Halysaah Page 76 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 76….Wajen karfe sha daya na dare Khaleesat na zaune saman gadonta tana karatu a laptop din gabanta, ba sosai take gane karatun ba saboda yunwan da take ji, abincin da Housemate dinta ya siyo mata daxu ɗan kadan ta ci a ciki don bai mata dadi ba, tayi tagumi tana kallon slide din gabanta, kofar dake kallon nata taji kamar an bude, ta juya tana kallon nata kofar, after almost 5 mins ta sauka daga saman gadon ta dau hijab dinta har kasa ta saka sannan ta nufi kofa zata je kitchen ta hado shayi, dama tun daxu ta kasa fita ne don kar ta hadu da Housemate dinta a parlor, don yanxu wani kunyansa kawai take ji, a hankali ta bude kofar ta fito corridor tana tiptoeing, tana fara sauka downstairs ta tsaya da mamaki tana kallon Housemate dinta dake kwance 3 sitter idonsa a lumshe, duk da ba wuta me haske bane kunne a parlon amma tsaf take iya ganinsa, juyawa tayi ta kalli dakin dake kusa da nata with confusion, ko dai kunnenta ne yaji kamar an bude kofar dakin? Lokaci daya taji gabanta yayi mugun faduwa bayan Abdul ya fado mata a rai, kaddai Housemate dinta mance kofar yayi a bude yayi bacci, tana cikin wannan tunanin zuciyarta na bugawa aka bude kofar dakin dake kallon nata, wani kara ta kurma a mugun tsorace tun ma bata ga wa zai fito daga dakin ba, Jay ya mike da sauri yana kallonta, sai kuma ya nufeta da mamaki yace “What happened Housemate?” Tana hada ido da Ajay da ya fito daga dakin shi ma yana mata kallon mamaki ta durkusa wajen ta fara kuka tana jin har lkcn zuciyarta bai dawo dai dai ba, tuni Jay ya karasa inda ta durkusa yana kallonta yace “Me ya faru?” Tana kuka a hankali ta daga idanuwanta ta kallesa tace “Tsoro ya bani ai, ni na zata fa ya tafi daxu…” Ajay yaji kamar yayi ball da ita ta gangara downstairs tsabar yanda ta bashi haushi, don shi kansa sai da ihunta ya juya masa kai, Jay dai kallonta kawai yake ya kasa cewa komai ma, Ajay ya fara saukowa downstairs fuska daure yace “Tashi ki ban waje kar inyi ball dake a nan, silly gal” Turo baki tayi tana goge idonta ta basa hanya yayi tafiyarsa downstairs ya bar su a wajen, ta ɗan daga kai a hankali ta kalli Jay dake ta kallonta ya ma rasa me zai ce, boye fuskarta tayi da hijab din jikinta tana lekosa ta ɗan space din da ta bari a hankali tace “Kayi hakuri, ni wallahi ban san a gidan nan zai kwana ba shi ma, na zata ya tafi tun daxu” Murmushi yayi mata, calmly yace “It’s fine Halysaah, you need something?” Ta gyada masa kai, a hankali tace “I want to take tea” Yace “Ohk, let me get you some, ki koma dakin ki” Tana murmushi cikin sanyin murya tace “Thank you” Daga haka ta juya ta koma sama zuwa dakinta, shi kuma ya sauka downstairs Ajay ya bi sa sa kallo har ya shiga kitchen, kwafa yayi ya dau remote ya kunna TV, after some minutes Jay ya gama hada mata tea ya debar mata cookies a plate sannan ya tafi sama, Ajay ya taɓe baki ganin yanda ya maida kansa Boy Boy dinta kawai, alhalin ko 5% din treatment din nan baya yi ma Hadiyah, Jay na kai mata shayin sama yayi knocking ta fito ta amsa amma ta kasa kallonsa, cikin sanyin murya tace “Nagode sosai” Kai kawai yayi mata nodding, slowly yace “Good night Halysaah” Ta juya ta koma cikin dakin ta kulle kofar. Washegari wajen karfe tara na safe Khaleesat ta sauko downstairs bayan tayi wanka ta shirya duk da bazata je school ba ranan, kallonsa ta dinga yi yana kwance saman kujera ya rufe fuskarsa da karamin towel ya kife wayarsa a kirji, karasawa tayi har inda yake kamar tana son gano wani abu, lokaci daya ya cire towel din fuskarsa suka yi ido hudu, komawa baya tayi with shock tana ɗan zare ido tace “Ohh, I tot it’s my Housemate” Ya mike zaune yana kallonta babu yabo babu fallasa yace “Kin taɓa ganinsa da wannan kayan? Ko kuma ina wasa dake ne?” Ta ɗan langwabar da kai tace “To ai dai bazan san ba shi bane, since you are having the same height and complexion with him” Yace “I could slap you idan baki fita a gabana ba Malama” Ta wani taɓe baki ta nufi kitchen, irish ta diba ta fere wanda zata yi using, tana yanke yanken veggies da zata soya kwai da shi a ranta tana mamakin Why Ajay is in the house instead of her Housemate, kawai daga jiya zuwa yau ya mata masifa sau biyu, turo baki tayi ta ajiye wukan sai a sannan ta zaro ido ta dau irish dinta ta zuba a man gyada da ta dora don har ta manta da man gyadan, rufe baki tayi da hannunta jin fire alarm din kitchen din ya dau ruri, gaba daya ta mance da shi, don in dai zata yi soye soye wani lokacin lullubesa take da Shower cap dinta ta yanda bazai yi detecting komai ba balle ya fara tona mata asiri yana ruri, ta juya ta fito daga kitchen din tana kallon Ajay kamar munafuka tace “Don Allah ka zo ka min stopping din alarm din ya dena” Ajay yace “A’a ki dai kona masu gida ni ina ruwana, kin zata a Nigeria kike ba” Ta marairaice tace “Don Allah mana, kaga it’s very loud fa” Ko kallon inda take bai sake yi ba, ta juya ta koma kitchen din tana kallon inda smoke alarm din yake, ita bata ma san ya ake kashewa yayi shiru ba, ta rage abun girkin zata sake komawa parlor ta masa magana ta kusa cin karo da shi zai shigo kitchen din, komawa gefe tayi tana kallonsa har yayi silencing smoke alarm din sannan ya fita daga kitchen din, Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da girkin da take yi, bayan ta gama ta fito daga kitchen din dama iya wanda zata ci da Housemate dinta kawai tayi, tana kallon Ajay tace “Housemate dina fa?” Bayansa ya nuna mata alamar gashi ya goya shi, juyawa tayi ta wuce sama ya bi ta da wani kallo, tana shiga dakinta ta dau wayarta ta zauna gefen gado tayi dialing number Housemate dinta, yana fara ringing ya daga, in his calm voice yace “Good morning Halysaah” Ta ɗan yi murmushi kamar yana ganinta ta fara wasa da gefen duvet dinta a hankali tace “Good morning” Yace “How was your night?” Tace “Alhamdulillah, naga baka nan” Yace “Yea i went to get something, i will come over later” Tace “I made some breakfast for you” Yace “Really” Tayi shiru bata ce komai ba don har ranta ta so ya ci breakfast din, yace “Ohk give me 30 mins zan dawo sai in ci” Tayi murmushi har sai da dimples dinta ya lotsa tace “Toh Allah ya kawo ka lafiya” Katse wayar tayi sannan ta mike ta fita daga dakin ta koma downstairs, bata ko kalli Ajay ba tayi wucewarta kitchen ta ajiye ma Housemate dinta nasa breakfast din ta dau nata ta fito, hada ido suka yi ta sauke idonta har zata wuce sai kuma ta ɗan kallesa tace “There is everything available in the kitchen, idan kana son kayi making breakfast for ur self” Ya juya ya kalleta yace “Kee, ki shiga hankalin ki, ni ba Jay bane” ita dai tayi tafiyarta sama bata ce masa komai ba. Da yammacin ranan Khaleesat na kitchen tana stew taji an danna bell, fitowa parlor tayi amma ta kasa karasawa gun kofar gabanta na faduwa, kaddai Abdul ne ya biyota, tunawa da tayi Ajay na gidan sai kuma taji hankalin ta ya kwanta, amma dai bata karasa gun kofar ba tana tsaye inda take, sama ta kalla ganin Ajay na saukowa downstairs, bai kalli inda take ba ya nufi kofar ya bude, Safiyyah ta koma gefe ganinsa ta fara kame kamen yafa mayafinta tace “Yaya Ajay ina wuni” A takaice yace “Lafiya” still kuma bai bata hanya ba, yana tsaye bakin kofar, Ta ɗan sosa kai tace “Kwana biyu nace ko laifi nayi maka da ban sani ba Yaya Ajay” Kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace “Kin taɓa ɗaga hannu ke kin mari namiji da har kika zuga kawarki tayi hakan?” Safiyyah ta gwalo ido ta cire handbag dinta a kafada tace “Na rantse da Allah ba da sanina tayi haka ba, ta yaya zan zugata? yanxu ma wallahi zuwa nayi zan mata fadan abinda tayi bata kyauta ba, ita Khaleesat bata jin magana kwata kwata ne, ko ni bazan daga hannu in mari lukeke irin Abdul ba, i am trying my best in dinga sakata a hanya amma abun yaci tura, ka tambayeta wallahi ni bani nace ta maresa ba” Ajay yace “Daga ke har ita za ku san yanda za ku yi da shi duk ranan da ya cafke ku a kasar nan…” Yana kai wa nan ya juya ya bar bakin kofar, Safiyyah ta tura masa maki, sai kuma ta shiga parlon tana gwale ido, ganin Khaleesat a tsaye a parlon sai kuma ta washe baki, suka zauna a nan parlon Khaleesat na tambayarta daga inda take ganin uban gayun da ta ci, kasa kasa take bata labarin Birthday din karen wani coursemate dinsu da taje da yanda masu karnuka ke ta zuwa da nasu ita kuma bata da ko mage balle kare, can tace “Da na sani na su Housmate na ara na tafi da shi wallahi” Khaleesat don takaici ma ta kasa ce mata komai sai kallonta take, Safiyyah tace “Har hotuna fa sai da muka yi da karnuka gwanin ban sha’awa in gaya maki” Khaleesat ta taɓe baki ta mike ta tafi duba stew din da take yi, bayan ta fito ta ajiye ma Safiyyah drink din da ta dauko mata ko zaunawa bata yi ba Safiyyan tace “Me jarababben nan ke yi a gidan ki, ina Yaya Housemate din mu?” Khaleesat bata san sanda ta fashe da dariya ba don Ajay yana bakin stairs a tsaye, kamar Safiyyah ta sani ta juya da sauri tana ganinsa ta sinne kai kamar munafuka, dai dai nan Housemate ya shigo parlon, Yana shigowa Ajay ya nufi kofa ya fice alamar dai shi yake jira dama, Safiyyah ta gaida Housemate da fara’arta tana masa sannu da zuwa, ya amsa ya karaso ya zauna parlon yana kallonta yace “Social function kika je ne haka” Tayi dariya har da tafe hannu tace “Eh wallahi birthday din karen wani coursemate din mu na je” Jay yayi murmushi yace “To sannu da dawowa” Tace “Shi ne nace bari in biyo ta nan, kwana biyu ban san me nayi ma Cousin dinka ba sai yayi ta ɗaga min hanci idan ya gan ni….” Jay ya shafa kansa yace “Don’t mind him, wani lokacin haka yake” Safiyyah ta taɓe baki tace “Gaskiya abun nasa ba kyau…” Jay ya ɗaga ido ya ɗan kalli Khaleesat dake tsaye parlon tana kallonsa kamar ranan ta fara ganinsa, suna hada ido ta tura masa baki ta juya tayi wucewarta kitchen ya bi ta da kallo, duk Safiyyah na kallonsu tana ɗan murmushi, sai kuma ta rataye jakarta a kafada still smiling tace “To ni zan koma gida Housemate, kafin yayana ya fara kirana” Jay ya maida dubansa kanta yace “Kin jima da zuwa ne?” Tace “Ai ko minti goma ban yi ba, Cousin dinka ne ya bata min mood dina don ban ji dadin abinda yayi min ba, kawai albarkacin ka ya ci yasa na danne zuciyata, har fa da ce min ni nake zuga Khaleesat a America, abun nan ya min ciwo wallahi” Housemate na murmushi yace “Kiyi hakuri, but kinsan me Safiyyah…. Don Allah ko da kun sake haduwa da shi a school kar ki ce zaki yi wani sa’insa da shi” Safiyyah tace “Wai Abdul?” Yace “Eh” Tace “Ai tun da yayana ya hanani ban sake ba wallahi, ko zagina yayi iyaka in kira masa 911 kar yaje ya min wani mugun abu, amma na dena kulasa” Yace “Good….” Mikewa yayi yace “Let me talk to your frnd in the kitchen” Tana ɗan murmushi tace “Ohk” Kitchen ya nufa bayan ya shiga ya kulle kofar ya jingina jiki ya rungume hannu yana kallon Khaleesat dake goge goge a kitchen din bayan ta gama stew din da take yi, ta kasa juyawa ta kallesa, a hankali yace “Weldone Halysaah” Ta ɗan yi murmushi kawai, yace “Let drop off your friend at home” Ta gyada masa kai alamar to, yana kallonta yace “Sai mu je park daga can ko?” Sai a sannan ta ɗan kallesa, sai kuma tayi murmushi ta juya masa, shi dai kallonta kawai yake, after some seconds a hankali yace “Get ready ina jiran ki” Daga haka ya bude kofar kitchen din ya fita, Tsaye ya tarar da Safiyyah tana jiran su fito ta kama gabanta don bata gane irin wannan kallon da taga suna ma juna ba, Jay yace “Ki jira ta shirya sai mu yi dropping dinki a gida” Komawa tayi ta zauna tana murmushi tace “Ai ko Nagode, bari in maza inyi cancelling ride dina” Yace “Idan ta shirya ku sameni a Garage” Safiyyah tace “Toh” Fita yayi daga parlon, Khaleesat na fitowa kitchen Safiyyah ta gaya mata abinda Housemate dinta yace, a tare suka tafi dakin Khaleesat, Safiyyah ta zauna gefen gado tace “I wish i have freedom like you in this country….” Khaleesat tayi murmushi tana duba kayan da zata sa tace “Yanxun ma ai abinda kika ga dama kike yi, gashi har da zuwa birthday din Dog” Safiyyah tace “A’a wallahi, kinsan da yanda na fito yau kuwa, ni da ma ayi sacking Mustapha a wajen aiki su tattara su koma Nigeria” Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba, tana fiddo kayan da zata canxa Safiyyah tace “Waow, dadina dake in kika so akwai fashion, kina sa wannan kaya ai har ku dawo gida Housemate bazai gaji da kallonki ba” Khaleesat tace “To bazan sa ba” Zata maida kayan Safiyyah ta tare press din dakin tayi bake bake a wajen tace “Ke dalla wasa fa nake maki” Da kyar Safiyyah ta lallabata ta saka kayan daga karshe, bayan nan still tayi forcing dinta ta ɗan yi mata light make up a fuska, Safiyyah ta koma gefe ta rike haɓa tana kallonta tana nazarin ace ita Allah ya ba kyan Khaleesat irin abubuwan da zata yi a duniya ai sai Allah, can ta sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya tace “Kullum kika yi sallah ki dinga gode ma Allah Khaleesat, he created you differently, wallahi you are so beautiful….” Khaleesat ta wani kalleta, sai kuma ta tsaya gaban madubi tana duba abinda zata goge a fuskarta, just eye pencil da powder kadai Safiyyah ta shafa mata, sai lip gloss shi ma lightly, ta ma rasa abun gogewa a fuskar tata, cause there is nothing special, a hankali Safiyyah dake ta kallonta tace “Ji fa lips dinki wani ba sai ya rantse kin shafa jan baki ba kawata, wallahi ki dinga addu’a idan zaki fita don nasan mutane ne daddaya basa tanka ki a zuciya idan kika fita suka gan ki, duk da dai nan kasar kowa ma da hasken sa” Safiyyah ta zaro ido tace “Lahhh, mun bar Housemate dinki a garage tun daxu fa” Khaleesat ta marairaice mata tace “Ni wallahi kunya nake ji Sophie, i am not comfortable with the dress and the make up” Safiyyah tace “Naga jaraba, idan ku ka yi auren haka zaki dinga kunyar tasa?” Khaleesat ta bude baki tana kallon Safiyyah ta ma kasa cewa komai, Safiyyah ta fixgo hannunta bayan ta tayata daukan handbag dinta ta ja ta suka fita daga dakin, har suka fito daga apartment din Khaleesat taki sakin jiki, Safiyya ta karɓe makullin apartment din a hannunta tace “Tafi ki shiga mota zan kulle gidan” Khaleesat taki tafiya, haka kawai aje bata kulle kofar da kyau ba Abdul ya samu hanyar shiga gidan, Safiyyah ta gama kulle kofar ta juya tana kallon Khaleesat tace “Don Allah ki dena yin abu kamar yan unguwan ku mana, America fa ne nan” Khaleesat ta kai hannu handle din kofar ta murda taji sa a bude, wani kallo tayi ma Safiyyah ta kwace makullinta ta kulle kofar da kyau, Safiyyah tace “Oho na zata ya kullu, mu je” Tunda Khaleesat ta nufi garage Housemate ke kallonta babu ko kiftawa, Safiyyah da taya bera bari ta bude mata front seat tana murmushi, Khaleesat ta wani kalleta sannan ta shiga motar ba tare da ta bari sun hada ido da Jay ba, Safiyyah ta koma bayan motar ta shiga, he wants to compliment her amma yayi shiru saboda Safiyyah, ya fara driving yana kallonta lokaci lokaci, daga karshe ya kasa hakuri yace “You look beautiful Halysaah” Safiyyah dake bayan motar ta fara blushing kamar ita aka ce ma haka, tana ɗan murmushi tace “Nima na gaya mata wallahi, amma ta zata am just pulling her legs, nace mata kyanta na daban ne a cikin kyawawa, duk mijin da ya aureta ya more a rayuwa, ko bacin rai yake ya kalleta zai ji ransa yayi fari ƙal, kuma ace ta samu miji me kyau kamar yanda dae kake din nan, waiiiii Allah kadai yasan yanda kids din ku za su zama don kyau…” Khaleesat taji da ma kawai hakura tayi da fitar nan gaba daya tsabar kunya, shi kam Jay murmushi kawai yake idonsa akan titi yana driving, Safiyyah ta bude jakarta ta ciro wayarta ganin Mustapha ke kiranta ta danna wayar a silent a fusace ta mayar cikin jaka, Jay ya kalli Khaleesat yayi kasa da murya yace “Wani park din kike son mu je?” Karaf a kunne Safiyyah, tace “Park za ku je Yaya Housemate” Yace “Yeah Safiyyah” Safiyya tace “To aje da ni mana don Allah sai in zama photographer” Khaleesat ta dafe kanta, Jay na murmushi yace “To nawa za a biya ki for the Job?” Ta kyalkyale da dariya tace “Haba, ko er lemonade ne kawai a siya min” Yana dariya yace “To an gama, amma baza a kira ki a gida ba?” Tace “A’a ba wanda zai neme ni wallahi” Ko da suka isa park din Safiyyah taki yarda ta zauna kusa da su Khaleesat wai za su yi inconveniencing dinta tana son ta nutsu tayi enjoying ambience din wajen da kyau, Khaleesat tasan duk scope din barin ta daga ita sai Jay ne yasa Safiyyah tace haka, shi ko Jay yaji dadin hankalin da Safiyyah tayi a nan, hotuna tace zata fara masu kar yamma yayi sosai, dadi kamar zai kashe Safiyyah ganin azababben kyan da hoton da ta fara masu yayi, can ta karasa inda suke tsaye tace “Ba fa wanda zai tsaya a space din nan da ku ka bari a tsakaninku gwara ku cike sa kawai” Khaleesat ta wani kalleta, Shi dai Jay Murmushi kawai yayi, Safiyyah tace “Ka ɗan matsa kusa da ita kadan Yaya Housemate so that the space won’t make the picture look somehow” Slowly ya matsa kusa da Khaleesat yana kallonta yana murmushi, Khaleesat ta ganta er karama a kusa da shi ga daddaden kamshin turarensa da ya cika ta, tuni Safiyyah ta koma baya da gudu ta ci gaba da daukan hoton da take tana washe baki, farin ciki kamar ya kasheta, haka ta dinga controlling dinsu wajen daukan hotunan, tace su koma can, tace su dawo nan, ta tabbatar tayi masu hotuna masu bala’in kyau, har dai daga karshe Jay yace mata ya isa ita ma ta shigo su yi hoton, zai ba wata er Africa dake wajen wayarsa ta masu hoton har Safiyyah amma Safiyyah taki shiga tace “A’a kar in bata maku hoto ina baƙa da ni” Dariya Housemate yayi haka dai ya lallabata ta shigo aka yi masu hoton su uku, Safiyyah na murmushi tace “Amma fa tunda nake daukan hoto ban taɓa daukan wanda ya dauku kamar hotunan nan da na maku ba wallahi” Jay na murmushi yace “Dollar nawa za a baki to?” Dariya tayi ta tattara lemonade dinta da tacos da ya siya mata tace “Wannan ma da aka siya min Allah ya amfana” Daga haka ta kara gaba ta bar masu wajen, Jay was amaze at how Safiyyah snapped the pictures so well, ya kasa daina kallon Khaleesat a hoton, the pictures where so beautiful, Khaleesat tun da ta kalli hoto daya ta kasa ci gaba da kallon sauran ta koma ta zauna kawai, after a while ta daga ido ta ɗan kalli Jay taga kallonta yake, da sauri ta maida kanta kasa, a hankali yace “Halysaah” Bata dago kanta ba still tace “Uhm” Yace “Me yasa baki sakin jiki da ni yanxu? You weren’t like this before, ko don nace zan aure ki?” Sunkuyar da kanta tayi alamar kunya, yace “To meye amfanin zuwa nan tunda baza ki saki jikin ki ba, i want us to have a quality time together amma kiyi ta sunkuyar da kai….” Tana murmushi a hankali tace “To ai kunya nake ji” Yace “To kalleni zaki dena jin kunyan” Taki dagowa tayi shiru, yace “Halysaah” Tace “Ni bazan iya ba” Bai sake ce mata komai ba, ganin haka ta daga idanuwanta ta kallesa taga kallonta yake, murmushi yayi mata murya can kasa yace “You are specially made Halysaah” Rufe idonta tayi tana murmushi a hankali tace “Thank you” Yace “Kin dai ji me kawarki ta ce ko?” Khaleesat ta daga ido ta kallesa tace “Me ta ce?” Yayi kasa da murya yace “We will make beautiful Babies together….” Khaleesat ji tayi wani azababben kunya ya rufeta, yana murmushi yana kallonta yace “Ni ko guda daya kika bani me kama dake i will appreciate…” Kamar zata yi kuka tace “Ni dai mu tafi gida” Yace “A’a sai kin ban labari, kina ban labari ko daya ne sai mu tafi” Shiru tayi, sai kuma tana wasa da straw din drink din gabanta tace “Wani irin labari?” Yace “Ko ma wani iri ne, ko kuma ki bani labarin yanda ku ka hadu da Funny frnd dinki Safiyyah” Khaleesat tayi murmushi ta dago kai tace “Ohk….” Babu bata lokaci ta fara basa labarin farkon haduwarta da Safiyyah a school, shi dai kallonta kawai yake ko kiftawan kirki baya yi, everything about Khaleesat is just beautiful and breathtaking, tsakaninta da Allah take ta basa labarin Sophie ashe ko sanin abinda take cewa bai yi ba ya kafeta da ido with many imagination running his mind, daga bada labarin Safiyyah kawai ta saki jiki a wajen, dama kuma haka yake so… kamar yanda ya so hakan ne ya faru don they had a wonderful time together, labari sai wanda ta manta ne bata basa ba a kan experience dinta a America tun daga shekaran da ta zo har zuwa yanxu, wani yayi dariya, wani yaji tausayinta wani ya ga wautan ta, babu abinda ya kara burgesa da ita tana basa labarin sai turancin ta, she was so vocal, duk da timidness dinta she was very outspoken kamar ba a unguwan nan da gidansu yake ta tashi ba, he never knows she speak so well sai yau, yayi kasa da murya yace “You know what Halysaah?” Ta girgiza masa kai tana kallonsa, a hankali yace “I love you so much” Rufe fuskarta tayi da sauri tana murmushi… Sai wajen karfe bakwai suka bar park din, sai da suka fara dropping Safiyyah a gida before heading home, Jay na parking Khaleesat ta kalli motar Ajay dake parking Space, can ta kalli Jay tace “Is he waiting for you?” Jay yace “I don’t think so, kinsan yana da aboki a Neighborhood din nan shi ma PhD yake, the frnd is at the far end of this street, External defense dinsu is around the corner….” Khaleesat tace “Ohk har da kai?” Jay yace “Yea in sha Allah, period din exam din ku ne Defense dinmu” A hankali tace “To Allah ya baku nasara” Yana murmushi yace “Ameen” Tace “To a ina zaka yi parking since he is occupying the space?” Yace “Zan je gida in dawo anjima” A hankali tace “To ni kadai a apartment din?” Yace “Ga motar Ajay kina gani, ai yana ciki kenan” Shiru tayi tana kallonsa, ya mata murmushi yace “Mu je in raka ki ciki to” A tare suka sauka daga motar ya rakata har cikin apartment din, yana kallonta calmly yace “Can i go now?” Jingina tayi da bango a kusa da shi ta langwabar da kanta kawai ta marairaice tana kallonsa, ya sauke idonsa daga kallonta trying to calm his self down, a hankali yace “I need to go Halysaah, ki kulle kofar” Daga haka ya juya ya fita daga parlon without looking at her, ta bi sa da kallo kafin ta kulle kofarta….*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
