Hausa novels

Halysaah Page 140 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 140…Ajay na shiga part dinsa ya sa ma kofar key, tsabar yanda Khaleesat ta girgiza har Ikcn bata tashi a inda yayi dumping dinta ba a babban parlon, ko Kallonta bai yi ba ya nufi parlonsa kamar zai tashi sama, ta bi sa da kallo babu ko kiftawa zuciyarta na wani irin bugawa, kawai taga ya juyo ya dawo parlon yana kallonta Strictly yace “Do not say anything to anyone duk tambayar da za a maki Yana kai wa nan yayi wucewarsa parlonsa taji yayi banging kofar, Khaleesat ta fashe da kukan tashin hankali ta zamo abar tausayi, kuka kawai take a parion kamar ranta zai tita, daga karsne ta mike tana tafiya a hankali ta tafi parlonsa bugun zuciyarta na tsananta, ganin yana Bedroom ta karasa ta murda kofar taji ya sa makulli, ta juya hawaye na sauka idonta ta koma parlor ta zauna tayi tagumi, knocking din kofar parlon taji ana yi ta mike a tsorace duk da kofar a kulle yake, muryar Mami taji a bakin kofar, hakan yasa ta karasa zuciyarta na bugawa ta bude kofar, Mami ta shigo tana kallonta tace “Ina Junaid din?” A hankali Khaleesat tace “Yana daki” Mami ta nufi cikin parlonsa Khaleesat ta bi bayanta bayan ta kulle kofar parlon, knocking kofar dakinsa Mami tayi tana kiransa, After a while ya bude kofar, ya ki kallon Mami, Mami ta shiga dakin tana kallonsa tace “What happened Junaid? Me ya hadaka da shi haka??” Ajay yayi shiru bai ce komai ba kuma bai daga kansa ba, a fusace Mami tace “Magana nake maka ko baka ji na ne” Ya dago idonsa a hankali yace “He is just daring me in this house, dama kuma tara sa nake, ko shekaranjiya a gaban Mai martaba ya gaya min maganar banza” Mami tace “Shi ne zaka masa irin wannan duka Junaid? Ko dai baka da hankali ne?” Ajay ya ki cewa komai, Mami tayi shiru tana ta kallonsa, daga karshe ta juya kawai ta fita daga dakin Ajay ya mayar da kofarsa ya sa makulli, Mami na kallon Khaleesat tace “Me ya masa yau din yayi masa wannan duka haka?” Hawaye na sauka idon Khaleesat ta girgiza ma Mami kai kawai alamar bata sani ba tunda ya mata warning kar ta fadi komai, Mami ta nufi kofa ta fita daga bangaren, Khaleesat ta tafi ta kulle kofar ta fashe da sabon kuka ta sulale wajen, Walid dai tuni aka yi asibiti da shi hannu a karye. Tun bayan da Mami ta tafi Ajay bai sake fitowa daga dakinsa ba, Khaleesat dai na ta zaune parlor tana tunanin wannan wane irin bala’i haka, sai lokacin sallan juma’a Ajay ya fito daga bangarensa sanye da fararen kaya kamar ba abinda ya faru zai tafi masallaci, sau daya ta kallesa ta sunkuyar da kanta, yana kallonta yace “Have you eaten?” Duk da bata ci ba kawai ta gyada masa kai, ina taga nutsuwar cin abinci ita kam, yana fita parlon taji ya kulle daga waje, bai je masallacin da ya san Mai martaba da mutanen gidan ke zuwa ba, yayi tafiyarsa masallaci me nisa. Bayan isha’i Ajay ya nufi fadan Mai martaba tare da Khaleesat dake biye da shi a baya zuciyarta na bugawa, tun safe Mai martaba ya sanar da zaman, Ajay ne karshen shigowa ya tarar da kusan duk familyn gidan zazzaune a babban parlon, hatta wa enda ke nesa duk sai da suka amsa kiran Sarki suka zo, tun daga iyaye har ‘ya ya da jikoki, Walid ma na zaune parlon da katon bandage an nann kansa ga hannunsa da aka daure saboda karyewan a da yayi, fuskarsa duk a kumbure, ga targade kashi kashi a kafafuwansa, bakinsa ma yayi suntum, Aunty dai na zaune idonta duk sun kumbura don kuka jira kawai take taga hukuncin da Mai martaba zai dauka kan Ajay kafin ma ta ce komai don tun safe taki magana a gidan, Ajay bai yarda ya kalli kowa a parlon ba ya zauna kusa da Mukhtar ya sauke kansa kasa, kowa na parlon kallonsa yake banda Sarki, Khaleesat jiki a sanyaye ta tafi ta zauna kusa da Mami, ita ma aka bi ta da hararan tsana, for 5 mins babu abinda Sarki yace a parlon, ko ina was absolutely silent, in da sabo duk sun saba don sarki sai ya iya bata kusan minti goma bai yi magana ba kamar dai yana nazarin abubuwan da zai furta before saying anything, daga karshe Sarki ya sauke ajiyar zuciya dama an riga an bude waien da addu’a tun Ajav basu karaso ba tunda haka ne sai mai martaba ya fara magana cike da nutsuwa da kuma dattako… ina da labarin abinda ya faru a gidan nan yau da safe, which is so unfortunate, bana kuma tunanin akwai wani abu da Ahmad zai fada da zai yi justifying abinda yayi ma dan uwansa ignoring my few days ago warning akan duka a cikin gidan nan, don haka Ahmad is not and will never be capable of ruling this Emirate one day one time, babu ta yanda za ayi a ba madambaci mulkin masarautar nan, shi ne naga yana da kyau in tara ku nan in fara sanarwa tun daga cikin gida cewar Ahmad Junaid Yusuf is hereby dethroned as the prince of this great Emirate, daga rana irin ta yau na sauke sa a matsayin Yariman wannan masarauta….” Ajay ya daga kai a hankali yana kallon Mai martaba babu ko kiftawa kamar yanda kowa na parlon ke kallon Sarki with utmost shock, Khaleesat ta daga kai hawaye cike idonta tana kallon Ajay, Aunty sai gyara Alkyabbar jikinta take tana kara kallon sarki da idanuwanta kamar za su fito don sai taga kamar mafarki take ba daga bakin Mai martaba hakan ya fito ba ko kuma ita ce bata ji da kyau ba, Jay ma sai kallon Mai martaba yake babu ko kiftawa, Mami ta sauke idanuwanta a hankali, the announcement came as a shock to everyone in the parlor babu wanda ya kawo wannan hukuncin sarki zai yanke kan Ajay, Sai da sarki ya bari kowa ya gama processing abinda ya fada sannan ya ci gaba cikin nutsuwa yace “And from tomorrow in sha Allah Ahmad Jawwad will be crowned the Prince of this great Emirate through all proper rite” Sai da numfashin Aunty ya dauke na yan dakiku, ta dinga kallon sarki babu ko kiftawa, duk tunaninta Walid zai nada sabon Yarima tunda Walid ne second blood son dinsa, kowa na parlon was in a shock da jin wannan hukuncin na mai martaba. Daga can Fulani Aseeyah ta bude baki ta fara magana “Amma Allah ya taimake ka….” Dakatar da ita Sarki yayi yace “Ban bukaci Opinion din kowa ba, and this is disrespect to the king Fulani Aseeyah” Mami tayi shiru, Hadiyah ta kalli Ummi da farin cikinta ya kasa boyuwa sai kallon Mai martaba take unbelievable, hawayen farin ciki ne ya hau sintiri fuskar Hadiyah ta dinga ganin abun kamar a mafarki wai mijinta ne Yariman Masarautar nan yanxu, Mai martaba ya ci gaba yace “Na saka Makama ya sanar ma masu sarautu, tun daga Hakimai, dagatai da sauransu duk su hallara a fada gobe su shaida wannan sauyi da aka samu sannan a nada sabon Yarima, and mind you all… no one is in the rightful place or position to question the decision of the King in anyway, and as for you Ahmad Junaid bana son ganin ka a duk inda kasan za mu hadu a gidan nan, keep a reasonable distance from me, idan ba haka ba you will be surprise at my next action toward you….” cikin kakkausar murya Mai martaba ya kare maganar sannan ya mike ya bar parlon, Ummi ta daga hannu sama da karfi tace “Alhamdulillah Ya Allah Nagode maka, Alhamdulillah” Jay ya daga kai yana kallon Mami da ta kasa ma dago kanta, su Gimbiya Firdausi da Kilishi sai kallon Aunty da hawaye ya cika idonta suke, can Aunty ta mike ta fice daga parlon don kar ma ta fashe da kukan takaici a parlon, Ajay ya mike fice cikin wani irin yanayi na gushewar tunani… bude pampo, she felt guilty don komai ya taru ne saboda ita, Mikewa tayi ta bi bayansa da sauri hawaye na zuba idonta, Mami dai ta bi ta da kallo, Khaleesat na shiga Bedroom dinsa taji yana bathroom ya bude shower, komawa parlor tayi ta cire hijab din jikinta ta hade kanta da kujera tana kuka sosai, she is feeling really bad, she cried for 20 minutes a parlon, daga karshe ta mike ta goge hawayen idonta ta shiga cikin dakinsa, zaune ta gansa gefen gado ya dafe kansa bayan ya fito wankan ko goge jiki bai yi ba, wasu hawayen suka taru idonta ta karasa har gabansa ta tsaya, ya dago kansa a hankali yana kallonta, bata san sanda ta rungumesa ba ta dora kansa a kirjinta tana shafa wet hair dinsa hawaye na zuba idonta, lamo yayi a kirjin nata yana sauke numfashi a hankali, sai kuma taji saukan hawayensa a kirjin nata, daura lips dinta tayi a gashin kansa giving him kisses.

Back to top button