Hausa novels

Fentin Zina Page 35 Hausa Novel

***Cikin sanyin murya Abdul ya kira sunan Ameena da saida sigar jikinta ya soma tashi tayi maza ta kawar da tunanin daya shigo kwakwalwar ta don tasan zaiyi amfani da wannan hanyar ne kawai domin ya yaudare ta ta fada cikin tarkon shi don haka ta juyo cikin zafin nama da ita kanta bata san tana da shi ba ta nuna shi da yatsa tace.Tun wuri ka kwashi kafafunka ka bar wajen nan kafin ka tunzura ni in aikata maka ba daidai ba don zan rufe ido neinci mutumcin ka sosai don haka ka gaggauta barin nan wajenkuma kada ka sakegigin dawowa, daga haka taja kwafa ta nufi kofar da zata sada ta da cikin gida tana cewa lokacin da take kallon fateema. Ki tabbatar ya bar munshago tunda babu sisin sa a ciki. Tayi shigewarta ciki. Mikewa yayi sum-sum ya fice yana waiwayen kofar databi.Koda inna ta dawo fateema ta bata labarin abunda ya faru cewa tayi Allah ya kyauta amma kunyi daidai gara kada ya sake dawowa tunda bashi da amfani dawowar.Ameena dake kai lomar tuwo bakin ta tace nama rasa meya kawo shi idan ba neman magana ba wallahi ko tausayin shi banji ba tunda ban aikeshi ya aikata abunda ya aikatadinba.Hakane adda kuma bayan duk yasan haka zai wani zo mana gida da fuskar shi kamar an soya mai.Hira suka cigaba dayi kamin zuwa can Ameena tamike ta barsu ta shige daki.*****Bikin fateema ya rage sati uku yau ta tashi da zazzabi mai zafi sosai don haka baba malam ya baiwa Ameena kudi ta kaita asibitin kudi don layi yayi yawa sosai a asibitin gwamnati ga rashin zuwan likita da wuri sannan idan yazo dinma baifi yayi attending mutane biyar zuwa goma ba yace ya tashi.A gaggauce suka shirya mai napep ta tara musu tana rikeda hannun fateema ta fada mishi sunan asibitin da zai kaisu, tun shigarsu asibitin abubuwa da yawa suka shigadawo mata cikin tunaninta nan take wani faduwar gaba ya risketa sai ta shiga karanto addu’o’i a zuciyarta kamin ta samu sassauci suna sauka suka shiga reception inda zasu zauna bin layin ganin likita, ki zauna bara in yanki kati inzo. Ameena ta fada, gyada kai fateema tayi kawai don ko magana ma bata son yi. Barin gurin Ameena tayi ba jimawa ta dawo daidai layi yazo kansu don dama mutum biyu ne a gaban su. Bata kai ga zama ba suka shige bayan na ciki ta fito, kallo daya doctor Amina Abdulkadeer ta mata ta gane ta don ta matukar bata tausayi a wancan lokacin shiyasa har ta iya rike fuskar ta, irin kallon da taga likitar na mata sai ya sanyaya jikinta ta shiga takurewa da dari dari har suka zauna a inda aka tanada domin zaman patient. gaisheta sukayi inda likitar ta dauki empty file ta saita biro domin fara rubutu ta dago ta kallesu ta tsaida idonta akan fateema tace meye sunan ki?.Fateema cikin muryar rashin lafiya tace sunana fateema Ibraheem.Rubutawa likitar tayi kana tace meke damun ki, ina ke miki ciwo?Ina dan jin ciwon kai amma ba koda yaushe ba sai zazzabi kuma cikina daga ta sama kadan yana ciwo sosai kamar ana hura mun wuta a ciki haka nike ji.Dan kallonta dr. Amina tayi ta rubuta wani abu jikin wata karamar paper ta mikawa Ameena tace gashi zaku je lab kuyi gwaji sai ku kawo sakamako. Karbar takardar tayi ta kama hannun fateema ta mikar da ita suka je lab din sunyi sa’a babu layi aka dibi jinin ta babu jimawa sakamakon ya fito suka koma office din likita, tun daga bakin kofa kamshi mai dadi ya ziyarci kofofin hancin su hatta da fateema da take cikin halin rashin lafiya sai data lumshe ido da sallama suka tura kofar suka shiga Ameena ce a gaba cikin natsuwa ta zauna a inda ta tashi dazun ta kalli gefen da saurayi matashin da bazai wuce shekaru talatin da uku ba zaune ya daura kafa daya kan daya yana dannan waya kyakkyawa ne sosai dinnan kuma farine shima kamar ta, sam hankalin shi baya kansu hasali ma bai san wai wasu sun shigo ba.Ina takardar sakamakon gwajin?. Dr. Amina ta fada da dan karfi don wannan ne karo na biyu data yi magana amma bata ji ba.Firgigit Ameena ta dawo daga duniyar tunanin data fada ta sosa keya Allah ma ya taimaketa ba barin da yake take kallo ba ta mika ma likitar karamar paper din, karba tayi ta duba sosai kamin tayi rubutu a cikin file din sai ta kara rubutu a wata karamar paper banda ta farkon ta mikawa Ameena ta karba sai ta soma bayani kamar haka.Tana fama da malaria sosai a jikinta ta kiyaye kwanciya cikin rigan sauro, sa’annan tana da ulcer peptic mai yawa shima saboda haka zamu bata gado a mata treatment a daura ta a kan magani amma dole sai ta kiyaye wasu abubuwan cinta kamar kayan ruwa na gas, da yaji da man-gyada ki kai wannan takardar female ward zanzo da kaina in mata treatment zasu kawo komai kafin inzo, ta maida kallonta kan fateema tace sannu kinji Allah ya sawwaka.Gyada kai tayi, Ameena tace mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi Allah ya kare ki yasa kifi haka Allah ya kara miki budi na alkhairi.Ammar dake zaune daidai ajiye wayarsa daidai ta shiga kwararowa mahaifiyar sa abar sonsa da kaunarsa wannan addu’ah da muryarta mai zaki data yi amsakuwwa a cikin kwakwalwar sa gaba daya ya dago manyan idanunsa masu yin jagora wurin daukar hankalin ‘yan mata ya sauke a kansu daga inda yake ya shiga yi musu kallon tsab nan take yaji wani abu da bai san menene ba yana fisgar zuciyar shi zuwa ga yarinyar da bai taba ganinta ba, bai san ya zura mata idanu ba har saida yaga sun bacewa ganin shi ma’ana sun fice daga office din sai yayi maza ya daidaita natsuwar shi tun kamin mahaifiyar shi ta lura da yanayin daya shiga.Koda sukaje female ward suka nuna takardar da sauri aka basu gado wanda yake kusa da bakin kofa nan takai fateema ta kwantar da ita.*****Dr. Amina tana kokarin mikewa Ammar ya rigata tashi ta bishi da kallon tuhuma ta mishi alama da hannu akan ina zaka je? Murmushi yayi ya sa hannu ya shafa sumar kanshi ba wani mai yawa sosai bane amma akwai sumar kuma yasha gyara ba kadan ba. Ammy zan raka kine kinsan bana so ina nisa dake! Ya fada a shagwabe kamar wani karamin yaro.Haba Ammar ba jimawa zanyi ba ka zauna yanzu zan dawo.Make kafada yayi irin yadda yara keyi idan basa son abu yace nidai zanje ammy kiyi hakuri kije dani dan Allah. Ya fada yana kara narkar da murya domin zuciyar shi azalzalarsa takeyi akan yaje ya sake ganin wannan yarinyar.Toh shikenan anace idan ka nacewa mutum kan abu tofa bai isa yayi sakat ba ba tare da ya samar maka abunda kake so ba.Murmushi yayi daya sa dimple dinsa suka lotsa yace ina kaunar ki ammy na…Daga haka suka jera zuwa female ward, fateema tana kwance Ameena tana zaune a gefenta ta kusa da kafafunta ta mika hannu ta kama kafafun kamar mai shirin yi mata addu’ah tace yaya kikejin jikin yanzu fatyyy?. Dan yamutsa fuska tayi tace adda wallahi babu sauki ji nake kamar mutuwa ma zanyi.Kul! Kada na sake ji ko so kike ki daga mun hankali na yanzu dan Allah ki bar fadin irin wannan maganar idan na rasa ki ni kuma in zauna da waye? Wa zai kaunace ni ya fahimceni kamar yadda kikeyi yanzu fateema? Insha Allah zaki samu lafiya da yardar Allah kinji bari likitar tazo ta miki abunda ya kamata zai dan lafa kinji.Gyada kai tayi ta lumshe ido.Sannu fateema kinyi ta jira na ko sorry ya jikin? Dr. Amina ce ta fada lokacin da take shigowa cikin inda fateema ke kwance tana kai hannu jikinta don taji yanayin zafin.Bude ido fateema tayi tace da babu sauki.Kamshin daya daki hancin ta shiya tilasta mata lumshe ido ta bude su ta sauke ajiyan zuciya amma bata bari fuskarta ta fallasa abunda ke zuciyarta ba.Shima a nashi bangaren zuciyar shi ce ke bugawa da sauri da sauri bai taba fadawa a tarkon so ba hasalima duk wani mai bada muhimmanci ga soyayya a matsayin wanda baisan me yake yi ba yake kallonsa sai yau lokaci guda rana tsaka ya tsinci kanshi dumu dumu a cikin kauna tsundum.Allah Allah yake ta juyo su hada ido amma taki sai wani abu ya fado masa a rai ya matsa kusa da Dr. Amina ya duba priscribtion na abubuwan da suka kamata a mata ta girgiza masa kai tace Ammar ka faye kafiya wallahi ka bar mun aikina ka wuce office ka jirani.Lumshe ido yayi ya bude yace ammy bani da lafiya ne nima so nake idan kin gama duba ta ki dubani nima.Rikicewa tayi ta hau tattaba jikin shi ko zata ji alamar zazzabi amma bata ji ba duk da haka hankalin ta bai kwanta ba ta dube shi tama mance tana kokarin treating patient ne( Ammar shine kadai dan da ta haifa a duniya shiyasa take masa wani irin so na fitar hankali).Ammy ki duba patient din ki.Ok tace ta juya kan fateema tace sorry my dear ta daura mata ruwa ta mata allurori ta yima Ameena bayani sosai taja hannun Ammar suka tafi office, ba don ya so ba yabi mahaifiyar shi dukda yadda zuciyar shi ke tura shi kan ya juyo ya kara kallon ta, babu halin yin hakan don ba yanzu daga haduwar farko yake son wani ya fahimci alakar da zuciyar shi ta daukar masa ba da ganin farko.Cikin wayo da dabara ya duba file din fateema ya dauki address ba tare da Dr. Ameena ta sani ba.Kwanan su biyu aka sallame su kuma kullum Ammar sai ya pake da zai raka ammy domin kawai yazo ya ganta yaji dadi kuma har yau ammy bata gano manufar shi ba.*****Tana zaune a shagonta tana dinka wani zanin gado cikin wanda take some hadawa fateema taji karar tsayuwar mota a kofar gidan su bata kawo komai a rai ba ta ci gaba da aikinta cikin natsuwa da kwanciyar hankali sai ga wani yaron makwabtan su ya shigo shagon yace anty Ameena ana kiran ki a wake wai ince miki kinyi bako. Duban yaron tayi tace bako kuma? Kuma wai ni ameenar? Kaje kace wai waye ne?.Yaron ya juya ba jimawa ya dawo yace wai yace don girman Allah ki fito ko ki bashi izinin ya matso kofar gida.Jim tayi kamar tana tunani sai can tace ba matsala kace ina zuwa. Fita yaron yayi ta dan tsaya tayi jim daga bisani tace cikin ranta um koma waye oho bari dai inje in gani don nasan Abdul dai bazai dawo ba.Koda ta fito ya juya baya yana waya cikin kasa da murya ya jingina a jikin motar shi, ta karasa kusa dashi tare dayin sallama.Juyowa yayi da jin zazzakar muryarta yana sakin murmushi ya amsa sallamar, ita kuma zaro ido tayi cikin zuciyarta tace na shiga uku me kuma wannan yazo yi a nan?. Sai taji ya bata amsa da cewar, nazo ne na karbi abunda kika sace mun a asibiti. Bata san zancen ya fita ba sai da ta ji ya bata amsa kirjinta ya buga dummmm ta dafe kirjin a rude cikin in ina tace innalillahi, sai ya karasa mata da wa inna ilaihi raji’un.Dan Allah Kayi hakuri wallahi bamu taba sata ba kuma bazamu fara akan ku daga kwanciya a asibiti ba kuma ga kamilar mace mutumiyar kirki irn Dr. Ameena wallahi ko wani naga zai aikata mata laifi sai inda karfina ya kare don zan kare ta.Murmushi ya saki a karo na barkatai yace yarinya kenan, toh ki kwantar da hankalinki ki bar daga wa Ammar hankalin ki da farko dai sunana Ammar sadeeq mahaifina dan kasuwa ne ya rasu shekaru hudu baya haka nima dan kasuwa ne sosai mahaifiyata ta jima tana mun sha’awar inyi aure amma banyi gamo da yarinyar data kwanta a raina naji na samu natsuwa da ita ba sai ranar dana fara ganinki a asibiti a takaice dai INA SON KI,Wani irin dum taji a tsakiyar kanta take tsigar jikinta ya tashi zuciyarta ta shiga hali na tashin hankali irin wanda mutum ke shiga yayin da ya rasa wani zabi ya kamata yawa kansa.Shima a nashi bangaren shirun daya ji sai ya saka shi cikin rudanin kada taki amincewa don ya tabbata idan ta ki amincewa da soyayyar shi ikon Allah nekadai zai iya hana zuciyar shi bugawa cikin kasa da murya ya soma cewa.Da ganin farko naji kin shiga raina sai kuma naji kin burgeni daga yadda kike mu’amalantar abubuwa ban fahimci soyayya ce ta mun fisga daya ba har sai dana koma gida bacci ya kauracewa idanuna tunanin ki ya shiga reto a kwakwalwa ta kamar yadda jirgin leda ke reto a sararin samaniya ban fahimci girman son da nike miki ba har saida aka sallame ku daga asibiti ya zama bana ganin ki sai jin dadi na ya ragu, dan Allah ki tallafe ni ki agaje ni ki bani dama in shiga cikin jerin masoyan ki na tabbata zakiyi alfahari dani domin da aure nazo bada wasa ba alfarma daya zaki mun kada kiki amincewa na rokeki. Ya karashe tare da hade hannayen shi guri guda alamar roko.Tun daga kasan zuciyarta take jin wani irin yanayi game da shi idan donta itane ta riga tayi amanna dashi amma daga ta tuna cewar mahaifiyar shi itace likitar data auna ta ta gano tana da shigar ciki ba tare da aure ba kuma tayita kuka tana rokon ta data cire mata cikin sai taji bazata iya bashi dama ba don bata tunanin mamar shi zata yadda ya aureta, ta wata fuskar kuma idan ta tuna kirkin Dr. Amina da faram faram dinta sai taji cewar ba komai bane zata iya amincewa auren danta wanda tafi so fiye da komai sai ta tuno ranar da yace mata bai da lafiya a gabansu yadda ta rude had ta manta akan aikinta take har saida ya tuna mata.Ajiyan zuciya ta sauke mai karfin gaske saboda ta samu damar harhado duk kalaman da zata fada mishi wanda wata kila bazai sake dawowa kusa da inda take ba idan yaji.Zura mata ido yayi sosai tare da son karantar yanayin ta.Ammar kace sunan ka ko? Na farko zan fada maka ni ba yarinya bace karama a yanzu da zan tsaya boye boye shiyasa na zabi na fada maka gaskiyar zance tun kafin na bari kayi nisa a so in cutar da kai, na taba aure watannin baya kadan baikai shekara ba da aurena ya mutu sannan kafin nan na taba haihuwa ina da da guda daya kafin nayi auren na haife shi a gida yanzu haka ya kusan 6yrs mahaifiyar kama shaida ce domin ita tayi mun gwaji ta gano ina dauke da ciki don haka ina mai baka shawara ka nisan ceni ba lallai tarayyata da kai ta zama alkhairi ba domin ni mai datti ce ina dauke da FENTIN ZINA a jikina wanda bazai goge ba har karshen rayuwata, ban face da zama uwa ta gari ba saboda nima ba ta garin bace don haka na rokeka ka tafi kada ka sake dawowa kai ba irin wanda ya kamata ya so mace iri na bane kada ka bata lokacin ka da rayuwar ka akan mace mai da wanda kowa ya shaida an haife shi ne ba tare da aure ba dan Allah ka tafi. Ta karasa fada zuciyarta cike da kuna hawaye suna sintiri a kumatunta kana ta juya da gudu ta fada cikin shagonta ta turo kofar tana jin kamar ta aikata ba daidai ba, kamar ta hanawa zuciya abunda take muradi, kamar ta cutar da gangar jikinta da ruhinta, tana jin kamar tana rabuwa da wani abu wanda yake mai mahimmanci a rayuwarta, tana jin kamar ta koma ta ce dashi ta fasa ya dawo suyi soyayya zata aure shi zata bashi dukkan soyayya da kulawar da yake da bukata.Sosai taji zuciyarta ta mata nauyi.Ammar a inda ta barshi anan ya daskare a tsaye kamar an kafa shi haka zalika ya tsare inda ta tsaya da ido kamar yana ganinta a wurin. Fadar tashin hankalin da yake ciki ma bata lokaci ne domin ya tsinci kanshi ne a cikin halin da bai taba koda mafarkin kasancewa a ciki ba, mace mai da wanda kowa ya shaida cewar an haife shine ta hanyar zina? Tambayoyi ne pal a kwakwalwar sa wadanda yake bukatar amsoshi amma babu mai bashi dole ya hakura, gefe daya kuma zuciyar shi na fada mishi karya kawai ta mishi domin ya nisan ce ta amma koma meye zaiyi bincike akai kuma sai ya tabbatar da gaskiya kamin ya yanke hukunci amma for now zai bata gap har zuwa ya gama binciken sa akan ta……………EESHERT ADAMU

Back to top button