Matar Hariji Page 13 Romantic Hausa Novel
Kukanta takeyi yanaci gaba da gasa mata jikinta tana rirriqeshi har ya gama ya tayata tayi wanka ya koya mata yanda zata tsaftace jikinta sannan sukayi alwala suka fito tanata sauke ajiyar zuciya, a haka sukayi sallar magrib da Isha ya tashi yayi shafa’i da wuturi.Itakam kwanciya tayi saboda wani zazzabi da ya saukar mata, bayan ya idar ya dagata ya dorata a gadon yana yimata sannu itakuma sai qara langwabewa takeyi tana rawar sanyi, hankalinsa ya tashi matuqa babu shiri ya kira likitan office dinsu ya sanar dashi yana buqatar pen relief.Yana gama wayar ya fita ya samo mata abinda zataci s kitchen, daqyar ya rinqa bata tana hadiya daqyar tana narkewa a jikinsa tana kuka shikuwa duk ya rude tsoro ya kamashi a ransa yace “dama ashe haka duk wata mace takeshan wahala a darenta na farko amma wasu suke sarayar dashi a titi?”Bayan ya gama bata abincin ya miqe ya fita saboda jin da yayi ana taba qofar, ya bude suka shigo da likitan yayi masa jagora har dakin cikin harshen turanci yayi masa bayanin komai ya dubata sosai yace “kawai rashin sabone shiyasa Amma zata ware insha Allahu”Magunguna ya bata tare da shawara sannan yace masa idan ya samu lkc yaje zai hadashi da wani likitan gargajiya, gdy yayi masa ya rakashi ya dawo suka shata filin dambe akan itafa bazatasha maganin bature ba saidai yaje rugarsu gurin Boka Bawa ya karbo Mata magani.Kai abufa tun anayin na hankali har abu ya gagari kwandila ta rikice masa babu abinda takeyi sai kuka da surutai tana wani mimmiqewa, shikam wannan rana yayi danasanin tabata da yasan haka zata zame masa dama bai fara ba ya qyaleta yayita kallonta.Ganin dai abin bana hankali bane yasashi fara yimata addu’a yana tofa mata tanata buge bugenta ya riqeta gam a jikinsa sun dauki tsayin lkc a haka sannan yaji ta fara keta gumi tana sauke numfashi ya kwantar da ita ya qara qarfin A.C ya zauna ya zuba Mata ido yana kallon kyawun surarta mace har mace sai gidadanci.A ransa yana cewa wannan da ace kuma shidin wani cikakken namiji ne qila sai tayi sati tana aljanu, shima kwanciya yayi a gefenta ya rungumeta tsam a jikinsa da haka bacci ya daukesu, washegari lfy Lau suka tashi sai zazzabin dabai saukaba da kuma wani mugun tsoronsa da takeji.Excuse ya bayar a gurin aiki ya tsaya kula da ita takuwa narke ko miqewa yace tayi sai tayita kuka wai ita ciwo ya faffarkata ya yayyagata🤣Kayy Lameer yana ganin tujara ko tabata bai isa yayiba saita rushe da kuka haka ya rinqa binta.Kwanansu biyu a Lagos ya daukar Mata malama Salmah babbar macece mijinta ya rasu anan gaban quarters dinsu kadan to tanada ilimi sosai dan koyarwa ma take a wata secondary itace zata zama malamarta, duk wani Abu da yasan zaa buqata ya siya suka fara karatun addini dagashi har Malama Salma sunsha mamakin yanda ta iya tundaga izu daya har zuwa izu biyar duk wata aya da aka datso Mata saita cafe.Gata Allah yayi Mata baiwar saurin fahimta ko a na bokon ma da wuri take gane abubuwa, bayan malamar ta gama ma ta tafi zama sukayi dashi yana qara koya mata.Cikin abinda bai wucce wata gudaba ta iya rubutun hausa da karantawa duk abinda aka rubuta zata karanta, nan suka koma koya Mata turanci shima babu wata wahala ta fara iyawa ga karatun addinin shima shiga yake dake fresh brain dinta take gata gifted aikuwa yanajin dadin hakan sosai.Gwanin dadi suke tafiyar da rayuwarsu da malamarta ta dauketa tamkar yarta ko girkin ma dayace zai kaita chattering school ta koya cewa tayi ya bari zatake koya Mata, idan suka gama karatun boko sai su shiga kitchen suyi girki kala daya da lemo shima don kada su cika ta kasa ganewa.Duk bayan wata guda yake zuwa kano yayi sati ya dawo cikin wata ukun abubuwa da yawa sun faru Jiddoh ta fara wayewa ta gegije ta fara zama babbar mace saboda bayayi mata kiwon mugunta kuma bai qara yunqurin kusantarta ba ko wasannin ma da yake dan koya Mata har yanzu kuka takeyi tanace masa iskanci ne.Daqyar da taimakon Malamarta ta daina ce masa Kado ta koma kiransa da babe aikuwa tunda babe ta zauna a gabanta a gaban uban kowa kiransa takeyi da babe shima yace mata babe.A bangaren Mubaraka ma Abu da dama sun faru harga Allah ita mantawa ma takeyi da cewar mijinta yanada wata Matar bayan ita saidai idan farkanta daya kwallafa rai akan Baben yayan nasa yayi Mata mgn kasancewar shi yakan kirashi haka video call to wani lkcn idan yana gda zanganshi rungume da Hauwah din ko kuma yaji yana Kiran babe.Hakance tasa kullum yake qara kwadaituwa da amaryar yayan nasa yakeso shima yaji abinda yayan nasa yakeji a jikinta.Itakuwa Jiddoh harkan gabanta kawai takeyi Koda ya siya mata waya ma babbar gaske bata wani damu da itaba garama idan Zaliha qanwarsa ta kirata takan dade suna waya kasancewar bayan Lameer din da Alh Ali mahaifinsa sai Zalihan sune kadai suke sonta sauran duk yan partyn Mubaraka ne garama babban yanansu Hamza shikam babu ruwansa duk da Mubaraka ta kasance qanwar Matarsa.Wata dawowa da zaiyi lkcn sunada wata bakwai da aure yace ta shirya su tafi tare aikuwa tayita murna harda kissing dinsa kasancewar malamarta ta koya mata kissa da kisisina sinka sinka Lameer yanashan shagwaba a gurinta kaya kuwa batasa manya saidai idan fita zasuyi.Ranar juma’a bayan ya tashi daga aiki suka shirya suka tafi qauyanci da gidadanci duk babu sai wani yauqi takeyi tana narkewa a jikinsa shikuma sai tarairayarta yakeyi yana biye mata ko a mota drivern yasha kallo yanda suketa rungumar juna suna tsotse bakin junansu yana wani shafeta abin kamar a amurka, haka da suka hau jirgi ma ta lafe a jikinsa har yanzu mugun tsoron hawa jirgi takeyi shi kuwa ko a jikinsa kodan aikinsa ne tuqa jirgin oho.Tun kafin su sauka kasancewar shigowar dare sukayi ya turawa Muneef saqon zuwansu yace yazo ya daukesa a airport, lkcn suna tare da Mubaraka suna qullah yanda zasuyi su dauke hankalin Lameer din dagakan cikin Mubaraka daya shiga wata na tara.Kuka takeyi masa tana fada masa ta lura kamar Lameer bayason cikin nata kamar yanda yaso na Fadwah nan take bashi lbrn yanda sukayi tace “ranar dana fada masa inada ciki wata hudu a kwance yake amma zabura yayi ya miqe yace “yaushe na samu ciki da har yakai wata hudu?Saida na tubure masa na rinqa kuka nace masa ashe duk zaman da mukeyi zargina yakeyi, to ganin na tashi hankalina Ina Shirin kiran Hajiya na fada Mata yasashi cewa shifa ba wani abu yaje zargi ba kawai dai mamaki yayi, to da qarya da qarairayi nace masa ai kwanciya yayi yanzu shine ya tashi”Sauke numfashi Muneef yayi yace “dadina dake kinada kwanya sai ki tashi ki gyara gashinan isowa yanzu ya turomin saqon naje na daukosa a airport” a tsorace ta dafe qirji tace “na shiga uku yanzu jin dadina zai yanke kai nifa yanzu ko sha’awarsa banayi Allah”Tafawa sukayi ya qifta mata ido yace “karki wani damu muna jorner” da haka ya fice itakuma ta tashi ta fara dauke duk wani abu dazai iya bashi damar gane wani abu, saida ta gama komai sannan ta shiga wanka ta fito ta zauna ta sheqa kwalliyarta ta fito parlourn ta harde.


