Fentin Zina Page 7 Hausa Novel
*****Idan shureim yazo gidan nan matsalar da zan samu da Abdul daban ne.Umm ta kara sauke ajiyar zuciya ta kwanta saman kujerar tana ci gaba da tunaninta.Ba jimawa taji karar bude gate da shigowar motar shi mikewa zaune tayi ta dan gyara zaman rigarta ta fita ta samu daidai zai karaso falon, ta mika hannu zata amshi jakarshi ya kauce yana fadin, barshi kawai zan karasa dashi.Bata ja zancen ba ta bashi hanya ya wuce ciki ta bishi a baya ta shige toilet dinshi ta hada masa ruwan wanka ta fito tace, na hada maka ruwan wankan kaje kayi sai kaji dadin jikinka.Ok, kawai yace ya fada toilet din, zama tayi ta daura tagumi daga bisani ta tashi ta ciro mishi kayan da zai saka ta ajiye ta fito don tunda suka samu sabani a wancan ranar basu kara samun zaman lafiya mai kyau ba tayi iya kokarinta amma yaki bata dama koya saurareta saita kyale shi ta cigaba da kyautata mishi kamar yanda ta saba.Yanzu ya daina kwana dakinta sai batayi fushi ba take binshi dakin nashi amma kullum kwanan bakin ciki takeyi don a saman gadon yana kwance yake wayar shi da maryam harda irin hiran da basu kamata ba duk tana ji batayi magana ba ta barwa Allah ya mata maganin abun tunda tasan baifi karfin Allah ba.Wannan kenan.Da shirin shi ya fito cikin shigar shadda milk colour mai kyau yana ta zuba kamshi tana zaune a falon ko bai fada ba tasan gurin maryam zaije, take taji wani tukuki yana damunta a kirjinta idanunta sukayi bala’in nauyi kanta dama baya rabo da ciwo a kwanakin nan saboda damuwar da take ciki.Ki tabbatar ki kwashe kayakin ki dake cikin wannan dakin gobe domin za’a zo ayiwa amaryata jeren kayanta a ciki.Allah ya kaimu lafiya tace ba tare da ta dago ta kalle shi ba don gani take kamar ba Abdul dinta bane wannan kamar an sauya mata shi.Sakai yayi ya fice yana kara zaman hularsa, ta kalli inda ya tsaya tayi murmushin yake tace, Allah ka bani ikon cinye wannan jarabawar, Allah idan auren nan babu alkhairi kayi gaggawar tarwatsa shi, idan akwai alkhairi ka sassauta kishina ka bani ikon karban sa hannu bibbiyu.**** *****Kofar gidan su maryam ya tsaida motar shi ya kira wayarta ya sanar mata yana waje, ba’a dau lokaci ba ta fito tana rangwadan data saba ita ba wani nama gareta ba sai son lankwasa kamar maciji gata kamar an daurawa muciya zani.Ya shagala da kallonta har baisan tazo kusa ba saida ta hura masa iska a fuska sannan ya farga, juyawa tayi ta koma gefen mai zaman banza ta zauna tana fadin, nayi tsammanin bazaka zo din bane harna cire rai.Ya Kada kai, ba haka nike ba! Nakan tsayu akan maganata kema zakiyi shaidar hakan ai nike ga, ya fada yana tsire ta da ido.Hakane masoyi kuma gashi kayi lattin zuwa saidai mu fasa fitar zuwa gobe don naga dare ya somayi kada in shiga lokacin uwar gida!.Kada ki damu kome zamu yi ki daina sako zancenta a ciki bana son hakan.Toh shikenan, zamu iya tafiya yanzu?.Baice komai ba yaja suka wuce, sunje wurare wurin uku kafin ya dawo da ita ya parka ta juyo ta kalleshi ta kashe mai murmushi tace, zanyi kewar ka masoyi.Nima zanyi kewar ki amma komai ya kusa zuwa karshe tunda na kusa mallakarki a matsayi mata ta yadda zan samu cikakken iko akan ki da jikin ki zan mallaki komai naki zanyi yadda naso daa………La la la nidai na wuce kada ka ballo mun ruwar da bazan iya dakatarwa ba, tana fadin haka ta fita a motar tana daga masa hannu.Shima daga mata hannu yake yi yana mamakin kanshi da irin yadda yake zakewa akanta baya iya controlling kanshi, da haka yaja motar bai tsaya ko ina ba sai gidan mamarshi dazun tayi kiranshi tana son ganin shi.Cike ya samesu a falon suna hira suna shewa kamar basu san dare ne ba.Bayan sun gaisa mama ta dubeshi tace dama akan maganar kudin nan dana fada maka ya kamata ka kawo su domin gobe nike da bukatar su.Jinjina kai yayi yana cewa toh gobe idan zan fita office zan kawo miki su.Hakan yayi ka kyauta da fatan wannan matsiyaciyar bata baka matsala ba ko har yanzu?.Eh mama ai tun dama nasan bazata bani matsala ba.Da yake soyayyarta ta rufe idanunka ba duk abunta ta yi baka gani, yanzu tunda aka saka bikinnan yaci ace ta kirani tamun Allah sanya alheri amma saboda ta nuna mun iya kiyayyarta da auren naka sai ta share bata kira ba, Allah Allah nike a daura auren nan hankalina ya kwanta insan nima dadin suruka.Mama kenan! Ita da za’a karawa kishiya ai tausaya mata ya kamata ayi kuma bata jin dadi ma kwanakin nan.Eh yo ba dole ba? Ai in bata yi hakan ba bazata gwadawa mutane halin da take ciki ba ita da take sauran wasu ma!.Mikewa Abdul yayi don har cikin zuciyarshi maganar karshen nan ta bugeshi bai dace mama tayi irin wannan maganar ba, bama shi kadai ba har kannen shi guda biyu saida suka ji babu dadi akan hakan ba.Bai samu kowa a falon ba kuma bai wani damu ba don gani yake shige matan da yake yi ne ya sanya take kokarin ganin ta saka shi abunda baiyi niyya ba ya wuce dakin shi.Tana kwance tana chart da fateema ta fada mata gobe za’a kawo kayan amarya tazo ta taimaka mata su fitar da na cikin tunda har yayi magana.”Kada ki daga hankalinki Adda zan fadawa inna sai in zo babu damuwa.Nagode da kulawarki gare ni ina kaunar ki.Haba Adda nifa ‘yar uwar kice nice wacce tafi cancanta ta kwantar miki da hankali fiye da kowa.Hakane! Ki zo da safe irin 7:30 domin na fiso mu gama kafin suzo.Kada ki damu insha Allah zanyo sammako.Kashe datar tayi bayan sunyi sallama ta mike ta gyara jikinta ta kimtsa ta nufi dakin Abdul da sallama a bakinta, baya cikin dakin yana bandaki don taji karar ruwa.Ba’a jima ba ya fito daure da karamin towel, kallo ta bishi dashi tana jin yarrr a jikinta tsigar jikinta sun tashi wanda hakan ya faru ne sakamakon sha’awar data taso mata sai tayi saurin saukar da kai kasa don kada yaga irin kallon da take mai.Bata ci nasara ba domin sarai ya ganta kuma yasan ma’anar wannan kallon yace a ranshi, mace da jarabar tsiya kawai.Koda suka kwanta bayan ya gama komai, ganin bazai neme ta ba sai ta danne bacin ran da take ji da kunci ta neme shi, ya biye mata saidai ko mintuna biyar cikakku baiyi ba ya samu gamsuwa alhali ita a lokacin ne ma take jin cewar an fara buga wasan.Yana kokarin raba jikisa da nata ta kankame shi tana cewa dan Allah kada ka mun haka ka barni na samu natsuwa daga gare ka, ya girgiza mata kai yace ki sake ni mana ke bakya gajiya ne sai naci haba abunda ake yinshi da marmari ke zaki mayar dashi abincin ki?.Yana gama fadin haka ya sauka a gadon ya fada toilet don fitsarine ya matseshi, ta bishi da kallo hawaye na zuba daga idanunta gashi wani iri takeji a kasanta kamar ana mata yawo babu abunda take bukata face ta samu kusanci da mijinta sai dai hakan bazai samu gareta ba shikam babu ruwan shi kullum haka yake, fitowa yayi daga toilet din yana mata kallon mamaki yana rayawa a zuciyar shi, har dan wannan abun zai saka ta kuka?.Kuyi hakuri da dan wannan ku gafarceni, har kullum ina kaunar ku.



