Fentin Zina Page 20 Hausa Novel
*****Jijjiga inna tayi tana neman mikewa idanunta na kallon Ameena bakinta na motsi alamar tana son furta wata kalma amma ta kasa.Goggo ce ta riketa tana tausarta akan tayi hakuri ta kula da lafiyarta saita warke za’a yi zama akan maganar.Girgiza kai inna takeyi hawaye suna zubowa daga gefe gefen idanunta guda biyu still tana kokarin magana cikin kokarin nata ne ta samu ta fisgo wasu kalmomi ta furta tace.Bana son ganinta na tsaneta ta fice daga ganin idona.Haka dai yasa dole likitocin suka sallami Ameena domin ta samu sauki sai kasala da zazzazi suka rubuta mata magunguna taje pharmacy ta siya ta wuce gida da yake safiya ne lokacin, jinin inna ba karamin hawa yayi ba sakamakon damuwa da bacin rai.Dakyar aka mata allurar bacci kafin suka samu natsuwa.Ko data isa gida bata tarar da baba ba kasancewar dama idan ya fita masallaci baya dawowa da wuri, dakinsu ta shige ta ajiye abubuwan hannunta ta fito tsakar gida ta shiga bayi tayo fitsari ta fito ta daura alwala ta shiga ta gabatar da sallah bata tashi a gurin ba ta ci gaba da tasbihi da istigfari tare da yiwa kanta addu’ah na samun sassaucin hukunci daga gurin iyayenta.Tana zaune a gurin taji motsin shigowar baba malam, wani irin bugawa zuciyarta tayi yayinda cikinta ya murda mata ta kasa tashi domin koda tayi yunkurin yin hakan kafafunta bazasu dauketa ba haka ta hakura ta zauna cikin fargaba da zillon zuciya.Sanda taji takun baba malam a bakin kofar dakin su kadan ya rage numfashi ya rabu da gangar jikin ta.Dago labulen yayi tare da yin sallama ya shigo ba tare da ya jira a amsa ba don yasan babu kowa a dakin amma me.Idanun shine suka fara yimai tozali da abunda baya kaunar gani a yanzu ko kusa, take ya buga wani wawan tsaki yana mai kawar da kai daga kallon bangaren da take ko gaisuwar da take mai bai amsa ba ya dauki abunda ya shigo dauka ya fita abunshi.Hawayen tausayin kanta da kuma nadama ne suka shiga kwaranyo mata daga cikin idanunta suna gangarowa har i zuwa kan kumatunta, zata fi so ace ya mata dukan tsiya lokacin daya shigo ya fiye mata wannan dabi’ar daya nuna mata, ganin kuka bazai fishsheta ba yasa ta mike tare da share hawayenta ta fita tsakar gida ta soma tattare wanke-wankensu tayi ta share gidan sannan ta dora girki, tuwon shinkafa miyar kuka tayi lokacin data gama tara tayi don haka ta shirya abincin a babban basket dinsu ta sa babban hijabinta tasa safa ta dauki nikab dinta ta saka ta fice daga gidan ta tari napep zuwa asibitin.*****A asibiti kuwa bayan fitan Ameena goggo ta dubi fateema tana tabe baki tace yarinya kamar ta kirki ashe shaidaniya ce daga ta ciki?Ko kadan fateema bata jin dadin kalmar da goggo ta jefi addanta da shi ba amma sai tace um kawai.Goggo ta sake cewa kinga ko tanan sai ki dauki darasin rayuwa kada ki maimaita abunda yayar ki tayi don naga yanzu ba’a shaidar dan mutum domin ana zaton wuta ne a makera sai kuma aganta a masaka.Fateema ta kasa hakuri don dama ita akwai saurin zuwa wuya tace goggo ko ita addan ma na tabbata tsautsayi ne kuma hakan Allah ya kaddaro a rayuwarta bata isa ta tsallake ba don haka zamuyi mata uzuri tunda kowa yasan ba halinta bane hakan.Ke ai dama mara kunya ce shiyasa ma ban cika shiri dake ba fitsararriya kawai toh ko ubanku Ibraheem bai isa ina fadi yana fadi ba.Haba goggo dan Allah ki daina zagin baba malam shifa baima san munyi wannan maganar ba kumama goggo daga fadin gaskiya sai ki fara zagina ki hada da mahaifina?, fateema ta fada tana turo baki irin bata ji dadi ba.Kaji mun ja’irar yarinya yaushe nayi zagi ma a cikin zance na kinga wallahi ki kiyayeni ko in balla ki anan mara kunyar banza.Fateema ganin inta cigaba da tsayuwa a gurin zata furta abunda bai kamata ba don tana daga cikin irin mutanen da idan ransu ya baci basu cika iya sarrafa kansu ba shiyasa koda yaushe take kiyaye wani abu ya hadata da mutum.Waje ta fita ta zauna a reception tana danna wayarta.Ba’a dau lokaci ba Ameena ta shigo dauke da basket din abinci ta zauna kusa da fateema cikin murya mai fidda tsantsar nadama da kunya ta soma cewa.Nasani cewa koda kowa zai gujeni ya hantare ni banda ke a cikin su inaso ki yarda dani wallahi tsautsayi ne da kuma kaddarar faruwar hakan amma wallahi ban taba aikatawa ba nasan nayi kuskure dana biye wa son zuciyata wurin ganin na ceci soyayyata a gani na kenan ban sani ba ashe rami na haka mai fadi da tsayi dazai rufeni tare da duk wani buri nawa hakika na aikata babban kuskure na mika yardata danayi wa wanda bai dauki komai gane dani ba face mugunta da cin amana dan Allah kada kibi layin su inna wajen barin gefena ki barni in samu sanyi daga gareki kinji kanwata, ta karashe tana mai kuka kasa-kasa.Adda taya kike ganin zan yarda dake a halin yanzu? Ki duba fa kiga irin halin da kika jefa inna a ciki meya shiga tunanin ki adda? Akan so? Kin bani mamaki.Fateema! Wallahi ko Qur’ani zaki bani zan dafa in kuma rantse miki da cewa sau daya hakan ta faru kuma bazan miki karya ba, nan ta kwashe duk abunda ya faru ranan ta fada mata tana sheshaheka.Haba adda domin kawai yace zai rabu dake sai kika biye masa? To saime idan ya rabu dake din? Kinga yanzu ya jefa ki a matsala ya kuma yi tafiyarsa ya barki kinji tsoron ya rabu dake kin bashi kanki, shi kuma yayi amfani da karfin son da kike mishi ya cimma burin shi akan Ki, bazan miki karya ba na ji miki kunyar hakan.Kama hannunta Ameena tayi tace dan Allah ‘yar uwata ki tausaya mun, nasan ba lallai su baba malam da inna su fahimceni ba amma ke nasan zaki fahimceni, nasan bani da kwarin gwiwar tunkarar su inna da magana makamanciyar amun adalci amma ke zan iya, a halin yanzu ke kadai ce madafa ta idan na rasa ki yaya zanyi da rayuwata wallahi tun ranar da abun ya faru banida natsuwa na kasa samun sukuni toh amma kaddara ta riga fata, nayi nadama nayi nadamar sanin Ahmad, nayi nadamar da bata da adadi a yanzu fata nike inama Allah zai dauki rayuwata koda zan huta da abunda ke damuna kuma wata kila su inna su iya yafe mun idan suka ga babu ni, nayi nadamar rashin jin maganar baba malam dana saurare shi nayi biyayya wa maganar sa da duk wannan bai faru ba.Fateema ta daura hannunta akan na Ameena tana cewa, na fahimceki adda kuma zan taya ki bawa su inna hakuri insha Allah nasan zasu karbi uzurin ki saidai mu dukufa wajen yin istigfari domin ubangiji ya yafe mana laifukan mu.Murmushi Ameena ta dan saki tace nagode kanwata Allah ya miki albarka, Allah ya kareki daga sharrin duniya da abunda ke cikinta, Allah ya kare ki daga sharrin zamani.Ameen Adda.Ameena ta mike ta sauki basket din tana kokarin shiga ciki fateema ta dakatar da ita ta hanyar fadin.Kawo na shigar dashi kina da bukatar kidan bada gap wa inna harta huce gudun ta miki mummunan baki.Daga haka ta karbi basket din tayi ciki dashi.Zama Ameena tayi inda ta tashi ta dafe kanta da duka hannayenta tana furta “Astagfirullahallazi laa’ilaaha illa huwal hayyul qayyoum wa atuubu ilaihi” ya Allah ka gafarta zunubbaina ka bani karfin zuciyar daukar wannan jarabawar daka jarabceni da ita ka sanyawa iyayena dangana a zuciya ka sassauta fushinsu ya Allah.Ta karasa cikin karyewar murya.****Baba malam na daga kofar shigowa reception din yana kallonta hawaye sun taru a idanun shi suna neman zubowa, tun daga fara maganar su yake tsaye a gurin ya matukar jin tausayinta sannan ya yarda da dukkanin abubuwan data fada sai dai hakan bazai sa ya fasa daukar hukunci akanta ba saboda koda gaba makamancin hakan bazai sake faruwaba.Hannun rigar shi ya saka ya share kwallar data nemi zubo mishi sannan ya tako cikin takunshi na wadanda suka kwankwadi ilimi cikin kamala da natsuwa har ya iso inda take zaune baiko kalli inda take ba dukda yaji gaisuwar da take mishi ya shige dakin da aka kwantar da inna din.Jingine baya tayi tana sauke ajiyan zuciya tare da sakin huci kamar tayi tseren gudu.Baba Malam ya Tura kofar da sallama goggo ta amsa masa fateema ta jawo masa kujera ta bashi ya karba ya zauna ita kuma ta fita waje bayan ta gaishe shi ya amsa.Baba Malam ya kalli goggo yace barka da safiya yaya.Yauwa barka dai ka shigo?.Eh sai yanzu na samu zuwa kuyi hakuri fah.Ai babu komai ya gidan ka sa wani abu a cikin ka kuwa?.A’a, ya fada yana girgiza kai, sai idan Allah ya nufa na koma gida insha Allah zan ci.Ai ga abinci nan daka ci kawai kafin ka tafi.A’a kudai kuci kawai, ya mai jikin?.Toh da sauki sai dai tunda aka mata allurar bacci bata farkaba har yanzu amma jikin Alhamdulillah sunce ma idan ta farka suka ga babu wata matsala zasu sallame mu mu koma gida.Toh Allah ya bata lafiya.Ameen, amma kai kuwa ibraheem meya faru haka a gidan ka? Yaya ka bari tarbiyyar gidan ka ta lalace haka har ta kawo wannan matakin?.Ya numfasa yace yaya kiyi hakuri bayan an sallameta sai mu zauna amma wannan maganar bata nan bace.Toh babu damuwa ta fada tana watsa hannayenta.Daidai nan inna ta fara motsi da idanunta alamar farkawa har ta bude idanun ta sauke su a kan mijinta sai take taji kwalla na zubo mata.Girgiza mata kai yayi yace kiyi hakuri kibar zubar da hawayen ki babu komai kada ki daga hankalin ki.Gyada kai tayi tana yunkurawa don tashi ta zauna ya taimaka mata yasa mata pilo a bayanta ta jingina.Yace ya kike jin jikin yanzu?Dan yamutsa fuska tayi tace da sauki sosai saidai zuciyata ce data yi nauyi sosai.Wannan ma zai tafi insha Allah amma sai kin cire damuwa a ranki.Girgiza kai tayi tace hum don’t baka san yadda nike ji bane shiyasa malam.Na sani, shiyasa ma nace kiyi hakuri tun farko.Bana bukatar ganinta, idan ina kallonta tuna mun take da abunda ya faru dan Allah kasa tayi nesa dani.Haba rukayya meye kike cewa ne haka? Shin ke bazaki dauki kaddara ba, yanzu kamata yayi musan ta yadda zamu bullowa al’amarin, cewar goggo dake kallon inna.Inna zatayi magana baba malam ya dakatar da ita yana cewa, kiyi hakuri ko meye zamu tattaunashi daga baya yanzu ki bari ki samu sauki a sallameki.Badon taso ba tayi shiru amma kasan zuciyarta radadi take ji har bata kaunar ta bude ido taga Ameena don ji take kamar ta shake ta ta mutu ta bar duniyar gaba daya.Haka suka ci gaba da zama jugum goggoce ta rufe shirun da cewa rukayya a zuba miki abincin ko?Inna ta girgiza kai kana tace waya dafa?Ameena ce ta kawo daga gida.Koda shi kadaine ya rage a matsayin abincin da zanci in rayu sai dai na mutu.Rukayya! Rukayya!!……Cewar baba malam kana ya dora da cewa banason kina nuna fushinki har zuciya game da lamarin nan domin koda baki furta mummunar kalma a kanta ba ki sani wannan fucin da zuciyarki ke ciki sanadiyyar ta zai iya jefa rayuwarta cikin halin kakanikayi na rokeki ki sassauta zuciyarki ko domin gyara sauran mutuncin wannan yarinyar sai dai idan kina so Allah ya hukunta ta ta hanyar jarabtar ta da fadawa shaidaniyar hanya wannan kuma yana daga abunda kika yanke. *EESHERT ADAMU*



