Gargadar So Chapter 23 By M Shakur
Kawai tausayi taji tabama kanta saisa takasa rike hawayen dan tana cikin jarabawan rayuwa, she’s 30 batai aure ba babu miji, kowa is pressuring her, her biggest support, her biggest fan is her best friend Ni’ima da tun suna yara suke tare, kawancen amana da iyayensu sun zama daya ma, she’s not a small girl when she sees love she knows love, wani irin kaddarane wannan? Baban Yaseer can never be her amsa nooo please Ya Allah not my best friend’s husband, ganin hawaye yakasa tsayawa daga idanunta asanyaye Aliyu yace “I’m here for you, I will forever be right here! Ina taredake Hawwa in good times and bad times, dare da rana, I’m right here” ahankali yadaura hanky kan fuskanta wani sanyi taji dayasa ta lumshe idanunta da sauri takai hannunta i ta karbi handky tana goge fuskanta, tadanja majina dadan ragowan karfin zuciya tace “maisa kabiyoni Baban Yaseer? Nace kabiyoni ne must u follow me everywhere? Must you get involved in my issues? An gayamaka I can’t take care of myself ne ko I need your protection”? Ataushashe yana kallonta ganin ranta abace, cikida zazzafan kauna yace “sabida bazan taba iya bacci ba bayan nasan kina irin wannan hanyan, I care for you” ahankali Hawwa tace “wat if something happens to you”? Asanyaye yace “I don’t care koma menene yasameni I just wanna keep u safe” abu tahadiye a wuyanta sai kawai ta juyo ta yunkuro tace “I need to change my tire, spare tire na booth” matsamata yayi tafito tai booth yabi bayanta tana bude booth din takai hannunta zata dauki tayan yarigata dauka yace “let’s go muje motana ki zauna” tsayawa tayi tana kallonshi, “muje dan Allah Hawwa dare ne mu kadai a titi” batai musu ba yayi wajen motanshi da ita yabude mata gaba ta shiga ta zauna ya maida yarufe sannan yadawo booth nata yaciro supanu yaje gaban motan yana kwance tayan dayay less, sosai Hawwa take kallonshi kaman yauta fara ganinshi abubuwa da dama suna yawo aranta, tana zaune awajen saiga yan sanda sunzo wajen fitowa tayi ta nuna musu ID card dinta tayasu gyara tayan sukayi, suna gamawa Baban Yaseer yabar musu motanshi yabasu kudi su tsaremai sannan yashiga na Hawwa, hakan yasa ta zagayo ta zauna ya kunna motan yaja waje tajuyar da kanta tana kallo ahankali yace “do you think is right kije kidan Anty ki middle of the night? Kodai idan mukaje zaria namiki booking hotel, idan gari yawaye saikije”? Tana kallon waje batare data juyoba tace “zan iya zuwa wajen Ammi na anytime anyday” gyadamata kai yayi bai sake magana kusan 30min sai chan yace “Hawwa it’s okay not to be okay” lumshe idanu tayi tabude anatse yace “you got this! Karki bari kalaman Baba natabaki, karki karaya, I hate seeing you like this” yadan kalleta yanda take kallon waje yace “kinji” gyadamai kai tayi daganan basu sake magana ba harsukakai zaria, nunamai hanya tadingayi har zuwa wani gida a wani anguwa mai dan kyau da mutunci, saukowa tayi ta zagayo tadan kalli Baban Yaseer dake kallonta tace “dan bani car key” zare key motan yayi yabata yana kallonta, a gate tasaka wani key dake jikin motan tabude kofan tashiga ciki tana sallama tsakar gida ne mai fadin gaske, tourchlight taga an haskewa taji muryan yan dattijuwa na “waye awajen gate din nan” ana bude kofa da gudu Hawwa tai wajen kofa matan na bude kofa dadan charbi a hannu Hawwa ta rungumeta da karfi tace “Ammiiii na” ririketa matan tayi tace “Hasbunallahu wa ni’imal wakeelu Hawwa kece da daddaren nan, ke tashi kiga na ganki lafiya Hawwa” tadago Hawwa daga jikinta murmushi Hawwa tayi tace “Ammi baban Naseer na waje bani key gate na bude ya shigo da mota saiya dan zauna zuwa safiya yakoma Abuja” wani dan kallo Ammi tamata tace “Baban Yaseer kuma? Aliyun Ni’ima”? Gyadamata kai Hawwa tayi Ammi tabata key fita tayi Ammi itama tafito tana haskawa bude gate din Hawwa tayi yashigo da motan ta maida gate din tarufe Ammi tace “maraba da Baban Yaseer, sannunku sauko sauko” Saukowa yayi kanshi akasa cikeda kunya yace “Ammi mun sameku lpy” cikeda fara’a tace “Alhamdulillah ina jikokina? Da y’ata Ni’ima hope duk suna lpy”? Akunyace ya gyadamata kai yace “Alhamdulillah” murmushi tayi tace “muje nakaika side din su Baffa ka kwanta bazakabi hanya da tsakar daren nan ba sai idan Allah ya kaimu da safe akawo maka abinci ne”? Dasauri yace “a’a Ammi dare nayi bana iya kara cin abinci” satan kallon Hawwa yayi dake gefen Ammi tana wasa da hannunta yamika mata car key ta yace “take” dan dagokai tayi kafin tasa hannu ta karba Ammi tace “muje” suka wuce suna hira itakuma tawuce wajen motar ta booth taciro akwatinta ta gu huri ta shiga dashi ciki, bayin Ammi tafada tana cikin wanka Ammi tashigo tasami waje ta zauna yanda ta ganta haka tasan dawani abu.Towel din Ammi ta dauro tafito Ammi ta kalleta tace “zonan Jidda” kayan shafanta tadauka tazo kusada Ammi ta zauna tana bata cream dinta a hannu Ammi ta karba tana sauke ijiyan zuciya tace “meya faru?” Dan shiru tayi sabida kawai taji komi yadawo mata sabo, hannunta Ammi takama tana shafa mata mai kafin takalleta strictly tace “ya akayi kike tare da mijin kawarki at this type of time and day Hauwa’u”? Baki tabude zatai magana saikuma tadan sauke ijiyan zuciya Ammi tace “speak” anatse tace “Ammi wlh I don’t know cus ni ko kiran Ni’ima ma banyi da abun yafaru ba, probably Baba ne yakirasu to check ko ina gidansu, saita kirani daga gayamata ina hanya zanzo wajenki hala to shine ta turoshi” Ammi na kallonta ta sauke ijiyan zuciya tace “Hawwa babu wani naki dabaisan relationship dinki da Ni’ima ba, yarinyar nan kawar amana ce, yanda kika daukeni haka tadaukeni, don’t ruin friendship naku under no circumstances, you know maganan danake” gyadamata kai Hawwa tayi tace “nasani Ammi” saikuma ya tashi daga gadon ahankali zuwa akwatin nata tadauki dogon riga na bacci tasaka ta zare zanin wankan ta shanya ta dawo gadon tahau ta daura kanta kan cinyan Ammi tareda sauke ijiyan zuciya tabude watsapp tama Ni’ima chat “Just got to Ammi’s place, Ni’ima why did you send Baban Yaseer? Why” tura chat din tayi taga yayi layi biyu alamun datan ta a kunne amman ba’a budeba jira tayi ta amsata but shiru ijiye wayan tayi ahankali tana lumshe ido kafin kaceme bacci yayi awon gaba da ita dan tagaji yau. Yanda bacci ya shigeta yasa Ammi bata tadataba ta shiga dakin yammatan ta su biyu Amina da Ramla ta tadasu don salla itama tayi sannan tasa suka shiga kitchen cus taji Baban Yaseer yafice salla.Wuraren 7 yashigo gidan a tsakar gida yaga Ammi tareda Ramla datake gwadama yanda ake buga kosai sun hada gawayi dan basu soya kosai a gas, ganinshi yasa Ramla tace “ina kwana Baban Yaseer” murmushi yamata yace “lpy lau” yace “ina kwana Ammi” murmushi tamai tace “an tashi lpy sannu da kokari fa Aliyu, Allah ya maka albarka, bari yanzun nan zan kawoma kosai nariga an dama kamu saina kawoma kayi karo kafin kashiga hanya” girgixakai yayi yace “no Ammi bazanyi kari ba bana kari da wuri yan sanda na barma motana chan hanyan kaduna dole nafita yanzu Ammi” yayi maganan yana ciro kudi daga aljihunsa daya samo a ATM fitan nan nasa a kujeran tsakar gida dake gefen Ammi ya ijiye kudin yace “aba Hawwa idan ta tashi, wannan kuma aba su mai girki” cus baisan sunan Ramla ba, hade fuska Ammi tayi tace “kaga dauki kudaden nan karna saba maka Baban Yaseer” dasauri yajuya yayi gate yace “Ammi nagode” yafice dasauri dudda har ranshi yaso yaga Hawwa kuma sarai ta tashi tun dazu har salla ma tayi kawai bataso ta ganshi ne kawai yasa bata fitoba, tanajin fitanshi tafito falo Amina dake gyaran falo na ganinta tai ihu sosai “Ramla Ya Hawwa ta tashi” tawani zo dagudu tai tsalle tafada jikinta Hawwa tai dariya sosai Ramla tasaki kosan datake ta rugo dakin aguje itama tai tsalle kawai Hawwa tai kasa suna kanta, Ammi ta shigo dakin ta kwadamusu duka abaya tace “Oya ku dagamin ita bance ku karyamin diya ba” kankamesu Hawwa tayi tace “Ammi I missed my babies” hararansu Ammi tayi tawucewarta tafito tashiga soya kosan da kanta tunda taga shirme suke Hawwa tafito tareda su tana Ammi wai ina su Hamza da Ahmadu? “Hamza na school, Ahmadu yace anjima zaizo da matarsa su gaidake, Baffan ku na dayan gidan sai gobe zai dawo nan amman hala anjima ki gansa” murmushi tayi ta karbi kosan tana soyawa su Ramla nabata labari she looks so happy Ammi tayi murmushi ganin ayanda idanunta sukadan kumbura jiya sabida kuka sun sauka sosai yanzu kaman batayiba.Wuraren 12 Ni’ima taji ana bude gate, tunda tasan Hawwa bata taba taga miss call na Hawwa taki kiranta back ba sai yau, nor tai replying message nata, jiya tamata message shiru, da safen nan takirata sau biyu ba amsa sai tamata magana tace “call me idan kin dawo daga hospital Best, su Ramla nata tambayanki”.Jin ana bude gate yasa ta tashi dagakan kujeran tawuce da sauri tashiga kitchen, ita kadaine agidan su Yaseer na school sai though 1 suke tashi on Friday, sallama taji yayo yashigo abu kawai taji yatokare mata zuciya tama kasa amsa sallaman, kofan bedroom nasu taji yabude ya shiga sannan tasauke ijiyan zuciya tashiga fito da flasks da plates tana ijiyewa a dinning tazauna a dinning din saikuma chan tamike tawuce bedroom din nasu ta zauna bakin gado tanajin karan zubam ruwa ba’a wani jimaba yafito daure da towel a waist yadan kalleta hada idanu sukayi tana kallonshi kaman yau tafara ganinshi dauke kai yayi da sauri yawuce wajen wardrobe nasu yace “wife ya gida? Su Yaseer basu dawo daga school ba”? Tana kallonshi kaman gunki tace “basu dawo ba tukunna” gyadamata kai yayi ya tsaya gaban mirror yadau mai yana shafawa yakasa wani maganan, kalulu ta hadiye a wuya tadan bude bakinta kadan saikuma tarufe sai chan kuma tace “ka kuwa sanar da Hawwa kana sonta?!” Dum! Haka maganan yadaki kunnenshi man daya diba zaikai jikinshi yashafa kasa shafawa yayi yajuyo yakalleta suka hada ido yace “wace irin magana haka kikeyi Ni’ima”? Mikewa tayi a fusace ta nunashi da hannu tace “don’t you dare lie to me, nasan son Hawwa kawata kake why are you hiding it? Eh maisa kake boyewa bayan ka kamu da mugun sonta” hade giran sama dana kasa yayi yadan dafe kanshi yace “kinsan mene? I don’t want your drama this afternoon I had a long journey I just want to sleep peacefully, dan Allah ki kyaleni I don’t know wat you are talking about” yajuya zai wuce yanda abu kecin zuciyan Ni’ima batasan sanda tai ihu ba tace “Namiji munafuki, namiji mara amana, namiji butulu! Aliyu I know everything! I know about hotunan Hawwa dake wayana da duk ka sace suna wayanka, I know kana stalking friend dina kana biye biyenta kana mata hotuna without her knowledge, how dare you kana karyata cewa sonta kake don’t be a coward, kaji be a man for once mayaudari kawai” “Ni’eematullah!” Baban Yaseer yakirata azafafe idanunshi sun kada sunyi ja, yace “yes yes yes I love Hawwa! Yes inason kawarki! Yes I love your best friend Ni’ima and so what!?” Hannu Ni’ima takai tadaura kan bakinta tana kallonshi completely heart broken hawaye masu jarababben zafi na saukowa daga idanunta, yace “do you think I’m happy with the fact that I’ve fallen in love with your friend? Kin dauka choice dina ne? Kokin dauka son Hawwa ya tambayi izinina? Why are you insulting me calling me names mena miki? Tayaya na yaudareki? Kinga na sanar da ita ina sonta ne? Ko kinga nayi wani abu ne? I love Hawwa yes and I also love you! Sabida I don’t wanna hurt you saisa all this years ban auri Hawwa ba, I can’t bring kaina into to hurting u that much, nasan yanda zakiji, I know wat kishi is! Yes I love Hawwa, and I also love Ni’ima, nima I don’t know mesa Allah zai dauramin soyayyan kawaye biyu kuma best friends, I know this same reaction kikeyi maybe na gayama Hawwa ina sonta zatamin more than yours, so just let me be, ban miki komiba ban yaudareki ba, and bance zan auri Hawwa ba cus nasan bazata yardaba, but all I know is harna mutu bazan taba daina son Hawwa ba, son danake mata yawuce tunani na, when it comes to Hawwa banmasan me nakeyi ba, I just want her to always be happy, I want to protect her, and always be there for her and make her happy, that’s just it” yayi maganan yana komawa wardrobe yadauki kayan dazaisa yafice daga dakin, Ni’ima tafashe da kuka bana wasaba gwanin ban tausayi tana zubewa akasan dakin…….
TOH JAMA’A IMAGINE MIJINKI NA SON BEST FRIEND DINKI, YAYA ZAKIJI???
HOW WOULD YOU HANDLE THE SITUATION???
KAI YAYA ZAKIYI NE????
IDAN KECE NI’IMA MEZAKAYI KO YAYA ZAKIYI DA HAWWA???
THINK AND TELL ME
Visit Kundin Hausa Novels For More Novel

