Hausa novels

Zakuna Biyar Page 14 By Princess Teema

“Ina son ka kaini asibiti anjuma a duba mun karafunan dake kafata ɗin nan, dan na fara jin canji”. Abba ya faɗa ba wai dan hakan ya so faɗa ba, so yake yi ya taushesa ya ce ya rage tsanar Rimsha, amma kwarjinin ɗan nasa yasa ya canza maganar………. “Okey Abba”…. A gaggauce cikin girmamawa su Harleen suka ɗaga mashi gaisuwa, mugun tsoronsa kowa yake ji, basa wasa da abin da ya shafesa, dan yana nan kullum fuska a haɗe kamar hadari, ɗan banzan kuma ga shegen kyau mai tsananin shiga rai, in ka gansa sai ka sake kallo, musamman idan ya motsa ɗan bakin nan zai yi magana wasu dimple a both sides na soft kumatunsa suka lotsa, sai ka kallesu ka sake kallo, ka ji tamkar kada ya daina magana, ga bala’in daɗin murya sai rashin mutunci cike da cikinsa, maganar ma sai ya yi ra’ayi yake yi ƙasa-ƙasa dan bala’i, idan ka ji ruwanka, in ma baka ji ba kai ka sani, shi dai baya maimaita magana, kuma dole ayi abin da ya umarta ko an ji ko ba aji ba.Da fine ya amsawa su Harleen ciki-ciki. Ya faɗa tare da yunkurawa ya miƙe, Abba na son yi mashi magana amma yana shakkarsa, har ya haye sama tsakaninsu Harleen zuwa Abba babu wanda ya sake yi mashi magana.Kai tsaye ɗakin Ammie Aryan ya nufa. Yana haurowa staircase suka ci karo da Vash dake ƙoƙarin sauƙowa. Ai take Vash ya natsu sosai ya haɗe malaman jikinsa game da dawowa taitayinsa, cikin ladabi da girmamawa ya ɗaga mashi gaisuwa, kallo ɗaya Aryan yai mashi tare da wucewa yana amsawa da kalma ɗaya watau lafiya, daga nan bai sake magana ba har ya isa kofar ɗakin Ammie. Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga, tana zaune a saman wata haɗaɗɗiyar shinfiɗa na Dubai rug da yake da laushi kamar kushi. A gabanta ya zauna tare da ɗaga mata gaisuwa. Rufe littafin dake hannunta ta yi, hisnul Muslim take karantawa dama. Tana cikin arabian dress farare kal, ta yi rolling veil a kanta, ta yi kyau sosai ƴar dattijuwar, kuma kana ganinta kaga bakuraishiya, dan su kyansu na daban ne kuraishawa ba, tushen fiyayyen halitta kenan, to bama dole su Aryan su yi kyau ba, jinin kuraishawa ake magana fa!.”Good morning Ammie”. Ya faɗa yana riko hannunta……. Fuskanta babu alamar fara’a ko kaɗan ta amsa da. “Morning my son, how was your night?”……. “Cool and what of you?”. Ya amsa da shi da kyar tamkar wanda aka yi wa dole……. Shiru ta ɗan yi kafin kuma ta sake amsawa da. “Ina zaka je na ganka a haka?”……… Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da. “Meeting with some doctors that visited my hospital yesterday, i don’t have time yesterday bcos of that passing out, so yau zamu yi zama da su”. Ya faɗa yana gyara nose mask na fuskansa.”Ga shi ina son ka kai Rimsha ta yi shopping na school tin da an kusa buɗewa”. Ta faɗa cike da fargabar abin, dan tasan ba ƙaramin wuta ta kunna ba, dan dai ma ita uwa ce, dik iskancin Aryan baya mata, sai dai ya yi shiru kawai idan ta faɗi abin da bai mashi ba…… Yanzun ma dai shirun ya yi, amma kana ganin face ɗinsa zaka san lallai ko kaɗan bai ji daɗin maganar Ammie ba, wai ya kai Rimsha shopping, ya yi nadamar zuwa gaida ita da ya yi ma dik da ba fa zai kai Rimsha ɗin ba.Jin bai amsa bane yasa ta ce. “Aryan, sai yaushe zaka daina nuna tsana ga yarinyar nan ma rainiyar ALLAH ne? Ka manta cewa ba laifinta bane? Ka manta cewa kai ƙanin mahaifinta ne da bata da biyunka? Ka manta yadda mahaifinta yake kaunarka? Ka manta yadda kuka shaƙu da shi? Ka manta yadda tin tana ciki mahaifinta yake kaunarta? Meyasa ba zaka maye gurbin kaunar da mahaifinta ya nuna mata a ciki kai ka nuna mata a zahiri ba?”……. Yunkurawa ya yi zai miƙe ba tare da ya yi magana ba, ya dunkule hannunsa ya zura a aljihu gudun kada ya kai naushi, ba dan Ammie ce ta yi wannan magana ba da hmmmm a dai yi shiru kawai.Da sauri Ammie ta riko ɗayan hannunsa, slowly ya ɗago ido suka kalli juna, kara ɗaure fuska tamau ya yi, yana jin zuciyarsa na zafafa zafinta sosai, Ammie ta tina mashi da daddyn Rimsha, shaƙuwar da suka yi ta zarce tinanin mai tinani, shiyasa ya fi jin zafin mutuwarsa.”Tafiya zaka yi tin bamu gama magana ba?”….. Shiru bai amsa ba, babu alamar ma zai motsa bakinsa, dan yana gudun daddana mata maganganu masu zafi. Ganin hakan yasa ta sake shi, dan tasan hali. Cikin zafa ya miƙe ya fice waje da saurin gaske har kamar zai tashi sama, bayansa ta bi da kallo tana addu’a ALLAH ya shirya mata shi, daga haka ta mayar da hankali kan karatunta. Yana fitowa ya isko parlo ba kowa, dan haka ya fice waje abinsa, bai tsaya jiran Abba ya fito ya kaisa asibiti ɗin ba dan an ɓata mashi rai. TO KUN JI YADDA GIDANSU VASH YAKE KO? MU MOTSA GABA. ————————-LEO.Zaune yake a gefen bed ɗinsa yana waya da Noor da ya takura mashi a lallai su haɗu tin da dikkansu a CRYSTAL PALACE suke, shi kuma Leo ya ce ba yanzu ba, Noor ya bari sai next week, shi ma fa yana son ganin Noor ɗin, kawai dai yana da tsari ne. Zayra’an ne ya shigo ɗakin bakinsa a ɗauke da sallama ƙasa-ƙasa, yana sanye cikin three-piece suit masu mugun kyau da tsada, sai tashin fitinanne kamshi yake ye, still dai face ɗinsa da nose mask da ya hanaku ganin ainahin kamanninsa gabaɗaya. Sallamar Noor Leo ya yi tare da katse kiran, sannan ya haɗe natsuwansa waje guda tare da jawo laptop ɗinsa da yake aiki a ciki tin ɗazun. A gefensa Zayra’an ya zauna ba tare da ya yi magana ba. “Good morning bro”. Leo ya faɗa in a cool way kuma with full respect to his bro ɗin. Shiru Zayra’an bai amsa ba, sai ma hannu da ya kai ya ja laptop na Leo yana kallon abin da yake yi. Da sauri Leo ya kallesa tare da cewa. “Dama room ɗinka zan zo yanzu, bro will you help us?”. Ya faɗa yana mai da kallonsa a kan yayan nasa da kya, har da ɗan juyo da jikinsa. Tin da suka dawo bincike yake yi a kan mission da zasu tafi, yana neman bayanai kan ayyukan dikka, to dikka mission huɗun ya ɗan samu bayanai sama-sama, sai mission a kan IRON FIST ne bai samu komai ba, kan shi ta ɗaure over, ya rasa gane komai, dama shi ne yake son zuwa ya tambayi yayan nasa, dan in baku manta ba na faɗa maku yayansa babban barde ne, jami’i ne da AZURE ta yaye shekarun baya, yana da sani ninkin ba ninkin su.”IRON FIST, IRON FIST, IRON FIST”. Zayra’an ya maimaita sau uku cikin yanayin da ba zaka iya tantance muryansa wace iriya bace ba kafin ya ajiye laptop ɗin, sannan ya miƙe tsaye, a sanyaye ya ce. “Ka yi wanka, idan ka shirya ka sameni a room ɗina, i want to go out now, so hurry up”. Yana gama faɗar hakan ya wuce ya fita. Bayansa Leo ya bi da kallo cike da ƙauna har ya kurewa ganinsa. Gently ya miƙe tare da ɗaukar wani binoculars ɗinsa ya nufo view ɗinsa, binoculars kamar kallo-kallo za’a ce ne kome! Ni ban ma san ya zan kwatanta maku shi da hausa ba, zai dai je kallon waje mai ɗan nisa kenan, zai yi amfani da wannan dan hango abin dake nesa, nasan kun gane me nike nufi. To shi ya ɗauko nasu na sojoji da ake basu a barrack ya nufi view. Sanye yake da sleeping dress, yanzu ya tashi daga barci fa ya hau aiki a kan mission da zasu tafi. Yana zuwa ya danna curtains control, take labulayen view ɗin suka hau yaye kansu da kansu.Take wani tangamemen view na glass wall ya bayyana, glass control ya danna, a take glass na view ɗin ta buɗe, tsayuwa da kyau ya yi a wajen ta ciki tare da sanya binoculars ɗin ya fara kalle-kalle a cikin wajen, CRYSTAL PALACE daga sama waje ne mai shegen kyan kallo, ɗaukar hankali da sanya nishaɗi da farinciki.Can a kalle-kallen nasa ya hango kamar mutum ne tsaye a benen dake facing nasu, hakan yasa ya yi zooming dan ya ga menene a wajen. Ai a take ya ɗan kawar da kansa daga jikin binoculars ɗin kafin ya sake mayarwa, motsa lips ɗinsa ya yi tamkar zai furta magana sai kuma ya fasa, kafe wajen da ido kawai ya yi na almost 10 mins. Lokaci guda kuma ya yi gaggawar ɗauke kallonsa tare da ja baya, da sauri ya danna glass control, ya rufe glass ɗin tare da mayar da curtains ɗin ya rufe, a saman bed ɗinsa ya jefa binoculars kafin ya wuce ya nufi toilet. A natse ya yi wanka, ya fito ya shirya cikin hoodies milk color bayan ya shafe jikinsa da STAR BODY LUSH, daga nan ya ɗauki wayansa da laptop ɗinsa ya fito.Kai tsaye room na yayansa ya nufa. Tsaye ya isko yayan nasa yana rike da waya tamkar yana typing wani saƙo ne. Gado ya wuce ya zauna yana faɗin. “Brother tin da na dawo ban ga Yah Champion and Yah guru ba, ina suka je?”……….. Kun ji da kyau me Leo ya tambaya kuwa? Yah Champion and Yah guru, nasan kun ji da kyau kamar yadda nima kunnuwana suka ji mun da kyau! Kenan Leo yana da alaƙa da IRIN FIST amma bai san su ba ne? Idan na cinka daidai Zayra’an shi ne Lion na su Champion?. Balain can!.Bari in warware maku wani abu, dan bana son kwakwalwarku ta shiga ruɗani sosai, ainahin ruɗani yana gaba, to idan kuka fara rikicewa tin yanzu kwakwalwarku da wuya ta iya ɗaukar ruɗanin gaba, shiyasa yanzu zan warware maku wannan rikicin kam, idan na so kara rikitaku ba zan warware maku ba, sai dai in ce maku Leo da Zayra’an suna zama a wani gida ne daban, hakan zai nuna maku kamar basu da alaƙa da IRON FIST, kada ku manta CRYSTAL PALACE tana da gidaje dayawa, dan haka ba lallai Leo ya zauna da IRON FIST gida ɗaya ba idan na so rikitaku, sai dai ba zan so ku rikicen ba! Dan haka mu je ku ji su waye su na hakika tin yansu kafin mu shiga ainahin ruɗani.IRON FIST su da a farko suka kasance jiga-jigan jami’an da AZURE ta yaye a shekarun baya ya aka yi suka rikiɗe suka zama terrorists? A lokacin da Lion ya je ɗaukar Leo a Barrack ai na faɗa maku shi ɗin babban jami’i ne da Azure ta yaye ko? To ya aka yi suka rikiɗe zuwa ƴan ta’addan da duniya ke nema? Meyakefaruwa ne?. Kamar yadda kuka ji ne! Leo kanin IRON FIST ne amma ba tare da yasan su ne IRON FIST ɗin ba, kuma kamar yadda kuka ji, IRON FIST jami’ai ne da AZURE ta ya ye. Akwai babban dalilinsu na rikiɗewa su koma terrorists a idanun duniya, da farko fansa suka shiga ɗauka, sun ga akwai dalilai da dama da zai sa su cigaba da abin da suke yi shiyasa suka cigaba bayan gama ɗaukar fansa, in taƙaice maku labari su ɗin ba terrorists kai tsaye bane, duniya ke kallonsu a matsayin terrorists, amma su ɗin Earthsentinel.Yes confirm ana basu kwangilar kashe rai, kuma suna kashewan, amma su sun san irin waɗan da suke kashewa, wai kun san kai tsaye su waye su kuwa? Ba zaku taɓa gane karatun a yanzu ba, dan dik yadda kuke tinaninsu sun zarce nan, su ɗin faɗa suke yi da duniya gabaɗaya ba iya ƙasarsu ba, suna da kaifin kwakwalwar da gudun aikinta ya zarce gudun bullet ɗin sniper gun, sun yi gagarumin zama dan tinanin mafita ga duniyarsu, a nan suka gane daga in da matsalar duniya na farko ta samo asali, watau idan suna son gyara a farko dole sai sun kawar da demokraɗiyya daga idon duniya, sun cire sonta da aka cusawa al’umma, idan ba haka ba, babu abin da zai gyaru a duniya!. Shiyasa suka sayar da ransu gabaɗaya.Dik waɗan da suke bin mulkin demokraɗiyya a cewarsu juya mutanen ake yi ba raɗin kansu suke bi ba, dan haka demokraɗiyya ita ce abin da zasu fara kawo karshenta, idan waɗan nan Team ukun suna tinani kuma suna hasashen abubuwa zaku zaci ba mutane ne ke magana ba, saboda ALLAH ya basu baiwar da hasashensu yake zamana gaskiya, a kullum da hasashensu suke aiki ba da bincike kai tsaye ba, yes suna binciken, amma dan su tabbatar da hasashensu suke yi, kuma suke samun nasara.Takaitaccen tarihinsu, sun taso ne su ukun nan, tin suna yara, da guru da Lion basu san iyayensu ba sai dai iyayen Champion kawai, sun rayu cike da son juna, tin suna yara idan ka taɓa ɗaya daga cikinsu haɗuwa suke yi sai in da karfinsu ya kare, amma a hakan kada ku zaci basa faɗa! Kunga Lion da Champion mugun faɗa suke yi idan ta kwaɓe masu, guru ne ɗan ba ruwana, shi ne kuma mai sulhuntasu, idan suka ɓata Champion ya tafi ɗakinsa yaki kwana da Lion, in ya je ya gagara yin barci, shi ma Lion ya gagara yin barci, abin dariya sai Lion ya ce da guru ya je ya lallaɓa Champion ya dawo su shirya, shi fa Lion ɗin ba zai je ba, dan dikkansu suna ikirarin ba zasu taɓa furta kalmar sorry ba a rayuwarsu, dan haka ba zai cewa Champion sorry ba. Idan guru ya je ya lallaɓa Champion ya dawo fa sai dai ya samu waje ya zauna saman gado, babu mai cewa wani kala, a haka zasu yi barci cikin jin daɗin zasu kwana waje guda, washegari faɗar zata kare, dan suna tashi daga barci zasu fara yi wa juna magana, to haka suke har suka girma, yanzu haka in ta kwaɓe masu suna iya gwabza faɗa, guru ne middle man a cikinsu mai sulhu, kuma kun san zafin zuciya da zafin zuciya idan ta haɗu dole ake samun haka, ga su da kafiya, halinsu iri ɗaya, ba wanda zaka tankwara a cikinsu ya tankwaru, kowanne idan ya yi magana ɗaya ya yi ne, kunga dole a gwabza idan ra’ayi ta banbanta a kan abu. Guru dai yana nan kamar Manassa, komai normal ne a wajensa, ya fisu hakuri, kuma shi yana iya control zuciyansa, shiyasa basa faɗa da shi, kuma shiyasa shi ne mai lallaɓasu ya masu sulhu, amma waɗan nan biyun, da Lion da Champion, balai, ai in aka samu saɓanin ra’ayi abin baya kyau jama’a, faɗarsu gara faɗar dawakai, amma su in ta kwaɓe sai sun yi damaging na komai a wajen da suke, su jiwa kansu ciwo, kuma su yi fushi da juna, amma su gagara barci idan ba tare ba.To a taƙaice kun ji su waye Lion ko, to bari ku ji waye Champion, kun tina Dr Aryan na gidansu Rimsha? Shi ne ainahin Champion, shiyasa da zasu je AZURE ƴan albarkan suka rufe fuska da nose mask, dan in dai GAT ya gansu sai ya ganesu, ai na faɗa maku shi ya horasu a lokacin da suke matasan sojoji, kunga kuwa tsab zai ganesu, dan Champion da Lion dik sun je AZURE a ranar, amma babu wanda ya san sune, guru ne bai je ba. Masu ta cewa kai yayan Leo ya haɗu matuƙa to yayan Leo dai shi ne Lion na IRON FIST, kuma dik da baku ga ainahin fuskansa ba yana sanye da nose mask wannan shi ne ainahin kamanninsu shi da Champion, kamanin da duniya take neman gani ruwa a jallo ta rasa.Kun san kuwa tin da su Lion suka kuduri niyyar kawo karshen dik wata zalunci da munafurtan al’umma da ake yi dole ne dama a kirasu da ƴan ta’adda, dole ne a nemi ko da halin yaya ne yadda za’ayi a gama da su, an shafa masu bakin fenti cewa su ƴan ta’adda ne, an sanya dik wani ɗan ƙasa yana jin tsanarsu, dan su suna kisa ne bisa radin kansu ba dan a yaba masu ba, dan haka basa fitowa su sanar da al’umma cewa gurɓatattu suke kashewa, su kuma manyan duniya suna fitowa ne su nunawa al’umma cewa mutanen kirki IRON FIST ke kashewa! Yanzu kun gane dalilin da yasa kenan aka tsanesu kuma ake kiransu da ƴan ta’addar da duniya gabaɗaya take nema ko?.Aikinsu na faɗa maku wa duniya gabaɗaya suke yi wa ba ƙasa ba, dan haka ko shugaban wata ƙasa ce yake aikata ba daidai ba suna kashesa ba sai iya na kasarsu ba!.Yauwa yanzu kun gane dalilin da yasa Champion ya hana Rimsha shiga motarsa a school da ya je kenan ko? Saboda shi ne Dr Aryan, kuma ya tsani Rimsha kun sani! Ba da ainahin fuskansu suke fita ba in baku manta ba, shiyasa Rimsha bata ganesa ba, ai kun san da ta san shi ne ko kusa da motarsa ba zata zo ba, amma bata sani ba. TO A TAKAICE WAƊAN NAN SU NE IRON FIST, SAURAN BAYANI ZAKU JI A GABA.Ga shi dai kuna gani an cusawa su Leo tsanarsu, an ce zasu yakesu a cikin FIVE MISSION da zasu tafi ɗin nan, to ALLAH yasa su yi sauran 4 mission ɗin lafiya, shi kuma na biyar ɗin dani da ku dik mun san abu ne mai wahala gano su waye IRON FIST, dik da cewa Leo yana da karfin hali da kaifin ƙwaƙwalwa ne irin na yayan nasa, amma babba kam babba ne a ko’ina, idan suka yi wasa Zayra’an zai gwada masu fifikon iya aiki, amma zamu ga yadda zata kaya kam. Ku baku yi mamakin yadda halin Leo and Lion yake kamanceceni ba kafin ku san su waye su? Baku yi mamakin yadda halin Vash and Champion suke kamanceceniya ba?.Note, family ɗin Aryan basu san cewa yana ɗaya daga cikin IRON FIST ba, shiyasa ma ya yi karatun likitanci dan ɓadda kama, Ammie bata sani ba, haka su Faryan basu sani ba, to ku kaɗai na faɗawa, Dr Aryan Dr ɗin ɓadda kama dai shi ne Champion namu na amana, ko Seraph bata san ainahin kamanninsa ba, amma kunga ita Rimsha ta sani, watau a littafin nan akwai rikici ne na kin karawa, kai kun san me nike hangowa a gaba kuwa? Ban son rikicewar tai maku yawa ne, yanzu ai nasan kun gane karatun ko?. To mu koma kan labarinmu. —————————Kai tsaye room na yayansa ya nufa. Tsaye ya isko yayan nasa yana rike da waya tankar yana typing wani saƙo ne. Gado ya wuce ya zauna yana faɗin. “Brother tin da na dawo ban ga Yah Champion and Yah guru ba, ina suka je?”……….. Yana rufe baki sai gasu sun shigo a tare, dikkansu yau da ainahin fuskokinsu, dan basa ɓoyewa Leo kansu a matsayinsa na ƙaramin ƙaninsu kuma ɗan zamisan da suke son rena ya zama bakin damisa kamansu wanda ko sun rasa ransu a wannan aiki sai maye gurbinsu, shi ne dalilin da yasa suka turashi AZURE, kuma shi ne dalilin da yasa Aryan ya tura Vash ma AZURE, dan su kansu sun yarda da horon AZURE, suna son renon kannen nasu ne su zama tamkar su, ta yadda ko sun mutu zasu karisa masu aikin da suka fara. YANZU WASAN ZAI FARA.Amma fa still sun hana masu karatu ganin kamanninsu, dan kuwa suna sanye da nose mask dikkansu a yanzu ma, kuma daga yawonsu suka fito ƴan albarka.Da sauri Leo ya juyar da kallonsa a kansu, ai yana ganin sune ya nufesu a natse. Champion ya fara hugging yana faɗin. “I missed you over my brother”……… “Miss you too our Leo”. Champion ya faɗa cike da kauna. Shi Leo ya ɗauka su Champion aminan yayansa ne kawai, bai san sun wuci nan ba. Sake Champion ya yi ya rungumi guru dake ta faman kallon Lion, magana da ido suke yi, kun san sun kware. Bayan sun raba jiki da juna Leo ya ce. “Na ji daɗin ganinku brothers, dama ina son ku tayani duba mission ɗin nan namu, brothers i want to to help me about this IRON FIST, na kasa samun bayanai ko kaɗan ne a kansu”. Kallon Lion Champion and guru suka yi, da ido suka yi magana, Lion ya ce masu su kyalesa da shi. “Let’s go”. Lion ya faɗa yana kallon Leo dake faman jiran amsar su Champion. “Bro ina zamu je?”. Shiru Lion bai sake yin magana ba, sai dai ya wuce gaba, da sauri Leo ya rufa mashi baya, Champion and guru suka dawo wajen bed suka zauna, Champion ya jawo laptop na Leo dan su ga irin aikin da yake ƙoƙarin yi a kansu.Shi kuwa Leo yana fitowa suka ci karo da wannan ƙosasshen heron nasu, da gudun gaske zakin ya yi kansa alamar oyoyo. Rungume juna suka yi saura kaɗan zakin ya kada shi, a hankali ya fara shafa jikinsa har izuwa gefen wuyansa kafin ya sakesa tare da yi mashi nuni da ɗakin da su guru suke yana faɗa mashi ya je can……. Da gudu zakin ya nufi wajen, shi kuma Leo ya bi bayan yayansa suka yi waje. My people me kuke tinani wai? Akwai kallo fa. Ashe dole su Abba da su Faryan su ji shakkar Dr Aryan, member na IRON FIST wasa ne? Champion ake magana ba. Tab.————————– AZURE.Sanye suke da sportswear ɗinsu, guntun wando zuwa cinyoyinsu da riga mai karamin hannu, Arya na rike da stick na snooker tana tsaye kusa da wajen buga snooker tasu, while Angelina na rike da basken ball ɗinsu tana kallon Manassa dake ƙoƙarin ɗaure igiyar takalmarta. V na rike da nata sandar snooker tana kallon balls ɗin, tinanin yadda zata buga ta cinye Arya take yi, while Arya na jiranta ta buga, su Manassa kuma suna buga basket ball kenan, daddy na office, sojojin dake tsaron wajen sai satar kallonsu ta ƙasar ido suke yi, yara sun fara zama ƴan’mata, 15 years suke da yanzu, matasan tula-tulansu sun ƙara girma da cika, hips ɗinsu a cike dam, musamman V da ta fita daban. Sojojin nan tin da su ba duwatsu bane sai haɗiyar yawu wuke yi, bare ma idan suka ga V da Arya, sun fi sauran farin jini da shiga rai. Wata ƴar aikinsu ne ta shigo wajen da gudu tana faɗin. “Aunty V wayarki tin ɗazun ake ta kira”. Da sauri V ta fasa buga balls ɗin, jikinta na rawa ta karɓi wayar tare da dubawa. Wanda take zaton ne dai ya kira, dan ga shi number US ce, dama ya ce mata idan ya je gida ita zai fara kira da numbersa na can. Jikinta har yana ɓari wajen ƙoƙarin yin picking up Arya ta kwace wayar tare da cewa. “Zo mu karisa game ɗin nan kafin ki tsaya shiriritarki”.Haba kuka ta fasawa Arya game da magiyar ta bata wayarta, Arya taki, ta ce sai sun gama. Sai da Angelina ta zo da sauri ta kwace wayar ta miƙa mata tana faɗin. “Ke kina da son saka V kuka, wai ina ruwanki da soyayyarta ne?”. Wani irin harara Arya ta dallah mata kafin ta ce. “Ki daina shiga hurumina Angelina, idan ina yanke hukunci kina mun katsalandan watarana ba zaki ji ta daɗi ba”. ……. “Dukana zaki yi ne?”. Angelina ta faɗa tana harararta ita ma. “Kina tinanin ba zan iya dukan naki bane?”. Cikin fushi Arya ta faɗa.Angelina zata yi magana Manassa ƴar ba ruwana ta ce. “Har yanzu ba zaku daina faɗa ba”…… Harara su biyun suka dallah mata kafin Angelina ta ce. “Ke ina ruwanki?”. ……… Wai kun san da cewa suna faɗa kuwa? Dik yadda suke kaunar junan nan idan ta kwaɓe masu ba karamin gwabza faɗa suke yi ba, kamar zasu kashe juna, musamman Arya da Angelina, kuma abin da baku sani ba dikkansu Manassa aka fara haifa, amma Arya ta zage da cewa ita ce babba, sai suka bar mata girman, amma ban da haka Manassa ce farkon faɗowa duniya, sai Angelina, Arya ce ta uku sannan V. “Babu ruwana ku cigaba da yi”. Manassa ta basu amsa. Tsaki Arya ta ja tare da jefar da stick ɗin hannunta, ta nufi side na pool ɗinsu dan ta ɗan yi linƙata saboda ta haɗa zufa a wannan game da suka buga. Ita kuwa V Angelina na bata wayarta ta bar wajen da gudu tana murmushi, garden na gidan ta shiga ta zauna saman kujera tare da fara ƙoƙarin kiran number, dan call ɗin ta katse.Sau uku tana gwadawa call ɗin yaki shiga, daga karshe ta kunna data ta shiga Whatsapp. A nan ta ga saƙonsa na cewa sun sauƙa lafiya. Murmushi ne ya bayyana a kan face ɗinta ga kuma guntun hawayen kukan da Arya ta sanyaya, kan contact ɗin ta shiga tare da rubuta mashi call me. Tana turawa ba’afi 1 min ba sai ga kiransa ya biyo baya ta direct call. Jikinta har yana rawa wajen yin picking. “Hello”. Ta faɗa cike da matsuwar son jin voice ɗinsa, yana daga kwance saman katafaren bed ɗinsa, ya tada kai da cinyar daddynsa dake mashi tausa, wai kun san yadda daddy yake ji da Noor kuwa? Ɗah namiji ɗaya kamar rai, magajin dik waɗan na kadarori ai kun san dole a ji da shi sosai. Sai wani shagwaɓasa daddy yake yi yana matsa mashi damatsan hannu, wai sun sha tafiya ya gaji. Kawai dai daddy ji dashi yake yi, ba wani gajiya, baya son ko ƙuda ya taɓa mashi ɗan lelensa.Noor wasa-wasa soyayya na son koya mashi wasu ɗabi’u, yana jin kunyar daddy ya jisa yana hira da mace, amma ba zai iya hakura bai kirata ba tin da ta ce ya kirata, shi ne ya ce wa daddy wai abokiyar aikinsa ne, shi kuwa daddy ya ce okey, ya kasa kunne yana jinsu. “Where did you drop your phone na dinga kira baki ɗaga ba?”……… Ɗan shagwaɓe murya ta yi tare da cewa. “Sorry, na barsa a ɗaki ne ni kuma ina waje muna buga snooker”……. Satar kallon daddy ya yi, sai yaga baya kallonsa, ƙasa sosai da murya ya yi kafin ya ce. “You look so beautiful this morning, you melted my heart, since da na shiga plane, I’ve been thinking about your beauty, your smile, they way you hug my dad, I felt like…….”. Kasa karisawa ya yi saboda ɗago ido da ya yi suka haɗa ido da daddy dake kallon ɗan bakinsa, yana magana ne yadda daddy ba zai jisa ba, shi ne daddyn yake karantar ɗan bakin nasa. Turo baki ya ɗan yi tare da cewa. “Daddy stop it nooow, stop looking at me”. Ya faɗa yana miƙewa zaune tare da hararan daddyn nasa. Gefe daddy ya koma yana faɗin. “Dole na bar kallonka tin da an samu wacce take melting heart ɗinka”…….. Pillow ya ɗauka ya fara kaiwa daddy dukan wasa yana faɗin shi a kyalesa. “Wai ni na kulaka ne? Na kyaleka ai”. Daddy ya faɗa. Kwanciya ya koma ya yi tare da ɗaura pillow ɗaya a wajen bakinsa wai dan ma kada daddy ya karanci lips ɗinsa……. Shi dai daddy gefe ya koma yana jiran a gama wayar yau dole a faɗa mashi budurwa ce ko abokiyar aiki?.”My heartbeat daddy kake wa haka ko?”. V da gabaɗaya kalamansa na ɗazun suka gama tsumata ne ta faɗi hakan, ta ji daɗin yadda ya ce ta yi kyau yau da safen nan, abin ya yi mugun sanya zuciyarta ya yi fari. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. “Daddy ne yake tsokanana dai”. Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce. “Daddy yana sonka sosai”. Tarar numfashinta ya yi da cewa. “Over to over ma kuwa, fiye da kansa”……. Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa. “Mu yi video call?”…… Wurga dara-daran eyes ɗinsa a kan daddy ya yi kafin ya amsa da. “Later after daddy ya fita”. “Okey where’s my Auntys?”. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. “They escort Aunty Luna, tana da meeting a ofishin jam’iyyar da suka tsai da ita takara”….. Sosai V ta yi mamakin jin cewa Luna ƴar siyasa ce, da sauri ta ce. “Dama Aunty Luna babba ce?”…… Tambayar ta so bashi dariya, amma sai ya fiske da cewa. “She’s 35 years old, Aunty Lusi 30 years old, then my two sisters da suka mutu, sannan Aunty Lisa 25 years, sai ni”. Ya kai karshen maganar tare da kin faɗa mata shekarunsa. Gaskiya ne, Aunty Luna gogagiyar ƴar siyasa ce, daddynta ya bata goyon baya ɗari bisa ɗari, kujerar Gwamna take nema, sannan macece mai son jama’a, saukin kai da tausayawa talakawa, ga kyauta kamar me, har shi daddynsu yana da tsananin kyauta wanda daga garesa suka koya, dik Sunday sai sun bi gidan marayu da gajiyayyu sun raba masu kayan abinci da tsabar kuɗi. Ita kuma Auntu Lusi CEO ce ta SLBANK, babban banki ne sosai. Ita kuwa Aunty Lisa yanzu take degreenta na biyu a fannin lafiya. Kun san shi kuma Noor ina ALLAH ya jefasa ai, so dik yaran daddy Noor suna da abin yi, zakaru ne da ƙasa ke alfahari da su, basu tsaya cewa su mata ne kawai babu abin da zasu iya ba, sun tsaya tsayin daka, sun yi aiki tukuru dan gina gobensu dana iyalansu, sun samu uba wanda ya jajirce a kansu dik da babu uwa!.”To kai shekarunka nawa?”. V ta tambaya cikin zolaya. “Kamar naki suke”. Ya bata amsa yana mai da kallonsa a kan daddy. Kukan shagwaɓa ta sanya mashi kan lallai ya faɗa mata shekarunsa, to yaro yana cikin shauƙin sabuwar soyayya ina zai so ɓacin ranta, sai kawai ya amsa mata da. “23 nike da shi”. Tana turo baki ta amsa da. “Wow”. Kafin ta sake cewa. “Meyasa ka sumbaceni da safe?”……. Yana satar kallon daddy kaman wani mara gaskiya ya ce. “Bcos you look so beautiful”……. Jujjuya eyes ɗinta ta yi kafin ta ce. “Iya shikenan?”. Shiru ya ɗan yi, can ya ce. “No, but zamu yi magana leter”……. Kukan shagwaɓa ta sanya mashi tare da cewa. “Ni ban yarda ba, sai ka faɗa mun yanzu”. Da sauri ya amsa mata da. “Okey stop crying, a daina melting heart ɗina da wannan shagwaɓa, faɗa mun meyasa daren jiya kika gudu dan kawai na tare maki hanya kada motoci su haskaki?”. Tana turo baki game da shessheƙa ta amsa da. “Saboda ka sanya na kwanta a kirjinka mana, dik ka rikitani”…… Can ƙasa a takaice ya ce. “To kirjina ba naki bane?”……… Ai ji ta yi tamkar ta fasa ihu saboda daɗi, amma ta daure wajen rike kanta, murmushi yasa bakinta yaki rufuwa, sai da ta sanya hannunta ɗaya ta toshe ɗan bakin nata tare da lafewa a jikin kujerar tana sauke ajiyar zuciya. Shi kuwa saboda tsabar daɗin soyayya bai san time da ya zame pillow ɗin ba, ya mirgina ya dawo jikin daddy yana faɗin. “Ya kika yi shiru? Ko ba naki bane?”. Ai kara kashe murya da haɗaɗɗen shagwaɓarta ta yi wajen cewa. “Da gaske ka mallaka mun kanka?”….. “Ko baki so ne?”. Ai har tana tuntuɓen harshe wajen amsawa da tana so. One side smile ya sake tare da kamo kyawawan yatsun daddy yana murzasu cikin wani irin jin daɗi, take ya shiga romantic mood, ya manta da cewa daddynsa ya rike ba ita ba, da hira ta yi daɗi ma har da zura yatsun daddy a bakinsa yana biyewa V.Kun san yarinyar da iya soyayya, tuni tasa ya susuce mata, ya dinga zuba kalaman da bai san ya iya su bama, idan ta sa mashi wani shagwaɓa gagara rike kansa yake yi, sai ya juya ya kifa a saman bed ɗin, still kansa na saman laps na daddy yana ɗan ciza yatsun daddyn da ya zura a baki. Ai shi dai daddy baki ya sake yana kallon ɗan nasa, gabaɗaya ya gama goge mashi hadda ɗan ƙaniya.Sun ɗauki good 1h suna hiran nan kafin ta katse kiran saboda su Arya dake faɗa, Arya da Angelina ke ta faman faɗa tin na ɗazun, Angelina ta bi Arya wajen pool suka cigaba, shi ne ta ce mashi tana zuwa ya bata 10 mins, dan zuciyarta ba zata iya juran faɗarsu ba, kada ku manta zuciyoyinsu a haɗe yake, tana jin tsananin zafin abin da suke yi, dik hankalinta ya koma kansu.Tana katse kiran ya ɗauki 10 mins kafin ya dawo cikin hayyacinsa da kyau, slowly ya ɗago da kallonsa a kan daddy, sai yanzu ya tuna suna a tare ashe. Da sauri ya zabura ya miƙe zaune yana ɗan rarraba dara-daran European eyes ɗinsa a kan daddyn nasa. Sai kuma ya ce. “Daddy seriously it’s not what you’re thinking, she’s my friend”. “Ni na tambayeka ne? Ko ka ji na ce ba friend ɗinka ba ce?”…….. Shiru ya ɗan yi tare da fara shafa curly hair ɗinsa yana son tuna kalaman da ya dinga faɗawa V, watau ya gane me ya faɗa ko da ace daddy ya ji ma yasan ta ina zai ɓullowa lamarin. Can ya tuna ya ce mata kayan da ta sanya da safen nan yasa ya ga komai nata yadda yakamata, kuma ta yi daidai da irin zaɓinsa. Da sauri yasa hannu ya toshe ɗan bakinsa, sai kuma ya ɗan ɗaga jera guda, kashe mashi ido ɗaya daddy ya yi tare da cewa. “Dik abin da ka faɗa na ji, okey dama boy kana da irin macen da kake so ko? Har da cewa breast ɗinta sun yi daidai ko? To zo nan ka faɗa mun waye ya koya maka dikka wannan?”. Ya kai karshe yana ƙoƙarin kama kunnen Noor.Ai a miliyan Noor ya diro kasan bed ɗin, da gudu ya nufi waje yana faɗin. “Daddy ka iya sa ido, ni kada ka sake dawowa ɗakina, I’m matured now”…….. Da gudu shi ma daddy ya diro ya bi bayansa yana faɗin. “Jirani in kamaka sai ka kalli tsabar idona ka faɗa mun kada in sake zuwa ɗakinka saboda ka girma, kuma yau sai ka faɗa mun daga ina ka koyi waɗan nan kalamai kai da kake kullum a ɗaki baka fita sai da ka tafi AZURE! Ko a can ka koyo?”. Yana magana yana binsa da gudu.Sama Noor ya yi yana faɗin. “Kada ka wahalar da kanka daddy, ba zaka iya kamani ba, now I am a soja from AZURE, the best army academy in the world”……….. “Bari in gwada maka cewa ni kuma tsohon ɗan wrestling ne, kafin ka fara training na rigaka”. Daddy ya faɗa yana ɗan haki, while shi Noor ko a jikinsa, da gudun gaske ma ya fito harabar makeken filinsu dake ta sama, a nan garden ɗinsu yake, pool ɗinsu ma a saman yake. Yana shiga garden ɗin ya ɓuya a bayan wasu tsadaddun kujeru yana nunawa Aunty Lisa dake zaune tana waya hannu a kan kada ta bari daddy yasan yana wajen. Tana manne da waya a kunne ta amsa da to, yanzu suka dawo gidan, call ɗin GAT yasa ta zauna a garden ɗin tana amsawa, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya tana yi mana wasa da hankalin daddy GAT ɗinmu, taki bashi haɗin kai dik da bai fito ya faɗa mata ainahin abin dake ransa ba, ya tambayeta ya school ta ce normal, sai ya ce ya soyayya ta ce ita bata yi, ya ce saboda me, shi ne ta ce mashi ta tsani maza.Hankalinsa ya tashi sosai, ita kuma tana nan tana mashi dariya, dan ta yi alkawarin sai ta wana hankalinsa sosai kafin ta amince mashi dik da cewa ita ma ta fola mashi. Yana zaune a office ɗinsa, ya manna waya a kunne idanunsa a kan tarin takardun zaman da suka yi da result na aikin kowani yanki, dama yana kan dubawa ne ya kirata. A natse ya ce. “Meyasa kika tsani maza kika kuma tsani soyayya?”……. “Saboda ɓata lokaci ne da shirme”. Ta bashi amsa cikin halin nuna ko in kula, wai irin ta nuna mashi bata damun nan ba. Ai bai san lokacin da ya ce. “Lallai ina da babban aiki a gaba na”. Ba. Sai da ya ji ta ce. “To ka karisar da aikin naka mana daddy, sai mu yi waya wani lokaci”. Sarai ta gane nufinsa fa, amma ta yi kamar bata gane ba. “Daughter zaki bani ciwon kai ko?”. Ya faɗa yana ciro tissue, gumin dake keto mashi a fuska ya goge tare da jan dogon numfashi, kalamanta suka sanya ya fara haɗa gumi dik da sanyin Ac dake office ɗin. A ransa ya ce bari ki shigo gidana dik zan rama ne, a fili kuma ya tsaya sauraran amsarta……. “Daddy ni kuma zan baka ciwon kai? Me na yi maka my lovely daddy?”.Har cikin ransa ya ji daɗin yadda ta ce my lovely daddy, nisawa ya yi tare da furzar da iska mai ɗan ɗumi daga bakinsa, a natse ya ce. “Daughter, soyayya tana da daɗi sosai”……. “Kai daddy ba wani daɗi, dik shirme ne da ɓata lokaci”……… “Da gaske tana da daɗi, ki jarraba”. …… Tana faman guntse dariya ta amsa da. “No daddy, ba wani daɗin, dik wahala ce da ɓata lokaci”. “Daughter, ki bani dama zan tabbatar maki da cewa soyayya tana da daɗi, zan koya maki yinta, idan har na koya maki kuma kika ji bata yi maki ba zan yarda da zancenki”. Ya faɗa cikin wata iriyar sigar da wane mutum ya iya musawa wannan murya……. Wani irin abu ta ji ya tsaya a zuciyarta, musamman yadda ya yi maganar cikin yanayi na kwantar da hankali, ai sai gabaɗaya ta ji ina, ba zata iya ja ba kuma, da kyar ma ta iya cewa. “Daddy zaka iya jarrabawa, amma ni nasan ba wani daɗin da zan ji”. Wani irin daɗi ya ji na wannan amsa tata, a ransa ya ce sai dai in ba hannun soja kika shiga ba, a soyayya ai su ɗin karshe ne, a fili kuma sai ya ce. “For sure zaki ji daɗi, ba dai kin baiwa daddynki dama ba?”. Kai ta gyaɗa mashi alamar yeah kafin ta amsa da e. “Zamu yi waya da daddare, daga yau zan fara aikin koyawa babyn daddy soyayya”. Ya faɗa yana matso da wasu takardu gabansa. Tana sakin ƙayataccen murmushinta irin na Noor ta amsa da. “To my daddy, ka kula mana da kanka”…… Ya ji daɗin kalamanta, ya amsa da. “Okey babyn daddy”….. Daga haka bata sake cewa komai ba ta katse kiran. A daidai lokacin daddy ya shigo da gudu yana faɗin. “Where’s my pleasure?”. Kai ta ɗan girgiza game sa cewa. “Bai shigo nan ba”. Juyawa daddy ya yi, ya fita da gudu. Yana fita Noor ya fito, zuwa ya yi ya rumgumi Aunty Lisa yana faɗin. “That’s my Aunty, the reason why I love you kenan”. Ya faɗa tare da manna mata sumbata a kumatu. Ita ma sumbatarsa ta yi, daga nan suka cigaba da hira cike da kulawa game da kaunar juna. ————————-🔥SERAPHINAKwance tashi babu wuya a wajen ALLAH, sun fita daga jss 2 zuwa 3 a yanzu, ta mai da kai kan karatu sosai, bata kula kowa sai Rimsha, a yanzu dik karshen sati Champion yake zuwa wajenta, ya rage daga wata-wata zuwa sati-sati, hakan yasa suka yi mugun sabo, ta saki jiki da shi sosai, idan ma tana da damuwa jira take yi sai ya zo ta faɗa mashi, a yanzu da shi da Rimsha kawai ta yarda, ita ma Rimsha ba koma Seraphina take faɗa mata ba, kuma har yau Rimsha bata san wannan daddyn Seraphina shi ne Uncle Aryan ɗinsu ba.Kamar kullum, sun fito daga room ɗinsu zuwa class, tafe suke a tare cikin natsuwa, Rimsha ita ta rike masu rucksack ɗinsu, saboda Seraphina yau bata jin daɗi, ta tashi da ciwon ciki sosai, dan ma suna Exams ne yasa ta daure zata je class.A tsakanin class ɗinsu da hotel suka haɗu da wani kyakkyawan baturen yaro, yana rike da rucksack ɗinsa zai wuce, ga boys ɗinsa nan a biye da shi, da alama irin yaran nan ne marasa jin magana. Zasu wuce ya ce. “Heyyy come here!”. With harsh voice ya yi maganar, hakan yasa ya firgita Seraphina. (Masu cewa Princess dan ALLAH ki dinga saka sunan Seraph complete ya fi daɗi to ga shi ina sakawa, shikenan, kun ji daɗi na saka maku sunan complete? Seraphina.)Da sauri ta riko Rimsha, ita ma Rimsha ɗin tsorata ta yi, hakan yasa cikin ladabi suka je gabansa dan amsa kiran. Cike da gadara yaron ya ce. “Which class are you?”. Ya faɗa yana nuna Seraphina da har jikinta ya soma kerma saboda tsoro.”Jss 2″. Murya na rawa ta faɗa. Kallon santala-santalan cinyoyinta ya yi kafin ya ce. “You’re beautiful”. Ya faɗa yana shafa kansa, matashi ne da a ƙallah zai iya kai 18 years haka, ɗan Ss3 ne. Shiru suka yi basu iya amsa mashi ba. Ya ga violet eyes da bai taɓa ganin irinsa ba, gata kamar madara ai dole ya rikice, ba ɗalibai na, Seraphina dik and Rimsha dik da ƙananin shekarunsu harta malamansu sonsu suke yi, kowa yana son abu mai kyau.”Go, I’ll come to your class and meet you there”. Ya faɗa ba tare da ya jira amsarsu ba ya wuce gaba abinsa. Wucewa suka yi suka nufi assembly hall. In a coll way Seraphina ta ce. “Jiya daddyna bai zo ba, da zan faɗa mashi cewa cikina ya dinga ciwo tin shekaran jiya”. A shagwaɓe ta faɗa. Rimsha zata yi magana daga bayansu muryan Madam Rohisha ya katsesu da cewa. “Seraphina, your daddy is here, go and meet him in my office”. Wani irin murmushi Seraphina ta saki tare da cewa. “Rimsha my dad is here, let me go and meet him”. My people ni Star Lady na fara wani hasashe, anya Seraphina ba kanwar Vash bace kuwa? Kada ku manta Abba ya kafa dokar hana soyayya a gidansa, kuma kada ku manta auren haɗi ya yi wa mahaifin Vash da mahaifiyarsa, to ina ga shi kuma mahaifin Vash yana da wacce yake so shiyasa ya aureta ya kaita wani wajen suna soyayya, ku tuna wani abu ɗaya! Meyasa daddyn Seraphina bai zauna da su ba? Baya yarda a gansa tare da Dr, and dik yadda aka yi kunga Champion ya santa, Dr Aryan kanin daddyn Vash ne, idan kuka buga lissafin zaku ga wani amsa fa, ko shiyasa hankalin Champion ya tashi a lokacin da ta ce ita ƴar Dr ce? Kenan yasan yayansa ya yi auren sirri? Kenan yasan Dr? Kenan shi ne wanda Dr take cewa kanin baban Seraphina wanda shi kaɗai ta yarda da shi? Kunga kenan alama ya nuna tasan sauran danginsa ba zasu karɓeta ba, kila tasan ba’a auren soyayya a family ɗin! Champion kanin daddyn Seraphina ne kenan? Kuma kanin daddyn Rimsha! Kai wannan fa hasashena ne, kowacce ta yi nata, alƙalamina ne kawai yasan me yake ɓoye a duhu, shi kuma zai fito damu haske, dan haka mu je zuwa. Bata jira amsar Rimsha ba ta juya da sauri ta nufi office na madam Rohisha, cikinta na tsananta murɗa mata, amma farincikin jin ya zo yasa bata mai da hankali a kan ciwon cikin nata ba. Da sauri ta shiga office ɗin. Tana ganinsa ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. Yana zaune a saman visitor chair, still dai bada ainahin face ɗinsa ya zo ba, kuma yana sanye da nose mask.Rungumeta ya yi, can ƙasa in a cool way ya ce. “I missed you so much my daughter”…….. Tamkar zata yi kuka ta ce. “Daddy ina ka je jiya Sunday baka zo ba?”………. “I went to a meeting, that’s why i didn’t come, is there something wrong?”. Ya faɗa ne kawai, amma ba wani meeting, suna can suna tsame gurɓatattu daga cikin masu kyau, kun san sai sun ɗauki shekara suna haɗa bayanai da bincike a kan mutane, idan suka tashi cikin sati guda suke kawar da gurɓatattu a kasashe daban-daban da dama.Kuka ta ɗan sanya mashi tare da rabe jikinta da nasa, ta ɗaga rigar uniform ɗinta tana faɗin. “My stomach hurts to much”…….. Da sauri ya ɗaura hannunsa dake fari tas kamar madara a saman cikin nata, yana waro idanunsa a kan face ɗinta sosai ya ce. “What did you eat?”. …….. Kai ta fara girgizawa kafin ta ce. “I didn’t eat anything apart from our normal food”. Take damuwa ya bayyana a tattare da shi, jawota jikinsa gabaɗaya ya yi, ya rungumeta sosai tare da ciro wayansa ya hau kiran Madam Rohisha a kan ta zo ta yi masu jagoranci zuwa hospital na school ɗin, sannan ya gyara mata zama a jikinsa, ta kwantar da kanta a saman buɗaɗɗen kirjinsa dake da faɗi sosai, ya tura hannunsa cikin rigarta saman cikin nata, ya fara karanto mata ya hayyu ya ƙayumu bi rahamatika asta gisu aslili sha’anin kullahu, walatakil illah nafsi ɗarfata aiy, wala ilah hadin minan nas. Idan ya karanta sai ya hura a hannunsa ya shafa mata a ciki. A daidai lokacin……..

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

Back to top button