Mijin Marigayiya Page 26 Hausa Novel
Yana fita ta zame tayi kwanciyarta sai dai bata rufe kofar ba. Tana jinsa ya dawo dakin ya leka fuskarta tayi kamar bacci take, don haka ya fice ya barta bayan ya kashe mata fitila. Yayi zaton kamar yanda ta amsa masa da daddare zata tashi ta shirya yara, sai dai abinda tayi jiya shi ta sake maimaitawa. Ta saka mukulli ta kulle dakin, ya buga har ya gaji bata bude ba; don haka ba tare da bata lokaci ba ya tsaya a kan yara suka shirya ya kwashesu ya kai su makaranta. Kafin ya dawo ta fice ta bar masa Rashida a gidan. Takaici ne ya sake kamashi; to me Khadeeja ta mayar da shi ne? wannan wane kalar taurin kai ne take yi haka? Kuma me take nufi? Yanzu me take so yayi mata; yaya ma zai yi da ita don gaskiya idan ba so take ya doketa ba bai san me zai yi mata ba.Haka ya shirya ya fice ya nufi office.Har ya kusa karasawa office din dabara ta fado masa; ya karkata kan motar ya nufi gidan su Khadeeja. Gara yaje ya kai kararta waje Baffa in ya so su tsawatar mata don shi yanzu idan ba duka ba bai san me take so yayi mata ba. Ya ci sa’a ya sami Baffa yana shirin fita, bayan sun gaisa Baffa yace ‘Lafiya kuke dai na ganka da sassafe ko?’Nan ya mayar masa da abinda ya faru da kuma yanda Khadeejan take rufe kanta a daki, sai dai ce masa yayi ya rasa Khadeejan ne a waya shiyasa ya tura sakatariyar tasa.Baffa yayi dariya yace ‘Kishi ne nasu na mata ya motsa, ka san a kan wata macen komai son da matarka take maka to za aji kanku. Kada ka damu bayan Magriba ka daukota ku zo nan. Zan kirawota don ma kada tace zata yi taurin kai.’‘To Baffa, na gode.’Yayi musu sallama ya fice yana jin dadin matakin da ya dauka tunda ya san ko babu komai Baffa zai yi mata fada kuma ya san dole ta shiga hayyacinta._____Suna shirin shiga lecture wayarta tayi kara, tana dubawa taga Baffanta ne don haka ta ja da baya ta nemi waje ta amsa. Bayan sun gaisa yace ‘Khadeeja, na cewa Mustapha ku zo bayan magriba ke da shi kin ji ko?’Tace ‘Um Baffa yau? Wani abu ya faru ne?’‘Babu abinda ya faru, ku dai zo din.’‘To Baffa in sha Allahu zamu zo, in ya dawo zan gaya masa.’‘Kada ki damu na gaya masa ma, yanzu ya bar nan.’Ta amsa suka yi sallama da Baffa tana dariya, don ta san inda zancen ya dosa, ta gane Mustapha kararta ya kai duk da bata zata haka ba.Ta jiyo motsin shigowar Mustapha gidan amma bata yi zaton zai yi saurin tafiya ba, don haka ma ta jira sai da ta gama abinda takeyi tunda ta jiyoshi da Baffa a tsakar gida. Sai dai ga mamakinta ko da ta fito Baffa ta tarar shi kadai, yana shirin shigewa mota tayi sauri ta karasa. Tace ‘Naji kamar kai da Mustapha ne, ko har ya tafi ne?’Ya tsaya yana rike da murfin mota yana cewa ‘Shine, matar tasa ce ta fara gwada masa tutsun nata shine ya taho kawo kara da sassafe.’‘Ikon Allah, Khadija Iya-rigima. Me tayi kuma?’Ta Nan ya bata labari kamar yanda Mustapha ya bashi, ya kara da ‘Na ce su zo bayan Magriba don itama yanzu zan kirawota na sanar da ita kada tayi taurin kai, kin san hali.’Tayi dariya ‘To Allah ya kaimu, ai an auna arziki ma da aka dauki lokaci haka bata fara rigimar ba.’Suka yi dariya ta yi masa a dawo lafiya ya wuce sannan ta koma ciki.………Sai da yamma tayi sannan ta kirawo Khadeeja a waya, bayan sun gaisa tace ‘Me ya hadoki da Mustapha ne ya kawo kararki da sassafe ne?’Tayi adriya sannan ta bata labari, bayan ta gama ji tace ‘Ikon Allah, to neman mata Mustaphan yake yi kenan ko kuwa dai aure yake nema?’‘Nima ban sani ba Mommy, amma dai ko ma menene ai da akwai cin fuska ace ina yawo a taxi ita kuma tana yawo a motar mijina; at least ya bari ta aureshi sai ya bata wannan ikon. Kuma sannan idan itace zata dinga yi masa hidimar yaransa ai sai ta karba gaba daya ni kuma na huta gaba daya.’Mommy tace ‘Um! Da wannan, amma dai ki bari abi abun a hankali. Saura kuma idan kun zo kiyi shiru ki ki yiwa Baffa bayani ya yanke miki hukunci in ma ya ga dama yace ki bawa Mustaphan hakuri.’Tayi ‘yar dariya ‘Ba zan yi shiru ba Mommy.’Suka yi sallama suka ajiye wayar.………Sai dab da magriba ya dawo gidan, ya yi mamaki da ya jiyo Rashida da Afaf a kitchen suna kokarin dafa abincin dare; a tunaninsa tunda ya san Baffa ya gaya mata yana nemansu ya kamata ace ta shiga hankalinta.Bayan ya amsa sannu da zuwansu ya wuce dakinta; kofarta a rufe take, ya saka mukullinsa yaji har yanzu bata cire mukullin ba don haka ya daure ya kwankwasa.Sai da ta gama yaukinta sannan ta bude ta rige hannun kofar ta matsa ya shige. Ya so ya zare mukullin kofar to amma sai ya ga idan ya zare ai duk da haka ba lallai ta dinga fita daga dakin ba balle ma ta dinga yin hidimar da ta saba; tunda dai wulakanci ne kawai ta shirya zata yi.Don haka ya bi bayanta suka shige dakin, tun kafin ta gama zama a inda ta tashi yace ‘Baffa ya gaya miki muje yana nemanmu ko?’Cikin halin ko in kula tace ‘Karfe nawa zamu je?’Ya so ace ta bashi dama suyi magana su kashe wannan rigimar in ya so ya kirawo Baffa yace masa sun shirya amma sai dai ga alama ta fi so suje wajen Baffan.Yace ‘Da na dawo daga masallaci sai muje.’Ya juya ya fice daga dakin ba tare da ya saurari amsarta ba.Ta bi bayansa da harara tana dariya; wato shi uban ‘yan son kai har yanzu bai ga laifinsa ba don haka ita yake tsammani ta bashi hakuri kenan. Tabbas yau sai ta kure wannan son zuciyar na Mustapha duk da har yanzu wata zuciyar tana gaya mata kada taje ta yiwa mijinta tonon asiri a wajen iyayenta.………Yana dawowa daga masallaci ya sameta a shirye, ko zama bai yi ba suka sallami yara suka fice daga gidan.Suna shiga gidan suka sami Mommy wadda ta basu umarni su karasa parlor din baki domin Baffa yana can yana jiransu. Yana zaune a kan kujera 3-seater don haka Mustapha ya zauna daga gefen damansa jikin 2-seater ita kuma Khadija ta koma daya gefen jikin single seater ta zauna. Bayan Baffa ya amsa gaisuwarsu ya dubi Khadeeja yace ‘Dije, me ya hadaki da maigidanki ne kika daina kula shi shi da yaransa?’Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace ‘Baffa ba daina kulasu nayi ba.’Kafin Baffa yace wani abu Mommy ta shigo da sallama Nabila tana biye da ita dauke da tray wanda aka jera ruwa da lemo a kai, don haka Baffa ya tsaya ya amsa sallamarta. Ta nunawa Nabila inda zata ajiye tray din daga kusa da Mustapha, ta ajiye ta gaida Mustaphan sannan ta mike ta fice daga parlor din ita kuma Mommy ta kara ta zauna a kan kujerar da Khadija take zaune a kasanta.Ya juya ya gaida Mommy, bayan ta amsa Baffa ya sake duban Khadeeja yace ‘Ya aka yi Dije ina saurarenki.’Tace ‘Baffa ba daina kulasu nayi ba fa.’‘To ai yace kusan kwana uku kenan ba kya kula kowa sai dai kawai ki kulle kanki a daki kin bar yara da mai aiki sannan kuma gari yana wayewa sai ki fice ki tafi makaranta. Kawai saboda ya tura sakatariyarsa taje makarantar yara kun hadu.’Ta faki ido ta share kwalla; ya riga ya bawa Baffa kanun labaran don haka duk yanda take son ta kare mutuncinsa ba zai yiwuba domin itama dole ta kre kanta a wajen mahaifinta. Ta gyara zama tace ‘Wallahi Baffa ina bakin kokarina wajen kula da gidan da yaran, kuma babu laifi duk mun sami fahimtar juna da yaran gaba daya. Duk wata hidimarsu ni nake yi, kuma nice nake daukosu daga makaranta ranar da bana nan kuma sai mai-aikina ta daukosu. To shine ranar Monday suka yi open day a makaranta; nice na saba zuwarmusu don haka tun weekend suk gaya min, shi kuma na manta bamu yi maganar ba. Don haka gari na wyewa da na shirya zan tafi school sai na tsaya makarantarsu. Shine sai na ga har ya tura sakatariyarsa taje musu.’Baffa yayi dariya yace ‘To ai babu komai Dije, watakila don baku yi maganar bane kuma kin ga ita din ai sakatariyarsa ce zai iya sakata wannan aikin duk da dai personal ne.’‘Ni Baffa ba zuwanta ne ya bata min trai ba…’ nan ta bashi labarin yanda taga sakatariyar a motar Mustapha din da kuma yanda tunda ta aureshi sau daya ya taba kaita makaranta a motarsa da kuma yanda ko ta shirya baya yarda ya fita da ita. Da kuma yana wasu lokutan tana tsaye a bakin titi yake dawowa daga kaisu; bata sani ba ko yana ganinta amma ita dai tana ganinsa.Baffa ya kalli Mustaphan ya kalli Mommy sannan ya kalli Mustapha wanda yayi tsamo-tsamo don bai zata Khadija zata kawo wannan maganar ba; shi da yaga ta daina damuwa ya rage mata hanya ma ya zata ta hakura gaba daya don haka bai san tana jin haushinsa a kan wannan ba.Yace ‘Ikon Allah, yanzu a ce a ki ragewa mutum hanya sai kace wani wanda ake jin haushi? Ko dai akwai wata matsalar ne Mustapha?’Nan da nan ya fara gyara zama kansa a kasa cikin rawar murya yace ‘Babu wata matsala, em… dama yawancin lokutan ne ai bata shiryawa da wuri su kuma yaran idan 7:30am tayi rufe musu gate za ayi. Umm.. shi yasa dole muke tafiya, kuma wasu lokutan ma idan na kaisu gidan nake dawowa sai daga baya nake fita.’Tace ‘Baffa ai ko ya dawo zai fita idan nace ya rage min hanya sai ya san abinda zai fada wanda zai sa ba zai tafi dani ba don haka ma tun tuni na daina tambayarsa.’Suka dan yi shiru na dan lokaci Mustapha yana ta kokarin hada ido da ita yayinda ita kuma take ta kokarin kauce masa don ko gefen da yake bata kalla ba.Baffa yace ‘Shikenan abinda ya saka ki fushin ko akwai wani abun?’ kana jin muryarsa kuma ka kalli fuskarsa zaka san ransa ya sosu matuka, domin karsashi da rahar da ya fara wannan tattaunawar da su duka babu…
