe kayan bane, nan wani gefe ne kamar na sirri wanda ba kowa yasan ana sauƙe kaya a wajen ba, watau idan jiragen ruwan suka kusa isowa madakata in da ake sauƙe ƙaya, sai su ratse hanya, su ratso gefe can nesa daga in da ake sauƙe ƙaya, sai su dakata a wannan waje, kuma jiragen ruwa basa wannan ratsen sai tsakar dare, suna tsara tafiyarsu yadda sai dare zasu kusa isa madaka in da ake sauƙe ƙaya.Tin da suka doso wajen wasu mahaukatan karnika suka fara haushi da karfi-karfi, alamar securitys dogs ne, waɗan da aka horar da su dan gadi, kun san su dik yadda suka ji motsi sai sun yi haushi. Aikuwa suna wannan haushin wasu kartin maza suka fara firfitowa daga cikin jiragen ruwan dake faffake a bakin ruwa, wasu ma ba’a sauƙe lodin kayan dake kansu ba.Maza ne mada karti da a ƙallah zasu kai 30, dikkansu yawancinsu babu riga a cikinsu, suna murɗe sosai, dama kun san tsaron irin wannan waje sai masu rai da lafiya game da jini a jiki ake baiwa, dan kome zai zo su iya tarewa. Hannayensu rike da gabza-gabzan torchlight masu masifar haske, suna wani bubbuɗewa suka fito da nufin su ga su wanene?……… Ganin haka yasa Leo ya ce. “Is time for game”…… Yana faɗar haka tin bai rufe baki ba Noor ya diro ƙasa daga bayan nasa. Da gudun gaske suka dare suka rabu. Dik suka kama wajen ɓuya, wasu suka ɓuya bayan kwantainars, wasu kuma bayan jiragen ruwa. Haske ko’ina waɗan nan karti suka fara yi suna wani irin numfashi irin na gardawa. Kewaye lungu da saƙo suka fara yi da haske, while dik in da suka yo sai sojojin AZURE sun kauce sun ƙara ɓuya. Wani shirgegen ƙato ne ya zo ya wuce saitin in da Noor ya laɓe, ya wuce gaba yana haske-haskensa. Ai yana wucewa Noor ya fito, dik da baya jin kuzari a jikinsa, haka ya bi bayan mutumin, yana zuwa ya sanya hannunsa ya shaƙo wuyan mutumin ta baya, ya matse da hannu ɗaya tare da sanya ɗayan hannun ya toshe mashi baki.Fafutuka ya fara yi yana neman yadda zai kwaci kansa, sa dai ina, renon AZURE ba wasa ba, sai da Noor ya kaisa ƙasa, sai da Noor ɗin ya tabbatar baya numfashi, sannan ya sakesa tare da karɓar light ɗin hannunsa, ya kasheta game da turata cikin aljihu kafin ya damƙi ƙafar mutumin, ya ja shi a ƙasa tamkar kayan wanki, bakin ruwa ya kaisa ya jefar sannan ya dawo ya laɓe.A daidai lokacin shi ma Zaynish ya muɗe wuyan wani da ya zo ta kusa da shi, aikuwa yana dab zai haskasa Zaysh ya yi kukan kura ya danke wuyansa, ya murɗe ya karyeta. Yana karyewa Noor ya sake damke wani, shi ma murɗe mashi wuya ya yi ya karya. A tare Leo da Zaynish suka damki wasu biyun, dikkansu murɗe masu wuya suka yi suka karya. Daidai lokacin shi ma Vash ya damƙi wani shirgegen ƙato, ya murɗe mashi wuya.Faɗar ta koma yaƙin sunkuru, suka dinga yi masu ɗauki ɗaiɗai har sai da suka kashesu tas, sannan suka kutsa cikin kwantainars ɗin. Har lokacin karnukan suna haushi, sun bi dik wanda suka kashe sun ɗauke torchlight ɗinsa sun kashe. Nufar in da suka ɗaure karnukan a jikin wata bishiya Leo ya yi, ya je da nufin ya kashe karnukan, amma sai ya ga suna da mugun kyau sosai, irin manya-manyan karnukan nan ne masu tulin gashi a jiki, ga su farare tas, hakan yasa suka burgesa, su biyu ne, ɗaya gashin jikinsa har yana jan ƙasa, ɗaya kuma bai ƙarisa kai na wancan ba, bujumaye da su tamkar zakuna.Shafa kawunansu ya yi, hakan yasa suka yi shiru, sai ya wuce ya kyalesu da nufin idan sun gama abin da ya kawosu zai kwance karnukan su wuce da su. Gaban wani ƙaton kwantaina suka tsaya, hannu Leo ya sanya wajen jikin container, sai ya ga alamar gari-gari. Tsanin dake jikin container ya kama ya hau, Noor na rike da light yana haska mashi, ya haye zuwa wajen da aka sanya sarƙa aka ɗaure container sosai. Ƙasa ya sauƙo, suka shiga cikin wata jirgin ruwa, a nan ya samu almakashin tsinka sarƙa. Dawowa ya yi, Noor na haska mashi haske ya sake hayewa sama, karfi yasa ya datse sarkar, sannan ya sauƙo, Zaynish da Noor suka haɗu suka buɗe marfin container. Dallah light a ciki suka yi. Kaya ne shirye a cikin kwalaye, an shiryasu datsan-datsan. Leo ya ce Zaynish ya sauƙo da kwali ɗaya su gani. Ba musu ya sauƙo da shi, suka farka bakin suka buɗe. A tare suka ɗago suka kalli juna, wasu irin sinadarai ne na haɗa ƙananan boma-bomai, shegen tsada ne da waɗan nan sinadaran. Kai kawai Leo ya jinjina, bai yi magana ba, ya ɗauki almakashin ya matsa zuwa container na gaba, ya datse sarkar da aka rufeta. Zaynish da Vash suka buɗe marfin, while Noor yana ƙoƙarin rufe kwalin sinadarin boma-boman nan, a matsayinsu na sojoji dik wannan karatu sun san shi, hmmmmm su suka san me aka shirya a wajen, shiyasa kuka ga Leo ya girgiza kai kawai.Suna buɗe container na biyun kuwa kwalayen drugs ne a cike a ciki. Leo ya ce Vash ya sauƙo da kwali ɗaya. Da sauri ya sauƙo da shi. Buɗe kwalin suka yi, wasu irin magunguna ne wanda aka ɓuye ainahin manufar drugs ɗin, aka ɓuye ainahin daga ina suke, a jikin kwalin maganin an rubuta made in Avaris, amma sai ga shi sun kama maganin a bakin tekun shigo da shi ƙasar, kunga kenan dama daga waje ake shigo da su aka ɓoyewa ƴan Avaris gaskiya, aka ce a ƙasar ake haɗa masu.MAGANIN ME?. Mu haɗu a page na gaba dan jin wani irin magani ne? Gaskiya mutanen ƙasar Avaris suna ganin rayuwa, daga ganin wannan magani ba gaskiya aka ƙullah ba, saboda an rubuta cewa a ƙasar ake haɗa maganin a jikin kwalin, to ga shi kuma ashe daga waje ake shigo da shi, ya ALLAH! Ana cutar da su dayawa, ALLAH sarki, idan gaskiya maganin ya ƙunsa ba za’a ɓuye daga in da ake haɗa shi ba!.

