Hausa novels

Halysaah Page 108 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 108 Cikin tsoro Khaleesat ke bin parlon da kallo jin bata sake jin haushin karen ba, nan taga karen ya bar parlon ya gudu saboda koran da Ajay yayi masa, a hankali ta fara matsawa daga kusa da Ajay tana masa wani kallo, shi ko yaki kallonta yana kallon TV, hararansa tayi ta sauka daga kan kujeran tayi wucewarta sama tana share hawayen idonta tana jin kamar ta fashe da sabon kuka don takaici, sai a sannan ya bi ta da kallon gefen ido ya dau Juice dinsa yana sipping, tana isa stairs ta sake juyawa ta kallesa suka hada ido, wani hararan ta jefa masa ta haura sama tana jin wani mugun haushin sa a rai. The next day da ya kasance Saturday har goma da rabi Khaleesat bata fito daga cikin daki ba, har cikin ranta ta tsorata da karen gidan, kiran Safiyyah ne ya shigo wayarta ta daga ta kai kunne, Safiyyah tace “Kin fasa zuwa apartment din naki ki dauko items din ki ne?” A hankali Khaleesat tace “Ai ba makulli a wajena Sophie, kuma tsoron ma fita ko nan da parlor nake” Da mamaki Safiyyah tace “Kamar yaya?” Khaleesat kamar zata yi kuka tace “Sophie he is frightening me with their dog in this House” Safiyyah tace “Dog kuma? Dama shegen karen na raye? Nuna masa kika yi kina jin tsoron karen?” Khaleesat ta fashe da kuka a hankali tace “Kinsan ai ina jin tsoron kare ni Sophie, kuma kin fa san karen kato ne and it’s fierce, wallahi jiya suma ne kawai ban yi ba da karen ya biyo ni daga na je kitchen” Safiyyah tace “Tabdi, to shi kuma sai ya zuba ido shegen karen ya bi ki?” Khaleesat tace “Wallahi babu abinda yace kuma bai hanasa ba, kilan ma shi ya kira karen da ya ga na shiga kitchen don sanda na shigo parlon ni ban ga karen ba” Safiyyah tace “Ko wani salon mugunta fa Ajayn nan da kike gani ya sani, meye kuma na barin kare ya dinga tsorata ki a gida in ba iskanci ba, amma kece kika nuna masa kina jin tsoron karen tun farko shi yasa, ban da haka tun yaushe zan rotsa masa duk abinda hannu na ya kai, wallahi idan karen ya sake zuwa kusa da ke ko wani abu kika gani ki dauka ki buga masa a kai, ko kuma ki kira 911 sun tafi da shi, ta ya za a bar irin wannan kosasshen karen a gida yana firgita mutane karen da ya kamata ace yana gidan zoo saboda girmansa, bari ma ina zuwa gidan yanxu ni kin san ba tsoron karen nake ba, ki shirya kafin in karaso” Khaleesat ta ɗan bude ido bayan ta tuno warning din da yayi mata jiya, da sauri tace “Kin ga Sophie ki bari zan fara gaya masa zan je debo kayana sai mu hadu a can apartment dina kawai, kuma wallahi idan muka je bazan dawo gidan nan ba don i can’t withstand living together with him, ba shi da tausayi kwata kwata” Safiyyah tace “To zai yarda ki zauna apartment din har ya siya maki foodstuffs da abubuwan bukatan gida kuwa?” Shiru Khaleesat tayi, kafin a hankali tace “Akwai kudi da yawa fa a account dina” Safiyyah tace “Ayya wanda Housemate ke tura maki ko?” Khaleesat ta sauke ido bata dai ce komai ba don duk kudaden da Housemate da Ajay din suke tura mata ne a account din, cause sanda Housemate baya nan Ajay ma ya tura mata kudi sosai, Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace “To Allah ya kyauta, Allah sarki Housemate, ko wani hali yake ciki oho an dai cuce sa kawai, ki shirya ki fito ina jiran ki” Khaleesat ta daga kai da sauri jin an bude kofar dakin, murya can kasa tace “Bye Safiyyah….” Daga haka ta katse wayar ta ajiye taki yarda ta juya ta kallesa, wani mugun haushinsa take ji har cikin ranta barin yanda ya bari kare yayi tormenting din rayuwarta jiya da daddare, yana tsaye daga bakin kofar ya hade rai yace “What did I tell you yesterday?” Kamar zata yi kuka ta rungume hannuwanta still not looking at him tace “Ta yaya zan fito in hadu da karen da ka bari yana yawo a gidan nan yana tsorata ni” Yace “Ina ruwanki da shi? Zamanki yake aka ce maki a gidan?” Ta hade rai tace “Ni wallahi tsoronsa nake bazan iya fitowa ba yaje ya cije ni, kawai ni dai ka taimaka ka maida ni apartment dina I can cope alone there, ai da can ni kadai nake zamana” Daga sama har kasa yake kallonta kafin yace “Kina da kudin biyan hayan apartment din kenan?” Shiru tayi, sai kuma ta juya tana kallonsa, Calmly yace “The driver in this house is purposely employed here because of u, don haka you have to be making breakfast and dinner with his ration, I can’t be paying him for ur services at the same time buying him two square meals in this state, don haka kina da hannuwan ki biyu da za kiyi maku girki da ke da shi” Khaleesat ta dinga kallonsa kafin tace “To da wannan shegen karen a gidan nan ne zan dinga zuwa kitchen inyi girki? Didn’t you see the way the dog is being fierce at me?” Sai kuma ta fashe da kuka ta rufe fuskarta da pillow tace “Ni wallahi bazan iya zama gidan nan da karen nan ba” Yayi mata wani kallon sama har kasa sannan ya juya ya fice daga dakin, breakfast ya kawo mata har dakin, ita dai taki kallonsa, sai da taga ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita. Khaleesat was more than eager taga Monday yayi ta tafi school don gidan wasn’t a comfort zone for her, gaba daya ji take kamar a ƙaya take ga boredom da ya isheta, gashi a tsorace take da karen gidan, duk da tun ranan Friday da ta ga karen ya tsorata ta da daddare throughout jiya da yau bata ga ko gilmawan sa ba, kamar yanda Ajay yayi instructing dinta in dai tayi girki sai ta ajiye ma Driver nasa abincin don iya su uku ne kawai a gidan babu wani worker, wannan yasa yau lahadi taji jiki wajen gyaran babban gidan tun daga upstairs har downstairs, she made sure she cleaned everywhere, haka ta gama aikin duk jikinta na ciwo saboda gajiya, tunda ta tafi daki wajen karfe dayan rana bata sake sakkowa ba sai kusan magrib shi ma don ta dafa ko taliya ne saboda driver, kamar munafuka ta sauko downstairs tana bin ko ina da kallo incase zata hango legend amma taga babu shi, da mamaki take kallon boxes dinta na can apartment dinta da wasu items tare da laptop and reading materials dinta, taɓe baki tayi ta karasa tana duba items din daya bayan daya, after some minutes duk ta kai su sama zuwa daki sannan ta dawo kasa ta nufi kitchen tana yi tana waige waigen ko zata ga legend don ita dai a tsorace take har ta shiga kitchen din ta kulle kofa, shopping ta gani birjik a kitchen island din, tana tafiya a hankali ta tafi gun ledojin, daya bayan daya ta dinga fiddo kayan shopping din, she made sure she arranged everything a kitchen din wanda zata jera a babban fridge duk ta zuba su ciki, cookies iri iri ta gani da kayan ciye ciye masu tsada, su ma duk ta ajiye su, bayan kusan minti talatin ta gama setting komai a mazaunin sa a kitchen din, ta zuba wasu bottled water cikin fridge, daga karshe taga ledan abinci biyu a kitchen din yayi masu order, she felt relieved don dama in don ta ita ne shayi kawai zata sha bazata dafa komai ba don ta gaji, ta dau leda daya ta bar ma driver daya ta juya ta fita daga kitchen din ta koma sama…… Khaleesat na zaune ita kadai a favourite spot din da suka saba zama da Sophie idan suka fito lectures, Safiyyah kuma taje amso masu snacks da wani frnd dinta ya masu order, it’s been weeks now da suka yi resuming school don har sun fara preparing for quizzes, har Safiyyah ta karaso Khaleesat bata san ta karaso ba don tayi nisa tunanin da take, Safiyyah ta taɓe baki ta zauna gefenta tace “Kina nan kina aikin naki kenan” Sai a sannan Khaleesat ta daga kai a hankali ta kalli Safiyyah, Safiyyah tace “Kawai ki dora ma kanki tunanin da bazai fisshe ki ba, ni dai ina gaya maki semester din karshe ne dai wannan in ba so kike ki samu matsala ba and you know what that means” Cikin sanyin murya Khaleesat tace “Even if it is once ai da sai yayi min reply yaji ko me zan ce masa Sophie, you know how painful it is mutum yayi ta ignoring messages dinka bayan duk yana gani….” Safiyyah ta kalleta ta zaro mata ido tace “Ke… Ke fa matar aure ce yanxu Khaleesat, bar ganin auren naki da Ajay a gantale haka, to reply din me kike son Housemate yayi maki? so kike ya biye ki ku fara chatting ko me? salon ma aga chatting din zargi ya shiga dama irin wannan gidan nasu gidan kananan zance don duk gidan sarauta gidan zance ne don haka gwara ma kar ya biye ki ya kama kansa wallahi, sannan fa shi ma yana can da matarsa, may be ma yayi move on suna can suna cin amarci tunda babu yanda ya iya an hanasa ke kinga he will just make the available the desirable, ke kuma kina nan kin damu kanki da tunani ji yanda kika rame don Allah kamar warce bata cin abinci, shi dama Housemate ana zaune lafiya ma ya share mutum balle an masa laifi? Ai kar ma ki saka ran zai bi ta kan message din ki, ashe har kin mance halinsa kenan” a hankali Khaleesat ta share hawayen da taji ya kawo idonta, Safiyyah tace “Shi kuma Ajayn ya fitar da shegen Legend din a gidan ko yana nan har yanxu? Ni rainin wayonsa ne ma yasa kika ga bana cewa zan je gidan don na lura ya karo sabon walakanci yanxu, kar wataran ya gaya min maganar banza in masa rashin kunya” Khaleesat ta taɓe baki tace “Ke ni fa sai mu yi kwana da kwanaki bamu hadu a gidan nan ba, kin tuna wani time da na taɓa zama gidan sanda Aymaan ya biyoni har apartment dina?” Safiyyah tace “Eh” Khaleesat tace “Toh yanda bama haduwa da shi wancan lokacin a gidan yanxu ma haka ne, although he is around amma sai mu yi many days bamu hadu ba tunda kinga da safe nake tahowa school kuma bana komawa gida sai yamma sosai, ko bani da lectures kinga sai na shigo school har Saturday saboda bana son zaman gidan kwata kwata, so bama haduwa gaskiya, aikin gidan ma na dena yi because he makes sure everywhere is clean, ko nace zan yi gyara gyara da asuba sai in ga ko ina neat, kinga yana gyarawa kenan” Safiyyah ta rike haɓa tana kallonta da mamaki, can tace “Tabb, to ku kuma haka naku salon auren yake kamar yanda ake yi a film? Ba ruwansa ma ko kina lafiya ko otherwise a matsayinsa na mijin ki? Ko kun mance mata da miji ne ke da shi?” Khaleesat tayi ma Safiyyah wani kallo sai kuma ta kauda kai, Safiyyah tayi shiru tana ta kallonta kamar dai tana son yin tambaya amma bata san ta yanda zata fara tambayar ba, bayan few seconds kawai tace “So you mean ba ku ma taɓa kwana daki daya ba kenan har yanxu da shi?” Khaleesat ta juya ta kalleta tace “Daki daya kamar ya? Saboda me za mu kwana daki daya?” Safiyyah ta zuba mata ido tana kallonta, Khaleesat ta kauda kai fuska daure tace “For what reason za mu kwana daki daya?” Safiyyah tayi mata kallon gefen ido kamar dai tayi shiru sai kuma dai tace “Kin fi ni sanin reason din ai” Khaleesat taki kallonta tace “Ban san wannan reason din ba” Safiyyah tayi er dariya, bayan kusan minti daya tace “No matter yanda aka yi auren dai mijin ki ne shi ki ji in gaya maki, in ma ke kika ki yarda ku kwana daki daya nasan kin san repercussion din hakan, ba ruwan Allah da yanda aka yi auren ko kuma abubuwan da suka janyo aka yi auren, aure dai aure ne koma yaya yake, yanxun nan sai ya kai ki wuta idan baki yi hankali ba” Khaleesat ta fara harhada kayan karatun ta without looking at Safiyyah cause she finds the conversation nasty in her ears, a takaice tace “Zan tafi gida since we are done with today’s lecture…..” Safiyyah dai kallonta kawai take, can ta ɗan yi murmushi bata sake cewa komai ba, har sai da Khaleesat ta mike zata bar wajen sannan Safiyyah tace “Yau kuma da wuri zaki koma gidan kenan? ke da kike jin kamar ki dawo kwana cikin makaranta tsabar rashin son zaman gidan?” A takaice Khaleesat tace “Ehh, na gaji ne yau, bacci zan je gida in yi… Sai gobe” Daga haka tayi wucewarta tana dialing number driver dinta don yana nan area din, Safiyyah dai ta bi ta da kallo tana murmushi a ranta ta fara tunanin banda dai abubuwan da suka faru wacce mace ce zata samu irin Ajay tayi ta claiming bata son sa? Ai sai dai shi yace baya so cause he gat everything, ilimin ne, kyan ne, asalin ne, wayewar ne, ko kuma dukiya? uwa uba ga sarauta, ai sai dai macen ta yaudari kanta tace bata so, although tasan ita dai Khaleesat da gaske take har cikin ranta ba lallai duk wannan qualities din su yi freaking dinta ba tunda ita ga wanda zuciyarta ke so…. Khaleesat ta dade bata ji haushin Safiyyah ba kamar irin wannan rana, she was really angry at her cause bata yi expecting irin wannan maganar daga gareta ba, ta yaya zata gaya mata haka ita da bata taɓa kallon Ajay a matsayin wanda za su yi wani abu wai shi aure tare ba, status dinta da shi will remain the way it is, ba wani aure a tsakaninsu, shima kuma a wajensa tasan irin kalan tunaninta yake yi, bazai taɓa kallonta a warce za su yi rayuwan aure ba, basu hango wani abu wai tarayyan aure between dem ba, har ta isa gida her mood was really spoilt, ta bude motar ta sauka tayi wucewarta cikin gidan, Allah ya so gobe Saturday ba ma ta da lectures balle taje school ta hadu da Sophie taji sabon takaici, ita da kullum ke cewa an ci amanar Housemate menene zai kai tunaninta zuwa irin wannan tunanin da tayi yau, what came over her to think that way? wato so take a ci amanar Housemate din da gaske kenan, tsaki Khaleesat tayi ta shiga cikin parlor, as usual babu kowa parlon tayi wucewarta sama zuwa daki, wanka tayi ta canza kaya tayi sallah tayi kwanciyarta, sai wajen biyar da rabi ta fita daga dakin zata tafi kitchen ta dora girki yanxu dai kwata kwata ta dena ganin Legend, tun da ta sauko downstairs take kallon wanda ta gani zaune cikin parlon har ta karaso inside of the parlor sannan ta gaishesa, ya juya ya kalleta greeting her also, Ajay dai na zaune parlon yana danna wayarsa fuskarsa babu yabo babu fallasa, sauke kanta tayi ta nufi kitchen, tana shiga kitchen din da few minutes sai ga Ajay ya shigo ta juya tana kallonsa ya hade rai yace “Ke baki da hankali ne da kika ga mutum a parlon baza ki koma sama to cover ur self up properly ba?” Ita dai bata ce komai ba tana dibar vegetables da zata yi amfani da shi wajen girki, ya juya ya fice daga kitchen din, kusan awa daya tayi a kitchen din tana girki don ba iya ita da Driver ta dora ma girkin ba har da Walid da ta gani a parlor, bayan ta gama ta fito har sannan Walid na parlon, Ajay ma na zaune and none of them is saying anything kamar kurame, shi Ajay wayarsa kawai yake dannawa at the same time yana operating din laptop dinsa dake gefe, shi kuma Walid kallon TV yake ya ƙishingiɗa kan 2 sitter, Khaleesat ta wuce sama Ajay ya bi ta da kallon gefen ido. Sai a sannan Ajay ya juya ya kalli Walid yace “Oxford din nan garin suka maido convocation din nasu na wannan shekaran kenan?” Kamar Walid bazai ce masa komai ba, sai kuma dai yace “How will that be possible?” Ajay yace “Da na ganka a nan ne nayi tunanin a nan kasar za su yi convocation din” Walid ya kallesa yace “However, su Aunty ma idan suka ga dama nan gidan za su sauka not England, cause babu inda aka ce an siya gidan nan da sunan just one or two persons….” Daga haka ya mike yaki jiran yaji me Ajay zai ce yayi wucewarsa sama ya tafi dakin da yake sauka idan ya zo gidan, wanda rabonsa da Maryland yayi 3 years yanxu, after a while Ajay ya mike ya tafi sama shi ma ya nufi bangarensa. Khaleesat ta idar da sallan magrib ta fito sanye da hijab dinta har kasa ta sauka downstairs zuwa kitchen zata debi abinci, tana shiga kitchen din taga an ci abincin an bar plate da mug din da aka sha Coffee a sink, tunda take gidan bata taɓa ganin an bar used utensils unwashed a kitchen ba, sai da ta fara wanke plate din ta goge inda aka yi littering da abinci sannan ta dau plate ta fara dibar wanda zata ci kenan aka bude kofar kitchen din ta juya, Walid ne ya shigo ya kulle kofar, ta sauke idonta ta kauda kai ta ci gaba da abinda take, yace “Akwai abincin ne?” Kai ta gyada masa without looking at him tace “Akwai….” Ya dau plate ya karasa har inda take tsaye ya tsaya yana kallonta yace “Can i have some of it?” Bata yi tunanin zai karaso har wajenta ba hakan ya ɗan sa ta daburce ta gyada masa kai da sauri tace “Ga abincin nan….” wanda ta fara zubawa a plate ya dau spoon ya diba ya kai baki yana gyada kai yana kallonta kamar me kirga kalamansa yace “Waow, you are a great cook, the meal taste delicious, did you learn catering? Are you a chef?” Ita dai sai kokarin matsawa take daga kusa da shi don dab da ita ya tsaya, bata yarda ta dago kai ba ta fara zuba wani abincin a plate with confusion, hannu ya kai ya rike plate din har hannun nasa na taɓa nata yace “John Hopkins kema kike na gan ki big gal” Ƙin cewa komai Khaleesat tayi tsabar shock, kawai bata ankara ba taga ya kai hannu chin dinta ya dago kanta yana kallon fuskarta yace “Hey I am asking you a question” Daburcewa tayi ta fara gyada masa kai alamar eh, sai kuma ta sakar masa plate din ta juya zata bar kitchen din yayi saurin rikota yace “Kee, are you alright? Ina maki tambaya zaki fita” Warce hannunta tayi da sauri ta fice daga kitchen din zuciyarta na bugawa, sama ta tafi tana waigen ko ya biyota don duk ya tsorata ta, tana shiga Bedroom dinta ta kulle kofar ta tafi gefen gado ta zauna with shock tana processing abinda ya faru.*Halysaah is 500 via 3276052019 Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*

Back to top button