Halysaah Page 206 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 206…Nenne ta saki baki tana kallon Khaleesat, can ta gyara zama tace “Kika yarda da wa?” Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalli Nenne tace “Ya Abdul” Nenne ta riƙe haɓa tace “Tabdi, wato saboda kin samu ɗan arziki me sonki yana tarairayar ki shi yasa har kika mance ukubar da kika sha a hannun Awdul ko?” Khaleesat ta girgiza kai a hankali tace “Me yasa iya sharrin Abdul kawai ku ke gani kuma ku ke tunawa Nenne? Duk matakin da na taka a rayuwa Abdul ne sila babu wani kwaskwariman da zai canza haka, shi ne mutum na farko da ya fara son ganin ya inganta min rayuwata ta yanda zan zamo matar nuna ma sa’a a lokacin da ya so aurena, da Abdul ba ya so na tsakani da Allah bazai taɓa daukar hanyar gyara min rayuwa ya bani ingantaccen ilimi har ayi sha’awata a wani wajen ba, don haka idan iya sharrinsa ku ke tunawa ni kam alkhairinsa ya take sharrinsa a wajena, kuma har cikin raina nake kyautata masa zato yanxu, dama can a baya shi din mai ibada ne kuma yana karatun qur’ani sosai duk da halin sa, ni zan shaide sa akan haka” Nenne ta kyabe baki tace “Shege shi ke manta alkhairi dama ai, amma kuma tsorona Allah tsorona Awdul baza ki taɓa hanani dena tsoronsa ba bari ki ji in gaya maki, haka kawai bazan biye sintirin da yake mana ba a gidan nan in dau jikata in basa, ai Haiydar din ya kusa komawa turai don a can yake aiki, zan ga da sunan wa zai ci gaba da zuwa layin nan, kuma fa in dai ya zo unguwan sai ya shigo ya gaisheni, saboda ya ga bana amsan kudinsa ya ma dena bani, zai dai shigo ya gaisheni, wani lokacin har ya ci abinci, banda Zahra’u dake kwaɓa ta da tuni na koresa ni dai, ba ruwana da jaraba” Bude kofar dakin aka yi, Noor ta shigo da sallama, zaro ido tayi ta tafi ta rungume Khaleesat cike da murna tace “Aunty yaushe kika zo?” Khaleesat na murmushi tana kallonta ganin yanda ta girma, ga shi sak ita a sanda take shekarunta, ta dago kanta tace “Not long ago, Ina Islam?” Noor na murmushi ita ma tace “Na bar su a baya da kawayenta” Juyawa tayi ta gaida Nenne, Nenne ta amsa tace “Kuna yan biyu baza ku jeru ku dawo gida tare gwanin sha’awa ba, ni ban taɓa ganin yan biyu masu yin haka ba sai a kan ku” Noor dai bata ce ma Nenne komai ba ta mike ta nufi fridge din dake dakin ta bude, Nenne ta hade rai tace “Lafiya?” Noor bata kalleta ba ta ciro ruwan gora tace “Ruwa zan dauka” Nenne tace “Kiyi min me da shi?” Noor tace “Uncle yace in kai masa….” Nenne tayi mitsi mitsi da ido tace “Ai dama na sani, ke kika zuba min ruwan a firijin ko kuma shi Ankle din ne ya zuba min? kullum sai kin shigo min daki kin daukar min ruwan gora kamar ke kike siya min, uwar me yasa baza ki kai masa piya water ba” Noor ta tura baki ta juya ta fita daga dakin tana rike da ruwan goran, Nenne ta kalli Khaleesat tace “Munafuka ce fa, saboda shi ita ma take dawowa da wuri ta bar er uwar a gantale a hanyar makaranta, duk ina lura da qita, to uban me yake tsara mata da take Allah Allah ta dawo ta dau min ruwan gora? To ni dai ba ruwana, in maye ya manta uwar ɗa dai bata manta ba….. Kar nake kallon Awdul” Khaleesat dai taki tanka mata, tunawa tayi ta bar Ajay a waje bata san sanda ta mike da sauri ba har sai da taji kanta ya juya mata tayi saurin dafa bango jiri na dibanta, Nenne ta mike tace “Subhanallahi, lafiyar ki? Me ya faru” After some seconds a hankali Khaleesat tace “Wallahi na mance yana waje” Tana fadin haka ta fice daga dakin don jirin da take ji ya ragu, compound ta fita taga Abdul zaune cikin sabon Pavilion da aka gina a compound din, ga qur’anin Noor a gabansa, Noor kuma na tsaye gefensa, tana ganin Khaleesat ta ajiye bottle water din hannunta kan table sannan ta fita zuwa gun ta, tana kallon Khaleesat tace “Aunty wai tafiya za kiyi? Umma fa bata dawo ba” Khaleesat tace “Ba tafiya zan yi ba, karatu ku ke yi ne?” Noor tace “Muraja’ah kawai nake yi” Khaleesat tace “Ohk, kin ga mota a kofar gida da kika dawo yanxu?” Noor ta girgiza kai tace “A’a babu mota, wai tare ku ke da Uncle ne?” Khaleesat tace “Tare mu ke, je dai ki duba ko yana waje” Noor ta juya ta nufi gate, Khaleesat kuma ta juya ta koma cikin gida, ba a dau lokaci ba Noor ta dawo ta tarar da Khaleesat zaune parlor tace “Aunty babu mota, kilan ya tafi” Lokaci daya jikin Khaleesat yayi sanyi, ta mike ta koma dakin Nenne, handbag dinta ta bude ta ciro wayarta tayi dialing numbersa, har ya katse bai daga ba, few seconds later sai gashi ya kirata, a hankali tace “Why did you leave?” Yace “Zan dawo anjima, naga kuna da baƙo a gidan” Khaleesat tace “That doesn’t mean, he isn’t here because of us ai, we met him instead” Ajay yace “Haka ne, take care of ur self, zan je gidan sarki ne yanxu in gaishesa…” Khaleesat tace “Sarkin garin nan?” Yace “Eh” Tace “To yaushe zaka dawo?” Yace “Idan ma ban dawo yau ba zan dawo gobe” Shiru Khaleesat tayi, yace “Take care” Daga haka ya katse wayar, Nenne dake ta kallonta tace “Ke dai ban san sanda zaki yi hankali ki waye ba, don shashanci da hauka dama tare ku ke kika bar sa a gantale kamar ɗan iska a kofar gida?” Ko kulata Khaleesat bata yi ba ta mike ta dau handbag dinta ta fice daga dakin ta tafi dakin Ummanta. Wajen karfe tara Khaleesat ta dawo daga parlon Babanta, tun karfe takwas da ya dawo ta je gaishesa sai yanxu ta fito, tana shiga bedroom din Ummanta ta kwanta kan gado tana sauke numfashi a hankali, don duk ta gaji dadewan da tayi zaune parlon Babanta, Umma dai kallonta kawai take don ta gane ba ita kadai bace, Noor dake dakin ta mike ta nufi Khaleesat ta duka kusa da ita tace “Aunty baki da lafiya ne?” Khaleesat tace “Lafiyata qlau, ina Islam?” Noor tace “Tana can dakin Nenne” Umma dake ta kallon Khaleesat tace “Me za ki ci?” Khaleesat ta juya ta kalleta a hankali tace “Akwai fruits Umma?” Umma tace “Sai dai a siyo maki, bari in kira almajirina a waya ya zo ya siyo maki….” Mikewa Umma tayi ta dauko wayarta, Islam ce ta shigo dakin da waya a hannunta tana kallon Noor tace “Wannan wayar fa?” Noor ta zaro ido tana kallon wayar don second phone din Abdul ne da ya bata tun sanda ta dawo islamiyyah ta sa masa caji, Umma dake kallonta tace “Wayar waye?” Noor tace “Na uncle ne, ya bani in sa masa a caji kuma ni na manta, kilan shi ma ya manta” Umma dai sai kallonta take haka ma Khaleesat, Noor tace “Gobe idan Ya Haiydar ya shigo sai a basa ya ajiye masa” Islam ta ajiye wayar nan gaban madubin Umma ta fita daga dakin. Washegari da rana Khaleesat na dakin Nenne, Nenne ta cikata da hira, ita dai ba tanka ta take ba don bata son magana, yarinyar Mama Zubaida ce ta shigo dakin tace “Nenne Uncle yana parlor yana gaishe ki wai” Nenne tace “Waye kuma Ankle, ke kuma shaidaniya don kar ki tafi islamiyyah kika fake da ciwo ko” Yarinyar dai ta juya ta fita, Nenne ta kalli Khaleesat tace “Wai ya zo gaisheni, shi baya gajiya da gaisuwa ne, so da yawa har nan dakin fa suke shigowa da Haiydar su gaisheni” Sallama Abdul yayi a bakin kofar dakin, Nenne ta amsa, Khaleesat ta jawo veil dinta ta yafa, bude kofar dakin yayi ya shiga, inda ya saba zama a dakin ya zauna ya gaida Nenne, da fara’a Nenne ta amsa tana masa sannu da zuwa ta mike ta bude fridge ta dauko masa ruwa da lemo, Khaleesat sai kallonta take, Abdul ya kalli Khaleesat yace “Ina wuni Hajajju” Khaleesat ta kallesa da sauri don mamakin Nenne ya sa ta manta bata gaishesa ba tace “Ina yini Ya Abdul” yace “Ya gida?” Tace “Alhamdulillah, ya aiki?” Yace “Alhmdlh” Nenne ta koma ta zauna tace “Ya su maman ka kuwa Awdul, ran nan Haiydar ke ce min yaje gidan ku har ya dubata da jiki, ashe bata da lafiya” Abdul ya sauke kansa yace “Eh bata da lafiya” Nenne tace “Ayya, Allah Ubangiji ya bata lafiya” Yace “Ameen” Khaleesat ta kallesa tace “Allah ya bata lafiya” Yace “Ameen, tana yawan tambayar ki kuwa, ta dade bata da lafiya, not too long ma ta tambaye ki she said she wants to discuss something with you, and I told her that won’t be possible cause you are a married woman” Khaleesat ta sauke idonta tace “Allah sarki, Allah Ubangiji ya bata lafiya” Yace “Ameen” Nenne ta mike ta dauko masa wayarsa tace “Wannan yarinya kafin ta tafi islamiyyah ta bani in ajiye ko da Haiydar zai shigo in basa, wai jiya an saka maka a caji ka tafi ka mance wayar” Abdul ya amshi wayar ya ɗan yi murmushi bai dai ce komai ba, yarinyar daxu ce ta sake dawowa dakin tace “Nenne wai anyi baƙo” Nenne tace “Baƙo kuma? In ji wa?” Yarinyar tace “Yanxu ya shigo parlor” Nenne ta mike ta yafa gyalenta tace “Bari dai in je in gani, gidan nan ai baya rabo da jama’a, duk samarin unguwan nan sukan shigo wani lokacin su gaisheni” Tana fita daga dakin, Khaleesat ta kalli Abdul tace “I will speak to my husband, if he permit me sai in je in duba Momy da jiki” Abdul ya gyada kai yace “Alright then” Mikewa yayi yace “Zan koma, a gaida min Umma” Khaleesat tace “Zata ji” Juyawa yayi ya fita daga dakin, Nenne na ajiye ma Ajay uban ruwan goran da ta kwaso a parlon Malam Ali sai ga Abdul ya fito parlon, ya karasa tsakiyar parlon suka gaisa da Ajay, Nenne na washe baki tace “Kaga ashe Yarima ne ya shigo” Shi dai Ajay kansa na kasa, Nenne tace “To ina Ahmad fa?” Ajay ya daga kai yace “Sun fita ne da matarsa” Abdul yayi ma Ajay sallama, Nenne tace “Har zaka tafi kenan Awdul” Yace “Eh zan tafi Nenne” Nenne tace “To a gaida mutan gidan” Yace “Za su ji in sha Allah” Kofa ya nufa Ajay ya bi sa da kallo, Nenne tace “Bari in ma Zahra’u magana ta fito ku gaisa Yarima” Daga haka ta nufi dakin Umma….. Bayan minti ashirin da zuwan Ajay gidan Khaleesat ta fito parlor nan ma Nenne ce ta takurata sai ta fito, tana fitowa taga baya parlon, ta fita compound har zuwa kofar gida taga babu motarsa, ta fi minti biyu tsaye bakin gate din, ta juya a hankali ta koma cikin gidan, wayarta ta tafi dakin Nenne ta dauka sannan ta shiga parlon Babanta ta kulle kofar ta zauna kan kujera tayi dialing numbersa. Sai da ya kusa katsewa ya daga, a hankali tace “Why did you leave?” Yayi shiru at first, sai kuma yace “Kamar ya?” Bata kara cewa komai ba, hawaye suka ciko idonta, after few seconds yace “Good evening Jeeddah” Da kyar tace “Ka dawo ka daukeni, na gama zaman da zan yi” Yace “A’a ni ban ce zan dauke ki ba, you can spend as much time as you want to spend, in dai kina bukatar wani abu ki gaya min” Bata ce komai ba, yace “Hello” Nan ma taki cewa komai, after some seconds ya katse wayar, sake kira yayi ta goge hawayen idonta tayi silencing wayar ta mike ta fita daga parlon taki picking call din. Wajen karfe biyar da rabi Khaleesat ta fito kofar gida bayan Mai gadi ya je yace ana sallama da ita, kuma a gaban Nenne da Ummanta ya bada sakon a bakin kofar parlor, da ace ba kowa Parlon da bazata fita ba, tana tafiya kamar warce aka tilasta ta karasa gun motar ta bude front seat ta shiga ta kulle motar bata dai kallesa ba, shi kam kallonta kawai yake, can yayi kasa da murya yace “Baƙon naku ya tafi?” Sai a sannan ta kallesa tace “Is that why you are giving me attitude?” Ya ɗan bude ido yace “Ni na isa? Naga baki da lokaci na ne shi yasa na tsaya lane dina” A fusace tace “To wajena ya zo shi baƙon? Ko kuma ni ce na kirasa nace ya zo gani nan na zo gidanmu?” Masifa ta rufe sa da shi tana fadin duk maganganun da ya zo bakinta, shi dai yayi shiru bai ce komai ba yana sauraronta, sai da ta gaji don kanta tayi shiru tana sauke numfashi, calmly yace “Allah ya baki hakuri” Bude motar tayi zata sauka ya rikota yace “Jeeddah” Ta fashe da kuka sosai, ya bi unguwan da kallo ganin babu kowa ya jawota jikinsa a hankali yace “Na fa ce kiyi hakuri” Cikin kuka tace “Ni ka kyaleni kawai” Yace “To wa zan rike idan na kyale ki?” Shesshekan kuka ta dinga yi yana bata hakuri har tayi shiru, ta hade rai tace “Sai kace wajena yake zuwa a gidan” calmly yace “Nasan wajen Noor yake zuwa ai” Tace “To da ka sani kake nuna min attitude?” Ya ɗan yi murmushi yace “Jiya fa mance ni kika yi a kofar gida, daxu kuma da na zo kika ki fitowa kika bar ni a parlor” Tace “Ni kawai mu tafi na fasa zaman gidan, bazan zauna ba” Ya ɗan bude ido don gobe za su tafi Benue da Jay kuma baya son ta sani, kwantar da murya yayi yace “A’a ki dai kara kwana biyu wife….” Don ya kauda zancen kafin ta dage sai sun koma gida yayi saurin canza maganar yace “So what did you think about his relationship with Noor?” Ta daga kai ta kallesa, a hankali tace “Nenne bata so, Ummata ma haka, duk tsoronsa suke ji” Ajay yayi shiru, calmly yace “But Abdallah have turned a new leaf long ago, kuma ina ji a raina da za a basa ita zai riketa da amana” Khaleesat tace “Nima ina masa kyakkyawan zato amma sun ki su gane hakan, ina kuma duba alkhairan sa a gareni” Ajay yace “Ya fadi intention dinsa a kan Noor din ne?” Khaleesat tace “A’a amma kusan kullum sai ya zo gidan nan” Ajay ya ɗan yi murmushi amma bai ce komai ba, Khaleesat ta kallesa a hankali tace “Ice- cream nake son sha” Yace “To shiga gida, let me go get you the ice cream” Ta turo baki tace “Tare za mu tafi, don sai na zaba wanda nake so” Bai ce komai ba ya tada motar yayi reverse suka bar layin, bayan sun siyo ice cream din zai maidata gida ta marairaice tace “Yanxu gida zaka kai ni?” Yace “Kin fiye rigima yarinyar nan” Kallonsa take cike da shagwaba, sosai take missing din kasancewa tare da shi ita kanta ta rasa gane dalilin haka, jiya ma kasa bacci tayi saboda wani urge da ta dinga ji, kamar zata yi kuka tace “To ni dai mu fara zuwa gida zan gaya maka wata magana, idan na gaya maka sai ka maida ni gidanmu” Yanda ta narke masa har ta kashe masa jiki, yayi kasa da murya yace “Me zaki gaya min wife?” Ta kai hannunta jikinsa ta taɓa sa tana masa wani kallon shagwaba, zaro ido yayi ganin inda ta taɓa masa, ta boye fuskarta da sauri tana murmushi, kawai ya tada motar direct ya nufi gida, jam’in da bai samu ba kenan na Magariba da isha’i ranan, ita kuma saboda kunyan yan gida kawai ta kira Ummanta tace sun je gidan Sarki ne. Washegari babu yanda Ajay bai lallaba Khaleesat ba akan tayi zamanta a Kano su je Benue su dawo amma kememe taki, Jay dai bai ce masu komai ba at first, amma da ya tuna condition dinta shi ma yayi mata magana ta zauna a Kano ba sai ta bi su ba kawai ta fashe masa da kuka kamar wanda ya fadi wani mugun abu, bai sake cewa komai ba ya kama kansa ya koma gefe ya bar ta da mijinta, haka nan suka kama hanyar Benue tare da ita….
