Karfe A Wuta Chapter 38 By Ayshercool
Indabo ya cigaba da jujjuya wayar yana kallonta.Sosai jauhar ta ji babu daɗi, hanata zuwa bikin da Al’amin yayi, ba ta san dalilin sa na yin hakan ba, kuma bai gaya mata ba, ba ta san me za ta ce wa su mama ba, su yarda da ita.Kuma yayi fuska, ya hau hura hanci yana wani basar da ita, dan ma kar ta ce zata yi fushi da maganar hanata zuwa bikin da yayi, shiyasa yayi sauri ya rigata fara fushin.Haka ta wuni, idan ta tuna abun sai ta ji ba daɗi, da duk in da za ta je, ba ruwansa, amma yau bikin ‘yar uwatta, ya ce ba zata je ba, Al’amin kenan.Sai dai tayi iya ƙoƙarinta, ta danne fushinta, ba ta canza masa ba, amma yanayinta kallo ɗaya yayi mata ya gane, a cikin damuwa take, kuma ya san hakan yana da nasaba da hanata zuwa biki da yayi.Can gidansu amarya hafsa, ana ta rawar kai, an sha gyaran jiki, magungunan mata kuwa ba a magana, fatar nan ta ƙara ɗashewa, tayi fara ƙal kamar aljana.Sai hura hanci ake yi, za a auri mai kuɗi, mama kuma sai yi musu lumbu-lumbu, kamar tana tare da su a komai.Suka din ga karɓar kuɗi a wurin Alhaji mu’azzam kamar ba gobe. Shi kuma duk abun da suka nema, haka zai ba su.Zakiyya ta saka hafsa ta tambaye shi, wai a ina za su je honeymoon. Murmushi ya yi da ta tambaye shi ya ce “Hafsa yawon ƙasashen duniya har sai kin gaji, dai ƙasar da ki ke so zamu je” hakan ya ƙara fasa mata kai, ta din ga jin cewa ta gama dacewa.Al’amin ciwonsa ya fara warkewa, kasancewar ba shi da ƙan jiki, ga kulawa da Jauhar take yi da shi sosai da shan magani.Ta ɗaura aniyar, fara ɗora Al’amin a turbar tafiya masallaci kuma, ya din ga salla a cikin jama’a, kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, ya kwaɗaitar da al’ummarsa, mussaman da ciwonsa ya kame, dan ya fara saka riga ya fita ma.Sai dai fa aikin ba na wasa bane ba, dan wasu lokutan idan ta tashe shi sallar, har a idar tana fama da shi bai tashi ba, mussman idan a cake yake, idan ta yi alwala kuwa ta zo tashinsa, ƙarshe sai ta ta alwalar ta karye, shi kuma bai yi ba.Sai dai ta tsananta addu’a da gaya wa Allah. “Ya Allah ga bawanka Al’amin, kai ka halicce shi, ka shirya wanda suka aikata laifuka fiye da nasa, Ubangiji Allah ka shirya mini shi. Allah ka sa ya shiryu a sanadin zamana da shi, Allah kar ka saka na ƙosa ko na gaji, Allah ka dubi niyyata ta son zama da shi da yin biyayyar aure kamar yadda ka umarta, Allah dan kunfayanunka ka shiryi wannan bawa naka”Duk in da jauhar ta ji Addu’ar biyan buƙata, irin su salatul haja, salla raka’a biyu, fatiha da sura, idan ta idar ta mayar da goshinta ƙasa, ta karanta la’ila ha illa ant subhanaka inni kunt mina zalimin. Ƙafa arba’in da ɗaya, ba ta ɗagowa sai ta gaya wa Allah buƙatunta.Salatul tasbih, da sauran tasbihai haka take yi, tana yi wa Allah magiya da yin tawassuli da su, ta roƙi Allah ya shirya mata mijinta, ya haɗa kan su su zauna lafiya.Yau ta samu yayi sallar asuba ƙarfe shida saura da ƙyar, ta dawo dan ta saka shi yayi azkar, ta tarar har ya kunna sigari daga idar da sallar.Bai yi tsammanin za ta dawo ɗakin ba, kawai ya ji sallamarta ta shigo. Kamar yadda tayi tsammani, bai daina sha ba, kuma ya tsuke fuska.Ta ƙarasa gabansa ta zauna, ta zuba masa ido.”Kin san an hanaki shaƙar hayaƙi ko? Kin san ba cikakkiyar lafiya ce da ke ba””Kai ma bai dace da kai ba, ina gaya maka ina son lafiyarka, su kan su masu kamfanin abar sun yi gargaɗi a kan haka, dan Allah ka ajiye magana zamu yi”.Bai ajiye ba, yayi mata shiru yana cigaba da fesar da hayaƙin wani wurin daban.Tashi tayi ta zagaya, in da yake fesar da hayaƙin tana kallonsa.”Meye haka ne wai?””Dan Allah ka ajiye mu yi magana””Ina jinki ai” wani abu mai ɗaci ta haɗiye, kawai ta tashi ta bar masa ɗakin.Ta koma ɗakinta ta tsaya, kuka ya ƙwace mata, sai ta fara saito abubuwa, sai Al’amin ya sake burkice mata, tun da suka yi aure take yi masa addu’a, amma abun nasa sai a hankali.”Kul jauhar, kar ki yi saɓo, ko ki yi wa Allah butulci, Allah sami’ul alim ne, idan ka roƙa baka ga tasirin abun ba, lokacin ne bai yi ba, tun da shi ya ce mu roƙa zai amsa, kuma Allah ba ya sabon aiki’ wata zuciyar ta gargaɗe ta.Istigfari ta cigaba da yi, ta nemi wuri ta zauna a tsakiyar gadonta, tana cigaba da tasbihi.Sai da gari yayi haske sosai, ta fita tana aiki, ya fito cikin takun ƙasaita, ya nemi wuri ya kame a kan kujera.Sai da ta kai zuciyarta, sanna ta iya ce masa “Ina kwana?””Lafiya ƙalau” a ranta ta ce ‘Ka yi laifi, kuma ka maze kana hura mini hanci, da ni ka ke zancen’.Ta ajiye masa karin kumallonsa, ta koma ɗakinsa, ta na gyarawa, yanzu ya rage watso mata kaya daga wardrobe, sai dai ya tara mata kayan wanki, a kan katifarsa.Tsayawa yayi a bakin ƙofa, yana kallonta.Yayi gyaran murya ya ce “Kin ce zamu yi magana, ta menene?”Ta kalleshi ta ce “Ka manta kawai” ta ƙarasa maganar tana kwaso kayan wankin za ta fita.Har ta gota shi, ya janyo ta kamar wata ‘yar tsana, ya tsuke fuska ya ce “Gaya mini menene?”Ta sunkuyar da kanta, hawaye ya fara zubowa daga idonta, wani na bin wani.”Menene kuma yanzu?”Cikin rauni ta ce “Kai ne””Na yi me?””Kusan kullum sai ka sakani kuka mussaman kwanan nan, na ce dan Allah ka daina shan komai ka ƙi dainawa, haba master wane irin uba ka ke son ka zama idan Allah ya bamu zuriya? Ina son in ga ka daina shan komai ka daina abun da ka ke yi. Amma ƙir-ƙiri ɗazu ka ƙi daina sha”.Ya ce “Ke, wai an gaya miki daina shaye-shaye kamar daina cin tuwo ne? Ina ƙoƙartawa fa, duk kin addaba mini, ina ji ina gani, asuba ina shan kara biyar zuwa sama, amma ɗazu uku kawai na sha amma ba kya gani, kuma yaushe na ganki, balle a tara wata zuriya? Shiyasa ma ban bari sun ƙaraso ba tukuna sai na gama abun da nake yi. yayi maganar yana basarwa.Wata irin kunya ta kama ta, jin abun da ya mayar da maganar.”Ki daina damuwa, ina ƙoƙari sosai, ba zan iya dainawa ba, sai na cika burina, mutum ɗaya kawai zan kashe, shikenan”Jauhar ta kalleshi ta ce “Kisa kuma? Ana ga ƙura kana ga yaƙi, idan an yi nan sai ka yi can”Dogon harshensa ya zaro mata, yayi wani irin murmushi, sai ta ga kamar ya canza gaba ɗaya, ya dafo kafaɗarta kamar ƙawarsa ya ce “Bar wankin, zan yi ki haɗo da naki ma, idan na gama zan yi gyaran kwatar layin nan, duk an bari ta cushe da shara, me zaki dafa mana da rana?””Master ba ka da aiki sai zancen abinci ne?””To idan ban yi zancen abinci ba zancenki zan yi babyn roba””Saura ta katako, rana zata yi mini, ko wankin ka saɓa sai na yi mana ɗauraya”Al’amin ya ce “A’a ki yi aikin ki zan wanke” yayi maganar yana yi mata wani irin kallo tare da murmushi.Ita ma murmushin ta yi masa ta ce “Harshenka dogo ne, meyasa ka ke fito da harshe ne?”Ya ce “Rantsuwa ce, kowane specie ɗinmu, akwai irin ta su”.Jauhar ta yi dariya ta ce “Wai specie kamar a biology?””To in ce kowane ɗan daba?”Ta yi saurin girgiza kai ta ce “A’a ba na son wannan kalmar, babu daɗin ji”Ba tare da ta gane ba, yayi mata wayo, ta daina fushin da take yi, dan babban burinta ya kula ta, ya sakar mata fuska.Aka shiga satin bikin Hafsa, Anty Zakiyya ta kira Jauhar ta ce “Jauhar wai yaushe zaki zo ne? Ayyuka sun kacame, ko dai baƙin ciki ki ke yi da lamarin nan ne?”Jauhar ta ce “Haba Anty, ba haka bane wallahi. Kin ga maigidan ne ba ya jin daɗi, idan na taho babu mai kula da shi”.”Kamar yaya? Au mijinki ya fi ‘yar uwakki, kamar wani mijin kirki, da waye yake kula da shi idan ba shi da lafiyar?””A’a Anty, ai miji duk in da yake miji ne, yana buƙatar kulawa ne, ba dan….”Dalla yi mini shiru, har wani tinƙaho ki ke yi da wannan abun? Makakken ɗan wiwi.Ba tare da Anty ta sani ba, tuni ya karɓi wayar daga hannun jauhar, ya saka a kunnensa tana ta masifa “To ki zauna sai yadda yayi da ke, ai mutumin kirki mai kuɗi shi yake saka doka a bi, ba irin mijinki ba da har ki ke gaya mini wai ai miji miji ne ba”.”Makakken ɗan wiwi yana godiya, kuma kun san da makakken ne, ku ka aura mata ni. Ni na hanata zuwa matata ba baiwa ba ce, ta zo ta yi muku bauta, ba zata zo ba, idan kun ga dama ku bar bikin kar ku yi” Jauhar tana girgiza masa kai, amma sai da ya gama maganar ya jefar da wayar.”Master, iyayena fa, ba a haka yakamata a gaya musu ba, da ka bi a hankali, na san yadda zan gaya musu”.Al’amin ya ce “Kin san bani da tarbiyya, ban iya magana da manya ba””A’a ba haka nake nufi ba””Idan ma dai hakan ki ke nufi, idan kuma ban isa ba, ki shirya ki tafi “Jauhar ta ce “A’a ka ma isa, ai na fasa zuwan, amma ai ka yi mini alƙawarin zaka kai ni gidanta bayan bikin ko?” Tausayinta ne ya kama shi, ba dan haka ba da gidan hafsan ma ba zai bari ta je ba, amma ya tuna ɗan uwa duk in da yake daɗi ne da shi, kuma bai kamata ya hanata zuwa wurin ‘yar uwatta ba, amma kamar ko a jikinsa ya ce “Zan yi shawara”Anty Zakiyya kuwa, sai da kayan cikinta suka yanutsa, saboda tashin hankali da ta ji muryar Al’amin a waya.Sai dai jauhar ta sha zagi a gidan, ana cewa baƙin ciki ne da hassada ya sanya ba zata zo ba.Yaya saifu ya ce ‘m”Jauhara ba ta da irin wannan zuciyar, hankalinta na kan mijinta, wannan aure dai, in dai dan cin amana aka yi shi, ba in da zai je zai watse”.A fusace Anty ta ce wa mama “Ki ja wa ɗanki kunne, kar ya sake aibata mini auren ‘ya”An kai kwanaki huɗu ana events kala-kala na auren Hafsa, jauhar sai kallo da ta din ga yi, tana murmushi tare da jin babu daɗi rashin halartar auren yayarta, ga ‘yan uwa da abokan arziki duk an taru.Ita ma ta ɗora hotunan, tana yi wa hafsan fatan alkhairi.Aka gama biki, aka kai hafsa gidanta, wanda suke haɗe da uwar gidansa, kowacce part ɗin ta daban.Aka yi sayen baki aka watse, ya tara su yayi musu nasiha, bayan Uwargidan ta fita, Alhaji mu’azzam ya ce “Bari na je na ɗan ƙara rarrashinta, na san tana cikin damuwa” haushi ya kama hafsa, dan a zatonta yana zumuɗinta, ba zai saurari uwar gidan ba.Sai dai har ɗaya na dare bai dawo ba, ta kira wayarsa a kashe, tun tana saka ran ya dawo, har ta gaji, bacci yayi awon gaba da ita.Da safe ma, ga yunwa ga gajiya, amma ba ta ganshi ba, sai sha ɗaya na safe.Ya ce “Jauhar am sorry please” ta kalle shi cikin takaici ta ce “Jauhar kuma?””Afuwan Hafsat, wallahi madam ce nayi ta faman rarrashinta, taƙi yin shiru kin san kishi babu daɗi, shiyasa na zauna da safen nan ma da ƙyar na fito, duk a cikin damuwa ta ke, yanzu haka kanta ciwo yake saboda kuka, ina ga da kaina zan fita nema mata magani”Tamkar hafsa ta zabga masa mari haka ta kalleshi ta ce “Ni bana buƙatar kulawarka kenan sai ita?”Ya ce “No ba haka bane ba? Ai ke sabuwa ce, sai ta fiki shiga damuwa, bari na je na sayo mata maganin na kai mata, na yi ordern abinci, idan ban dawo da wuri ba ki karya kawai.Abu kamar wasa, har wurin kwanaki uku, bai saurari hafsa ba, wai uwargidansa ba ta da lafiya, har ma ya ɗauki fushi da ita, wai ba ta je ta yi mata sannu ba, ta ɗauki waya tana kuka ta sanar da Anty, Hankalin Anty ya tashi, ta ce ta je ta dubata ɗin, za su sake shiri su ma.Baya nan hafsa ta shiga duba ta, ta ce “Na ji an ce baki da lafiya, na zo duba ki”Ta ce “Ko ɗaya, lafiyata ras, kawai ina ƙoƙarin nuna miki ƙarfin ikon da nake da shi a cikin gidana da irin gangancin da ki ka aikata na shigo mini gida”Hafsa ta ce “Shigowar ai ita ce mai wuyar, tun da an ce hanawa ki ke yi, ni kuma na yi nasara na shigo, mu zuba da ni dake”.”Lallai yaro bai san wuta ba sai ya taka, ga fili ga mai doki”.Har hafsa ta kwana bakwai a gidan nan, ba su haɗa shimfiɗa da Alhaji mu’zzam ba, duk ɗokin amarcin da take yi, komai ya fita daga kanta, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ƙiri-ƙiri yake nuna mata shi ta matarsa yake yi ba ita ba, saɓanin abun da ya nuna mata a waje.Jauhar kuwa ta cigaba da yi wa master magiyar, ya taimaka ya bari ta je gidan hafsa tun da an yi bikin, kuma ta na son ta je gida ta gaida baba, ta bashi gudunmawar biki.”Ni fa nayi miki alƙawarin zuwa gidan yayrki, amma amarya ce, ya zaki je musu gida sati ɗaya da biki?”Cikin rashin fahimta ta ce “To ba a zuwa?””Eh, idan sun shirya samun zuriya su, ai ba za so ki dame su ba, idan lokaci yayi zan kai ki”.Anty da Rahila suka cigaba da yawon bin bokaye, ƙauye-ƙauye, dan su sake kama Alhaji mu’azzam, kuma ya saurari hafsa.Komai na buƙata gashi nan a zube, amma miji ya gagareta sai dai ta ganshi daga nesa.Tayi iya ƙoƙarinta, duk wanda ya zo, ba ta bari ya fuskanci tana cikin damuwa, ta baka abinci ka ci ka sha, idan zaka tafi ta baka na mota mai yawa, tayi ta hura hanci, saboda tana cikin gida na alfarma ga motoci a parking lot.Jauhar ta gaji da yi wa Al’amin magiya, ta ƙyale shi, dan kansa ya ce ta shirya, shi zai kaita gidan hafsan, su gaisa ya dawo da ita.Ta din ga murna tana yi masa godiya, amma ta ce “Dan Allah master a sakawa baburin nan salansar sa, idan muka fita fa saboda ƙarar da yake yi, sai kowa ya waiwayo ya kallemu”.Ya ce “Ni fa na fi son abuna a haka”Ta kwantar da murya ta ce “Na sani, amma a taimaka mini, ko so kake kowa sai ya ɗaga kai ya kalli babyn robar taka?””Zan duba””Yauwwa master na”Yayi murmushi ya ce “Naki, waye ya baki?”Ta ce “Allah ne ya bani, kuma na karɓa hannu bibbiyu ina yi masa godiya”Ta kira hafsa a waya, hafsa ta ɗaga da ƙyar tana cika tana batsewa, Jauhar ta ce “Anty hafsa ina wuni, ina ta kiranki ba kya ɗagawa””Bana kusa ne, shiyasa””Adress ɗin gidan zaki bani, gobe in Allah ya kaimu zan zo in sha Allah”Kamar hafsa ta ce mata ba ta so, b tare da la’akari da su ba su taɓa taka gidan jauhar ba, amma sai ta ga ya dace jauhar ta zo ta ga daular da take ciki, dan haka ta bata adress ɗin.Bayan ta gama wayar, ta ce “Master ta bani adress ɗin, babu wuya ma gane gidan nata. Zo mu yi kallo a wayata” ta yi maganar tana zama a kusa da shi.”Ni kallon nan gajiyar da ni yake yi”Ta ce “Ahh haba dai, ko kaɗan nan, yana da kyau ka samu abubuwan da za su din ga ɗebe maka kewa”Al’amin ya ce “To zaɓi ɗaya, ko dai ki sauke wannan abun, ko kuma a haƙura da kallon” yayi maganar yana nuna boti, da yayi ɗare-ɗare a kan cinyar jauhar.Jauhar ta kwashe da dariya ta ce “Boti master ya ce ka tashi daga cinyar matarsa” kwanciya magen ya ƙara yi, yana lafewa.”Ban taɓa ganin abun da ya raina ni ba, kamar ke da magen nan ba”Jauhar ta din ga dariya, ita yadda ba sa ga maciji da botin ma dariya yake bata.Ta zauna a kusa da shi, tayi connecting da mp, ta saka musu film.Ta kalleshi ta ce “Ka ji ko? Baby ake cewa mace, kai baka yi mini irin wannan kalar soyayyar, sai zare mini ido da sakani kuka”Yayi murmushi bai ce mata komai ba, sai dai ta ji ya saka hannayensa ya riƙe nata. Mintuna goma da ta ɗaga kai ta ga yayi bacci. Ta zuba masa ido yana bacci, a ranta ta cigaba da yi masa addu’a.Ta kashe wayar ta ce “Master ka tashi ka je ka kwanta tun da kallon ne ba ka so”Yayi shiru bai motsa ba. “Master””Mmm” ya amsa ba tare da ya buɗe idonsa ba.”Mu je na yi maka addu’a ka kwanta”Ya ce “Ɗauke ni, na gaji”Ta ce “Na ɗauke ka, ai kuwa da sai dai wata ba ni ba, aikin me ka yi ka gaji har haka?””Ƙasa muka kwashe tifa biyar, ban sha komai ba kuma na yi aikin, ni da su Walid”Jikinta a sanyaye ta ce “Har tifa biyar master. Baka gaya mini ba sannu, amma dai sun biya ku ko?”Ya tashi zaune ya ce “Eh, har na kai wa mai solar kuɗin, ya zo ya saka miki solar, ya kawo miki fankar solar zafi ya fara yawa kuma ba wuta”.”Solar kuma master? Da mun sai kayan abinci, zafi lokaci ne zai wuce, solar fa da tsada”.”An ce masu asma, ba sa son zafi” ya yi maganar yana tashi tsaye, tashi ta yi ita ma, sai ta rasa me za ta ce masa, ya nufi ɗakinsa, ta rasa ta ina yakamata ta fara ma. Akwai abubuwa masu muhimmanci da yakamata ace yana yi da kuɗi, da solar da ya saya, kamata yayi ace ya sai musu kayan abinci, ya ɗinka sutura da ko ɗan takalmi ne mai kyau na kwalliya. Duk in da ya kwashi taklminsa soso haka yake ƙarawa gaba da su, kayansa ma ita ta ware masu kyan ta kai ɗakinta, sai idan za shi wani wuri na musamman ko juma’a ta bashi ya saka. Sai dai ta san bai kyautu, ta nuna ba ta ji daɗin abun da yayi ba, domin ko ba komai, yayi ne dan ya kyautata mata.Ya nemi wuri ya kwanta, ta zauna a kan katifar, ta ɗora hannunta a kansa, tare da karanto masa addu’oin kwanciya bacci.Abun da jauhar ba ta sani ba, bayan ciyar da shi da ta din ga yi farkon auren su, Addu’ar da ya ji tana yi masa cikin magagin ciwo, tayi matukar tasiri a zuciyarsa, Addu’a ce da idan ba uwa ba, ba kowa zai yi maka ba. Addu’oin da take yi masa idan yayi mata wani abu na kyautatawa ma, ba ƙaramin daɗi yake ji ba. Ga uwa uba kirarin da take yi masa wasu lokutan, da suke fasa masa kai. Duk wani abu da zai yi baya manta tarin alkhairin ta.”Allah ya saka maka da alkhairi, ya buɗa arzikin ka, ya wadata mu da halal ya nesanta mu da haramun. Na gode sosai da sosai Allah ya biya ka da gidan aljanna, ya jiƙan iyayenmu”Idonsa a lumshe ya ce “Amin ‘yar aljanna, addu’ar ta yi daɗi” tayi murmushi ta tashi.Washegari da wuri ta shirya, tana ta murna za ta je gidan hafsa, ta wanke laifinta na rashin zuwa biki.Shi kuma ya ce zai kaita, amma ya din ga yanƙwanata.Ba su fita ba sai sha ɗaya saura, tiryan-tiryan, har gidan hafsa.Gida ne babba na gaske, Al’amin ya ce “Ba daɗewa zaki yi ba, da wuri zan dawo mu tafi””To Allah ya dawo da kai lafiya, take care”.Ya ce “To, ki shiga, sai na tafi””Saboda kar in gudu?””Idan kin gudu ma zaki dawo” yayi maganar yana tayar da babur ɗin sa.Juahar ta shiga har falon Hafsat, ta din ga bata haƙuri na rashin zuwanta bikin nan ta ce “Kin san halik maza wasu lokutan sai a hankali, babu yadda ban yi ba, amma ya hana, ba shi da lafiya lokacin” Hafsa sai ɗan fizgar kai take yi, wai ita dole ga matar mai kuɗi.Har la’asar tana gidan hafsa, bayan ta gama shan ƙamshin, ta saki jiki kuma suka hau hira, da yake ita ce sakuwar jauhar, daga ita sai jauhar.Ta din ga koɗa mata irin son da Alhaji mu’zzam yake yi mata, dan ta tura mata haushi. Jauhar kuwa ko a jikinta, ta ce “Wallahi yaya hafsa idan Allah ya baka miji mai sonka tsakani da Allah, duk wani ƙalubale mai sauƙi ne”Ta ce “Aikuwa shiyasa nake tausyinki, aure ba soyayya, ga miji sai a hankali”Jauhar ta ce “Aikuwa ke da ki ka yi na soyayyar ma, ba ki fi ni samun kulawa ba, da farko a tsorace nake da shi, tun da muka saba Alhamdilillah””Taɓ, haryanzu yana safarar cocaine ɗin?”Duk da jauhar ta ji haushin maganar ta ce “Da safarar cocaine yake, ai mun girmi zaman Kano sai Abuja”Al’amin ya kira jauhar, ya ce ya zo ta fito su tafi.Ta leƙa ta window falo ta hango shi, a cikin harabar gidan.Ta ce “Ɗago kanka sama ka ga” ya ɗaga kai, ya hangota.”To ka tafi, ba yau zan dawo gida ba, sai gobe””Wallahi idan ba ki fito ba, zan shigo har ciki””Kaikaikai, gidan mutanen za ka shigo?””Sai na shigo ɗin tukuna kenan?”Tayi dariya ta ce “A’a, rufa mini asiri, kar ka saka da ni da kai a zanemu, gani nan”Hafsa ta yi ƙuri da ido, tana kallon jauhar, tana leƙen Al’amin kuma suna waya, tana ta dariya.”Yaya hafsa, bari na tafi”Hafsa ta tashi ta ce “Mu je na raka ki”.Suka fito harabar gidan tare, yanayin Al’amin a yanzu, akwai nutsuwa a tare da shi, ba kamar lokacin da ya je gidan su ya ɗauki jauhar ba.Hafsa ta ce masa “Ina wuni?””Lafiya ƙalau” ya amsa idonsa a kan jauhar.”Ya ka ke hararata ne, ba gani na fito ba”Ya ce “Zaki yi bayani” motar Alhaji mu’azzam ce ta shigo gidan, yana hangen jauhar, ya ci wani irin wawan burki ya buɗe motar ya fito.Ya ƙaraso ya kalli Jauhar ya ce “Jauhar, dama kina nan?”Tayi murmushi ta ce masa “Eh, ina wuni?””Lafiya ƙalau jauhar, sai dawowa na yi aka ce mini kin yi aure, na ce ko wani laifin na yi miki? Hafsa ta ce mini dama akwai wanda ki ke so, shi ki ka aura, ni kuma baki gaya mini ba lokacin da nake neman aurenki”Kallo ɗaya jauhar ta yi wa Al’amin, ta ga ya murtuke fuska, idonsa ya fara kaɗawa zuwa ja.Ta ce “Eh, gashi nan a gabanka mijin nawa, Allah dama ya ƙaddara yayata zaka aura. Yaya hafsa sai anjima”.Ya ce “Tsaya na baki na mota” ya saka hannu a aljihunsa ya ɗebo kuɗin da bai san yawan su ba, ya miƙa mata ta girgiza kai ta ce “A’a na gode”Hafsa ta ce “Baby kawo ka ga” ta karɓi kuɗin ta turawa jauhar a jakarta, ta ce ba a mayar da kyautar manya, ku gaida gida. Tuni Al’amin ya juya ya fice, idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi wa Alhaji mu’azzam illa, da wuƙar da take cikin rigarsa a soke.Tun da suka tafi hanya, bai ce mata uffan ba, hakan ya sanya ta cikin matsanancin tashin hankali.Da ya ajiyeta a gidan ma, tafiyar sa yayi, bai ko shiga gidan ba.Ta din ga addu’a Allah ya sanyaya masa zuciyarsa. Duk yadda ya so ya sarrafa kansa ya kasa, sai da yayi shaye-shaye, domin rage raɗaɗin abun da yake ji, dan zuciyarsa har wani tururi take yi.Har sha biyun dare, idonta biyu tana zaune, tana jiran dawowarsa, ya koma mata Al’amin ɗin sa, dan ko sallama bai yi ba ya shigo, ya wuceta ya tafi ɗakinsa.Cikin fargaba, tana addu’a, ta bi bayansa, warin wiwi duk ya cik wurin.”Sannu da zuwa, nan zan kawo maka abincin?””Fita ki bani wuri, kafin na kakkaryaki na zubar. Idan ba kya son zama da ni, ba sai kin wulaƙanta ni, ta hanyar kai ni wurin tsohon saurayinki ba, shiyasa nake ta baki zaɓi tuntuni a kan zama da ni, ba dan na sarrafa zuciyata ba, sai na kashe mutumin nan har lahira yau, fita ki bani wuri, bana ƙaunar ganinki ma”.Ta marairaice ta ce “Dan girman Allah ka yi haƙuri, wallahi da na san zamu ganshi da ba mu je ba, ni saboda ‘yar uwata na je”.”Saboda ‘yar uwakki, ko kuma saboda ki ganshi?””Ya za ayi na je ganin wani, alhalin ina ɗauke da igiyar aurenka a kaina””Ki daina wani kwantar da murya, na riga na gane abun da ki ke nufi, da in da ki ka dosa, if you still loves him zan iya sakin ki, ki iya koma wurinsa, tun kafin na illata ki, ba zan juri wannan cin fuskar ba, nan gaba ban san me zaki aikata ba”Cikin tsananin ɓacin rai ta ce “Idan ka sake ni, hakan baya nufin rayuwata ta zo ƙarshe, jaririn da ya zo duniya ma Allah ya na iya karɓar rayuwar mahaifiyar sa, kuma ya raya mata shi. Ka yi mini duk hukuncin da ka ga shi ya dace ni” ta fice daga ɗakin, cikin tsananin ɓacin rai da damuwa.Ransa yayi matuƙar ɓaci, jin yadda ta gaya masa maganganu, gashi dama a cake yake, ya nemi wata ƙwaya ya haɗiya ya kwanta, dan kar ayi ɓatacciya. Da asuba ya farka, ya saba ta zo tayi ta fama ta tashe shi, amma yau taƙi zuwa.Yayi sallar asuba, gari yayi haske ya fito, amma ba ta fito ba, ya gaji da zama ya fita.Da azahar ma, abincinsa ta ajiye masa ta yi zamanta a ɗaki, idan yana falo tana ɗakinta, idan yana ɗaki sannan zata fito.Ya shareta shi ma, yana jiran ta zo ta bashi haƙuri kamar yadda ta saba, amma taƙi, sai ya ji gidan yayi masa duhu babu daɗi. Kusan kwanaki uku, ba wanda yake shiga harkar wani.Yau har ya cire kaya ya kwanta, ya tashi ya zauna yayi shiru yana tariyo maganganun da ya gaggaya mata, sai ya ji sun ɗan yi nauyi da yawa.Ya tashi ya tafi ɗakinta, kasancewar babu wuta, ya kunna fitilar wayarsa, ya shiga.Tana banɗaki tana wanka, ta jingina fitilarta a kan mudubi, tana haska mata cikin toilet ɗin.Ya ƙarasa gaban mudubin, ya ɗauki wayar ya kashe fitilar.”Waye a nan?” Tayi maganar cikin tsoro, dan ba ta san ma ya dawo ba.”Waye?” Yayi shiru bai yi magana ba.Da sauri ta gama kwara ruwan a jikinta, ta fito sai dai ɗakin yayi duhu, ba ta ganin komai.”Wai waye ne?” Tayi maganar tana laluba hanya.Direction ɗin da yake ta nufo, cikin tsoro, kawai ta ji ya zaunar da ita a kan cinyarsa. Cikin tsananin tsoro ta ware baki za ta yi ihu ya tsohe mata baki ya ce “Shhhhh, Al’min ne”
Ayshercool 08081012143
