Fentin Zina Page 1 Hausa Novel
Zaune take cikin falonta mai alfarma daidai gwargwadon mai arziki a karnin mu cikin damuwa ta dafe kanta da duka hannayen ta guda biyu idanunta na tsiyayar da hawaye gefe daya ga danta mai shekara biyar yana wasa a tsakar falon da kekensa wadda ta siya masa. Mijinta na tsaye a kanta cikin fusata da hargowa yana cewa.Nace zaki fada mun wanda naga ya fita daga gidana yanzu ko saina saba miki wato kin maidani shashasha bansan me nikeyi ba zaki kawo mun katon saurayi cikin gidana? Gidan aurena na sunnah? Bazan lamunta ba! Sam bazan yadda da wannan iskancin ba har wani zaki raina mun wayo wai yayanki ne eh naji yayankine amma ai muharraminkine shaidan na iya shiga tsakaninku ku aikata ba daidai ba nawa akayi kuma?Ta dago jajayen idanunta ta kalle shi tana sheshahekar kuka tace, yanzu zargina kake kenan? Kana zargina da aikata fasadi a cikin gidan aurena? Allah ya tsare ni da aikata wannan zunubin da bashida hukunci saina kisa, bance dole saika yarda dani ba amma tsakani na da Allah wannan yayanane ya jima ne baya gari sai jiya ya dawo shinefa yace bari yazo mu gaisa kenan yin hakan ya zama laifi? Danasan hakan zata faru da tun farko ban bari an gwada mai hanyar gidana ba da nasan hanyar da zan kaucewa zuwansa tun kafin yazo.Shureim dake wasanshi ya ajiye kekenshi ya taho gurin Abdul ya rike kafarsa ya duka kasa yace cikin sanyin murya, baba ka daina yiwa mommata fada bata aikata komaiba kayi hakuri.Abdul ya kara zuwa wuya ya tunkure shureim har saida ya fadi kasa ya nuna shi da yatsa kai kace sa’anshi ne yace, kai idanma kasan irin bakin cikin da nikeji idan na ganka bazakayi kuskeren dinga rabata ba domin kamar yadda na tsani mutuwata haka na tsani ganinka cikin gidana babu dai yadda na iyane kawai tunda na riga na jajibowa kaina.Shureim ya tashi ya nufi gurin mahaifiya shi yana matsar kwalla.Ta rungume danta tana zubarda hawaye masu radadi wani tukuki takeji a zuciyarta cike da tarin karaya da nadama ta mike taja hannun shi suka shige daki suka bar Abdul tsaye a gurin yana sababi.Zaunar dashi kan gadonshi tayi tana hadiyar abubuwa masu tarin yawa da suka taru a makogwaronta suna bukatar fitowa amma ta tauyesu ta hanyar mayar dasu cikin cikinta tana sauke numfashi.Shureim yace momma meyasa baba baya sona kullum saiya dakeni kuma ya zageni? Ni momma kawai ki daukeni mu kuma gidan kaka su suna sona tunda shi baya sona kuma kema sai yayi ta zaginki meyasa bazaki rama ba kina tsoron ya dakeki ne?Ta rungume shi tana kuka tace, kayi hakuri yarona duk ni na jawo mana! Tabbas ni na jawo mana, da ban aikata abunda na aikata ba da ban biyewa son zuciya ba, da ban biyewa rudin shaidan ba da duk haka bata kasance gare mu ba, kaichona ya Allah ka agajeni Allah na tuba ka yafe mun.Abdul tunda Ameena ta shiga ciki ta barshi a falo ya karaci sababinshi yayi waje.Da daddare ta zubo musu abinci itada shureim suka ci suka koshi duk da ranta babu dadi amma hakanan ta daure ta dura abincin ta koshi ta maida plates din kitchen ta Adana su ta dawo tayi wanka ta ma shureim wanka duk a cikin dakin shureim din take haka don bata yadda shureim din ya nufi dakinta tun lokacin da mai gidan ya nuna bacinran sa akan hakan sai take komai a dakin shureim din sai bayan ta gama wa mai gidan hidimominsa take dawowa dakin shureim idan yayi bacci ta koma nasu dakin yanzuma hakan ta kasance da taga yayi bacci ta rage gudun AC ta rufa mai bargo ta tofa masa addu’o’i kana taja masa kofar ta fita.Dakin ta ta nufa ta kara gyara kanta ta fesa turare tana baza kamshi ta chanja wasu kayan karamar doguwar riga iyakarta cinya yellow ce ai kuwa ta hau da jikinta sosai musamman da yake farace sosai kuma tana da dan kauri ma’ana kiba daidai wadaida cinyoyinta sun haska sosai cikin kayan ta kara fesa wani turaren kana ta bude drawer mirror ta sauki chuwing-gum ta jefa a baki ta rufe drawer ta fita daga dakinta ta ja kofar ta nufi dakin Abdul.A hankali ta murda handle din kofar ta shiga a kishingide ta sameshi saman gado yana danna waya yana murmushi da alamar chatting yake yi.Jin and turo kofar da kuma kamshinta daya kai masa ziyara duka kofofin hancinsa ya sanar masa isowarta don haka yayi saurin kashe wayar ya jefata can baya ya mike zaune da kyau yana binta da kallo.Ta karaso ta zauna dan nesa dashi kadan daga bakin gadon tace, barka da dare.Ya dago ya zuba mata idanu yana yaba zallar kyau da Allah ya hore mata ga wannan shiga da tayi ta dauki hankalinshi sosai ta tafi dashi.Kusan mintuna goma a haka babu wanda ya sake cewa kowa komai kuma bai amsa barkan data mai ba hakan yasa ta dan muskuta ta kwanta taja bargo ta rufe rabin jikinta ta lumshe ido.Ganin wankin hula zai iya kaishi dare gashi ta tasar mai da kwadayinsa yasa ya kashe wutar dakin ya matsa dab da ita ya kwanta ya fara lalubenta tana jinsa amma batace komai ba kuma bata motsa ba, ganin haka yasa ya dakata da abunda yakeyi ya sauke numfashi ya kira sunanta da murya mai nuna tsantsar bukatar dake tare dashi.Ameena…..Bata amsa ba amma ta tashi ta zauna.Shima tashin yayi ya zauna.Nasan abunda ya faru dazun ya bata ranki kuma na aikata kuskure akan hukuncin dana yanke da kalaimaina amma dan Allah kiyi hakuri hakan bazai sake faruwa ba.Ummm,,,, tace dashi.Nace ai kiyi hakuri ko bazan sake ba, sannan kinsan banaso ki barni da iyawata aduk sadda na bukace ki hakan yana sosa raina.Naji,, tace.Toh kinyi hakurin yanzu muci gaba?Ta dan numfasa kamin tace, gaskiya bazan boye maka ba da zakayi hakuri zaifi domin a halinda zuciyata take ciki bazan iya baka farin cikin da kake bukata ba sai dai idan kana ganin zaka iyayi a hakan toh babu laifi, tana gama fadin haka ta kwanta.Dake bukatar ta cishi da yawa hakanan ya bita yana laluba har ya biya bukatarsa ya tashi daman shi haka yake baya taba tsayawa da zarar bukatarshi ta biya baya jiran yaji ko ita tata bukatar ta biya saidai ya tashi, wannan yana daga cikin abunda yake kona ranta sosai domin ita macece mai yawan bukata kuma hakan da yakeyi sai ya zama ko tana da bukata bata tunkararshi domin wahala zai bata kawai kuma koda shi ya nemeta da kanshi bata marmari domin kanshi kawai ya sani.(Mata da yawa a wannan zamanin abubuwan da suke fuskanta kenan daga mazajensu so wannan abun ya zama ruwan dare don haka ba fushi zakiyi ba maganane tsakanin ki da mijinki idan da fahimta a tsakani zai fahimceki ya sauke hakkin ki dake kan shi idan kuma rashin lafiyace tayashi jinya da addu’ah har Allah ya kawo mafita idan stress nema kinfi kowa sanin yadda zaki magance masa, Allah yasa mu dace)Kwanciya yayi bayan ya mirgina gefe, ta mike ta fada toilet tayi wankan tsarki ta fito domin bata yadda sam ta kwana da najasa a jikinta saidai in akasi.Ta fito ta tsane jikinta da towel ta shafa turare da mai ta maida kayanta ta kwanta tana kallon bayansa daya juya mata tana ayyana abubuwa aranta har bacci yayi awon gaba da ita.Da asuba ta farka ta hada masa ruwan wanka a toilet tazo ta tasheshi sai da taga ya shiga bayin kafin ta fita ta nufi dakinta ta gabatar da sallah ta koma tabi lafiyar gado sai can gurin shida da rabi ta farka ta sauka daga gadon ta fito daga dakin ta nufi na shureim ta tada shi tasa shi ya shiga toilet din ta hada ruwa ta mai wanka tace yayi alwala suka fito ta shirya shi cikin kayansa masu kyau ‘yan kanti taja hannunshi suka nufi kitchen tasa abincin a microwave domin ya dumamu ta kunnan gas ta daura ruwa a tukunya kadan ta kawo cuttarta da kanumfari da na’ana’a da rabin garlic sai ganyen shayin ‘yan maiduguri ta jefa top tea guda daya ta kawo shuga tasa 7spoon ta barshi ya tafasa yana fidda kamshi ta kammala komai ta hada kan komai a babban paranti suka wuce falo ta ajiye a dining ta debi na shureim da nata ta bashi abincin ya rike ita ta rike lipton din suka wuce dakin shureim.Koda Abdul ya fito cikin shirinshi na fita wurin aiki ya yada zango a kan dining din yaja kujera ya zauna ya zubawa kanshi komai ya soma ci har ya cinye kafin ya soma kwalla mata kira.Ameena….Ta fito ta same shi ya mike tsaye rataye da jakarshi, na tafi office sakwara da miyar taushe zaki mana da yamma na ajiye miki kudi saman mirror.Toh Allah ya saka da alkhairi Allah ya bada sa’a ya kareka a duk inda kake.Ameen.Dan Allah kamun izini inaso inje gidan inna zuwa azahar sai in dawo in Allah ya yarda.Baza kije ko ina ba!Toh shikenan, ta fada da muryarta mai sanyi.Ya nufi kofa zai fita sai kuma ya juyo ya kira sunanta.Ameena..Ta tako zuwa inda yake ta tsaya tana wasa da yatsunta.Ya Matar kallon tsab kafin yace, kije amma kada ki dade sannan ki tabbatar kin saka nikab idan zaki fita ban yadda ki bari wasu suga fuskarki ba.Nagode Allah ya saka da alkhairi insha Allah yadda kace hakan za’ayi.Yau bazaki mun rakiya ba kenan? Ko har yanzu baki huce bane banace kiyi hakuri bane kam, ya fada yana tsare ta da ido.Tayi kasa da kai bata amsa ba domin gaskiya ya fada har yanzu bata huceba don sosai ya bata mata rai.Haba mana Ameenatu na kiyi hakuri mana umm ko in bar zuwa aikin ne inyi zaman rarrashinki har ki huce? Bana son fushinki, ya fada yana kokarin komawa falon.Ta ture shi da duka hannayenta ta danyi murmushi kaje aikinka kawai muje toh in rakaka tunda ka zama dan goye.Eh mana dan goye ne mana a gurinki.Idan kayi latti nidai babu ruwana, ta fada tana mai hararar wasa a ranta tana jin dama yata zama a haka amma kash wannan saurin hawan nashi da rashin bincike akan abu kafin yanke hukunci yana damunta sai takejin anya zamansu zai dore a haka kuwa?Saida ya fita daga gidan gaba daya ta komo falo lokacin shureim harya kai plates din da suka cidasu kitchen ya dawo falo don yana jin hirarsu ya san mugun ya fita.Ameena ta kalleshi lokacin da take zama kusa dashi ta shafa kanshi.Allah ya raya munkai ya kareka ya maka albarka.Ameen yace.Shureim kana son zama gurin kaka?Da sauri ya gyada kai yana eh! eh! zan zauna zaki kaini ne momma?Kai ta gyada masa tana murmushi zan kaika can ku zauna tare bana fatan tarbiyyar ka ta samu rauni sakamakon abubuwan da suke faruwa tsakani na da babanka zan kaika can hankalina zaifi kwanciya.Nan kuwa yaro ya fara murna.Cikin kankanin lokaci ta gama shirya kayan shureim ta musu girki ta zuba wanda zata kai musu ta zuba musu suka ci ta shirya su suka fito kofar gate din gidan kasancewar a bakin titi gidan nasu yake sai suka tsaya nan ta tari napep ta dau drop yanda zai kaisu har kofar gidan inna.Da sallama suka shiga gidan shureim ya tafi da gudu ya buda dakin inna ya shiga, inna ta fito dauke dashi a hannunta tana fara’a.
Alkalamin eeshert adamu✍️



