Karfe A Wuta Chapter 2 By Ayshercool
A ƙalla sun kai ƙarti uku majiya ƙarfi, suka riƙe shi, amma sai ƙoƙarin watsar da su yake yi, ga wani irin gurnani yana yi, kamar mahaukacin zaki.Da ƙyar suka haɗu suka kai shi ƙasa, suka daddane shi yana cigaba da ƙoƙarin watsar da su ya tashi.Ɗaya daga cikinsu da yanayin kamanninsa ya bayyana, ƙarara shaye-shaye ya huda shi, saboda yadda laɓɓansa suke baƙi ƙirin, ga wani irin ƙaton tabo a gefen fuskarsa.A hankali yake ɗan dukan bayansa cikin sigar rarrashi yana faɗin “Easy maza, easy, mun san ka na cikin damuwa da raɗaɗi, amma hakan ba mafita bane ba, ka yi haƙuri muna tare da kai ɗari bisa ɗari iya wuya” ya cigaba da maganar yana rarrashin sa.A hankali jikinsa ya saki, ya daina gurnanin da yake yi, ya lumshe idanunsa, ya rufe su, tamkar mai bacci. Sai da suka tabattar ya yi relaxing, sannan suka ɗaga shi.Major ne tsaye a gaban mudubi, yana ƙara kintsa jikinsa kamar wani matashi, ba dattijo ba, uwargidan sa na gefensa tana taimaka masa yana shiryawa, Ba tare da ya kalle ta ba ya ce “Arfa kuwa ta tafi aikin?”.Ta yamutsa fuska ta ce “Ta ga dama ta tafi”Ya jinjina kai ya ce “Punishment ɗin da na yi mata jiya, shi ya hana ta zo ta gaishe ni yau kenan,’? zan gamu da ita ne idan ta dawo”.”Dan girman Allah major ka ƙyale sabgar yarinyar nan, sai ka ce itakaɗai ce ƴa a gidan nan, komai ita su duk sauran ba ƴaƴa bane ba, da ba ka damu da lamarinsu ba?” Kallon da yayi mata ne ya sanya ta yin shiru, tare da sunkuyar da kai, bai sake ce mata komai ba, ya ɗauki mukullin motarsa ya fice.Cike da takaici ta sauka daga benen, ta fito main falon gidan tana mita.”Yaya ya dai? Meyafaru ne?” Duk da ba ta kasance mai sakarwa abokan zamanta fuska ba, amma haka kurum ta tsinci kanta da gaya mata abun da ya faru saboda takaici.”Major ne mana, gaba ɗaya ya tattara hankalinsa a kan yarinyar nan, kamar itakaɗai ce ƴa a cikin gidan nan, jiya kwana na ne, amma a barandarsa ya ƙare kwanan jiya, wai yana gadinta, abubuwan nan sun fara isata”Ɗayar ta taɓe baki ta ce “Ai ni na gaji, na zuba ido su ƙarata, abun da ba jiya aka fara ba, ba yau ba”.Anty, wadda take ta uku, da take karyawa, duk da ba da ita suke ba ta ce “Amma dai an yi abun kunya, kishi zan ce ko baƙin ciki da ƴar cikinku”A fusace Uwargidan major, da ake cewa Mama ta ce “Asiya, da ni ki ke ko wa?”Anty ta ce “Duk wanda ya tsargu, sai menene dan ya nuna mata kulawa ta musamman, duk kulawar da yake bawa sauran yaran bai isa ba? Ƴaƴa nawa ne a gidan nan, kowanne ya na bashi kulawa dai-dai da buƙatarsa ne, amma da yake kishi ya zame muku bala’i, mussaman ma ke, da kowa ma yi ki ke, kin fi mu daɗewa da shi, amma haryanzu ba ki san halinsa ba”Mama ta ce “Ba zan yi musayar yawu da ke ba ƙanwar bayana, dan ba ki isa ba, da wanda ya ajiye ki zan yi”.Anty ta ce “Idan ma ƴar cikinki ce, matsayinmu ɗaya matan major, kuma ni gaskiya nake faɗa” haka suka cigaba da ƴan faɗace-faɗacen su na kishi.Nabila kuwa da wasu lokutan a kan yi mata laƙabi da Arfat, tana zaune a katafaren office, itakaɗai sai aikin danna waya take yi, cikin nishaɗi kamar babu wani abu da yake damunta.Knocking ɗin ƙofar office ɗin aka yi, ta bayar da izinin a shigo.Nabila suka gaisa da matar ta ce “Nabila ko?”Nabila ta jinjina kai ta ce “Eh””Ki zo Barrister yana kiranki””Wane barrister?”Matar ta ce “Director. Dama ina son in yi miki magana. Kin ga wurin nan babbar organization ce, da muke dealing da mutane daban-daban, especially manyan mutane. Yana da kyau ki jajirce director baya son ragwanci ko harkar ko in kula da aiki, sai ku samu saɓani”Nabila ta yi murmushi ta ce “Na gane, na kuma fahimta na gode sosai” matar ta jinjina kai ta fita.Nabila ma tashi ta yi, ta fita ta tafi office ɗin da ake nemanta.Ta tarar da shi da wani babban mutum a zaune a office ɗin sa, ta gaishe su cikin girmamawa sannan ta kalli Director ta ce “Sir gani”Ya kashingiɗa ya ƙare mata kallo sannan ya ce “Nabila, what is actually wrong with you ne?”Cikin mamaki ta ce “Ni kuma? Me na yi sir?”Ya gyara zamansa ya ce “Anya ke ki ke son zama lawyer ko choice ɗin major ne? Tun da ki ka zo wurin nan you don’t care, sai dai ki zauna ki danna waya, ki yi ciye-ciye, sai kwalliya. Bama kya shiga cikin ma’aikatan ki ga yadda ake aiki, balle mu ga gogewarki, mu faa tura ki trials, dama zuba miki ido na yi amma na ga baki san zuru ba” Nabila ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa.”Ina buƙatar ganin canji a tare da ke, idan ba haka ba na fara kai ƙarar ki wurin Major, yanzu muna da client da yake son yin apeal, a kan wata shari’a da wasu mutane suka kai ƙararsa. Ki je na saka ki a team ɗin su barrister Habib, ki je ku tattauna yadda za ayi handling case ɗin. Effort ɗinki shi zai sanya na baki manyan cases to help your career”Ta risunar da kai ta ce “Ok sir” ta juya ta fara tafiya, sai dai mutumin da tarar a office ɗin, ya bi bayanta da kallo yadda ƙugunta ke juyawa, cikin skirt ɗin kayan jikinta.Office ɗin Barrister Habib ta je, aka sanar da ita suna ɗakin sirri, dan haka kai tsaye can ta wuce.Ta tura ƙofar ta yi sallama, suka amsa mata, ta nemi wuri ta zauna.Barrister Habib ya ce “Kin ga damar zuwa kenan?” Wani irin kallo ta yi masa, amma ba ta ce komai ba, su kuma suka cigaba da abun da suke yi.Shari’a ce a kan wani attajirin mutumin ya karɓe gonakin wasu ƴan ƙauye, ya basu diyya ya fara ginin kamfanin sarrafa shinkafa, sai dai suka yi ƙararsa diyyar da ya biya su, ta saɓawa yarjejeniyar da suka yi da shi, dan sam bai kai darajar gonakinsu ba. Ganin ba su da galihu, ya sanya bai damu da ƙarar da suka kai shi ba, sai da aka yanke hukuncin ya biya su, sannan ya ce zai yi apeal.Mamaki ya cika Nabila, irin maƙudan kuɗin da ya biya law firm ɗin su, a bashi lawyoyi su kare shi, ya isa ya ƙarawa mutanen nan, ya biya su haƙƙoƙin su.Nabila dai ta yi zuru da ido, tana kallon yadda ake harhaɗa hujjoji na halal da na haram, domin mutumin yayi nasara a kotu.Baƙin ciki da takaici suka isheta, sunan ƙauyen da abun ya faru kawai ya isa ka gane cewar masu ƙaramin ƙarfi ne. Dan galibi mutanen karaka da Allah suka dogara, da harkar noma suka dogara.Tashi ta yi tsaye ta ce “Excuse me please, na fara jin yunwa lokacin cin abincina yayi”Duka lawyoyin da shi kansa client ɗin suka ɗago suka kalleta.Habib ya ce “Ana tsaka da aikin?”Ta basar ta ce”Am sorry, am having a chronic ulcer, za a iya samun matsala, idan na cigaba da zama” daga haka ta ɗauki jakarta ta fice, tana mitar ba zata zauna a ƙulla wannan sharrin da ita ba, ranar lahira ta shiga uku.Ta koma office ɗin ta, ta yi alwala tayi sallar azahar, ta je ta samu Director ta sanar masa da tana da uzuri ta na son ta tafi, yayi mata iznin hakan.A hanya ta tsayar da mai napep, suka ɗauki sumayya, sannan suka tafi.Ta kalli Sumayya ta ce “Sumy, meyafaru ne? Na ga kina wani ɓata rai”Sumayya ta yi tsaki ta ce “Haushin kaina nake ji, da na karanci aikin jarida Arfa”Cikin mamaki ta ce “Amma meyasa, na ga shi ne zaɓinki?””Wallahi duk ya fita daga kaina, hira aka yi da honorable Indabo, wai an yi borehole a ƙananan Hukumomin da yake wakilta, an raba kayan makaranta ga ɗalibai. An kai bencina makarantun firamare da na islamiyyu. Last week aka ce na je na tattauna da al’umman local government ɗin, na je ni ban ga ayyukan da aka yi ba, na tattauna da mutanen ƙananan hukumomin, sun ce ba ayi musu ba. Na kai recording ɗin, aka saka, wai lawisa ba ta tantance shirin ba, ba ta sani ba aka saka, kin ga cin mutuncin da aka yi mini, wai zan lalata musu business wai sai na je na samo mutanen da zan yi hira da su, su ce eh an yi ayyukan su yi godiya alhalin ba ayi ba. Na zama maƙaryaciya kenan me zan ce wa Allah? Wai har da idan ban yi wasa ba, sai honorable ya saka an ɗaure ni”Nabila ta ce “Ikon Allah, ashe duk kanwar ja ce sumy, yo nima hakan take ai, wani tasonon Alhaji ne ya zo yayi kirim a kan kujera kamar damin doya, ya biya uban kuɗi wai za a kare shi, ya cuci talakawa ko kunya bai ji ba, kuma director ya sakani a team ɗin lauyoyin, ni dai ba zan yi ba wallahi, sai dai ya yi ta gaya wa Abban. Haka kurum a cuci mutane ka je ka cewa Allah me?””Wallahi Nabila, ba ki ji zuciyata ba, yanzu sai dai na je na tara maƙwabta na yi hirar ƙarya da su, a zo a sake sakawa, kuma wai sai na rubuta takardar ban haƙuri, ki ji fa”Nabila ta ce “Tirƙashi, wai ya ɗaure ki, to ya ɗaure ki shi ma ya hau da ɗaurin Allah ” Haka suka cigaba da tattaunawa, har suka isa in da sumayya za ta sauka.***Cikin tsananin tashin hankali, yake magana, kallo ɗaya zaka yi masa ka san hankalinsa a matuƙar tashe yake.Ya daki teburi ya ce “Kwamishina, dole fa ku nemo yaron nan, dole ku mayar da hankali a nemo shi a duk in da yake a ƙasar nan”Mutumin da yake zaune cikin kakin ƴan sanda ya ce “Honorable, ka kwantar da hankalinka, aikinmu baya buƙatar garaje da gaggawa, sai mun bi a sannu””Haba Cp, wane irin bi a sannu? Rayuwata na cikin hatsari, yayi iƙirarin kashe ni, dole fa a nemo yaron nan, ko be kashe ni ba, idan ya buɗe bakinsa yayi wata magana a kaina kashina fa ya riga ya gama bushewa, na san fa waye yaron nan ciki da bai”Cp ya gyara zamansa ya ce “Amma honorable, wace irin yadda ko alaƙa ce tsakanin ka da yaron nan, da har ya sanka haka, zamansa a gari yake barazana a gareka”Tsaki mutumin yayi ya ce “Kai har ka tambayi alaƙar da ke tsakanin ɗan siyasa, da tantirin ɗan daba, ɗan iska? Ku nemo shi dillalin wiwi ne, da hard drugs. Da kun ganshi ma kawai a harbe shi, kuma a tuhumi controllern gidan yari, a kan dalilin sakinsa, bayan ko shari’a ba ayi masa ba tsawon lokaci”Ɗan sandan ya jinjina kai ya ce “Shi controller ya ce court order ya karɓa””Ni dai ka yi mini wannan taimakon a nemo shi da gaggawa, dan yana cikin garin nan, tun da ga ayyukan ta’addanci yana ta yi yadda ya ga dama”.CP ya ce “In sha Allah, ka kwantar da hankalinka za ayi duk mai yiwuwa, zan nemi zaƙaƙurai daga cikin mutanenmu, da suke dealing da criminal cases, very soon zai zo hannu, DSP Nasir na san zai yi abun da ya dace in sha Allah””Yauwwa to shikenan, ko dai sanarwa za ku yi, ace duk in da aka gano shi a kamo shi, an sake shi ba bisa ƙa’ida ba”Da sauri ya ce “No ai ba haka aikin tsaro yake ba, ai wannan abun kunya ne ga hukumominmu, yanzu sanin in da yake shi ne babban target ɗinmu, dan yaron yana da wayo sosai, na bibiyi record ɗin sa, sai an yi taka tsantsan sosai wurin kama shi, sai an yi amfani da dabarun aiki, hatsabibi ne sosai””To ayi ƙoƙarin hakan dan Allah”.***Gudu-gudu sauri-sauri ta ƙarasa gida, saboda azababben fitsarin da ya cika mata mararta, tana zuwa ɗaki ta watsar da komai a kan gadonta, ta shiga banɗaki.Sai da ta gama fitsarin, ta ji iska na shigarta, tayi wanka ta fito, ta tattare kayan da ta watsar, ta samu riga ta shan iska ta saka, ta shafa turare ta fita.Kitchen ta shiga dan zuba abinci, ta ci karo da fate-faten wake a cikin food flask ɗin ta. A ƙule ta ja uban tsaki, ta fito babban falo kamar ta fashe da kuka, ta hau ƙwalawa mai aikinsu kira.”Baba magajiya!”Daga can wani sashen ta amsa da “Na’am, Arfa gani nan””Na ga faten wake yau?””Eh, umarnin Hajiya babba ne, ita ta ce ayi faten wake”.Cikin ɗaga murya arfa ta ce “Amma dai an san ba na ci ko? Kin dafa mini wani abun ne?”Magajiya ta ce “Wallahi har na ɗaukko doya na fara frayewa, na ɗan dafa miki, na soya miki miya, aka kuma sakani aiki”.Nabila cikin kwakwazo take masifa “Saboda tsabar an tsane ni, so ake na mutu a huta, in je aiki in dawo a kasa ajiye mini abinci, sai a dafa abun da ba na so””Ke Nabila meye haka ne, hajiya ce ta bayar da umarnin hakan, ki shiga kitchen ki dafa wani abun mana” Nabila ta kalli Yaya Sauda ta ce “In je in dawo yanzu, sannan in shiga kitchen in hau girki, bari in je in sha faten waken, duk abun da ya same ni, ku kuka kasheni, ai kun san likita ya hana ni cin wake””To ki je ki ci ɗin mana, idan kin mutun sai ne? Banda gulma amma ai ki na cin ƙosai da shinkafa da wake, ko duk su ba waken bane ba”Kamar ƴar goye, Nabila ta din ga zirarar da hawaye ta na bala’i.”Kar Allah ya sa ki ci abun da aka dafa, kya mutu da yunwa agola ƴar wahala”.Cikin tsananin fusata Nabila ta ce “Tun da dai ba shegiya ba ce ni da ubana, ai da sauƙi”Cikin son kunna Nabila, Sauda ta ce “Meye marabarki da mara uban?”Baba magajiya da ke tsaye ta ce “A’a Sauda, dan Allah kar ayi haka, ke fa babbace”Sauda ta ɗaga mata hannu tare da cewa “Babu ruwanki, ki wuce ki ƙarasawa mama aikinta. Ke kuma ki tsaya ki cigaba da hauka, banda samun wuri ina na taɓa ganin agola da miƙe ƙafa”.”Ai gara ni, agolar ce, kuma iya wuya ni ƴar gari ce, ba baƙuwar haure ba, jikar yarabawa. Kuma ni ba dan albarkacin ubana ba, wallahi da na daɗe da barin gidan nan, gara na je na kama gida na yi zaman kaina, iyaka ace ina zaman kaina, ba ɗan iskan da zai takura mini”Sauda ta tsaya ta ce “To ki je ki kama ki yi zaman kan naki mana, ke dama banda Abba a tsaye yake a kanki, ai ƴar zaman kantan za ayi, kuma ƴar gagara”.Nabila ta buɗe baki za ta yi magana, suka ji gyaran muryar Abba, daga saman bene. Tuni idon Nabila yayi jawur, saboda kuka da ɓacin rai.Ya ce “Magajiya” cikin sauri ta ce “Na’am ranka ya daɗe””A gabanki kina tsaye yaran nan suke faɗa? Ki ka kasa tsawatar musu?”Ta risuna ta ce “Tuba nake ayi mini afuwa”.Sauda ta ce “Wallahi Ab….” Ya dakatar da ita ya ce “Ban tambaye ki ba, kukan me ki ke yi ke kuma?” Yayi maganar yana kallon Nabila.”Faten wake aka yi, ba a dafa mini komai ba, kuma yunwa nake ji”Ya ce “Wannan abun kawai shi ne abun kuka kuma? Ke a rayuwarki ba zaki taɓa girma ba kenan?” Tayi shiru tana sheshsheƙar kuka, kukan da yake jin sa har zuciyarsa.”Magajiya, ko aikin wa ki ke yi, ki ajiye ki sama mata abun da za ta ci, ba biyanki nake dan a farantawa wani a ɓatawa wani ba, duk ƴaƴana nawa ne, babu banbanci a tsakaninsu”Ta risuna ta ce “In sha Allah Alhaji, za a kiyaye””Ke kuma, ki cigaba da faɗa da yayyenki, zaki ga yadda zan yi da ke. Kuma na gode da furunciki Arfa, zaki yi zaman kanki ko? Tun ina raye ki ke wannan iƙrarin, ranar da na mutu ban san me zaki aikata ba, kin kyauta” bai tsaya jiran me za ta ce ba, ya wuce ya koma ɗakinsa.Sauda ta yi wa Nabila gwalo, Nabila ta ce “Ai ke yakamata na yi wa gwalo, ni na yi nasara, tun da an ce a ajiye aikin babarki ayi nawa, banza ƙatuwar kwabo” Nabila ta wuce ɗakin su, tana tunanin ko dan wannan tijarar, ya isa tayi fatan tayi aure ta bar gidan nan.***Ɗan siririn matashi ne dogo, wankan tarwaɗa, sanye da kakin ƴan sanda, da ɗan hanzari yake bin wata doguwar baranda, wadda ta sa da shi da wata ƙofa.Ya buɗe ya shiga da sallama, ya sarawa wanda ya tarar a cikin ofishin, wanda da gani babu tambaya, ka san babba ne sosai a cikin rundunar jami’an tsaro, duba da yanayin ranks ɗin da ke maƙale a kafaɗar uniform ɗin sa, da kuma haɗuwa da tsaruwar office ɗin na sa.Ya ƙame tare da sarawa mai office ɗin, ya yi masa alama da ya zauna.Ya zauna tare da sake gaida wanda ya tarar a office ɗin, da uniform ɗin sa ke ɗauke da sunan ACP Solomon wada.ACP wada ya kalli matashin ya yi murmushi ya ce “CSP Nasir Yusuf”Nasir ya waro ido ya ce “Wane ni Yallaɓai, Dsp ɗin dai””Au Csp ɗin ne ba ka so? Ba abun mamaki ba ne ba, ka ji gobe kai ne Cp na garin nan, kai koma IG gaba ɗaya”Nasir yayi murmushi yana sunkuyar da kai.”Ƙwazon mutum babu in da ba ya kai shi, kuma kar ka yi mamakin ƙwazonka ya kai ka in da ba ka zata ba. Yanzu ba karatunka da kuma ƙwazon ne ya kawo ka matakin da ka ke yanzu ba?”Ya jinjina kai ya ce “Haka ne ranka ya daɗe”.Acp Wada ya ce “Good, wani aikin za’a sake baka, wanda mu ke buƙatar sa da gaggawa, direct order ce daga Cp,ya kuma ce a jinjina maka aikin office ɗin ka yana kyau”Nasir ya tattara hankalinsa ya ce “Ok sir, na gode sosai”Solomon wada ya ce “Nasir, idan ka mayar da hankali yadda ake so, ka gudanar da aikin nan, za ka samu cigaba a aiki sosai da sosai”Cikin girmamawa ya sake cewa “I will do my best in sha Allah”.”Good” ya ɗaukko wani file ya ajiye masa, sannan ya ce “Kwanakin baya, akwai wani ɗan daba, da ya addabi garin nan, kai ɗan garin nan ne za ka fi ni sani, wai shi Aminu ana yi masa laƙabi da viper.Shekarun da suka gabata yana tsare, sakamakon laifin da ya aikata, kafin kwatsam mu samu sanarwar cewa an sake shi. So bayan sakin nasa, akwai kokwanto a cikin sakin da aka yi masa ba bisa ƙa’ida ba ne ba, duk da controllern gidan yari ya ce order aka bashi ya sake shi, bayan fitowarsa ya cigaba da aikata miyagun laifuka a ɓoye, na sayar da miyagun ƙwayoyi tare da ƙyanƙysar sabbin ƴan daba, da suka hana jama’a zaman lafiya a garin nan, wanda yaƙi da wannan a ƙarƙashin kulawar office ɗin ka yake, a zone ɗin. Abun da muke so da kai shi ne, Aminu ya shigo hannu, ko ta halin ƙaƙa.”Nasir ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Ok sir, tabbas cases na dillancin ƙwayoyi da harkar daba, yana ƙara ta’azzara, amma laifin me yayi aka kai shi kurkuku? Kuma ya aka yi, aka sake shi ba bisa ƙa’ida ba?””Wannan ba huruminka bane ba, duk ba shi ne a gabanmu ba, kamo yaron shi ne abun da muka saka a gaba, wannan abun da ya shafi shari’a ne, ɓarnar da yake aikatawa ta yi yawa. Kuma a zone ɗin ka yaransa suka fi yawa, dan haka ka je ka yi iya ƙoƙarin ka a kai. Yabawa da nustuwarka, da jajircewar ka ya sanya muka baka aikin nan, ina nan ina saurarenka, ba a buƙatar ɓata lokaci. Ka je ka duba file ɗin a tsanake, akwai sauran informations da za su taimaka maka wurin kama yaron, da duk wani record na criminal acts ɗin sa yana ciki. Nan da gobe in Allah ya kaimu zaka dawo mini da file ɗin. ba na buƙatar kuma ka yi wani abu sama da haka, kar ka ƙetare iyakar da na gindaya maka”.”Ok sir, i will do mai best in sha Allah” ya ɗauki file ɗin, tare da sake sara masa ya fita.Ɓangaren Nabila kuwa, al’amuranta ba a samu sauyi ba, dan duk shari’ar da ba ta yi mata ba, ba za ta mayar da hankali a kai ba.Director kuma ya bar ta ne, saboda mutuncin mahaifinta Major Yusuf da yake gani, mutum ne na gari kuma akwai tarin alkhairai da ya yi masa, shiyasa ya ƙyale Nabilatake cin karenta babu babbaka.Nabila gaba ɗaya wasu lokutan sai ta ji tana danasanin karantar ɓangaren shari’a, yadda wasu abubuwan suke gudanawa sam ba sa yi mata daɗi.Hausawa suka ce sai hali ya zo ɗaya ake abota, ɓangaren ƙawarta sumayya ma haka, kusan ƙalubale ɗaya suke fuskanta, dan har gara ma Nabila tana da alfarma a wurin na ta aikin, Sumayya kuwa na ta babu sani babu sabo.Yau ganin motar Abba a gida bayan ta dawo daga aiki, ya sanya ta fuskanci yana gidan, dan haka da ta zuba abincinta, sai ta hau saman benensa.A falonsa ta tarar da shi da Yaya Nasir, suna magana, da alama magana ce mai muhimmanci suke yi, sai dai yayi shirin fita.”Abba sannu da gida” “Yauwwa” ya amsa a taƙaice.Sai dai ta na zama ya tashi ya yi wa Nasir sallama, ya fita ya bar falon.Nasir ya galla mata harara.A shagwaɓe ta ce “Dsp me na yi ne? Kwana biyu duk Abba ya canza mini, kai ma kuma kana hararata””Ba dole ya canza miki ba, duk kin gallabi kowa a gida, bayan na dawo daga kaduna ake gaya mini wai kin je biki kin yi dare, ƙarshe a haraba ki ka kwana yayi punishing ɗin ki, ba ki zo kin bashi haƙuri ba. Law firm ɗin ku director ya kawo masa ƙara, daga danna waya sai kwalliya ki ka iya, ba kya son aiki, yayi ta bashi haƙuri ya ce a kula da ke a koya miki aiki, ko ba a biya ki ba, shi zai din ga biyanki salaryn. Kwatsam jin kunnensa ya ji ki na cewa ba dan shi ba, zaman kanki zaki yi, kin san kwana nawa ya ɗauka ba ya bacci saboda wannan maganar da ki ka yi? Duk cikinmu babu wanda Abba yake lelensa kamar ke, amma sai ba shi kunya ki ke ko ta ina?”Cikin sanyin jiki, da tashin hankali ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ban zaci ran Abba zai ɓaci har haka ba, to kuma ba ka bashi haƙuri a madadina ba? Yaya sauda ce fa take ce mini agola, ni kuma ba na son na gaya masa. Ba na son fushin Abba, dan Allah ka tayani ba shi haƙuri. Maganganun Sauda ne suka ɓata mini rai, na yi dana sanin abun da na faɗa, amma dan Allah Yaya Nasir ka bashi haƙuri”Ya girgiza kai ya ce “No ni ba ruwana”Kuka ta saka masa tana cewa “Wallahi ba zan ci abinci ba, sai yanzu na ji maganar da na yi, ta yi nauyi ban san abba zai ji ba””Kin ga ya isa, kar ki saka ciwonki ya tashi na shiga uku, ya mayar da fushin da yake yi da ke kaina” ai kamar ya sake tinzirata, ta cigaba da sheshsheƙar kuka.Cikin tsawa ya ce “Ke wai dan ubanki meye haka? Am i your mate, ba magana nake yi miki ba?” Sai da ta razana, amma hakan bai saka ta daina kukan ba.Ya zuba mata ido, Nabila tun asalinta tun tana yarinya take fama da taurin kai na tsiya, yanzu ko dukanta zai yi, ba za ta daina kukan da take yi ba, balle ma yanzu ba wannan dan ta girmi duka. Har mamakinta yake yi, ƙatuwar budurwa ta kammala degree, kusan shekara ashirin da huɗu amma tana abu kamar yarinya ƙarama. Tsaki yayi, ya tashi shi ma ya fice, ya ƙyale ta, ta ci uban kukanta, ta kwanta a kusa da flask ɗin Abincinta ta hau baccin gajiya.A tsanake Nasir yake duba file ɗin da aka bashi, a kan Aminu viper, da aka ce lallai ya kamo.A record ɗin da ya duba, ya gano zuwan Aminun gidan yari, ba sau ɗaya bane ba, a kan mabanbanta laifuffuka da suke da alaƙa da harkar daba, da ta’amalli da miyagun ƙwayoyi.Sai dai abun da ya ɗaure masa kai, ba a shigar da dalilin da ya sanya, aka kai shi prison na ƙarshe ba, an dai nuna ya aikata wani babban laifi ne, da ga cikin manyan laifuka da bai kamata daga lokacin faruwar abun zuwa yanzu ace an sake shi ba, haka zalika an cire wasu abubuwa masu muhimmanci da yakamata ace ya gani a cikin file ɗin, sannan ga shi solomon Wada ya yi masa umarni da ya yi amfani da iya abun da aka bashi.”To menene dalilin haka?” Ya tambayi kansa, a lokacin da kan na sa ya ƙara ɗaurewa.Sake duba file ɗin yayi yana tunani, kamar ya taɓa duba wani case, makamancin record ɗin da yake cikin file ɗin, sai dai kamar sunan ba haka yake ba. “Aminu Viper” ya sake maimaitawa.
Ayshercool.
08081012143
