Zakuna Biyar Page 32 By Princess Teema
Karfe 4 na yamma daidai jirginsu ya ɗaga sai arewacin AVARIS! Sai farinciki suke yi zasu tafi babban mission, while basu san abin dake wajen ba, su dai suna murna kawai.WS-HOSPITAL.Cikin kwanaki ƙanƙanin su Maya suka yi mugun sabo da babys ɗin nan, abinku da suna yi wa yaran wanka kullum, su shafesu da mayuka, su gyarasu, basa hutawa aikinsu kenan, shiyasa suka yi mugun sabo da su, kun sansu kuma da shegen son yara, sai yara suka shiga zuciyarsu, shi darling dama ba’a magana, dan wlh wani irin mugun so suke yi wa babyn nan ba kaɗan ba.Kamar kullum, sun kammala yi wa babys ɗinsu wanka, sister Maya tana zaune rike da darling tana mashi wasa, yaro ya fara wayau, kamanninsa da Seraphina sai ƙara bayyana yake yi sosai, sai ma idan ya yi shiru yana wasa, ya ALLAH, kamar ka sacesa ka gudu da shi.Tongue ɗinta sister Maya take ta faman zura mashi a cikin baki yana sha, in ya fara tsotsa da ta cire zai fasa kuka. Sai mumushi sister Zinta take yi tana kallonsu, while ita ma tana rike da baby ɗaya daga cikin yaran nan.A lokacin kuma 3D suna cikin wani room a na ban mamaki a wani wajen da daga gani sirrintaccen waje ne, bakina ya yi kaɗan ya iya zayyana maku yadda wannan ɗaki yake, amma tin daga kan matakan tsaronsa, yadda yake da kofa mai amfani da tsaron wutar lantarki, babu wanda ya isa shiga wajen ba tare da izinin 3D ba, kana taɓa kofar wlh mutuwa zaka yi, lantarki ne zai jaka, zaku rantse da ALLAH lantarki kasar gabaɗaya aka karar da shi a wannan hospital ɗin, ta ko’ina haske sosai. A cikin wannan ɗaki gabaɗaya wasu mahaukatan injuna ne wanda zaku zaci factory ne, engines masu karfi, waɗan da suke sarrafa abubuwa, akwai ɗakuna dayawa a cikin wajen wanda ganinsu kawai tashin hankali.Kewaye 3D suke ta faman yi a cikin wannan ɗaki suna duba yadda ake aiki, waɗan nan injuna suna ta faman haɗa chemicals na wannan cuta tasu mai suna Nexapox-31, a wannan waje ake haɗa shi ana zubawa a kwalabe manya-manyan, nan ne matakin karshe kenan, bayan an ɗauko chemicals da su Maya suka haɗa, sai aka ɗauki asalin kwayar cutar da aka ruɓar, to a nan ake gaurayasu, cutar ya yi green sosai da sosai gwanin ban tsoro ma da tada hankali, daga yanayin ruwan cutar idan ka gani kasan wannan bakin zalunci kawai aka haɗa, sai ka ji karjinka ya buga.Komawa 3D suka yi office na Dr James, saboda sun duba cutar, abin da ya kawosu yi kenan. Can cikin meeting room ɗinsu suka shiga, a saman sofas suka zauna, shi kuma Dr James ya miƙe, computer ya buɗe tare da cire mata password, danna wasu lambobi masu zubin na sirri ya yi.Jim kaɗan aka ɗaga kiran nasa, a tinaninsu Dr Kamal zasu ga mutane kamar yadda kowa yake bayyana idan zasu yi waya ta kasuwanci, sai suka ga akasin haka, domin kuwa wani irin duhu ne bakinkirin ya mamaye ko’ina a cikin computer.Rarraba idanunsu suka yi suna jiran ganin haske ya bayyana mutum ya bayyana, sai suka ji shiru, can kuma suka ji wata fasasshiyar murya an ce. “Hello”. Kara zazzaro idanu suka yi, babu dai alamar mutane a wajen. Da suka zuba idanu sosai a saman computer ta gefe sai suka ga an rubuta WORLD SYSTEM, sun sha madarar mamaki, bayan shekaru 3 suna ta jin sunan WS a bakin Dr James sai yau suka taɓa ganin yana waya da su. Sun so ganin fuskokinsu, dan suna zargin kamar ba mutane bane ma, amma sai dai ina, bayan Dr James babu wanda ya sansu a duniya!. Watau su Dr Kamal dik rashin imaninsu sun jinjinawa WS har suke ganin kamar ba mutane bane su ɗin, tab! Babbar magana!!.Daidaita natsuwarsa Dr James ya yi kafin ya amsa masu hello ɗin, sannan ya ce. “Nexapox-31 is ready, ko a wannan sabuwar shekara da zamu shiga zaku iya sakinta wa duniya”……. Shiru aka ɗan yi na a ƙallah 2 mins, can wannan fasasshiyar murya ya sake cewa. “Wa sabuwar gwamnati muka shiryawa, sai bayan zaɓe, me karfin gudun aikinsa? Hope ya fi cututtukan da muka saya a baya?”.With full confidence Dr James ya ce. “Wannan ya fi dik wata cuta da ta bayyana a baya! Wannan tana tafe da su DNA, cuta ce daka iya fata-fata da ɗan adam, wannan cuta idan kana da rabon rayuwa ma ka rayu to zaka rayu ne babu kunnuwan jin magana, dan sai ta yi fata-fata da kai, bugu da ƙari wannan cuta tana ɓoyewa ne a cikin jiki na tsawon sati biyu, sai ta shiga jiki a hankali ta lalata dik wani garkuwar jiki, sannan take bayyana, a lokacin ko ni dana kirkireta yin maganinta zai ban wahala, dan wannan sati biyu da ta yi ta kashe komai na jikin ɗan adam, hakika ban taɓa yin project mai bala’in wahala da karfi irin wannan ba, so ku kwantar da hankalinku, komai zai tafi yadda kuke so”. Shiru aka sake yi na kamar 2 mins, sannan wannan murya ta sake cewa. “Muna son ganin yadda take aiki a jikin mutum, na san ba zaku rasa jarirai a ƙasa ba, ku gwada mana example a kan ɗaya daga cikinsu”…….. Kai Dr James ya jinjina alamar to, daga nan ji kake ɗiff sun katse kiran. Nisawa Dr James ya yi tare da zama kusa da Dr Kamal, a sanyayye ya ce. “Wasu mutane sun kirani jiya, wai suna son babys guda 50 zasu yi sadaukarwa”. Ya faɗa yana ciro wayansa…….. Cike da mamaki Dr Kamal ya ce. “Ban gane sadaukarwa ba?”…… Dr James yana pressing wayarsa ya amsa da. “Kasan yanzu duniya ta cigaba, irinmu masu kyankyasan jarirai mun fara yawaita, abin ya fara girmama a duniya, so yanzu dik jiga-jigan kungiyar matsafa ta duniya sayen jarirai suke yi dan sadaukarwa, sun daina amfani da yaransu na jini, sai dai su saya kawai su je su kaisu”. Dr Mark ya ce. “Na gani last week wai an kama wata mota cike da jarirai zata fita AVARIS, sai maganar ake yi, daga karshe aka gano manyan kungiyoyin tsafi ce ta sai jariran za’a fita da shi a kai masu, a lokacin na yi mamaki, dik tinanina mu kaɗai muke kyankyasan jarirai, ashe an fara samun ilimin a duniya”. Dr Kamal ya ce. “Duniya ta cigaba, matsafa sai sharholiya, kuma zasu karu a duniya, dan dama kasan wasu saboda bada jininsu ne yasa suke tsoron shiga kungiyar, saboda suna jin ba zasu iya bada ƴaƴansu ba shiyasa ba zasu iya shiga ba, amma yanzu lafiya lou, dik manyan kungiyar tsafi yanzu sayen jarirai suke yi”…….. Dr James ya ce. “Ba kowacce kungiyar tsafi take da karfin sayen jariran ba ai, kun sani ba ƙananan kuɗi bane, sai manyan jiga-jigan ƙungiyoyin da suka haɗa ƙasashe waɗan da manya a duniya ke ciki sune suke da karfin sayen jarirai, ko last year babys guda 50 da na cire a yaran da muka kyankyasa wani shahararren kungiyar matsafa na sayarwa”. Dr Mark ya ce. “Haka ne sai manyan kungiyoyi, dan har yanzu ina ga akwai kungiyoyi masu bada jininsu ko in ce ahalinsu ga tsafi, har yanzu cigaba bai zo masu cewa saye kawai zasu yi ba, su zuba kuɗi su samu kuɗi”……… Wani shu’umin one side smiling Dr James ya saki kafin ya ce. “Zamu ɗaga farashin kowa jariri this coming year, daga miliyan 100 zuwa 150, saboda naga yanzu dik sun fara wayewa, kowa baya son wani abin ya samu zuri’arsa, sai dai su saya jarirai, dan haka zamu ƙara masu kuɗi sosai, dan ai kungiyar tsafi akwai makudan kuɗaɗen jini na fitar hankali, dan haka dole mu kara, kai Dr Kamal nabaka nan da one month ka tabbatar ka kawo mana mahaifa guda 500, dik yadda za’ayi ma ayi, idan kashe mata za’ana yi ana cirewa, idan satowa za’ana yi ba tare da saninsu ba, kai koma me za’ayi masu ayi, mu dai mahaifa muke da buƙata!!”. Jinjina kai Dr Kamal ya yi, a dake ya amsa da. “Yazama dole mu samo, amma eggs da muke da su a ƙasa ai basu wuci 200 ba, yakamata mu samu wasu”……. Kai Dr James ya jinjina kafin ya ce. “Tin kwanaki uku da suka wuce na sanya aka yi wa ƴan matan da muke da su dikka alluran gonadotropins wasu kuma follitropin alfa gonal-f, a wannan wata zasu bamu eggs da dama, dan na tsokani ovaries na jikinsu sosai, zasu bada abin da ake so matuƙa.Dr Kamal ne ya ce. “Waɗan nan allurorin basu yi wa jikin mace yawa ba kuwa? Kada ya lalata masu jinin jiki gaba mu rasa daga in da zamu na samun eggs ɗin”…….. Ba tare da shayi ko ɗar bare tausayi ba Dr James ya ce. “Dole zai lalata dik wani kuzari nasu, zai gurɓata jinin jikinsu gaba kaɗan, kowani wata sai an yi masu shi, sai an tsokani ovaries ɗinsu sun fitar da abin da bashi suke fitarwa ba, su fitar da overdose, ai kunsan dole ya lalata masu jiki, amma ba yanzu bane, zasu iya ƙara shekaru 5 gaba suna bamu eggs, daga nan ovaries ɗinsu zai raunata, ya daina ma bada eggs ɗin gabaɗaya, a wannan lokacin amfaninsu ya ƙare, sai dikkansu mu kashesu at once”. Babu ɗigon imani a kan fuskansa ya faɗi wannan magana, mata rai 50 kake lissafin wannan allura zai lalatawa rayuwa, baka ji komai a ranka ba, har kake lissafin zaku kashesu gabaɗaya idan suka daina maku amfani suka daina baku abin da kuke buƙata. Already yasa an fara renon wasu matan a wani killataccen waje tin shekaru 5 baya, ba tare da saninsu Dr Kamal ba yasa ake renon yaran wasa idan waɗan nan sun lakace sun daina bashi eggs ya kashesu to ga wasu nan ya kyankyasa ana renonsu sai ya maye gurbi, shegen plan ne da shi.Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, wannan musifa dame tai kama, ran ɗan adam tamkar ran kiyashi, ba’a ɗauki mutum a bakin komai ba, ko da yake tin da ka iya kwantar da ƙananan yara, ka buɗe gabansu ka saka masu wannan karfe ka ciri eggs ɗinsu a can cikin cikinsu ai babu abin da ba zaka iya ba bakin shaiɗani, yadda ake cire eggs na mace ya tsaya mun a rai ni kam, ƴan matan dake virgin, basu san komai ba, ba’a taɓa buɗe wannan hanya ba, da yake kai ƙanin ifiritu ne, tsinanne, haka kake danna masu wannan karfe a ciki, dan kawai biyan buƙatarka, ai kai mutuwarka ba zata yi kyau ba, wlh 3D bala’i ne, ni ban taɓa jin kalar wannan rashin imani! Ba gara ma ace zina suke yi da yaran ba ma da ɗan sauki, amma kowani watan duniya ku kwantar da yara ku danna masu karfe a cikin ciki, ku wuce mahaifarsu har ku je kan ovaries ɗinsu, ku buɗe jakar da eggs ke ciki ku tura wannan karfe, ko wani iri baku ji a ranku, saboda kun yi hannun riga da tausayi da imani, ba sauɗaya ba ba sau biyu ba, dan bala’i kullum wata sai kun masu wannan abu, ga uban alluran da kuke kashe masu jiki da shi, dan wannan alluran lalatasu zai yi gaba kaɗan, ai kuna masu shi overdose, yana da side effects, yadda kuka san engine buga eggs suka samu ba mutane ba, shegu tsinannu makiya ALLAH da Manzonsa, hmmmm zaku girbi abin da kuke shukawa ne dan ubanku. Astagfirullah, 3D sun ɓatan rai sun sakani zagi shegu!Sun jima suna tattaunawa wanda ni takaicinsu ba zai barni in cigaba da kawo maku labarin abin da suke tattaunawa ba, daga karshe Dr James ya ce. “Zo ka mun video dan turawa WS shaidar aikin maganin nan, zo ka ɗaukeni bari mu yi gwaji a kan ɗaya daga cikin jariran nan mu gani”. Na shiga uku ni QUEEN OF SURPRISE, a kan jariran ma zasu yi gwajin cutar dan bala’i? Wannan wace iriyar musifa ce? Tamkar babu zuciya a kirjinsu fa!.Da okey suka amsa mashi, ya wuce gaba bayan ya miƙawa Dr Kamal wayansa, bayansa suka bi, wancan ɗakin da ake haɗa magungunar suka koma, jim kaɗan suka fito hannun Dr James rike da wata sirinjin allura da kuma ruwan maganin.Kai tsaye SECTION D suka nufa, dik in da suka wuce sai nurses sun zube ƙasa sun kwashi gaisuwa. Basu amsa kowa ba har suka shiga cikin ɗakin da su sister Zinta suke. Su Maya na ganinsu suka zube ƙasa dan kwasan gaisuwa. Wucewa ciki Dr James ya yi, ya fara bin yaran yana dubawa ya ga wanne yakamata ya ɗauka dan ayiwa gwajin alluran nan?. Daidai lokacin darling dake hannun sister Maya ya fara kuka, miƙewa tsaye da shi ta yi, ta fara jijjigasa tana shafa bayansa, ta saɓashi a saman shoulder ɗinta. Ɗago kai Dr James ya yi, zubawa babyn idanu ya ɗan yi, can kuma ya nisa tare da cewa Maya. “Bani shi a nan”…….. Bata kawo komai a ranta ba, ta yi sauri ta miƙa mashi shi. Karɓarsa ya yi tare da cewa Dr Mark. “Jawo mun bed ɗinsa nan”. Ya faɗa tare da fitowa gaban ɗakin.Sister Zinta dake zaune ne ta miƙe tsaye, idanunta na ɗan rawa a kan sirinjin alluran dake hannun Dr James, mamaki ya ɗan kamata. Jawo gadon baby Dr Mark ya yi, a kansa Dr James ya kwantar da babyn, ya gyara cinyarsa zai fara yi mashi allura kenan muryan sister Zinta ya dakatar da shi. “I’m sorry sir, wannan injection ɗin fa?”. Slowly ya ɗago da kallonsa a kanta, sai ya tina irin abin da yai mata last time, ba ya ce ta zo yana nemanta ba in baku manta ba, to hidiman babys yasa bata samu damar zuwa da wuri ba, shi kuma shegen zuciyar bala’i, tana zuwa ya koreta wai ta ƙara mintuna goma kan wanda ya ce, yana sonta fa, yana son faɗa mata abin dake ransa, sonta kamar ya kashesa, amma guy ɗin nan sai girman kan bala’i, haka ya koreta, tana bashi hakuri ya daka mata tsawar da ya sanyata fita da gudu tana fashewa da kuka, to tin daga wannan rana bai sake ɗaga ido ya ganta ba sai yau, tsabar iskancinsa mai lasisi ne.”Magani ne”. Ya faɗa a taƙaice.Dik da bata da ilimi ta fannin aikin 3D, amma a nata fannin ta gano wannan ruwan ba magani bane wlh, akwai sinadarin venomous spur toxin da nematocyst stored venom a ciki, wanda kuma venomous spur toxin tasan lalata jiki yake yi, yana kone fata, shi kuma nematocyst stored venom kumburin jiki yake, ya haifar da kuraje, ko yaya za’a kwaɓa sinadarai a irin kwarewarsu ita da Maya confirm zasu iya tantance wasu irin sinadarai ne a wajen, kada ku manta dik sinadaran da ake kawo masu a SECTION C ɗinsu sai sun tacesa sun cire mai karfi daga ciki, kunga kuwa dik wanda zai san wasu sinadarai a wannan hospital ɗin to ya biyo bayansu ne!.Bata yarda da hakan ba, jikinta na kerma, fuskarta cike da tashin hankali, dik da tsananin tsoron 3D da suke yi hakan bai hanata ce mashi. “Wannan ba magani bane,wannan ai cuta ce!”. Muryanta na rawa sosai ta faɗa……… Ai a miliyan Dr Kamal ya ɗago da idanunsa yai mata kallon ƙasan ido, sai kuma ya saci kallon Dr James da ko gezau bai yi ba. A karon farko yau an samu wacce ta ce da 3D wani abu a kan aikinsu.Kama kafan baby ya yi wajen cinya da nufin ya tsira mashi alluran. Ai sister Zinta bata san lokacin da ta damke hannun nasa dake rike da sirinjin ba, jikinta na tsananta kerma, idanunta cike tab da kwallah ta ce. “Ka duba da kyau, wannan cuta ce ba magani ba, ka bincika da…….”. Bata iya karisa maganar ba ta haɗiye saura sakamakon ɗago da eyes ɗinsa slowly da ya yi a kanta, a razane ta sake mashi hannu tare da ja da baya, hawayen da take ƙoƙarin rikewa ne suka fara zubo mata, bata san meyasa take kukan ba, bata san meyasa hankalinta ya tashi a kan wannan allura ba, tana jin wannan baby tamkar jininta ne, meyasa bata damu da sauran jariran ba sai wannan kawai? And meyasa kuma su 3D basu sakawa kowani jariri ido ba sai wannan darling ɗin Maya ɗin? Sun yi scanning na brain ɗinsa, bai ishesu ba, suka sake ɗeban jininsa, dik bai ishesu ba, yanzu kuma sai sun sake yi mashi wannan alluran? For what reason? Meyasa dik suka rikice suka tashi hankalinsu a kan jaririn da satinsa 3 kawai a duniya? Meyasa? Wannan shi ne tambayar dake cikin kwakwalwar sister Zinta. Ita kuwa Maya tambayar kanta take yi kan wai ina iyayen jariran nan dikka suke? 55 babys, kuma dikka babys ɗin 3 weeks suke da shi a duniya! Which is mean dikka rana ɗaya aka haifesu! Suna kama sosai, kenan uwa ɗaya ce ta haifesu? How? Meyasa ake basu madara ba nonon uwa ba? Meyasa su da suke matsayin nurses su suke masu wanka ba iyayensu ba? Kai abin da rikitarwa! Babban damuwarta ma a nan shi ne yadda yaran suke kamanceceniya, sai kuga babys 5 kamanninsu ɗaya kamar an tsaga kara, to ya haka? Wannan kamannin da suke da juna ya fi komai ɗaure mata kai.Jama’a idan baku manta ba a jikin kowacce mace suna cire eggs sama da goma ba? Kunga kuwa dole za’a samu kamanceceniya tsakanin babys ɗin, dan wasu uwarsu ɗaya ne! Sannan ita sister Maya ai ita kanta ce abin mamaki ko ya kuka ce? Bata taɓa mamakin yadda aka yi dikka nurses na hospital ɗin suke da 18 years a duniya ba, bata taɓa mamakin yadda suke kamanceceniya ba suma, bata taɓa tambayar ina iyayenta ba, dik bata yi wannan ba sai a kan babys ɗin nan saboda ita mayyan son yara ne ba!.Suna ji suna gani Dr James ya danawa darling wannan allura a jefen cinyarsa. A ƙasa da second 3 wannan kwayar cuta ta yawace jinin jikin jaririn nan.Lokaci guda wani irin jijjiga jaririn nan ya fara yi, gabaɗaya bakinsa ya gagara buɗuwa ya yi kuka, amma daga gefe-gefen kunnensa wasu hawaye ne masu ɗumin gaske suke zuba, kafafu da hannayensa dik wani irin kerma suke yi tamkar yana jin sanyi. Kallon Dr Mark Dr James ya yi kafin ya ce. “Dr yana aikin sosai, duba yadda jikin jaririn ya koma green sosai lokaci guda, lallai wannan abin zai yi yadda ake son ya yi wa duniya sosai, ban ƙara tabbatarwa ba sai yanzu dana ga zahiri, lallai na yabawa kaina ni da kaina!!”. Ya faɗa yana mai da kallonsa a kan jaririn da gabaɗaya a yanzu jikinsa ta saki, ba kuma mutuwa ya yi ba, ya koma ne babu abin dake motsi a jikinsa face idanu, hawayen dake zuba daga idanunsa sun dakata cak alamar azaban ta ninku kan wanda yake ciki, na tabbata da yana da baki zai ce gara mashi mutuwa a kan wannan gwajin da suke yi a jikinsa. Gyara hand gloves na hannunsa Dr James ya yi tare da kama kafan jaririn yana ganin tafin kafafunsa na yadda tsantsar jijiyoyin jininsa suka bayyana ruɗu-ruɗu saboda karɓar bakon abin da ya shigo cikin jinin da ya yi, skin ɗinsa ya koma green sosai kafin daga bisani ya fara komawa yadda yake, kana iya ganin yadda jini ke gudana a jikinsa, jijiyoyinsa suna harbawa alamar bakon abin da ya ratsa jininsa yanzu kamar ya fi karfin jinin jikin nasa. INNALILLAHI WA INNA ILAHIR RAJIUN, KUMA WLH DA RANSA BAI MUTU BA, HASBUNALLAHU WANI’IMAL WAKIL! Kada ku manta fa cewa suka yi a jikin nama zasu sanya wannan cuta, wanda ya ci wannan nama zai kamu da cutar, to imagine, shi wannan jariri kai tsaye aka danƙara mashi cutar a jiki, ba a jikin wani abu ya ci ba, sinadarin zallar cutar aka zuba a jininsa, ya rab, ya rahman, ya rahim, ya malik, ya kuddus, ya salam, ya mumin, ya muaimin, ya aziz ka kawo mana ɗauki a wannan duniya da muke ciki, duniya mai cike da ruɗani da tashin hankali game da zallar rashin imani, ka rasa a ina zaka yi gwajin sai a jikin jaririn da bai ji ba bai gani ba, bai san komai ba, ya ALLAH! 3D ina zaku kai hakkin waɗan nan jariran? Dik wani jariri da kuka kyankyasa in ma kun sayar ko kun kashe ku sani hakkinsu na kanku, in kuka sayar da su aka je aka yi abin da bai dace da su ba wlh jininsu ya rataya a wuyanku ne azzaluman banza tsinannu!!!.After kamar 5 mins da cutan ya gama yawo a cikin jinin baby sai me? Take yaron ya koma yadda yake, dama jijjigar shigar kwayar cutar jikinsa ne ta rikita shi, da ya shiga ya saje da jininsa kuma sai ya dawo daidai, cutar ta fara aiki a jininsa, sai nan da sati biyu zasu ga result, darling zai mutu ko kuwa?. Ya ALLAH.Tin da yai mashi wannan alluran sister Zinta and sister Maya jikinsu ya hau tsuma, yana wani irin kerma, sister Maya idanu ya cika tab da kwallah, idanunta a kan yaron. Ana gama mashi alluran ta matso da sauri zata ɗaukesa Dr Kamal ya rike hannunta. Da sauri ta juyo da kallonta a kansa, tsaida video ɗin da yake ɗaukar babyn tin shigowarsu yai tare da tura wayar aljihu bayan ya yi saving. Daidai lokacin ta juyo da kallonta a kan Dr Kamal, wani irin zafafan hawaye ta ji ya fara bin ƙuncinta. Tana son zuwa ta ɗauki babyn amma ya hanata, ganin ta fashe da kuka ne yasa ya jawota jikinsa, a lokacin ta samu damar sakin wani irin marayan kukan da ba san dalili ba. Da gudu sister Zinta ma ta yi kan baby tana son ɗaukarsa. Ajiye sirinjin hannunsa Dr James ya yi tare da cire hand gloves na hannunsa, ya miƙa hannu ya riko sister Zinta, tin da ta ga yadda babyn nan ya yi bayan an mashi wannan alluran ta kara gasgata cewa cuta aka zuba mashi. Kada ku manta dikkansu kullum suna sanye da doctors nose mask.Da sauri Dr James ya ce. “Dr Mark fita da babyn nan zuwa sashe na musamman dan killacesa”. In baku manta ba cutar tana yaɗuwa ne, ba zai yiwu a barshi cikin sauran babys har 2 weeks ya kawo result ɗinsa ba, dole a killacesa. Jan gadon nasa Dr Mark ya yi, har lokacin babyn na kwance shiru bai motsa ba, kamar wanda akai wa alluran natsuwa fa, ALLAH sarki yana jin bakon yanayi ne a jikinsa, jininsa na karɓar sabon abu, shiyasa ya natsu shiru, ya gagara ganewa jikinsa bawan ALLAH.Ihu sister Zinta ta fashe da shi tana ƙoƙarin kwace kanta daga hannun Dr James tana faɗin. “Babyn nan zai iya mutuwa, ku duba jikinsa, ku yi hakuri ku bari mu ceci rayuwansa, mutuwa zai yi, wannan cuta kuka saka mashi ba magani ba, ni ku barni zan taimaka mashi, ku sakeni, wayyo sister Maya darling ɗinmu, ni ku sakeni, zan iya taimaka mashi”. Tana magana tana ƙoƙarin kwace kanta daga rikon da yai mata, dik ta kiɗime ta fita hayyacinya.Dikka sauran nurses dake ɗakin ko kaɗan basu damu ba, dan su an sha gwada cuta a gabansu a kan jariri, sau nawa suna gwada cutuka a jikin jariran? A gaban idanunsu ma an sha scanning na kwakwalwar jariri, idan yai masu abin da suke so, suna mashi tiyata ne, wani yaron su saka mashi wani abin a kwakwalwar wanda alƙalamina ne kawai yasan menene ake saka masu a kwakwalwar kuma shi kaɗai zai warware maku a gaba, wani jaririn kuma idan sun gwada shi cire kwakwalwar nasa suke yi gabaɗaya, babu abin da basa yi wa jarirai, su sister Maya ne sabbin baki a SECTION D, shiyasa zasu damu, amma nan da shekara kaɗan zasu daina damuwa su ma!…………😭Jawota jikinsa Dr James ya yi, ya rungumeta sosai, hakan yasa dik sauran nurses ɗin suka ɗauke kallonsu daga kansu. Jikinta sai wani irin kerma yake yi, musamman Sister Maya da ta gama sarewa, ta gama saddakarwa mutuwa jaririn nan zai yi, idan ta rufe ido sai ta ga idanunsa yana zazzarosu lokacin da alluran ta ratsa jininsa, wannan ya fi komai tsaya mata a rai. Ganin yadda jikin Zinta yake kerma sosai ne yasa Dr James rage tsawonsa, ya ɗauketa cak yai waje da ita. A wani ɗaki kusa da na babys ɗin ya sauketa tare da riko hannayenta. Durkushewa ƙasa a wajen ta yi, wani irin kuka mai karfi ne ya kwace mata, a ranta tana jin idan suka barta zata je ta ceci yaron, kuma tana ganin kamar zata iya bashi maganin cutar, dan tasan chemicals, amma ina sun tafi da shi in da babu wanda ya sani, a can zai rayu na tsawon sati biyu, sai cutar ta gama game jikinsa, ta lalata shi, da wuya ma ya kai sati biyun, dan shi kunga kai tsaye aka danna mashi cutar ba daga jikin nama ko wani abin ya samu ba. Tsugunnawa a gabanta Dr James ya yi tare da riko hannayenta a cikin nasa, ɗago fuskarta da ya yi jaga-jaga da hawaye ta yi, ta kallesa kafin ta ce. “Sir please ka bari in je wajen babyn, mutuwa zai yi!”. “Is okay, ba zai mutu ba, wani gwaji muke yi, zamu dawo maki da shi a raye kin ji?”. In a low way sosai ya faɗa. Soyayyarta na kara ratsa mashi zuciya sosai……….. Da yake sun yarda da 3D sosai sai ta ce. “To yaushe zaku dawo da shi?”…….. Zubawa kyakkyawan fuskanta idanu ya yi, a sanyaye ya ce. “Kwanaki biyu kawai, wani magani muke nema na wata cuta dake ƙoƙarin shigo mana, to muna kokarin haɗa wannan maganin ne mu ka ce bari mu gwada a jikinsa, amma babu abin da zai same shi, so be patient”. Ta ji daɗin kalamansa, kuma ta yarda da shi, dan haka sai ta dakatar da kukanta, tana shessheƙa ta yi ƙasa da kai kamar mai tinanin wani abu. Hannunta ɗaya ya saki tare da riko haɓarta, ya ɗago suna kallon juna, in a cool way ya ce. “Smile, babynku zai dawo, naga kuna son babyn sosai, kaman ɗanki ko?”…… Munafuki yasan meyasa suke son yaron, domin yaron jinin IRON FIST ne, in baku manta ba su Maya ɗin ma ai kannen Lion ne ko? Kunga kuwa ai wannan baby jininsu ne, ba banza ba suke son shi.Ƙasa da idanunta ta yi, tana ɗan ɓoye fuska saboda kunyar ganin idanunsa take yi, cikin muryan kuka ta ce. “E muna son babyn sosai, yana da kyau sosai, ina jinsa har cikin raina”…… Kara ɗago haɓarta sosai ya yi, still taki ɗago idanu ta kalli nasa idon…….. “To kada ki damu very soon zaki samu naki babyn, kina so ko?”. Da sauri ta gyaɗa mashi kai, sai kuma ta ce. “Ko na samu nawa babyn zan rike darling, ina son shi sosai”. …….. A cikin zuciyansa ya ce thank God da tinanin yi wa yaron alluran cutar ta zo kansa, ba dan haka ba wannan yaro zai kawo mashi matsala, yanzu zai mutu kowa ya huta, ka ji yarinya wai tana son gwada mashi ta fi son darling a kan ɗan da zata haifa mashi, tab ashe gara da ya ɗauko hanyar kashe yaron kowa ma ya huta.Jin ya yi shiru ne yasa ta ce. “Yaushe zan haifi nawa babyn?”……. Ɗago idanunsa a kan face ɗinta da kyau ya yi, ya kurawa kyakkyawan fuskan nata idanu, can ya ɗan nisa kafin ya ce. “Idan mun tashi aiki ki sameni a office, yau ma ki ɓata mun lokaci”. Ya kare maganar cikin alamar gatse……. Da sauri ta ce. “Ba zan ɓata maka ba”. Sake haɓarta ya yi tare da miƙewa ya nufi waje, da sauri ta miƙe ta biyo bayansa, ɗakin jariran suka komo.A nan ya isko su Dr Kamal ma sun rarrashi Maya, tana zaune shiru, Zinta na shigowa ta je ta rungumeta tana faɗin. “Ke Sir James ya ce babu abin da zai samu darling ɗinmu, wai maganin cuta suke gwadawa, zai dawo lafiya lou”. Cike da farinciki sister Maya ta amsa da. “E haka sir Kamal ya faɗa mun, na ji daɗi”..Kallon juna Dr James and Dr Kamal suka yi kafin su juya su bi bayan Dr Mark, su kaɗai suka san me a cikin ransu shegu, sun san wannan babyn kam ya tafi kenan, sai dai wani! Amma sun kwaɗaitawa yara wai zasu dawo da shi, harda wani wai maganin cuta suke gwadawa, waɗan nan shegu akwai makiran mutane!.Suna fita suka je in da Dr Mark ya killace babyn nan, har lokacin yana kwance shiru, guard ɗaya suka sanya ya yi gadin yaron, daga nan suka fita suka koma office ɗinsu, Dr James ya karɓi wayansa, ya turawa WS video ɗin da suka yi wa yaron a lokacin da suke mashi alluran, ya ce nan da 10 days zasu samu result ɗinsu. Hakika sun yabawa wannan cuta, dan tin daga kan yadda jaririn nan ya yi wani irin jijjiga zaka san ba ƙaramin cuta bace, abin ya ratsa jininsa kuma ya fi karfin jininsa, sun yabawa Dr James sosai, sai suka ce zasu tura kafun alƙalami dala miliyan 100 yanzu, idan suka ga result zasu cike saura, dan dala miliyan 500 suka sayi cutar kawai ban da maganinta, shi ma maganin ciniki daban zasu yi.Ai ba ƙaramin kuɗi suke samu a kirkirar cuta ba, su kansu WS da suka sayi cutar ba karamar riba zasu ci ba, a kan maganin zasu fanshe kuɗinsu. Hmmmm ALLAH yasa shiruna ya zame mun alkhairi, bari in ɗan yi shiru, gaba da kallo, dan in na buɗi baki a gaba hmmmmm!. ————————-🔥CRYSTAL PALACE.A daddafe Seraphina ta yi barci yau, da kyar da suɗin goshi saboda rashin jin a wani hali daddynta yake ciki, washegari ta shirya tsab, sai dai har 8 ya cika Aryan bai zo ba, ta kira numbersa ya fi sau dubu, amma bata shiga. Haka ta tafi school da kafa da yake basu da nisa, amma har kuka sai da ta yi, bata saba tafiyar kafa ba, sai da ta shari 20 mins a tafiyar 5, tana tafiya a hankali tana ruwan hawaye. Wani waje ma ta samu ta zauna, Aisha nata rarrashinta dik da bata san me takewa kuka ba, amma taki yin shiru. Sai da suka fi 10 mins a zaune kafin ta miƙe suka cigaba da tafiya.Sun kusa isa school daga bayansu suka ki ana masu horn, juyawa suka yi a tare, nan suka ga uncle ne, kashe motar ya yi, ya fito da sauri. Sai ga shi a gaban Seraphina, cike da kulawa ya ce. “Good morning baby flower”. Cikin salo mai ɗaukar hankali ya faɗa. Sai kuma ya ce. “Oh God, meyasame kika yi kuka haka?”.Tamkar jira take yi a tambayeta, haba kuka ta fashe da shi har da shessheƙa. Kallon Aisha yai. “What happened to her?”……. “I don’t know, tin da muka fito take kuka”. Dawo da kallonsa a kanta ya yi, hannunta ya riko tare da janta zuwa wajen motarsa, ya sanyata ciki kafin ya tada motar sai da ya tabbatar ya rarrasheta, ita dai Aisha sai kallonsu take yi, ya ɗauko wani heart design cushion mai balain kyau white color ya damƙa mata a hannu, sannan ya ɗauko chocolate ya damƙa mata shi ba. Ba shi ya tada motar nan ba sai da ya tabbatar da ta yi murmushi, sannan ya tada suka ƙarisa cikin school.Shi kuwa Aryan a wannan lokaci yana zaune a tsakiyar gadon Lion yana danna wayansa, ya sauƙe numbersa dake na family, yana chantting ne da handsome VIR namu, korean guy mai capacity. Tambayansa ya karfin jiki Vir yake yi, dan jiya Lion ya faɗa mashi Aryan baya jin daɗi.Baki ɗauke da sallama ƙasa-ƙasa Lion ya shigo cikin room ɗin, hero na biye da shi a baya yana wani takun ƙasaita, da alama sun shirya. Sanye Lion yake da hoodie fara kal a jikinsa, ya ɗaure kitson kansa a baya, hannunsa rike da laptop ɗinsa. A gefen Aryan ya zauna tare da ajiye laptop ɗin a saman gadon. Slowly Aryan ya ɗago idanu kai tsaye sai kan dara-daran eyes ɗin Vir ta cikin laptop ɗin Lion. Zazzaro mashi ido Aryan ya yi cike da mamaki, kuma fa chatting suke yi, watau ashe yana chatting da shi, shi kuma yana video call da Lion.Kashe mashi ido ɗaya Vir ya yi, yana zaune gaban wani tabkeken swimming pool mai shaƙe da ruwa game da green light da ya sanya ruwan rikiɗa izuwa green mai ɗaukar hankali, hakika filin ya matuƙar haɗuwa, babu riga a jikinsa, hakan yasa kyakkyawar kakkarfan korean gorgeous body ɗinsa a waje, gashin kansa a kwance luff, ga wani haɗaɗɗen americano a gefensa cikin glass cup yana sipping.Ya kashewa Aryan ido ɗaya kafin ya ce. “Meyake damunka likita bokan turai?”…….. Harara Aryan ya dallah mashi kafin ya amsa da. “Ban faɗa maka ta chat bane?”…….. “Chat daban ganin ido daban, yanzu faɗa mun, amsa mun tambaya dan yanzu nine likita kai patient”. Gyarawa Lion ya yi ya kwanta yana kallonsu, a daidai lokacin guru ya fito daga toilet sanye da robe fara kal a jikinsa, yana rike da wata ƙaramar towel yana goge hair ɗinsa da ba zan kama maku kalarta ba, saboda bana son ku san waye guru yanzu, nasan ina faɗar suffarsa kaɗan zaku iya gano wanene.Zuba mashi idanu Lion ya yi yana karewa dik wani motsinsa kallo, dik ɗagowar da zai yi sai sun haɗa ido, hakan yasa guru ya ce. “Kallon fa?”. Hararansa Lion ya yi ba tare da ya yi magana ba……. “Zan je Nigeria gobe watakila”. Guru ya sake faɗe idanunsa a kan Lion……. Wani irin mugun kallo Lion ya dallah mashi kafin ya amsa da. “Babu in da zaka je!”. Karin haske, guru mahaifinsa ɗan Nigeria ne cikakke, ɗan Nigeria ɗin ma ɗan arewa, arewan ma Hausa Fulani ne babansa, mahaifiyarsa ce kuma ƴar wata ƙabila can na je na zaƙulo maku wacce labari zai zo ku ji tarihinta, dan bakaramin power suke da shi ba a wannan littafi, kun san ba zan taɓa yin tuya in manta albasa ba, ba yadda za’ayi ace Nigeria bata da power kaso 60 zuwa 80 cikin ɗari a littafin nan. Karin wani haske ZAKUNA BIYAR littafi ne da ya shafi duniya ba Nigeria kawai ba! Dan haka ZAKUNA BIYAR da ake ta nema sun kasance ne daga yankuna daban-daban suka haɗu dan gyara duniya!.Akwai jinin Nigeria tamu ta gargajiya, sai na leƙa korea na ɗauko maku mutum guda, na sake rugawa da gudu na tafi cikin ƙuraishawa watau arabs na sake ɗauko maku ɗaya, sai cikin European suma na ɗauko maku ɗaya, na last ɗin kuma jinin Avaris ne. So kada ku damu da lallai sai kun zaƙulo FIVE LIONS kun haɗasu sun cika biyar ɗin ciff, kada ku damu a hankali zasu haɗa kansu su kuma bayyana maku kansu, dan haka kada ku sanyawa kwakwalwarku pressure, na hutassheku! Dan naga wasu sun damu suna son sanin ZAKUNA BIYAR to ku kwantar da hankulanku………🙌🏻Da sabon salon ZAKUNA BIYAR yake tafe, haƙiƙa ZAKUNAN ne guda BIYAR, amma daga yankuna daban-daban na duniya na zaƙulo maku su, ku more karatu, sai ma mun natsa cikin STEP 2, zaku ci karo da surprise!.Vir ne ya amsa da. “Nigeria kuma ana zaune ƙalau?”……. Guru dake faman shiga wajen closet ɗinsu ne amsa da. “I miss mai Grandpa”……. Aryan ne ya ce. “Babu in da zaka je”…… Hararan Aryan ya yi kafin ya shige cikin wajen cleset ɗin nasu. Aryan ne ya ce. “Miss you more bro”. Ya faɗa yana kallon Vir. Ɗan sipping americanonsa Vir ya yi kafin ya amsa da. “Today remain 53 days in dawo ai”…… Lion ne ya katsesu da cewa. “Muna da aiki a gabanmu, let’s meet in our room”. Ya kai karshe tare da ɗaukar laptop ɗin, ya sauƙo ƙasan bed ɗin, Aryan ne ya rufa mashi baya kafin hero ya biyo bayansu. Kai tsaye ɗakin aikinsu suka nufa, a saman table kusa da Computers ɗinsu Lion ya ajiye laptop ɗin, ya saita yadda Vir zai ga aikins da kyau, sannan suka shiga aiki game da fara tattaunawa.Aryan ne ya fara buɗe saƙon Lion kan Avaris, dogon note ya tura masu a laptop ɗinsu kan yanayin rashin tsaron dake arewacin Avaris da ya jima yana haɗa bayanai da hujjoji a kansu.Duba saƙon Aryan ya fara yi, a daidai lokacin guru ya shigo, ya gama shirinsa cikin pj’s milk color, gaban nasa computer ya zauna tare da kunnata,



