Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 44 By Ayshercool

Gaba ɗaya ya kasa samun nutsuwa sai da jauhar ta farga ta ce “Master ya ne?””Na kasa samun Nura a waya”Ta ce “Allah sarki, ɗan uwa nagari in sha Allah zaka same shi, maybe ko babu caji ne a wayar”Ya ce “No, kusan sati fa kenan, na kira P.A ya ce mini suna nan lafiya, wataƙila wayarsa ce ta samu matsala, idan ma haka ne, ai ko wayar wani ya ara ya kira ni, tun da kusan kullum sai na yi waya da shi, na ja masa kunne”Jauhar ta ce “Haka ne, amma ƙara masa kwana biyu mu gani”Jiki a sanyaye ya ce “To shikenan”Al’amin ya hana jauhar duk wani aikin wahala, su halimatu ne ke zuwa ta yi guiding ɗin su, su yi mata snacks ɗin da ake kai wa wurin shayi, sai bead work da take yi tana daga zaune, shi ma faɗa yake yi yana mita.Iya haƙuri da ɗaga ƙafa ta san yayi mata, dan yau sakata yayi a gaba yana mita, ba dan yana son cikin nan ba, da tuni ya daɗe da bin rariya shi ma.”Master” ya ɗaga kai ya kalleta, ya haɗe rai.”Wai laifin me na yi ne?””Ni gaskiya na gaji, sai yaushe cikin zai gama ƙwari ne? Nima ai yakamata a duba lamarina”Murmushi ta yi, yadda yayi kicin-kicin, kamar wani ƙaramin yaro.”Lamba nawa ake so?” Tayi maganar tana kashe masa ido.”Na gaji da lamba uku huɗu, lamba ɗaya nake so” Jauhar ta ce “Baka damu da babyn nan ba ko?”Ya girgiza kai ya ce “Wallahi na damu da shi, ina son abuna, amma ba shikaɗai yake buƙatar ya rayu ba, kuma ba shikaɗai yake buƙatar ki ba” yayi maganar a marairaice.Ta ɗan yi shiru tana nazarinsa, da gaskiyar sa, kusan kullum ba ta da lafiya, tana kallo wasu lokutan sai dai yayi zamansa a ɗakinsa, ya busa hayaƙi, dan kar ya takura mata, ko ya karya dokar da aka saka saboda cikin.”Kin yi shiru fa”Dariya ta yi ta ce “Subhanallah, master da shagwaɓa, lamari ya ɓaci, to lallaɓani”.”Ai lallaɓakin nake yi””Inyee dama ka iya shagwaɓa baka taɓa yi mini ba, yanzu da da safe zan ce ka yi mini mazewa zaka yi kana hararata. To daga yau mayar maka da fankarka zan yi, dama ta fara tsufa”.Al’amin ya ce “Zan yi zuciya fa”Ta ce “To yi mana idan zaka iya, huta roro waken gizo yaƙi ‘ya’ya” tayi maganar tana jan dogon hancinsa.”A’a ba zan yi ba ma”Tayi murmushi tare da rungume shi.Har suka kwanta tana lafiya, sai cikin dare ya farka ya ganta a zaune, ta takure wuri guda.”Madarata, ya aka yi ne?”Jauhar ta ce “Bakomai, zafi ne ya dame ni””Zafi kuma? Ga fanka na yi?. Ko numfashin ne?”Ta ce “A’a, lafiya ƙalau nake numfashina”Ya ce “To ya aka yi na ganki a zaune?”Tausayinsa ya kamata, har istigfari take yi, ta gaji da ce masa ba ta da lafiya ba yau ba gobe.”Master ka kwanta dan Allah, na kasa baccin ne”Cikin damuwa ya ce “Ka kwanta ka yi baccinka””A’a ban yadda ba, akwai matsala ne, gaya mini?””Marata ce take ciwo”Cikin tashin hankali ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Allah ya sa ba zubewa zai yi ba, ya salam”Ta jingina da jikinsa ta ce “Ciwon fa ba mai damu bane ba, ƙullewa tayi, na ji kwanciyar babu daɗi, shiyasa na tashi zaune””Ko asibiti zamu je? Wallahi ina son cikin nan zahra, na kwaɗaitu da son ganin abun da zaki haifa mini, tun da muka rasa na farko, nake tunanin ko yaushe zamu kuma samu? Kuma mun samu wannan karon ma, zan yi dalilinsa, mu je asibiti kawai”.Cikin sigar rarrashi ta ce “Master, dan Allah kar ka ɗaga hankalinka, ba ciwo take yi mini ba, ƙullewa tayi ne sosai kuma na duba babu abun da yake fita. Ɗawainiyar da ka ke yi da ni ka da Allah ya gajiyar da kai, Ubangiji Allah ya nuna mini ka daina komai kan Allah ya kawo mana babynmu”Yayi ajiyar zuciya ya ɗora hannunsa a mararta ya ce “Ba zan taɓa gajiya da duk wani abu da ya jiɓance ki ba, ba alfahari nake yi miki ba, ɗan halak ne ni, kar ki taɓa sakawa ranki zan gaji, da ƙarfin ikon Allah ba zan gaji ba, in sha Allah, ni dai duk abun da ki ka ji na ciwo ki gaya mini dan Allah, ina son kasancewa da ke da iya adadin abun da zaki haifa mini, mu yi rayuwa mai tsayi da daɗi. In sha Allah zan yi iya ƙoƙarina na zama uban kirki ga ‘ya’yana, kuma miji abun alfahari gareki”Haka kurum ta ji jikinta yayi sanyi, da maganganun sa, ji take kamar akwai wani abu mai girma da zai faru da su, sai dai ba ta sani ba, na daɗi ne ko akasin haka.Ta sake lafewa a jikinsa, tana jin tsananin buƙatuwar son cigaba da kasancewa da shi a cikin rayuwarta, ita wannan kulawar da yake yi mata, tana shafe dukkan sauran abubuwan da yake aikatawa.Zuwa da safe ta ji ƙwarin jikinta, har ta ce masa zata makaranta, da ƙyar ya amince, saboda tana da test.Har ta fito ya karɓi jakarta, ya ce shi zai kai ta, kar ta hau ɗan sahu, ayi ta gargada da ita.Ya duba jakar ya ce “Ina inhaler ki?”Ta ce “Tana aljihun wandona””Meyasa ba zaki saka a jaka ba””Zai iya yiwuwa ciwon ya tayar mini, jakar tana nesa da ni, amma a wandona da na laluba zan ji ta””Allah ya baki ingantacciyar lafiya, ya rabaki da ciwon nan gaba ɗaya”Ta ce “Amin bugun zuciyata”Ya ce “Iyeeee?”Ta jinjina kai ta ce “Eh mana””To bani da kuɗi dai, kayan abinci zan sayo mana, idan kuma na ɗauka na baki shikenan”Ta tsuke fuska ta ce “Kai ba ayi maka abun arziki, da na yi maka kalamai, sai ka hau ce mini ba ka da kuɗi, me ka ke nufi”Al’amin ya ce “Ai ke ɗin ce, wasu lokutan haka ki ke yi mini, bana sanin lokacin da ki ke sakawa na zazzage miki aljihuna”Jauhar ta tura baki ta ce “Wannan kalaman wataran da kuɗi ba zaka ji su daga bakina ba”Take jikinsa yayi shock ya ce “Ban da irin wannan wasan” idonsa ya nuna ƙarara tsananin fargabar rasata.Ta basar da zancen, ya kaita makaranta.Abu kamar wasa, sama da kwanaki biyar, Al’amin bai ji ɗuriyar Nura ba, bai kuma same shi a waya ba, dan haka ya wanke ƙafa ya tafi gidan indabo, kasancewar ba shi da shamaki da gidan, babu mai tambayarsa wurin wa ya zo, ina za shi, kai tsaye ya shige.Ofishin indabo na gidan ya tafi, kasancewar imdabon yana Abuja, cikin sa’a ya tarar da P.A.”Mai zamani, ya aka yi ne?””Na kasa samun Nura a waya””To ai ina zaton wayarsa ta samu matsala ne kamar yadda na gaya maka”Ya girgiza kai ya ce “Ba zai yiwu ba, shirun yayi yawa. Ba zai yiwu na baku amanar yaro, garin da ba uwar sa babu ubansa na kasa samunsa a waya, kusan sati biyu, na zauna na yi shiru ba, ba zai yiwu ba, dole ka san duk yadda zaka yi ka haɗa ni da shi””Amma mai zamani ina nan yana Abuja, a ina zan iya haɗaka da shi?”Cikin ɗaga murya ya ce “Ka kira indabon, duk yadda zai yi ya haɗani da shi”P.A ya tsaya yana kallon sa.”Zaka yi abun da na ce, ko sai na saka maka ƙarfe?”Ya janyo waya ya kira Indabo, suka gama magana. Ya kalli Al’amin ya ce “mun yi magana da honorable, ya ce in anjima zai aika a duba shi, yanzu suna meeting da shugaban ƙasa”.Yayi ƙwafa ya juya zai fita, Abdul ya kawo kai shi ma ya shigo. Sai dai Abdul ya tsaya yana jiran Al’amin ya bashi hanya, wannan ce haɗuwar su ta biyu, kasancewar ba a ƙasar yake zaune ba, ya fi sanin ɗayan wato Ja’afar.Ala’amin bai tsaya jira ba, ya yi wa Abdul wata muguwar bangaza da kafaɗarsa, sai da ya dangana da faɗuwa ƙasa.A fusace ya miƙe zai bi bayansa, P.A da sauri ya tsare shi ya ce “Kul, sai ya yi maka illa, ba mutunci ya cika ba wasu lokutan”A fusace Abdul ya ce “Mahaukaci ne shi, baka ba ka ga irin bangazar da ya yi mini bane?””Yi haƙuri, ai duk abun da ka ga honorable yana bi a sannu, ka san ba ƙarami bane ba, yi haƙuri”.Ya kalli P.A ya ce “Babu ruwana za abun da yake bi a sannu, wallahi muka sake haɗuwa sai na koya masa hankali” ya juya ya fasa yin abun da zai yi.Har la’asar Al’amin yana kallon wayarsa, yana jiran kiran indabo, ya je wurin shayi, komai yana tafiya dai-dai, ya tafi gida.Yayi jajjage ya feraye doya, ya dafa ruwa ya zuzzuba a flask, duk ya rage wa jauhar aiki.Wayarsa ta fara ringing, ya ɗaga ya kara a kunnensa.Muryar Nura yaji ƙasa-ƙasa ya ce “Yaya””Kai Nura wani irin shirme ne zaka kashe waya, ko ta wani ba zaka ara ba ka kirani, ina ta tunanin meyafaru da kai?”Nura ya ce “Ka yi haƙuri dan Allah””Ya ake ciki? Na ji muryarka wani iri?”Nura ya ja numfashi ya ce “Zazzaɓi ne yake damuna, sun bani hutu ma, an kai ni asibiti an bani magunguna ma””Yasalam, kai daga zuwa garin mutane sai rashin lafiya, ko aikin ne da wahala?”Ya ce “A’a””To Allah ya sauwwaƙe, zan cigaba da kiranka, idan ka ga babu hali, kawai ka dawo gida”Nura ya ce “Godiya nake, Allah ya kiyaye ka ya ƙara tsawon zamaninka””Ka huta, ka kula sosai duk yadda ake ciki, ka sanar mini, ina fatan sun sallameka, dan na ga wata ya ƙare””Eh an bani kuɗi masu yawa ma, ka bani account number ɗinka, na sako maka abun da na samu, amma a ciki a sayawa Antynmu turimin atamfa dan Allah, da ita da babata a sai musu iri ɗaya”Al’amin ya ce “A’a, ta gode sosai, amma ba haka za ayi ba, ka ba wa maman abun da zaka bata, ka tallafawa babanka da wani abun ya sai kayan abinci”Nura ya ce “Shikenan, tun da ka ce haka, amma dan Allah ka saya musu atamfa iri ɗaya da mamanmu, tana sonta sosai “Al’amin ya ce “Zan duba na ga abun yi, ka kula da shan magani ka ji ko?””In sha Allah””Good boy, sai anjima” ya kashe wayar, sai ya ji wata irin sa’aida a zuciyarsa jin muryar nura, dan babu irin saƙe-saƙen da bai yi a kansa ba.Da jauhar ta dawo, aikin gida ƙarashe ne, duk yayi, sai godiya take yi masa tana yi masa addu’a.Jauhar tun da cikinta ya fara tasawa, da an buga gate, sai ta saka hijjabi tana ɓoyewa, wai kunya take ji.Yayi ta yi mata dariya, ya ce “Da ki ɓoye, da ki bar shi, ƙarewa haifarsa zaki yi ƙarshen kunya, gara ma ki bar shi kowa ya gani”.Cikin shagwaɓa ta ce “Ni dai ka bari na ɓoye abuna”Ya ce “Ai sai ki yi ta yi”Al’amin ya sha mamaki kuɗin da guduma ya turo masa, dubu ɗari da hamsin, wai a bawa babansa dubu ashirin kawai, sauran har da su oga liti da oga walid ya ce duk rarraba musu.Al’amin ya ce “Wai aikin direban ne aka baka wannan kuɗaɗen har haka?”.”Eh Oga, ka san birnin tarayya ne nan, kuɗi ba wahala suke yi musu ba, ka cigaba da yi mini addu’a, jikina ne babu daɗi”Al’amin bai matsa da bincike ba, ya ƙyale shi.Jauhar ta yi mamaki da ya kawo mata atamfa, sai Nura ne ya turo da kuɗi a saya mata iri ɗaya da mamansa.A lokacin ta ƙara yadda da ƙani ya ɗauki Nura, da wani ne daban ya bata, cewa zai yi ba zata saka ba.Al’amin da kansa tare da rakiyar su Walid, suka je suka kaiwa mahaifiyar Nura, abun da ya aiko a bata, ta din ga murna tana yi wa Al’amin godiya tare da yi masa addu’ar gamawa da duniya lafiya.Mai unguwa kuwa raina dubu ashirin ɗin nan yayi, a ganinsa tun da Nura ya tafi Abuja, dubunan ɗaruruwa zai aiko masa, ya fara zargin ko Al’amin ne ya rage kuɗin.Ɓangaren Abbu kuwa, Abba ɗan wurin rahila, ya haɗa kai da abokai, suka fara yi wa Abbu sata, da ƙaramar sata suke yi masa, wani ya gani ya kawar da kai, wani kuma ma bai san sun yi ba.Sai dai a wannan karon, satar da suka yi masa ba ƙarama bace ba, dan har ya kai ga reporting wurin Jami’an tsaro, da fari rahila ta ɗauka abun mai sauƙi ne, dan ta na ta yi wa Abbu masifar a kan me zai tayi mata terere da ɗa dan ya ɗauki kuɗi, ai shi mai rufa masa asiri ne yayi masa nasiha, sai dai ta girgiza da ta ji ya saka ‘yan sanda sun kama shi.Tamkar za ta yi hauka, da ƙyar ya saka aka sake shi, ya ce sai dai ya bar masa gida ya koma gidan ubansa, nan ma ta ce sai dai ya zaɓa ko dai ya zauna da ita da yaranta ko kuma idan ya matsa su tafi gaba ɗaya, ya ce ta kwashe yaranta su tafi.Sai da ta ga ba ta da sauran mafita, sannan ta koma lallaɓa shi, da ƙyar ya saukko.Juahar tuni ta fara zuwa awo, dan yau shi ya rakata awon ma, a wurin scanning aka nuna masa yadda zuciyar jaririn take bugawa.Gaba ɗaya ya rikice, bakinsa ya ƙi rufuwa, ya zubawa screen ɗin ido, yana ta washe baki yana murmushin.Jauhar ta ce “Ni fa na gaji zan tashi”Ya ce “Ɗan yi haƙuri, bari na ƙara ganinsa mana””Ka ga me? Me ake ganewa a nan, ni banda duhu ba na ganin komai”Al’amin ya kalleta ya ce “Sautin bugun zuciyar ta sa ne nake ji har cikin raina”Sai da mai scanning ɗin ya yi dariya, aikuwa ta tashi zaune ta ce “Ni na gaji, haka kurum, na fuskantar tun yanzu kafi son ɗan tayin nan, to ka matso ka saukko da ni”Ya miƙe ya saukko da ita daga kan gadon, ya ce “Ki din ga motsawa a hankali, kar ki takura shi”.Tayi murmushi ta ce “Idan ban tafi da gudu ba, ka ce ba ni ba ce”Ya ce “Yi haƙuri, ai dole na lallaɓaki” suka je aka gama yi mata awo, suka tafi wani shago na kayan jarirai, suka fara sayayya, kasancewar an ce musu tun a wata shida, kan ciki yayi bakwai ake haɗa kayan haihuwa, saboda haihuwa za ta iya zuwar mata a wata bakwai, sannan ya tanadi kuɗi, dan ba a san ya haihuwar zata zo ba, ko ta haihu da kanta, ko kuma ayi mata tiyata.Ta zo ta shirya kayan da suka sayo a wani ɓangare na wardrobe ɗin ta, kallon kayan kawai nishaɗi yake sakata.Washegari da safe, yana falo yana kallon wrestling, ta fito daga ita sai wata rigarsa da ta saka shirt ce, tayi mata yawa nesa ba kusa ba, iya cinyarta ta tsaya, sai kanta tayi kalba guda biyar, ta sake su ta fito tana miƙa tare da hamma.Ya buɗe mata hannayen sa, yana murmushi, ta ƙarasa ta zauna a kan cinyarsa, ya rungumeta ya ce “Sannu””Yauwwa. Ina kwana?””Lafiya ƙalau, ya jiki ya babyna?” Yayi maganar yana shafa bayanta.Ta ce “Ni babyn ko wa?””Ƙatuwa da ke ke ce babyn, unborn dai”Boti ya hawo saman kujera, ya hawo jikin Jauhar, Al’amin ya kai hannu zai cillar da shi, ta riƙe shi tana dariya ta ce “Master dan Allah ka bari magen nan ya huta, duk ya tsaneka saboda cin zalinsa da ka ke yi, akwai buƙatar na yi muku sulhu””Babu sulhu tsakanina da wannan abun”Ta ɗauki boti tana shafawa ta ce “Boti ku daina faɗa da master dan Allah” muzurun ya kawar da kansa gefe, Al’amin ya ƙwace shi ya ajiye shi a ƙasa, ya koma da baya yana kartar carfet ɗin yana yi masa kuka.Jauhar ta din ga dariya, ta ce “Wallahi daga kai har shi dariya ku ke bani”Al’amin ya lumshe ido ya buɗe, yana shafa cikinta ya ce “Duk kin zama ƙazama, kalli kin daina kitso, ga wata uwar riga kin saka, wadda sai an saka irinki goma a ciki, ni ɗaga rigar na din ga kallon jaririna””Master kenan, ba zaka gane ba, ni kaina ba na son zama da kan nan a haka, amma da an fara yi mini kitso zafi yake yi mini, kayana kuma duk sun yi mini kaɗan, amma idan na saka rigar nan taka, balance nake yi a ciki”Ya kashingiɗa a jikin kujera, yana cigaba da kallonta, yana jin wani irin kusanci da shauƙin kasancewar sa da ita wuri ɗaya. Kullum yana ƙara girmama lamarin Ubangiji yadda ya ƙaddara kasancewar su tare, wanda idan ba ƙarfin ikon Allah ba, babu abun da zai haɗa shi da ita, har ya nemi aurenta. To wa ma zai bashi auren yarinya irin jauhar a yadda yake.”Master ka san menene?”Ya girgiza mata kai.”Na ji an ce akwai lokacin da ma’aurata kan gaji da juna, ko miji ya ji matarsa ta gundure shi, dan Allah idan Allah ya raya mu ka fara jin irin haka a kaina, dan Allah ka yi haƙuri kar ka canza mini, na saba da kai sosai da sosai. Ina jin daɗin yadda na samu mai tausayina wanda ya mayar da ni mutum, yake zama ya saurari damuwata. Dan Allah ko nan gaba ka samu wadda ta fini, ko na fara gundurarka kar ka yi mini wulaƙanci ko ka manta da ni dan Allah” tayi maganar very serious.Ya ƙura mata ido, yana mamakin maganganunta.”To ai ni ko yanzu kin gundureni, duk kin hana ni rashin ji na, na saba da rayuwata ta ɓalla ƙarafa da hawa network duk kin hanani, zaman haƙuri kawai nake yi da ke, kin isheni”Wasa yake yi mata, kawai ya ga tana kuka.A ɗan rikice ya ce “Haba Madarata, ke yanzu idan aka ce miki zan yi miki abu makamancin haka zaki yadda? Ina sake maimaita miki ni ɗan halak ne bana manta alkhairi. A lokacin da kowa ya yasar da ni, yake yi mini kallon mara amfani a lokacin ki ka rungumeni a yadda nake, ki ka yi ya ɗawainiya da ni, ba tare da kin gaza kin ƙosa ba, bana fatan Allah ya nuna mini ranar da zance kin gundureni”Ta share hawayenta ta ce “Ka san wani abu, kai diamond ne da mutane ba su farga da shi ba, suke maka kallon mara amfani. Sai yanzu da ƙyallinka da haskenka ya fito”Ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana murmushi ya ce “Ke dai ki ke kallon hakan, ga al’umma na zama mara amfani, saboda ɗan daba ne ni””To ni dai kana da amfani a wurina”Yayi murmushi ya ce “A ɓoye fa rigima kawai ki ke so ki yi na rarrasheki, to na ji sannu yi haƙuri””Yauwwa mata da yawa ba ayi mus irin yadda ka ke yi mini ɗin nan, zuciyar zinare ce da kai master, kana da tausayi sosai da sosai” ta kara kunnenta a ƙirjinsa ta ce “Zuciyarka sai kiran sunana take”Al’amin ya ce “Ni dai yi magana a hankali, na ji babyna yana motsi, kar kwanciyar da ki ka yi ce kika takura masa, tashi zaune”Ta ɗaga kai ta kalleshi ta ce “Master, zaka dawo ka tarar da ni, ina ‘yar gala-gala da cikin nan, duk sai nuna banbanci ka ke yi”Shi ma kallon fararen idanunta yake yi yana dariya, ya ce “To breakfast fa, me zamu ci?” Ta tashi zaune ta ce “zan dafa maka wani abun, amma ni anty wasila nake jira, za ta kawo mini wainar gero”Ya tsuke fuska ya ce “Roƙo ko?” Ta ce “A’a geron da ka kawo na ɗiba na bata tayi mini, idan ni na yi ba zan iya ci ba”Ya ce “Ok”Har azahar yana gida, jauhar ta hana shi fita, sai azahar yayi shiri ya fita, saboda sallar azahar, yanzu jauhar ta daina fama da shi a kan yin salla a kan lokaci.Sai ga anty lubabatu, ta zo maƙwabciyar su mai ba ta aikin bead a gida.”Oyoyo anty lubabatu, yau ke ce a gidan”.”Yau gani na lallaɓo, an ce mini kin kusa juyewa, na ce bari na zo ga ya kike”Jauhar ta ce “Ohh ni zahra’au in ji wa? Ba a gaya miki daidai ba””Eh ba a gaya mini ba, ni na gani yanzu ai”Da sauri jauhar ta kalli cikinta ta ce “Haba dai dan Allah a na gani” Anty lubabatu ta kwashe da dariya ta ce “Lallai yarinya, wannan uwar ƙibar da ki ka yi ma da haka ki ke? Kin zama uwar mata”Juahar ta yamutsa fuska ta ce “Na yi muni ko?””A’a babu wani muni, wallahi kin yi kyau, kallo ɗaya mutum zai yi miki ya san a kwanciyar hankali ki ke. Jauhar gyaran gida aka yi miki haka, lokacin da na zo gidan nan kina amarya tsurar bulo ne fa, ikon Allah har da sola, wato a duniya idan Allah yana yinka ko wa ma yaƙi ka. Ga Alhaji mu’azzam can Allah ya bar su da shi, matarsa na ta gana wa hafsa azaba, abu har da ‘yan sanda, ya ce idan ba zata zauna da matarsa lafiya ba tayi mata biyayya ta tafi gida. Gidanku kuma ana ta tashin hankali, Anty zakiyya ta ce mama ke yi mata asiri”Cikin damuwa jauhar ta girgiza kai ta ce “Bari kawai Anty lubabatu, lamarin gidan nan namu sai Innalillahi wa Innalillahi raji’un, kuma wasu lokutan har da laifin baba, kodayeke shi ma sun mayar da shi sai yadda suka yi da shi, ai da ni aka ce ina yi wa hafsan asiri. Ko gidan ya hanani zuwa, sai idan da daddare ya kaini na gaida baba na dawo gida””Allah ya taimake ki, ke da suka so su tozarta rayuwarki Allah ya rufa miki asiri, ɗan daban da suka aura miki dan ki wulaƙanta, hakan ba ta faru ba””Tababs babu abun da zan ce wa Allah sai godiya, Anty lubabatu mijina a maza ɗari irnsa ɗaya ne tak. Daba da shaye-shaye su ne ƙaddararsa amma, ya ci sunansa amintacce rauninsa mutane suke kallo, basa kallon nagartarsa” sun daɗe suna hira sosai kafin ta tafi.Kusan duk bayan kwana biyu zuwa uku, sai hajiya kakar Al’amin ta kira Jauhar ta yi mata ya jiki, dan tun wani zuwa da tayi ta fuskanci hakan.Tun da ya fita da azahar har bayan magariba bai dawo ba, sai da ta kira shi a waya, ya ce mata gashi nan.Hnakali a tashe ya dawo mata, dan sai da gabanta ya faɗi ya ce “Master lafiya?””Nura aka kawo daga Abuja, wai ba shi da lafiya, tun lokacin nan da ya ce mini ba shi da lafiya, yake kwance”Ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, meya same shi haka?”Ya ce “Ban sani ba, an dai kai shi asibiti, na je na ganshi a galabaice, yayi magana ya faɗi meyake damunsa ya ƙi, na ga a galabaice yake sosai, an saka masa ruwa da sauran abun da yakamata gobe in Allah ya kaimu dai zan koma”.Jiki a sanyaye ta ce “Allah sarki Nura, sai da ka ce idan ba zai iya ba ya dawo, wataƙila dan kar ka yi masa faɗa ne ya zauna bai dawo ba. Allah ya bashi lafiya”Ya amsa da Amin.Ya ciro mata envelope ya ajiye mata.Ta ce “Menene wannan?”Ya ce “Duba ki gani mana”Hotunasu ne shi da ita, wanda galibi a wayarta suka yi, ya kai aka ciro su, sai kuma ƙatuwar viva, da aka yi frame ɗin hoton da suka yi na sallar eid ɗaya an rubuta musu happy marriage life, ɗaya kuma an rubuta first eid with habibi.Tayi murmushi ta ce “Kamat yayi a rubuta Master weds madara” duk da a cikin damuwa yake sai da yayi murmushi, ya ce da safe zai kafe a falo.Ta kalleshi tana murmushi, bai taɓa ce mata yana son ta ba, sai dai actions ɗin sa, yana tabattar mata da hakan. Da fari kai ba ka ce ya iya duk wani abu da yake da alaƙa da kulawa ba, saboda he’s always serious, sai dai a hankali ainihin halayensa suke fitowa.Jikin Nura yayi tsananta, kullum Al’amin cikin sintiri yake, jauhar ce mai lallaɓawa tayi musu girki, mahaifiyarsa ce take zaune da shi a asibiti tana kula da shi, gashi an rasa gane abun da yake damunsa, Al’amin har gona ya saka aka sayar masa a ƙauye, saboda kula da Nura, dan asibitin kuɗi ya saka aka mayar da shi.Da daddare babar Nura ta fita, Al’amin ya zo, cikin ƙarfin hali ya ce wa Al’amin “Yau ina Antyna ba ta zo ba?”Ya ce “Eh, ni na hanata zuwa, tayi nauyi. Nura yakamata zuwa yanzu ka gaya mini menene yake damunka, ana ta kashe kuɗi an rasa gane abun da yake damunkaa yayi maganar cikin damuwa”Nura ya ce “Idan na gaya maka ba zaka yi fushi da ni ba?””Ya za ayi na yi fushi da kai? Ka gaya mini in san ta in da zan kamo bakin zaren”.Ya riƙe hannun Al’amin ya ce “Na san ba lallai na rayu, amma ba ka da laifi ka taimaki rayuwata ne. Na gayawa mama na ce kar ta gaya maka. Lokacin da na ce maka na fasa tafiyar nan, Honorable ne ya ce sai ya yi ɗabi’ar mutanen annabi luɗ da ni, na ƙi yarda, ni kuma na kasa gaya maka, dan ya ce idan na gaya maka, kashe mai unguwa zai yi, amma idan na amince shikenan, ba wanda zai san an yi kuma zai bani aikin.Na ɗauka daga haka shikenan, sai dai tun da ya tafi da mu, a wani gida aka ajiye mu, abun da suke yi mana kenan, yana da masu kula da mu, babu ta in da mutum zai gudu, kuma ba shikaɗai ne yake yi mana hakan ba, akwai wasu manyan mutane a ƙasar nan, da duk zan gaya maka sunayensu.Kuma kamar tsafi suke yi ta hanyar amfani da mu, bana iya riƙe bayan gida, mama ce take gyara mini kafin mutane su zo dubiya, Indabo ya lalata mini rayuwa amma ka rufa mini asiri dan Allah, kuma kar ka zargi kanka! Ina da hujja mai ƙarfi da zan baka a kan haka!

Ayshercool 08081012143

Back to top button