Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 94 By Ayshercool

94Viper ya ɗan ja lokaci ya na kallon wayarsa, ya na tunanin mai indabo yake shiryawa, da har ya samu ƙwarin gwiwar kiransa ya na yi masa surutan iska. Kodayake bai kamata ya ce surutan iska ba, domin kuwa a rashin imani irin na indabo babu abin da ba zai iya aikatawa ba.Lambar Nabila ya yi ta kira, amma a kashe ba ta shiga, dan haka ya haƙura ya ci gaba da shirin fita.Ramma ta yinƙura ta ce “Bari mu tafi, na san ba dan albarkacin Anty Nabila ba, babu yadda za ayi a bari na shigo har na ganka, Allah ya baka lafiya ya baka ikon cin jarrabawar nan. Ba an hukuntaka da an tsaneka bane ba, ina fatan tuban da ka yi ya zama taubatan nasuha, kuma wahalar nan Allah ya sa ta zame mana kaffara baki ɗaya mijina” ya ɗago ya kalleta ya ce “Kai, rahama baki taɓa kirana da sunan da na ji yayi tasiri har cikin zuciyata kamar yau ba, da har nake jin eh lallai kin yafe mini ba. Yanzu kin yadda ni mijinki ne?”Ta yi ƙasa da muryarta ta ce “Ai zamantowarka mijina tuntuni na yarda da wannan, da ban yadda wannan cikin ya samu ba” murmushi ne ya suɓuce masa, ta tashi ita ma ta na murmushin, ta fita daga ɗakin har ta fice ya na daga ruf da ciki ya na kallonta, duk wannan wahalar da yake sha, ko sau ɗaya bai ji wani abu daga son da yake yi mata ya ragu daga zuciyar sa ba.***Nabila ta biya ta ajiye ramma a gida, sai dai ramma ta fuskanci mama ta sassauta fushin da take yi da ita, saboda ta ɗan samu sassauci saboda hukunta Abdul da ta ga an yi.Barrack Nabila ta koma, dan ita kanta ta ɗan tsorata da musayar yawu da su ka yi da Najar bunkure, dan ta san ba imani ta cika ba, amma da ta tuna da furucinta na cewar Jinin jauhar ya tafi a banza, sai wani nannauyan abu ya soki ƙirjinta.Kusan da ciwon mara ta wuni, daurewa kawai take yi, su ka ci abincin dare tare da madam Halima, ta na ta ba wa Nabila labarin yadda aka kashe mijinta, da yadda ta zama soja.Nabila ta ce “Taɓ sannu da ƙoƙari Mummy”Madam ta ce “Daughter ke ma fa za ki iya zama sojan nan, ki zama military lawyer. Ga Mijinki soja na musamman ke ma haka”Ta kalleta ta ce “Waye mijin nawa?””Ahh Viper mana”Nabila ta ce “Taɓ ba zan iya ba, gara na auri civilian irina, ni fa idan ki ka ɗauke tsiwa daga nesa nesa, ko gadin ƙofa ba zan iya balle wani soja, ko ‘yar agaji ba iyawa zan yi ba. Da ne da bani da hankali na ce wa Abba soja zan zama, ya ce ban isa ba, daga baya na fuskanci da na zama sojan, ba za ayi abin arziki ba”Madam ta ce “Haba dai, kar ki bayar da ni mana, and kuma ba soyayya ku ke yi da Viper ba, ba shi ne zai aure ki ba?””In ji wa? Mijin sister na ne fa””Ehenn your sister is late, and ba haramun bane a addinin musulunci, soyayya fa ku ke yi ina kallonku”Nabila ta ɓata fuska ta ce “Mummy ba ki gani dai-dai ba, ni fa marata ce take ciwo, gashi zuciyata sai tashi take yi kamar zan yi amai”Madam ta ce “Sannu, ko za ki je ki kwanta?”Abu kamar wasa Nabila ta gagara bacci, sai da madam ta kaita clinic, aka yi mata allurai ta dawo ta kwanta.Cikin dare madam Halima ta tashi ta na sallar dare, ta din ga jin ringing ɗin wayar Nabila a falo, ta fito ta kashe, ta ga Vi snake.Ta ɗaga ta ce “Snake ka ke kiran yarinyata cikin dare haka me za ta yi maka?”Viper ya yi murmushi ya ce “Important issue ne shiyasa na kirata””Salon ka hanata bacci, ba ta jin daɗi ne, bamu daɗe da dawowa daga clinic ba, ta samu bacci menstrual cramps ne yake damunta, ta na ta ciwon mara ta sha allurai dai, har da kuka dan sangarta. This your wife is not brave at all, lazy citizen”Murmushi Viper ya yi ya ce “Thank God ke ki ka faɗa ba ni ba, ayi mata sannu sai da safe”.”To shikenan sai anjima” ta kashe mata wayar ta ajiye.Da safe ta ga Nabila ta shiryo cikin uniform ta ce “Kin ji sauƙi za ki iya zuwa aikin ne?”Nabila ta ce “Eh Mummy, da sauƙi sosai”Ta ce “To Alhamdilillah, come and have your breakfast”.”I have no appetite, zan samu wani abu na ci, zan haɗu da Joseph a bakin gate, zan tafi”. Suka yi sallama Nabila ta fita.Babu shari’ar da za ta halarta, dan haka ta na office ɗin ta, ta na ta aiki, zuwa ƙarfe sha ɗaya na safe, ta ji yunwa ta addabeta, ta ajiye aikin ta fita.Ta fita babu daɗewa sai ga Viper ya zo.Ya tarar ba ta nan, amma yadda ta bar ƙaramar wayarta da jakarta ya tabbatar masa da ba nisa tayi ba.Ya ƙarasa gaban teburin, ta ajiye cake ga kofin tea da madara da milo, da alama tea za ta sha, ya janyo drowern teburin, nan ma ya iske gugguru da tarkacen alawoyi. Ya girgiza kai, a dai-dai lokacin ta buɗe Office ɗin ta shigo, hannunta riƙe da leda.Ta ce “Binciken me ka ke yi mini waye ya baka iznin shigo mini office ma?” Tayi maganar tana ƙarasawa.Ya ɗago ya kalleta ta ga idanunsa jawurrr.”Ba ciwon mara aka ce ki na yi ba, amma ki ke cin wannan kayan zaƙin?” Yayi maganar ya na tsareta da idanunsa.”Waye ya ce ina ciwon mara?” Tayi maganar ta na zaro ido.”Madam, na kira jiya da daddare ta ce kun je asibiti, and yanzu kalli tarkacen abin da ki ke ci, ko tausayin kanki ba kya ji. Duk ranar da ki ka zo haihuwa zaki yi bayanin wannan zaƙin da ki ke ci ba yau ba gobe saboda basir”Murmushi ta yi ta ce “Ba sai in zan haihun ba, adopting ɗin baby kawai zan yi, banda haihuwa dan tsoro nake ji, akwai wahala, idan ma zan haihu irin ɗayan nan is ok””Saboda ke haka aka yi miki? Ko kuma dan ke ki ka tsara wa kanki rayuwa?”Ta ce “No ai yarjejeniya za mu yi da babyna kafin mu yi aure, banda haihuwa” ƙura mata ido yayi, ya na lumshe su a hankali.Ta ce “Bari na wuce, kai ma sai na sammaka, ko ya aka yi ma ka san cin zaƙi na saka basir…..Kan ta ƙarasa maganar ya ce “Am once married”Ta ce “Eh haka ne, matsa na wuce to, bobon zan sammaka ko za ka ci gugguru. Wato bincike ma ka yi mini, duk ka kwaso mini kaya, ka ajiye a kan tebur” tahowa yayi zai faɗo a jikinta, ta ja baya kaɗan a tsorace. Ya dafe teburin ya na sauke numfashi.Jiki a sanyaye ta ce “Vi” ya ɗago jajayen idanunsa a wahalce ya kalleta.”Again? Me ka je ka sha ne? Na za ta ka daina gaba ɗaya, sai abin da ba a rasa ba. Ka yi shaye-shaye kuma ka taho hanya ba ka tsoro wani abu ya sameka? Me aka yi maka ma ka je ka sha kayan maye? Waye ya ɓata maka rai”Ya kuma jan numfashin, ya na lumshe ido.A hankali ya ce “Am so much thirsty, ina shan baƙar wahala, saboda daina ta’amalli da kayan maye. Idan ƙishirwar shan ta taso mini, sai na ji kamar zan bar duniya idan ban sha ba, is not that easy rabuwa da shaye-shaye” yayi maganar kamar zai faɗi ya na lumshe ido.”Me ka sha?” Ta tambaye shi cikin damuwa.Fito mata da dogon harshensa ya yi, duk ragowar farin ƙwayar da ya sha.Ta ce “Guda nawa ka sha?”Ya ɗago mata yatsunsa guda uku.Ya ce “Uku ne kawai, ban sake yi wa kaina allura ba ai, tun da ki ka shigo rayuwata, ki ka bani ƙwarin gwiwa da tabbacin zan iya sake rayuwa kamar kowa.Kin san da ba sa ɗaukata, yanzun ma ban yi tunanin za su ɗauke ni ba, sai da na zo nan gabanki, kawai su ka fara ɗibata, dole sai sun tona mini asiri” yayi maganar yana murmushi tare da layi.Ta numfasa ta ce “Muje ga kujera ka kwanta” juyawa ya yi yana neman kujerar, ta riƙe hannunsa, har kan kujerar.Ya hau ya kwanta a kai, ya na lumshe ido.Ta kalle shi ta ce “Idan ka sake shan kayan maye, sai na gaya wa ‘yar madara, dan ka san ba ta mutu ta barka a kan wannan tafarkin ba”Ya ce “A’a Abla””Idan ka kuma sha sai na gaya mata, duk ka ɓata mini rai ban ji daɗin ganinka a haka ba. Kamar ma na yi kuka wallahi””Sorry ba zan sake ba in sha Allah” yayi maganar bacci nannauya ya na kwashe shi.Ta tashi ta koma kan teburinta, dan cin abinci, ta na yi ta na gudanar da aikinta, ƙarshe ta ture system ɗin ta kifa kanta ta hau bacci, domin daren jiya ba ta samu isasshen bacci ba, saboda ciwo.***”Yaron nan ya fara bani tsoro, wai tambayata yake yi, in da P.A yake, ina tsoron kar na je ya san wani abu fa””Indabo, ka kwantar da hankalinka, babu abin da ya sani, kuma babu abin da zai faru, kawai zunzurutun barazana ce”Indabo ya girgiza kai ya ce “Babu lallai barazana ce, shegen yaro ne fiye da yadda ka ke tunani. Ga waɗancan asararrun jarababbun yaran sun sako ni a gaba, yanzu Kanon nake son shiga amma har fargabar hakan nake ji, amma hakanan zan je na gano Abdul.Wallahi zaman prsion ɗin Jafar bai ɗaga mini hankali ba, kamar na Abdul. Gidajen yarin Nigeria da babu gyara, babu kula a haka yaron nan yake rayuwa, wai a haka an yi masa sassauci saboda wata banzar yarinya, kodayeke ko ma menene shi ne ya janyo wa kansa ai”Mutumin ya ce “Ka yi haƙuri distinguish, yaran namu ne ka haife su, amma ba ka haifi halinsu ba, kuma duk kankarofi ne kanwa uwar gami, tun da shi ne yake amfani da ƙarfin ikonsa, ya hana ruwa gudu ko ta ko ina”Cikin takaici Inadabo ya ce “Could you imagine Alhaji Sada, yaron nan kuɗin da ake tuhumar nan tawa a kai, ware su aka yi saboda campaign ɗin sa, amma saboda sakarci wai ya tattare kuɗin a kan tsinanniyar yarinya ‘yar ƙauye, kuma hakan bai yi musu ba, sai da suka kai shi gidan yari, har da duka. Shi kansa alƙalin ba zan bar shi ba dan uwatar. Wani baƙin ciki da takaici da maimuna take gaya mini, wai yarinyar ciki ne da ita, ta cewa Abdul a zubar wai ba za a zubar ba, gaba ɗaya mutuncina da kimar siyasata ya zube, ban da Abdul ɗa na ne, da sai na yi masa aiken da babu dawowa. Amma ina nan ina shiri, Sai an kashe banzan yaron nan Viper, duk wata fitina shi ne yake ƙara kunnota. Gashi yarinyar nan ‘yar jarida twins ɗin matarsa ce, daga rahotannin da na samu. Shiyasa farkon ganina da ita na tsorata, na saka aka yi mini bincike a kanta, amma gaba ɗaya nasabarta ba ta yi alaƙa da shi ko waccan matar ta sa da aka kashe ba. Saboda mugun rainin wayo, shi ma wancan wawan, wai ya na bincike amma a gidansu yarinyar na haɗuwa da Viper bai sani ba, shi ma sai na ɗauki mataki a kansa”Honorable Sada ya ce “Duk dai ka yi haƙuri ka kwantar da hankalinka, ai mun gama shirya komai, aiwatarwa ce ta rage. Kuma muna da tabbacin za a sami mafita”Indabo ya jinjina kai da alamar gamsuwa da maganganun honorable Sada.***Barrister Habib ne ya shiga office ɗin Nabila, ya tarar da Viper a miƙe a kan kujera ya na bacci, Nabila kuma ta kifa kai ta a kan tebur ta na bacci.Gaba ɗaya sai ya ji babu daɗi, wani irin matsanancin kishi ya na taso masa, duk da ya san ko da me yake yawo, Viper ya fi ƙarfin yayi takara da shi, duk haryanzu bai gane in da suka dosa ba, daga ita har Vipern, amma kusancinsu yayi yawa.Ya ja da baya ya mayar da ƙofar ya rufe, ya na rufewa Viper kuma ya buɗe idonsa, ya bi ƙofar da kallo, ya mayar da idonsa kan Nabila da take baccinta a nutse, kamar ta samu gado.Ya daɗe ya na kallonta, sak ‘yar madararsa yake gani, duk da akwai tarin banbancin halaye tsakanin Nabila da jauhar, amma akwai abubuwan ta da suke burge shi, she’s very straightforward, very silly and arrogant.A hankali ya tashi ya kalli agogo, ya fice yaje ya yi salla, har ya dawo Nabila bacci take yi, kodayeke ba abin mamaki bane ba, ko lokacin da yana tare da jauhar, idan tana period kamar mai laulayin ciki, bacci ciye-ciye da saurin kuka.Ya daddaki teburin da ta kwantar da kanta, amma shiru ba ta motsa ba, “Ke wani daren za ayi miki ne?” Still ba ta motsa ba.Bayanta ya zagaya ya ja kujerar da take kai baya kamar za ta faɗi, razana tayi tare da yin wani ɗan marayan ihu.Ya ƙura mata ido ya ce “Ki tashi haka mu yi maganar da ta kawo ni””Na ji amma ka ajiye ni mana kar na faɗi”A hankali ya mayar da kujerar, amma ya sunkuyo ta bayanta dai-dai kunnenta, kamar zai yi magana, sai kuma yayi shiru, ta din ga jin saukar numfashin sa a jikinta.Kame jikinta tayi, ta ce “Bari na wanke fuskata, sai mu yi maganar” ta tashi ta nufi toilet.Ta dawo ta zauna ta kalleshi ta ce “Ka watstsake?” Ya ɗaga mata gira.Ta ce “Alright, ina jin ka, meyafaru?””Inadabo ya kira ni jiya, kuma tabbas tun da ya kira ni, akwai abin da ya taka yake jin ƙwarin gwiwa, har ya kira ni, amma menene shirinki ke yanzu?”Nabila ta jinjina kai ta ce “Alhamdilillah, dai-dai gwargwado muna da abin da ya sauwwaƙa, Bunkure na ta dragging ne to sai ta faɗi ɓarnar da ka aikata a baya””Nabila ba fa zan koma prison ba” yayi maganar very serious.Ta waro ido, sai kuma ta ɓata fuska “Nabila kuma garangatsau ba Ablan””Am very serious, kin san masifar gidan yari, ba fa zan koma ba”Nabila ta ce “Easy, in sha Allah ba abin da zai mayar da kai prsion, amma Vi”Ya kalleta. Ta kwantar da murya ta ce “Ina ganin yakamata mu fara zuwa kana ganin likitan ƙwaƙwalwa sab…Haɗiye maganar ta yi, saboda ganin kallon da ya yi mata.”Kallon mahaukaci ki ke yi mini kenan?”Da sauri ta girgiza kai ta ce “No, ba kallon mahaukaci nake yi maka ba, za su taimaka maka ne, ka daina ta’amalli da kayan maye gaba ɗaya, tun da ka na trying kai ma, za su taimaka maka, zuwa wurin likitan ƙwaƙwalwa ba ya na nufin mutum ya haukace bane ba”.Shiru ya yi yana kallonta. “Please Vi, kar ka ce A’a zaka iya daina shaye-shaye gabaki ɗaya, idan muka dage da zuwa wurin likitoci, dan Allah kar ka ce A’a ka ji””Ba zani ba””Dan girman Allah, kar ka yi mini haka ka taimaka dan Allah, ka ji Vi, na jinjinawa ƙoƙarin da ka yi, na rage kaso mafi rinjaye a shaye-shaye, amma za su taimaka maka, dan Allah ka yarda mu je”Tashi ya yi tsaye, ya ce “Tashi mu tafi” ba ta sake yi masa maganar ba, suka tafi.****Sanarwa ce ta fita, na ɓatan P.A ɗin Indabo, nan da nan da taimakon Sumayya, da murtala, aka cigaba da yaɗa ɓatan nasa babu ƙaƙƙautawa, kamar yadda Viper ya nemi su yi hakan, ta hannun Nabila.A yau ma kotun a cike take da ɗan Adam, domin kuwa daga cikin shari’un da suke ɗaukar hankali, har da ta Amini Viper.Viper ya zama shaida na ƙarshe da Nabila za ta gabatar wa kotu.Ya fito ya tsaya, Nabila ta tsaya a gabansa, ta jinjina masa kai alamar ƙwarin gwiwa.Ta numfasa ta ce “Malam Al’amin, ko zaka iya bayyana wa kotu, abin da ya faru a ranar da ka ke zargin waɗan nan mutanen da shiga gidanka, su kashe maka mata” Tana kai maganar ya tari numfashinta da “Ba zargi nake yi ba na tabattar””To meyafaru?”Ya yi ajiyar zuciya ya ce “Ina kwance na fara jin motsi a saman katanga, na taso na fito falo, aka haske ni da fitila. Na tambayi waye, ba na iya gane suwaye, sai gilmawar mutane, na ji an daki ƙafafuwana da wani abu mai nauyi.Kafin na yinƙura, na ji tsinin allura a wuyana, na yinƙura zan kuma tashi, aka daki ƙafafuwana, suka daddane ni, su ka ɗaure mini hannayena da ƙafafuwana.A lokacin Madaki ya sauke takunkunmin fuskarsa, da shi da lakwari, na kasa motsi, gaɓoɓina su ka fara sanyi.Idona biyu amma na kasa motsa ko ina a jikina, a dai-dai lokacin matata jauhar ta fito. Bayan yi musu magiyar su rabu da ni, Madaki… Sai kuma ya yi shiru, ya na haɗiyar yawu.Nabila ta jinjina masa kai alamar ya cigaba.Lakwari ya riƙe gashin kanta, Madaki ya hankaɗata, Madaki kuma ya sanya mata ƙafarsa, ta faɗo a kan cikinta. Su ka buga mini a kaina daga nan ban sake sanin meyafaru ba. Ya ƙarasa maganar a sanyaye.”Ka tabattar ka ga mutuwar jauhar?” Ya jinjina kai alamar eh.Nabila ta kalli alaƙali ta ce “Ina fatan wannan kotu mai adalci, za ta yi duba da shaidu da hujjojin da mu ka gabatar, ta tabbatar da adalci wurin hukunta ma su laifi”Aka waiwayi bunkure, kan ko ta na da abin cewa, ta tashi ta ta ce ta na da tambayoyi ds za ta yi wa Viper.Ta zo gabansa ta tsaya, ta kalleshi ya kalle ta, ta yi murmushi ta ce “Al’amin, binciken jami’an tsaro da ya gabata a kan kisan matarka, sun tabbatar da cewa, kai ka sha kayan maye, ka halakka matarka da hannunka, amma sai gashi ka na zargin wasu da shiga gidanka su ka kashe matarka”Ta sake kallonsa a tsanake ta ce “Ka na ta’amalli da miyagun ƙwayoyi, eh ko a’a?” Viper ya yi shiru ya na bin idonta da kallo.Nabila ta nemi a dakatar da Bunkure, saboda ƙoƙarin sanya Viper amsa laifi ta ƙarfin tsiya, sai dai ba a karɓi ƙorafin ba, aka ce ga ci gaba.”Ko ba ka amsa da bakin ka ba, amsar eh ce.Ya mai girma mai shari’a duniya kowa ya shaida Al’amin Viper ko in ce mai zamani, gawurtaccen ɗan daba ne da ya gagari al’umma, har a bayan tserewarsa daga gidan yari, ya ci gaba da aikata miyagun ayyukansa, na sara suka da dillancin miyagun ƙwayoyi”.”Objection my lord, barrister Naja’atu ta na kare waɗanda ake zargi ne, ko kuma ɗorawa mai ƙara laifuka da hanyar karkatar da shari’ar kan wani abu daban”.Aka gargadi Naja’atu Bunkure, ta ɗaukko wani file ta ɗaga ta ce “A bincike da yan sanda su ka tattara, akwai binciken likitoci, da gwaje-gwajen da aka yi masa bayan mutuwar jauhar, wanda a jininsa aka gano sinadarin wata allura, da ake amfani da ita a asibiti, wadda sai da matakai masu tsauri ake amfani da ita. Bayan haka akwai sauran ƙwayoyin da aka gano sinadaransu a cikin jininsa, wanda hakan yake tabattar da shi ya sha ya bugu, ya kashe matarsa da kansa. Da wannan nake roƙon kotu ta wanke waɗanda ake zargi, a hukunta wanda ya aikata laifin”Tsit kotun tayi, wani irin gumi ya tsatstsafo wa Viper, ba shi ba hatta su Walid, sun shiga cikin matsanancin tsoro da fargaba, ga su Abbu da mama hatta Alhaji mu’azzam da duk wani majiɓancin shari’ar, suka shiga cikin damuwa da tashin hankali.Nabila ta kalli Bunkure, Bunkure ta kalli Nabila tana murmushi.Nabila ta ce “Zan so kotu ta banu dama, na gabatar da doctor Muktar sharfaɗi”Aka ba ta dama, sak Viper ya yi, ya na tunanin shi kuma me doctor Muktar zai yi a nan.”Doctor ka gabatarwa da kotu kanka””Sunana doctor muktar sharfaɗi, ni ne likitan da na duba marigayiyya jauhar, na tabattar da inducing ɗin ta za a yi a asibitina, kuma ni aka samu na tabattar da mutuwarta a asibitin gwamanti na shiga asibitin safe.A report ɗin da na bayar, babu duka a jikinta ko kaɗan, faɗuwa ce, ta rasu ɗan cikinta ma ya mutu.Sai dai zan yi wani karambani, ban san wane irin bincike barrister ta yi akan allurar da take magana a kai ba, wannan allura ta na fara aiki ne mintuna biyar zuwa bakwai da yin ta, kuma tana tafiyar da ji da gani da consicous ɗin mutum gaba ɗaya, babu yadda za ayi wanda ya yi amfani da wannan magungunan ko alluran, ya iya sanin meyake yi, har ta kai ga ya yi kisan kai, kashe jiki suke yi gaba ɗaya Banbancin mutum da matacce numfashi ne kawai”Nabila ta numfasa, ta je gaban teburinta, ta ɗaukko wata envelope ta fito da wasu hotuna, ta ɗaga su ta ce “Mai girma mai shari’a, waɗannan su ne hotunan farko da jami’an tsaro su ka ɗauka, bayan ƙorafin da maƙwabta su ka shigar, na cewar sun ji ihun jauhar cikin dare, wayewar gari kuma sun yi ta bugu ba a buɗe gidan ba.Idan aka yi duba da hotunan, Al’amin kwanciyar da yayi ruf da ciki, hannayensa a kan gadon bayansa, ya na nuni da cewa tabbas ɗaure shi aka yi.A wannan hoton kuma, idan aka duba wurin ƙafafuwansa kasancewar ba dogon wando ne a jikinsa ba, akwai shaidar an yi traumatizing wurin, akwai alamar shaidar ɗauri a wurin.Idan har binciken jami’an tsaro dai-dai ne, kamar yadda Barrister Naja’atu ta faɗa, to ya tabatta toxicating ɗin Al’amin aka yi aka kashe matarsa.Idan kuwa har shi ne ya kasheta, zai iya zama tsautsayi ne, dan idan niyyar kasheta ya yi, zai daketa ne, ko jikinta ya nuna wani nau’i na cutarwa. Amma daga bayanan doctor Muktar, da hotunan da na gabatar, ina fatan Al’amin ya fita daga zargi, kuma za ta hukunta waɗanda suka aikata laifin”Da ido kawai Viper ya din ga bin Nabila, dan bai san yadda aka yi duk ta tattara waɗannan shaidun da hujjojin ba, sai a yanzu ya ƙara jinjinawa basirarta da hangen nesa.Alƙali ya yi rubuce-rubuce Alƙali ya ɗauki lokaci ya na yi, daga baya ya ce ya sake ɗaga shari’ar zuwa wata guda, domin yin zama na ƙarshe domin yanke hukunci.Kamar wata celebrity, haka Nabila ta fito daga cikin kotun, su Abba suka kewaye ta, kowa ya na tofa albarkacin bakinsa, su na jinjina wa ƙoƙarin da ta yi.Viper gefe ya koma ya tsaya ya na kallonta, yadda farinciki ya mamaye fuskarta.Sumayya ta saka mata abin magana, ta na tambayarta, yaya take ganin gudanawar shari’ar.”Babu abin da zamu cewa Allah sai godiya, muna sanya ran samun adalci,  a wannan shari’ar”.Hatta su liti ma, kasa ɓoye farincikin su su ka yi.Viper bai tsaya ba, yau ma saboda Abbu ya na wurin, ba ya son duk abin da zai haɗa shi da shi.Daga nan duk su ka watse, Baba ya na ta son lallaɓa Nabila ta dawo wurinsa, amma yadda ta nuna ba ta so, ya sanya ya ƙyaleta.”Thank you very much, for standing by my side, and show me way, to live another life as a different person, a really appreciate Abla, thank you once again take care. Al’amin”Murmushi ne ya suɓuce mata, sai kuma ta ɗan tsuke fuska a hankali ta furta “Alaƙarmu za ta zo ƙarshe, da zarar na kammala wannan shari’ar”Ayshercool08081012143

Back to top button