Hausa novels

Fentin Zina Page 9 Hausa Novel

****Murmushi maryam tayi tace kaima dai wasa kake ko.Kara washe baki yayi yace da gaske nike don dai ke bakisan irin farin cikin da nike jina a ciki bane.Eh nima ina cikin nishadi kwarai da gaske saboda samun abunda nike so, yanzu duk bama wannan ba wallahi yunwa nike ji kadan sama mana abunda zamu ci, ta fada tana karyar da wuya.Kada ki damu ai bazan bar amaryata da yunwa da gangan ba ki tashi barin dauko plate da cups sai muci wannan ai nasan zai ishe mu ko? Ya fada yana mikewa, ta gyada kai shi kuma ya fita ya nufi kitchen din Ameena, maryam na ganin ya fita ta zame mayafin gaba daya ta ajiye tana karewa dakin kallo babu laifi yayi kyau sosai don ba karamin kudi ta kashewa kanta ba bayan wanda iyayenta suka mata da sauran ‘yan uwa.Ya dawo dauke da plate sai cups guda biyu cikin karamin tray ya zauna yana cewa sauko ki taka a hankali ‘yan mata ki kula mun da motsinki taho in ciyar dake da hannun kauna cikin wake yake fadin hakan.Mamaki tayi bai taba mata irin wannan kalamin ba ashe dai zata mirewa love, shi ya katse mata tunani ta hanyar fadin, koda kin fiso in daukeki da kaina ina mai tabbatar miki zanyi hakan domin yau din takice ke kadai zan shayar dake kauna ta ban mamaki na abun tunawa a wannan daren oya sauko a hankali.A hankalin kuwa ta sauka daga saman gadon zata zauna a gefenshi ya girgiza kai yana nuna mata saman cinyar shi babu musu ko gardama kuwa ta dale kai haka ya soma ci yana bata har suka gama, ya mike ya maida plates din kitchen din Ameena ya dawo ya mikar da ita a inda take zaune yace wanka zamuyi sai muyi alwala muyi alwala muyi sallah sauran abubuwan zasu biyo baya.Ta shafa gemun shi tadan ja kadan tace an gama masoyi.Time da hannunta suka shiga bayin tubewa ya farayi kafin ya mata alama data tube itama,Tun a toilet din yaji yarr amma jikin shi kuma ya mutu domin yaga abu sabanin yadda yake hasashen shi wato na shanunta a shafe alamar har sun gaji sunyi bacci babu alamun cewa na budurwa ne sun fi kama da macen data shayar da ‘ya’ya uku zuwa hudu amma bai karaya ba haka suka gama wankan suka fito, da kanshi ya zabo mata sleeping dress din da zata saka shima ya fita zuwa dakin shi ya sako nashi pajamas din ya dawo lokacin harta kammala ta fesa turaruka musamman wani shu’umin turare mai ayyuka da yawa.Susucewa yayi daga sanda ya shaki kamshin turaren da ake masa lakabi da komin taurin kanka, shi kwata kwata kwakwalwar shi bata kawo masa amarya a daren farkon ta ya kamata ta kasance mai kamun kai natsuwa da jan aji ba, shidai a iya abunda yake zumudin samu kadai ya kawar da tunanukan shi akan komai.Tun kafin su kafin sukai ga kwanciya saman gado suka soma shafe shafe hardai suka fada kan gadon, tun yana abu da sassauci har ya kara kaimi kokarin shi yaga ya cimma burinshi, maryam kuwa tunda taji yana neman hanya taji yadda kasanta yayi mata zafi daga nan ido ya raina fata shi kuwa tunda ya saita baijin zai iya dakatawa gashi magungunan da tasha sun jika suna aiki kuka take iya karfinta tana rokon shi ya kyale ta……**** ***Ameena tunda ya ajiye mata ledar ya fita ta bude ido wani irin tukuki take ji na kishi kamar ta bishi ta janyo shi ta hana shi shiga dakinta saidai tasan hakan ba mai yiwuwa bane haka ta zauna tana ta karanta wasikar jaki har zuwa inda taji maryam na kuka tana rokon Abdul ya kyaleta daga ji kuma tasan ba kukan dadi bane face na wahala hakan ya nuna kenan da budurcinta ta taho gidan shi, ta kawo ‘yan matancinta gidan aurenta abunda ita ta kasa yi, nan take tausayin kanta ya kamata tare da hasasowa kanta irin zaman da zata koma yi a cikin gidan ganin tunani babu abunda zai magance mata face tarin damuwa yasa ta sauka ta nufi toilet ta dauro alwala ta shimfida sallaya ta tada sallah saida tayi raka’ah takwas sannan ta dakata saboda wani kugi da cikinta ya soma yi don rabonta da abincin kwarai tun jiya da rana, daukar ledar da Abdul ya ajiye tayi ta bude ganin gasashshiyar kaza da youghut sai ta tashi ta nufi kitchen, kama kugu tayi tana duban plate dinta daya dauka ya kai musu ta jinjina kai ta dauki abunda zata dauka tayi waje ta koma dakinta ta dan ci kadan wanda ta rage tasa shi cikin fridge din dake cikin dakin nata ta koma ta kwanta kanta na sara mata sosai ta runtse ido tana addu’ahr Allah ya turo bacci ya dauke ta.Kiran sallahr asuba ne ya tashi Ameena, ta tashi taji idanunta sunyi nauyi sakamakon kanta da har yanzu bai bar ciwo ba, babu bukatar ta tashe su ta tabbata sunji kiran sallahr, alwala tayi ta gabatar da sallah tayi addu’o’i ta linke sallayar ta koma ta kwanta don bazata yi girki ba babu kuma wani aiki mai karfin da zatayi ragowan yoghurt da naman jiya su zata karya dasu, bacci ne ya kuma daukarta har saida taji ana knocking din kofar ta sannan ta farka tana maijin babu dadi domin baccin bai ishe ta ba kuma mai dadin gaske ta fara, agogon dakin dake a manne ga bango ta duba karfe tara da rabi ya nuna mata, da sauri ta sauka daga saman gadon ta fada toilet ta wanke fuskarta ta goge da towel ta kalli kanta a madubi kafin ta fita taje ta bude kofar kamar yadda tayi tsammani Abdul ne, gaishe shi tayi ya amsa ba yabo ba fallasa yace kawo mana abinci muna jin yunwa ya juya da nufin tafiya tayi saurin cewa kayi hakuri banji dadin jikina bane banyi girki ba.Juyowa yayi yana kare mata kallo kamar zaiga gaskiyar abunda ta fada din a jikin ta yace what? Bakiyi girki ba kika ce? Wait amma kinsan amarya ta kwana a gidannan ko kuma na tabbata kin makale kunnuwa kinji abunda ya faru and kin fahimci cewar ta kawo mun ‘yan matancin ta shine kike bakin ciki kike so ki wulakan tani ta hanyar kin ba mata abinci taci? Ya fada yana wurga mata wani banzan kallo.Wallahi ba nufina ba kenan dan Allah ka daina alakanta hakan dani.Umurni nake baki yanzunnan ki shiga kitchen ki sama mun abunda zanci da amaryata in less than 20mins idan ba haka ba! Yaja kwafa ya wuce, cike da takaici ta koma daki karamin hijab ta dauro ta nufi kitchen ta dafa musu jellof din taliya wanda yaji kifi sosai ta hada musu lipton mai kayan kamshi takai dining ta jera ta nufi kofar maryam ta dan kwankwasa kadan bata jira sun bude ba tace abincin is ready yana dining daga ciki taji yace ki jira mu a falon gamu nan bata musa ba ta koma ta zauna kan kujera tana danna wayarta, sai gasu sun fito yana rike da maryam tana wani talewa kamar ‘yar kaciya tana dingisa kafa karshema ja tayi ta tsaya shima tsayawar yayi ya dubeta cikin kulawa da tsantsar kauna yace, sorry sweet heart nine Ko? Kiyi hakuri barin dauke ki kada ki fama ciwon.Kara langwabe kai tayi tana gyada kai tace kaine kaki saurare na kayi mun da zafi kuma kasan ni ban taba yi ba, ta fada tana kyabe baki kamar zatayi kuka.Nace kiyi hakuri ai, ya fada lokacin da ya daga ta kamar baby yaje ya direta kan kujerar dake gefen wacce Ameena ta zauna.Wash masoyi akwai zafi sosai nidai kada ka sake mun irin wannan kaji.Ki ma bar wasa yarinya wasan nan yanzu ma aka fara dama abunda na jima ina burine fa taya zaki ce dani a’a bama zan yadda ba kawai kiyi hakuri malama mantawa nayi kedin sabon hannu ce na miki wannan aika-aikar sannan da yake nima bansan kan abunba ban san yadda ake bi da budurwa ba, ya karasa kasa-kasa.Me kace baby?Babu komai zamuci anan ko zaki iya daurewa muje dining din.A’a anan dai zaka kawo kana ci kana bani ko masoyi hakan zaifi.Mikewa Ameena tayi don sarai duk tana jin duk abubuwan da suke cewa tun daga fitowar su har yanzu, akwai abunda kuke bukata ne ko zan iya tafiya, tayi maganar fuska a hade ta yadda bazai ma kawo mata wargi ba.Ayya yi hakuri maman shureim wallahi ban lura da kina falon ba kinsan ance hankali ke gani ina kwana!.Lafiya kada ki damu ki dauka a matsayin baki ganni din ba, ta juya bangaren Abdul, zan iya tafiya?.A’a ki zauna muci abincin kafin kada ace na fara rashin adalci a tsakaninku tun yanzu.Tayi murmushi tace babu bukatar hakan ai ka yadda da kanka, maganar mutane bazai dameka ba ni nasan wa nike aure ban damu da me za’a ce ba na barku lafiya, tasa kai ta wuce ta shige dakinta.Maryam ta kalle shi tace masoyi kamar fa bata ji dadi ba don hausa ta mana ina ji, nidai kaje ka bata hakuri bana so daga zuwana ace har irin wannan ya fara faruwa ai sai ace ni na hada ku.Girgiza kai yayi yace rabu da ita ai ba wani laifi muka mata ba.Ni dai masoyi kaje ka bata hakuri kaji for my sake!.Ba don yaso ba ya tafi dakinta ya same ta a zaune shima zama yayi fuska a tamke ya fara magana kamar haka,.Ameena bansan meyasa kike son aron dabi’un daba naki ba kina bijirowa dasu cikin zamantakewar mu, ki duba fa yanzu me aka miki da zaki shigo daki har da guzurin yada mana habaici toh mene laifin maryam? Bafa ita ta kawo kanta gidan nan ba, kuma kamar yadda kike matata haka itama matata ce babu wacce tafi wata don haka ki kiyaye da furucin bakin ki ni bana son tashin hankali ina fatan kin gane?Kanzil bata ce dashi ba kuma hakan ba karamin kona ranshi yayi ba ya tashi ya bar mata dakin, dafe goshinta tayi tana son gano menene aibun abunda tayi? Bata gano ba, hawaye suka soma sintiri a fuskarta tana rasa inda zata sa ranta taji dadi.Maryam ganin ya fito ba tare da Ameena ba tayi murmushi a ranta tace shegiya yanzuma kika fara ganin abu a cikin gidan nan sai kin gudu da kafafun ki, a zahiri kuwa ta aro damuwa ta manna a fuskarta tace, masoyi taki hakura ko?.Ajiyar zuciya ya sauke yana zama kusa da ita yace ba haka bane ai bamuyi mata laifin komai ba muje muci abinci.Anan suka bar tarikicen da suka bata suka koma daki har akayi sallahr azahar basu fitoba akayi la’asar bai fito yaje masallaci ba hakan bai wani bata mamaki ba daman tasan shi yana da wasa da ibada sam bai dauki hakan a wani abu ba.Wayarta ta dauka ta rubuta sako kamar haka.”ina ftn kana lfy naga lokacin sallah yayi harya gota baka fitoba, ka sani manzon Allah yana cewa sallahr jama’a tana da fifiko ga mai sallah shi kadai, sannan ina maka tuni cewa sallah itace abu na farko da za’a tambayi mutum a yayinda ya wayi gari cikin kabari dan Allah ka gyara”*Ta tura sai da taga delivery report ta ajiye wayar ta tafi kitchen ta fara hidimar dora abincin dare.*****Suna kwance suna hira sama sama yaji karar shigowar sako dake wayar tana kusa dashi ne sai ya dauka ganin sunan Ameena abun ya bashi mamaki ko me take bukata da zata masa sako? Daya gama karantawa karamin tsaki yaja ya mayar da wayar ya ajiye.Maryam dake kwance daga gefen shi tace lafiya kuwa?.Baice komai ba ya nuna mata sakon da ta turo mishi ta karanta data kai karshe tace tabdi jam! Wai dama kai haka kake an raina ka a gidan ka, wannan ai raini ne wato ta mayar damu kafurai bamu san darajar sallah ba ko? Koda yike ba laifinta bane kaine ka bata kofa.Karfin karasa magana yayi waje a fusace, tayi murmushi tana tafa hannu ashe kaima dai moloho ne ai kuwa tunda ka yarda na gano nufin ka da rauninka a kaina ka shiga uku daga kai har ita babu wanda zan bari yaji dadi har sai na raba ku…..EESHERT ADAMUMATAR MAJEEDADI

Back to top button