Hausa novels

Mejo Najeeb Page 34 By Autar Alheri

“Acikin soron gidan kuma setayi zamanta anan halima da Isseta kuwa suka riƙa hannun Ammi suka nufi cikin gidan…abakin panpo sukasamu innar halima tana wankin kayan sakawa.”Innarmu oyoyo innarmu cewar Isseta tana rungume innar halima datasaki baki kallonsu. “Maryama kece Hakan? Allahu Akbar maryama ina kikaje ne? Ina kikashiga aduniyarnan Maryama?Ina kikadosa alokacinda kikabar gidan mahaifinki? Maryama miyasa kakayi Hakan kina ƴamace? Maryama miye anfanin zamanki tare da halima idan bazaki iya ɗaukana uwa agarekiba, tanacikin maganar kuka yaci ƙarfinta…cikin sauri Isseta taƙara rungumeta sosai ajikinta cikin kukan itama tace “please innarmu Dan Allah kiyi haƙuri nayi kuskure amma kiyafemun wlh duk abinda kike tunani bahaka bane amma zanyi Miki bayanin komai dan Allah kiyi shiru….”bakomai maryama babu komai tafaɗa tana share ƙwallar idonta…hannunta Isseta taja sukaje suka zauna akan shimfiɗar da Halima tayi tazaunarda Ammin Isseta….Seda suka zauna tukunna Isseta taƙara bawa innar halima haƙuri tukunnah tashiga bata labarin abinda yafaru tsakaninta da mutanen gidansu abbanta yakoreta dakumu inda taje har kawo yanzu datake gidansu mijinta….tunda Isseta tafara bawa innar halima labarinta take kuka cikin mugun tausayin yarinyar shakka babu Taga rayuwa dominma Allah yatemaketa da wannan baiwar Allah (maah kenan) tashiga lamarinta da ba’asan iya inda abin zekaiwaba Allah yaƙara tsare gaba..Kallon Ammi tayi tace “wannan baiwar Allah fa daga ina kukazo da ita?? “Ammin Isseta ce inna itace wadda nake zuwa gunta asibitin mahaukata wadda kike bawa abinci idan zanje nakai mata..”ahh too Masha allah itace aibanganetaba halima tunda naji kince batada hankali amma kuma naga wannan kamar lafiyarta qalau.. “Hakane wlh inna bawanda zega Ammi yace batada lafiya kawaide dan bata maganane yanzuma Maah ce tace akawota wurinki Anan zata ɗan zauna kwana biyu muga yadda jikin nata yayi…Hakane kam to babu damuwa ai Allah dai yabata lafiya..Ameen y Allah suka amsa atare kana Isseta tace “inna akwai zam zam agidannan kuwa?? “Eh akwai barana ɗauko Miki tafaɗa tana Miƙewa domin taɗauko mata…Suna’nan zaune suna jiranta segata ko tadawo da gorar zam zam ahannunta tamiƙawa Isseta ɗin…bayan ta karɓa tayi kamar yadda maah Tagaya mata na saka wannan ƙololon acikinsu..Acikin gari Sosai brothers ɗin Isseta suka hargitsa garin gombe wurin neman ƙanwar tasu..domin kuwa nazeer yasanarda wani abokinshi yaron minister kuɗi dake garin Abuja wato fadeel sosai fadeel yashiga tashin hankali inda yabaza jami’an tsaro akan neman Isseta kab garin gombe dama wasu garuruwan dake cikin Nigeria….lokacinda su police ɗin suka Nemi picture ɗin yarinyar don anemota dakyar akasamu wani wanda suke tare itada zubaida da halima tun suna ƴan 10 year Kuma yanzu Isseta tazama cikakkiyar budurwa amma ba yadda za’ayi doline dashi za’ayi anfani wurin nemanta tunda babuwani, dashi suka shiga neman Isseta babuji babu gani..tofa Hakan yasa sosai police suka haddabi garin gombe babu shiga babu fita indai bayazama doliba kuma kowacce mota zata wuce se anbinciketa tukunnah zata samu damar wucewa ko governor jihar gombe dayaji labarin abinda police keyi a jihar yabincika se aka gaya mishi ƴar shugaban ƙasar Niger ce ta ɓata Alhaji Abdussalam idiris…aiyanajin Hakan yace aƙara lunka bincike da’akeyi duk inda wannan yarinyar tashiga abincikota yabada kwana ukku.😱 Tofa abu yabirkice agarin gombe abaki ɗaya duk wanda kecikin garin yasanda labarin ɓatan ƴar shugaban kasar Niger Hakan yasa abin ya fara yawo a social media.Gidansu IssetaYan kai amarya sun dawo lafiya Sedai sunzo suntararda baƙon al’amarin agarinsu dama gidansu baki ɗaya domin suna sauka kozama basuyiba samarin gidan suka Basu labarin abinda yafaru tundaga farkon zuwansu Hajiya Hannah harkawo yanzu…tunda mamansu yah balah taji wannan zancen hankalinta yayi mummunan tashi tanemi nutsarwa tarasa domin kuwa Taga zahiri tunda bataga iyya hassi ba agidan gaya kuma anbirkita garinsu sabida nemanta, “innalillahi wa’inna ilaihiraji’un to wai duk ya’akayi Hakan tafaru ya’akayi duk zamanda sukayida wannan yarinyar basusan cewar ba ƴar gidan bace seyanzu da rana taɓace? Wama zaatayiwa wannan tambayar acikin mutanen gidan? Mama bintu ko mlm Musa shida batama ganiba? Tab dijam lallai sun ɗaukowa kanshi jidalin dayafi karfinsu,,,tanacikin wannan zancen zucinne cikinta yamirda tasuri buta takewaya….afannin yaran gidan kuwa sosai zubaida da jidda suka yi farin cikin jin labarin Isseta ƴar wani babba ce ba ƴar gidan ba fatansu kawai ayanzu Allah ya bayyanata..anty bilki kuwa batayi farin ciki ba kuma batayi baƙin cikiba domin ita damuwarta ɗaya ce ƙwallafa ran datayi akan Isseta tasan ba samunta zatayiba domin kam koda anganta ayanzu tayi matanisa….haka dai gidan yazauna wasu na farin ciki wasuko na cikin magun tashin hankali yayinda yawon shiga ban ɗaki yaɗaurawa Mamansu yah balah aure.South AfricaJirginsu mejo Najeeb nasauka sekuwa ga motar hotel ɗin dasukayi bukking tazo ɗaukarsu dama su biyar sukaje captain Jameel, captain Ameer, sekuma su jagororin tafiyar…bayan sunje hotel ɗin kowannensu yaɗauki ɗaki ɗaya amma general parlor ɗaya ne bayan sunyi wanka sun huta duk suka bayyana a perlor suna fira inda kowannensu yabuɗe wayarshi tare da seta wayar da network ɗin ƙasar yadda Zasu iya magana a akowacce ƙasa batareda sunsaka layin ƙasar ba….aiko suna buɗewa Kiran Alhaji Abdussalam idiris nashigo wayar general faruk…cikin girmamawa yaɗaga yana gaida shugaban ƙasar nasu…Seda suka gama gaisawa kana Alhaji Abdussalam yashiga gaya mishi abinda kefaruwa dashi na ɓatan ƴarshi…cikin mugun mamaki general faruk yace “ranka yadaɗe dama Kanada ƴa mace bayan su sapwan?? “Eh faruk itace ƙanwarsu dan Allah idan kundawo daga tafiyar dakukayi kanemi temakon sojojin Nigeria wurin nemanta please, yafaɗa araunace cikin neman alfarma kamarba shugaba ba….ajiyar zuciya general faruk yasauke kana yace “shikenan ranka yadaɗe in sha Allah zamuyi iya baƙin ƙokarin mu Nida ƴan uwana zan sanar musu sutayani nemanta amma aturo muna picture ɗinta.. “toh shikenan za’aturo in sha Allah ngd sosai faruk.. “bakomai ranka yadaɗe Allah dai ya bayyana mana ita…ameen y Allah…daga Hakan sukayi sallama.”Miyake faruwane General?? Cewar general aliyu. “Wlh yarinyar shugaban kasarmu ne ta ɓata a Nigeria nan yabasu labarin abinda kefaruwa kamar yadda Shima alhaji Abdussalam ɗin yafaɗa mishi yanzu.. tunda yafara maganar gaban mejo Najeeb kefaɗuwa besan daliliba amma zancen yadakeshi sosai domin jiyayi kamar maryam ɗinshi ce taɓata🤩(alsarki mejo rashin sani tafi dare duhu) general aliyu kuwa sosai yajajanta abin shida su captain Jameel daganan suka shiga tsara yadda Zasu fuskanci abinda yakawosu..GombeGidansu HalimaWannan ƙololon na narkewa Isseta taɗauki ruwan taɗorawa amminta abaki tare da temakon halima suka samu tashinye kana suka shafe mata sauran akanta zuwa fuska kamar yadda Maah ta umurceta, bayan sungama suka zuba mata ido kawai suna kallonta kusan minti 10 basuga sauyi atareda itaba har aka yi minti 40 har sun fidda rai suna tunanin maybe bayanzu abin zeyi aiki ajikintaba kawai sukaga tafara hamma tana miƙa kamar wadda ake miƙewa duka kasusuwan jikinta namiƙewa arazane duk suka yi kanta suna neman riƙota kawai se sukaga tayi baya tafaɗi kwance se bacci…..dukkansu da ido kawai suka bita cikin tsoro da fargaba innar halima kuwa se addu’a take tofa mata domin dukkansu sun tsorata, kusan minti 30 tana akwance kamar matacciya sekawai sukaga tabuɗe idonta tare da yunƙurin mikewa zaune tana salati da bakinta take faɗar hasbinallah wani’imalwakin wani imalmaula wani imalnaseer…ido suka zaro atare suna ƙokarin temaka mata tamiƙe zaunen cikin mugun mamaki da tsantsar farin cikin ganin yau ɗaya sunga maganarta ara yuwarsu…seda tazauna Dede tukunnah tashiga binsu da kallo kamar yadda suma suke kallonta kafin tabuɗe bakinta dayayi mata nauyi dakyar tace hubbey…!

Back to top button