Halysaah Page 97 By Khaleesat Haydar
Washegari da safe Jay ya tafi bangaren Maminsa don gaisheta, bayan ta amsa gaisuwarsa tana kallonsa tace “Ya ku ka yi da Sarki?” Jay ya sauke idonsa yace “Mami sau uku ina yi masa magana….” Mami tace “Ba sau nawa kayi masa magana nake tambayarka ba Jawwad, cewa nayi ya ya ku ka yi da shi daga karshe?” A hankali Jay yace “Kinsan bazai yi magana me tsayi ba Mami, he was quiet at the end kuma yace min ya ji, i am just hoping he is convinced kuma zai yi considering duk abun da na gaya masa, don haka ko da zaki ga wani abu daban Mami ki sani i tried my best in maki yanda kike so, duk yanda nake jin nauyin Mai martaba i confronted him thrice just to please you Mami” Sallaman Aunty yasa Jay yayi shiru ya daga kai yana kallonta, Aunty ta karaso cikin parlon tace “Fatan mun wayi gari lafiya Fulani” Mami tace “Lafiya lau Alhamdulillah, ya kwanan su Zuwaira?” Aunty ta nemi kujera ta zauna tace “Alhamdulillah” Jay ya sauke idonsa ya gaida Aunty ta amsa sannan ya mike yana kallon Mami yace “Zan ɗan fita Mami, sai na dawo” Aunty tace “Zaka ɗan fita ko dai za ku fita, Boss din naka na can naga ai ya shirya yana jiran ka kaje ka ja maku mota” Ko kallonta Jay bai yi ba har ya fita daga parlon, Aunty ta taɓe baki tana kallon Mami tace “Tare fa za su fita da Junaid don naga Junaid din ya fito yana rike da makullin mota” Mami dai bata ce komai ba don abinda ya dameta daban a ranta, ba kadan maganar auren nan ya tsaya mata a rai ba, Aunty ta gyara zama tace “To yanxu yaya ake ciki? Mai martaban ya yarda a ɗaga daurin auren ko kuwa?” Mami ta girgiza kai tace “Ina tantama Fulani, don sau uku Jawwad din ke samunsa da maganar amma yaki ce masa komai, kin ga kuwa bai amince ba kenan” Aunty tace “Sai kace ba Sarki ba, ai ni nasan ko don ya nuna mana iyakar mu fa sai yayi abin nan da yaga ba ma so, ga abu ya zo a kurarren lokaci balle a bi ta kasa a lalata, amma dai kin san abinda zai faru?” Mami na kallonta tace “A’a sai kin fada” Aunty ta mike ta koma gefenta ta zauna tana kallonta…. Ko kallon Jay Ajay bai yarda yayi ba ya nufi motarsa, Jay ya bi sa da kallo yace “Ni zaka walakanta?” Sai a sannan Ajay ya juya ya kallesa yace “Since when did I become ur driver Jay, if you are not too fine to drive ga drebobi sai wanda ka zaba a gidan nan, why do I have to drive you, on a serious note bazan je unguwan nan me nisa ba da daddaren nan, gwara ma ace hanyar Kano na kama in san tafiya me nisa dama zan yi kawai, haba ai unguwan yayi nisa sosai ga hanyar babu kyau ga dare yayi, throughout the day time me yasa baka ce in raka ka ba sai da daddaren nan, beside i told you i am meeting a friend yana jirana, you met me already prepared to go out balle kace kirkiro fitan nayi” Jay dai kallonsa kawai yake, Ajay yace “Zaka je wajen budurwar ka sai kace sai an raka ka, idan nace bazan je ba kuma ya zama issue, kaje for once kai kadai mana, haba you are stressing me wallahi” Kallonsa kawai Jay yake yaki tanka sa, Jin Jay yaki cewa komai kuma bai fasa kallonsa ba yace “To in har zan je sai ka min full tank, sannan akwai shopping da zan yi online the bill is on you, agreed?” Jay ya wani kallesa, haka nan babu yanda Ajay ya iya suka bar gidan a cikin motarsa yana mita, Jay dai ko kallonsa bai yi ba, karfe tara saura mintuna Ajay yayi parking dai dai kofar gidansu Aunty Murja, Jay ya ciro wayarsa after some seconds ya kai kunne duk da ba kira yake ba don yasan ko ya kirata ba lallai ta ɗaga ba, he tried calling her once yesterday bata yi picking ba kuma bata biyo sa ba, can ya kalli Ajay yace “Can you pls call Halysaah’s line, I can’t reach her” Ajay ya juya ya kallesa, sai kuma yace “You can’t reach her? To ni ne zan iya reaching dinta kenan, ina ce same network muke using, in baka sameta ba ai nima haka, better still ka aika yaro cikin gidan ya kirata mana” Jay ya dau wayar Ajay dake ajiye, shi dai Ajay kallonsa kawai yake, number Khaleesat yayi dailing sai ga suna ya fito anyi saving as Jay’s girl, Jay ya daga kai ya kallesa, dariya Ajay yayi, shi kansa bai ma san me ya basa dariya ba, May be the way he saved the contact, can dai ya fixge wayar yayi sending kiran, Jay yace “Sunanta ne baka sani ba?” Ajay yace “Oho, Haseenah kake ce mata ko Haseelah” kiran na shiga bayan ɗan lokaci Khaleesat ta ɗaga amma tayi shiru, Ajay yace “Ke kika saka min katin zaki yi shiru Malama?” A hankali tace “Good evening” Yace “Ana jiran ki a waje” Tace “Wa?” Yace “Kar ki bata ma mutane lokaci Malama” Daga haka ya katse wayarsa ya daga kai ya kalli Jay dake kallonsa, bayan kusan minti shidda sai ga Khaleesat ta fito tana sanye da hijab har kasa, kallon motar kawai take kamar bazata karasa ba can dai tana tafiya a hankali ta nufi gun motar, Ajay ya kunna fitilar cikin motar, shi dai Jay kallonta kawai yake suna hada ido ta sunkuyar da kai, kamar munafuka ta zaga ta wajen driver seat inda Ajay ke zaune, shi kansa kallon mamaki ya bi ta da shi har ta iso side dinsa ta tsaya tana kallonsa tace “Ga ni” Ajay ya juya ya kalli Jay da ya ɗan yi murmushi kawai don ko kadan bai ji haushin hakan da tayi ba, Ajay ya sake kallonta yace “Me zan maki?” Duk da abinda take ji a ranta sai da ya bata dariya amma bata yi ba ta wani kallesa kafin ta saci kallon Jay taga kallonta yake, sunkuyar da kanta tayi, Ajay ya hade rai yace “Malama you are obstructing the air from reaching me, matsa daga nan” Ta wani kallesa tace “To ai kai ne ka kirani” Ajay ya juya ya kalli Jay da yaki cewa komai, can ya bude motar, ta matsa gefe har ya sauko, tsayawa tayi gabansa ganin barin wajen zai yi kamar zata yi kuka tace “Toh ba kai ne ka kirani ba, why did you call me?” Da mamaki Ajay yace “Wai ina wasa dake ne, kinga na saba kiran ki dama?” Juyawa yayi ya bi ta gaban motar ya wuce ta bi sa da kallo, can ta saci kallon Jay suka hada ido, sauke idonta tayi lokaci daya jikinta yayi sanyi, ɗan murmushi yayi ya bude motar ya sauko sannan ya zagayo inda take tsaye, ta ɗan koma baya a hankali tace “Ina yini” Yace “But you know what happened few days ago wasn’t intentional right?” Gyada masa kai tayi, cikin sanyin murya yace “To kiyi hakuri Halysaah, it’s the work of the devil” Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, yace “Kin hakura?” Ta gyada masa kai, yace “Ta yaya zan gane hakan?” Ɗan murmushi tayi ta jingina da motar bata ce komai ba, yayi kasa da murya yace “Kin riga kin ba Ajay insight cewar we had issues ai” Ta ɗan kallesa tace “Ai bazai sani ba….” Yace “Wa yace maki, ur reaction says it all…” Ta girgiza masa kai tace “Zai yi tunanin i am just pulling his leg saboda shi ne ya kira wayana” Jay yace “To shikenan Halysaah, just came to check on you, hope there is no problem” Ta gyada masa kai kawai, a hankali yace “Ki ci gaba da mana addu’a kin ji Housemate? We need it most at this point” Tace “In sha Allah, but….” Yace “But what?” A hankali ta jingina jikin motar cikin sanyin murya tace “No matter what ka zamo me yi ma Mahaifiyarka biyayya, may be aurenmu babu alkhairi ne shi yasa bata so….” Hawaye ne ya cika idonta ta kasa ci gaba, Jay dake ta kallonta da mamaki yace “Saboda me zaki ce aurenmu babu alkhairi Halysaah? Me yasa zaki ce haka? Kuma wa yace maki Mami bata son auremmu, ita kawai cewa tayi ga particular time din da take son ayi auren, Ajay ne ya gaya maki abinda ke faruwa har kika aiko min text din nan few days ago?” Cike da karfin hali Khaleesat tace “Da yaushe muke magana da shi har zai gaya min abinda ke faruwa, Kasan ai baza a boye min abinda Mom dinka taje tayi a gidanmu ba” Jay ya dinga kallonta babu ko kiftawa zuciyarsa na bugawa jin abinda tace, da kyar ya bude baki yace “Gidanku kuma Halysaah? Kina nufin Mamina taje gidan ku??” Khaleesat dai ta dinga kallonsa don reaction dinsa ya nuna kwata kwata bai san Mami taje gidansu ba, hawayen dake makale idonta ya gangaro ta sauke kanta, jingina yayi da motar ya ma rasa abinda zai ce zuciyarsa na bugawa da karfi, Khaleesat ta goge hawayenta cikin sanyin murya tace “Ai ya ma wuce don har Mai martaba ya aika an ba su Babana hakuri, and he spoke to them on phone” Jay was more than shock ya dinga kallonta babu ko kiftawa don duk bai san da haka ba babu wanda ya gaya masa har Mai martaba, a hankali yace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Khaleesat ta goge idonta cikin sanyin murya tace “I think it’s better mu jira har sanda zata so aurenmu, but for now mu hakura kawai, haka Abdul ya aureni Mom dinsa bata so na, yan uwansa basa so na, yanxu kuma….” kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai bayan ta tuna abinda Mom din Abdul tayi mata, don yana daga cikin mamakin da har yau ya kasa barin ranta, Lokaci daya Jay ya rikice mata ya fara bata hakuri, zuwa yanxu ta fahimci halin da yake shiga idan yaga tana kuka hakan yasa ta dake ta hadiye kukan nata tana goge idonta, damuwa ƙarara fuskarsa yace “Kina tunanin zan iya hakura dake no matter what Halysaah? Kinsan irin son da nake maki kuwa? What do you think will become of me idan na yarda aka raba mu?” Ita dai Khaleesat ta kasa ce masa komai hawaye na zuba idonta tana gogewa, Yayi kokarin calming kansa cike da karfin hali “Kiyi hakuri Halysaah amma no matter what ni bazan rabu dake ba, in sha Allah komai zai yi dai dai da izinin Allah, zan kira Aunty Farida in basu hakuri, I knew nothing about this babu wanda ya sanar min Billah” Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace “Ya wuce fa, abinda nace maka har gida Mai martaba ya aika a basu hakuri, ai kaga ya wuce kenan” Jay was speechless, bai taɓa tunanin abun Maminsa ya kai har haka ba, to menene yasa shi zata dinga masa pretending, wannan abun da take yi ne yake kara weighing dinsa down, shi abinda zata nuna masa daban abinda zata je tayi kuma daban, this is so heartbreaking to him, Ajay ne ya zagayo wajen yace “Pls I can’t endure the mosquitoes in this area anymore, in baku gama ba ka samu nearest hotel kawai kayi lodging ni gida zan tafi” Khaleesat ta daga kai ta kallesa, ya hade rai yace “Matsa min in shiga mota” Ta ɗan taɓe baki ta matsa, ya bude driver seat ya shiga, Khaleesat na kallon Jay a hankali tace “Shikenan sai da safe” Da damuwa yace “Ba mu gama magana ba Halysaah” Tace “Sai mu yi ta WhatsApp, ban gaya maka ba gobe da safe zamu tafi Kano da Aunty Murja da yarinyar kishiyarta sai Maman kishiyarta” Jay ya dinga kallonta, can yace “Amma shi ne baki gaya min ba all this while, gobe fa Friday” Ta ɗan yi murmushi tace “Na sani” Shiru yayi for almost 30 seconds kafin a hankali yace “In sha Allah zan zo da wuri sai in kai ku Kanon” Khaleesat ta ɗan bude ido tace “Tasha fa za mu je mu hau mota” Jay yace “Na ce zan kai ku, ku shirya da wuri…” A hankali tace “Toh Allah ya kai mu” Yace “Ameen” Hannu ta ɗaga masa alamar Bye bye sannan ta bar wajen, Jay dai ya kasa ce mata komai ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gida, jiki a sanyaye ya zaga ya shiga front seat yana kallon Ajay with disappointment written all over his face yace “Nasan kasan cewar Mami taje gidansu Halysaah a Kano Amma ka boye min baka gaya min ba Junaid” Ajay ya ɗan kallesa yace “To meye amfanin gaya maka, me zaka yi? She is ur mother babu yanda ka iya, Mai martaba did the needful, so babu amfanin gaya maka ayi ta jan magana…..” Jay ya dinga kallonsa kawai, Ajay ya daga kafada yayi igniting motarsa ya fara reverse, har suka isa gida babu wanda yace komai cikinsu, har sannan jikin Jay a sanyaye yake ya rasa dalilin da yasa yaji ya fara loosing hope kuma yanxu, yaji ya shiga damuwa fiye da wanda yake ciki a baya, bai taɓa expecting haka daga Maminsa ba, Ajay na parking Jay ya bude motar slowly ya sauka, Ajay ya bi sa da kallo har yayi nisa sannan ya sauke ajiyar zuciya ya kashe motarsa ya sauka shi ma, har ransa yake jin tausayinsa kuma shi dai yasan duk rashin kirkin Mami bata kai haka ba kawai Aunty ce ke instigating dinta tana exaggerating mata lamarin shi yasa take ta wannan abubuwan da take yi. Ajay ya kalli agogon wrist dinsa ganin there is still time ya nufi bangaren Abbansa don ya kirasa daxu suna unguwan su Aunty Murja, zai bude kofar parlorn aka riga sa budewa sai ga Mami ta fito daga parlon fuskarta a daure ko kallon Ajay bata yi ba tayi wucewarta, Ajay ya bi ta da kallo sannan ya shiga babban parlon, Zaune ya tarar da Mai martaba a parlon, Aunty dake zaune parlon ita ma tayi kasa da kai cikin kwantar da murya tana cewa “Allah ya huci zuciyarka ranka shi dade idan maganganunta sun maka zafi, Allah ya baka hakuri Me martaba, a gaskiya Fulani bata kyautawa sam, ban san me take son a mata ba, amma babu komai ita kanta tasan albarkacin wa take ci, kuma zata ci gaba da cin albarkacin nasa, Allah ya sanyaya ranka Mai martaba, Allah ya huci zuciyar ka, Allah ya baka hakuri” Ajay ya dinga yi ma Aunty wani kallo, sannan ya zauna kasan lallausan Carpet din parlon yayi kasa da kai yana gaida Mai martaba, Mai martaba ya ɗaga kai ya kallesa yace “Ka dawo Yarima” Ajay bai dago kansa ba yace “Mun dawo Ur highness” Sarki yace “To maa sha Allah, na ma ga takardun da na kira nake tambayarka daxu” Ajay yace “To in ba damuwa zan iya tafiya ur highness?” Duk da akwai maganganun da Sarki ke son yi da shi amma ganin Aunty a parlon kawai yace “Sure, Allah ya tashe mu lafiya” Mikewa Ajay yayi ya ɗan kalli Aunty yayi mata sai da safe sannan ya juya ya nufi kofa ya fita, direct bangaren Jay ya nufa yaji ya kulle kofar shiga part din nasa, hakan yasa ya juya ya koma bangarensa…. Ana idar da sallan asuba bayan Jay ya dawo masallaci ya tafi part din Ajay, bai samesa a bangaren nasa ba, ya zauna nan parlor ya jira har ya dawo, Jay ya ɗaga kai a hankali ya kallesa yace “Yau Halysaah da Aunt dinta za su koma Kano, na ce mata zan je da safe in kai su Kanon, but i don’t think I am okay Ajay, bazan iya driving din ba…” Ajay ya katse sa ya zauna yana kallonsa yace “What’s wrong with you?” Jay yace “I just need rest, zan kwanta ko zan ɗan yi bacci, shi ne nake son tunda bazan iya kai su Kanon ba ka taimaka kayi dropping dinsu motor Park su hau public transport, ban san nawa bane kudin motan but you can sort that out” Ajay dai kallonsa kawai yake, can yace “To me yasa baza a tura masu kudin motar ba kawai, har sai an je uwa duniyar unguwan nan nasu an dauke su an kai su Motor park” Jay ya mike yace “You just have to help pls, they are leaving very early this morning” Daga haka ya nufi kofa Ajay ya bi sa da kallo har ya fita, kawai yayi shiru ya kyalesa ne ganin da gasken he is not looking okay. Duk tunanin Khaleesat idan ta fito zata ga Ajay da Jay duk da Ajay ne ya kira wayarta, amma sai ta ga Ajay kadai, gaishesa tayi yace “I have where I am going, do not keep me waiting….” Juyawa tayi ta koma cikin gidan, sai da suka ɓata kusan 15 mins sannan suka fito, ya bude motar ya sauka yana gaida dattijuwar cikinsu sannan ya gaida Aunty Murja ya bude masu booth suka saka akwatinsu, ya bude masu back seat ya koma cikin motar ya zauna, sai da Khaleesat ta jira Inna da Aunty Murja suka shiga motar Zainab ma ta shiga sannan ta koma front seat ta shiga tana rike da handbag dinta, yan gidan gaba daya suka fito har da makota ana masu Allah ya kiyaye hanya har Ajay ya bar unguwan, at first tasha yayi niyyar dropping dinsu amma sai ya kasa hakan, still dai yana driving yana estimating lokacin da zai kai su Kano ga daurin aure yau, what if Mai martaba yayi realizing baya garin idan yana bukatarsa, daga karshe yayi deciding in ya samu available flight kawai sai ya bi ya dawo tunda bayan an sauko juma’a ne daurin auren and this is just few minutes to 7am, yana daukar hanya da raɓar AC ya bugi su Aunty Murja duk suka ɓige da bacci a bayan motar, tafiyar kusan 2 hours suka yi Khaleesat ta juya tana kallonsa a hankali tace “Don Allah zaka iya tsayawa, it seems I want to throw up” Ya daure fuska ya kalleta, tana ganin haka ta fara yunkurin amai tana rufe bakinta, gangarawa yayi gefen hanya yayi parking ta bude motar ta sauka, su Aunty Murja dai sai bacci suke basu san me ke faruwa ba, bayan kusan minti uku ya dau bottle water ya bude motar ya sauka ya nufeta, Mikewa tayi tana kallonsa a hankali tace “Ai ban yi ba” Yace “Kika sake tsayar da ni zan sauke ki inyi tafiyata Malama, you can’t come and be stressing me here” Amsan ruwan hannunsa tayi ta bude ta wanke fuskarta, sannan ta mika masa sauran, daga sama har kasa ya kalleta ya juya ya koma cikin mota ta bi bayansa….. Har kofar gida Ajay yayi dropping dinsu bayan sun sauke kayansu an shiga da su ciki su Aunty Murja suka masa godiya suka shiga cikin gidan, Khaleesat ta zaga ta driver seat tana kallonsa tace “Mun gode Allah ya saka da alkhairi, amma baza kayi breakfast ba?” Sai bayan da ta fada hakan ne ta tuna waye shi, ta langwabar da kai tace “Shikenan, are you going back to Bauchi?” Tada motarsa yayi yace “Kina da sako ne…” Murmushi tayi ta girgiza masa kai, sannan tace “Allah ya kiyaye hanya, Allah ya kai ka lafiya” Daga haka ta juya ta nufi gate zata shiga gida, sai da ta shiga gidan sannan yayi reverse ya bar unguwan. Karfe uku saura Khaleesat na zaune parlor bayan Aunty Farida ta gama yi mata gyaran gashi, tun da suka shigo gidan da safe ta samu labarin har yanxu da batun daurin aurenta yau hankalinta ya kasa kwanciya duk tunaninta till further notice duba da abubuwan da suka faru a kwanakin nan, ba ita ba har su Nenne da Ummanta da Aunty Farida kawai sun zuba ma sarautar Allah ido ne gani suke auren fa ba mai yiwuwa bane kawai dai baza a ja da Mai martaba ba, Umma kuwa ko baccin kirki bata yi ba daren jiya haka ta kwana sallah tana rokon Allah Ubangiji ya kawo sanadin fasuwar wannan aure don kwata kwata bata son auren kuma, bata fatan er ta ta koma gidan jiya, gwara ta dauwama a gabanta har Allah ya fito mata da miji wanda ba shi kadai ba hatta yan uwansa da iyayensa za su so ta kamar yanda yake son ta, har zuwa yanxu da Umma ke zaune bata fasa wannan addu’a a ranta ba don tana cikin tashin hankali da rashin nutsuwa a zuciyarta, Ahmad mutumin kirki ne wanda ko wace uwa zata yi ma er ta fatan samu amma tun da uwarsa ta zo har gida ta nuna masu bata son auren Khaleesat da ɗanta tayi masu rashin mutunci Umma taji aurensa da Khaleesat ya fice mata a rai, amma kuma ga Mai martaba a tsakani shi yasa suka rasa say din kansu akan lamarin duk suka zuba ma sarautar Allah ido, Nenne ce ta shigo parlon a gigice da almajirinta da wasu matasa yan Mariri duk sun sha fararen yadi tana kallon su Aunty Farida da Mama Shatu sai Aunty Murja dake parlor tace “Kun ji fa wai an daura auren da Ahamad din, yanxu almajirina ya shigo yake ce min daga wajen daurin auren su ke yanxu haka, mutane ba masaka tsinke a wajen har da sarakuna da manyan mutanen kasar nan, sai jiniya ake ta ko ina….” Sosai Umma taji gabanta ya fadi tana kallon Nenne babu ko kiftawa, Khaleesat sai da taji kamar amai zai taho mata tsabar yanda maganar Nenne ya kidimar da ita ya rikitata, har sai da ta kasa daurewa ta mike da sauri ta nufi bandakin dake parlon tana yunkurin amai, Nenne ta kalli wani matashi me suna Sagir don duk yafi sauran nutsuwa cikin samarin tace “Kai Sagir sai kaji ance an daura auren wa da wa?” Sagir yace “Ni iya na Khaleesat kawai na rike don daurin auren biyu aka yi Nenne” Nenne ta sharce zufar da ya keto mata tace “To ya aka ce na Khaleesah din?” Sagir yace “An daura aurenta da Ahmad Yusuf….” Mikewa Umma tayi ta bar parlon ta wuce daki hawaye na zuba idonta, Aunty Farida da duk jikinta yayi sanyi ita ma ta mike da kyar ta bi bayan Umma, Mama Shatu tace “To mu ai wannan abun farin ciki ne a gare mu, tun da aka daura auren dama Allah ya ƙaddara mijinta ne babu yanda uwarsa zata yi sai dai ta bi su da fatan alkhairi” Nenne tace “Atoh dai, ni dai wallahi nayi farin ciki matuka nayi murna, yanxu tashi za ku yi ku baza turaren wuta a gidan nan da kyar in jiga jigan masarautan baza su yo nan a gaida uwar yarinya da kakarta ba, maza tashi murja kar mu ji kunya” Amai sosai Khaleesat tayi a bandakin, nan da nan taji kamar zazzaɓi zai rufeta ta fito ta wuce dakinta da kyar, sai a sannan hawaye masu zafi suka fara sauka idonta, she is just confuse, ta rasa wani irin tunani zata yi, bata taɓa tunanin za a daura aurenta kwana kusa ba with the way things were going, ko dai almajiran basu ji da kyau bane ba ita ake nufi ba, tayi karfin halin jawo wayarta tana kallon screen din, da kyar tayi dialing number Jay, amma kamar daxu da ta kirasa bai shiga ba yanxun ma bai shiga ba, hakan yasa tayi dialing number Ajay, har ya katse bai daga ba, ta ɗan jira ko zai biyota kamar yanda ya saba, amma har bayan minti biyar bai biyo ba, sake kira tayi still har ya gama ringing bai ɗaga ba, bata taɓa kiransa a take bai yi picking ba ko ya biyo kiran, ajiye wayar tayi ta kwanta gefen gado hawaye masu zafi na zubowa idonta, a haka Aunty Farida ta shigo ta sameta tana kallonta cikin sanyin murya tace “Kun yi waya da Jawwad din ne?” Khaleesat ta girgiza kai hawaye na sauka idonta tace “Wayarsa a kashe” Aunty Farida ta zauna kusa da ita amma ta rasa ma me zata ce, su kansu fargaban auren nan suke balle ita, can Aunty Farida tace “To ki kira Junaid sai ya hadaki da Ahmad din” Khaleesat ta mike zaune tace “Na kirasa bai daga ba” Tana fadin haka ta sake dialing numbersa sai taji a kashe, ta daga kai ta kalli Aunty Farida, Aunty Farida ma tayi dialing number tasa a nata wayar, ita ma taji switch off.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*Ur evidence via 07087865788
