Uncategorized

Yadda Zaki Sabulun Da zai Sa Ki Dinga Kyalli, Santsi, Kamshi Sannan Yana Maganin Kurajen Fuska

 GYARAN FATA DA JIKI HADIN SABULU 

Dole maigida ko saurayi yai ta binki zai-zai to yaga kin yi kyau.

 SABULUN BITA ZAI-ZAI 

🧽 Dudu osun

🧼 Dettol

🍂 Sabulun Ghana

🌱 Garin zogale

🍁 Farar albasa

sai Ku hade su guri daya Ku kirba su a turmi ki mulmula Ku rinka wanke fuska zaku ga yadda fuskarku zata yi kyau.

Karanta>>> Mene ne Ciwon Sanyi 

Karanta>>> Amfanin Dabino Guda 50 Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

Karanta>>> Amfanin Zogale 20 A Jikin Dan Adam

 BITA ZAI-ZAI 

Sunan hadin kenan idan dai kana yin wannan hadin zaki sha mamaki za kibani labarin amfani hadin tabbas idan amarya tayi wannan hadin zata kidima ango har yakasa gane ta sai yayi da gaske ke dai yi mugani domin gyaran jiki.

🧽 Ayaba

🧼 Lemon tsami

🧽 Tataciyar madara

🧼 Kwai uku

Zaku sami ayaba mai kyau Ku bare Ku matse da hannun ko Ku markada yi laushi sai Ku zuba tataciyar madara Ku fasa kwai kamar uku amma farin zaku zuba sai Ku matse lemon tsami Ku gauraya shi Ku shafa a jikin Ku ya sami kamar tsayin ¹ daya sai kuyi wanka da ruwan zafi, idan har kuka lazimci yin haka ba magana.

Karanta>>> Maganin Amosani, Karyewar Gashi Da Kuma Zubewarshi Kyauta

Karanta>>> Illolin Kwanciyar Ruf Da Ciki Ga Lafiyar Mu

 SABULUN GYARA FATA 

Idan har kina San gyaran fata kina iya wannan hadin domin gyaran jiki, fatar ki zata yi kyau sossai.

🧽 Sabulun sel

🧼 Sabulun salo

🧽 Lalle

🧼 Zuma

🧽 Garin darbejiya

🧼 Sabulun premier

🧽 Kurkum

🧼 Sabulun zaitun

🧽 Dudu osun.

🧼 Dettol

Zaki daka sabulun duka ki zuba a mazu Bi ki zuba lalle da majigi a Kai da zuma da kur-kur ki juya shi sossai garin darbejiya kuma ganyen Zaki samun ki shanya ki daka ki tankade ki hada akan sabulun ki saka ruwa kadan ki juya yadda zai hade jikinsa Zaki ga yadda fatarki zata canja sirrin kyau.

Karanta>>> Sirrin Gyaran Nono Kashi Na Daya

 SA MAIGIDA BITA ZAI-ZAI 

Idan kina yin haka dole maigida yaga kinyi kyau fiye da ko yaushe jikinki da fatar fuskar ki zata yi haske.

🌹 Lalle

🌹 Kwanduwar kwai ³

🌹 Manja cokali ³

🌹 Kur-kur

Sai Ku kwaba su guri daya Ku shafe jikinku zuwa awa guda, sai Ku yi wanka da ruwa zalla in dai kyan fata ne sai dai agani a jikinku, kowa zaiyi sha’awar ki.

Karanta>>> Yadda Zaki Hada Kwalacca


 SABULUN KURAJE 

🛀 Asef soap

🛀 Pharmaderlm soap 

🛀 Ƙanwa

🛀 Jar dilka

🛀 Zuma

🛀 Lemon tsami

Ki goga sabulun kowanne guda uku, sannan ki zuba kanwarki dakakkiya cikin karamin cokali, kinkwaba dilka da ruwan zafi cikin cokali cin abinci daya ki zuba a ciki, ki matse lemon tsami daya a Kai kisa Zuma cokali biyar ki hada ki kwaba sosai, ki lailaya sai ki dinga shafawa a fuskarki kamar ya rage minti biyar kafin ki shiga wanka, Indan kin shiga wanka sai ki kuma wanke fuskarki da sabulun kamar uku ko Dama da haka.

Karanta>>> Yadda Zaki Hada Dettol Cikin Sauki

 SABULUN FIDDA TABO 

Ko Zuma Zaki Iya shafawa idan Zaki kwanta bacci sai da safe ki wanke da ruwan dumi.

👤 Misscoroline soap

👤 Shary soap

👤 Aloevera soap

👤 Garin alkama

👤 Zuma

👤 Ƙanwa kadan

👤 Lemon tsami Bari 1/1

Sai ki goga su ki hada ki zuba Zuma a ciki da lemon tsami da kanwarki ki kwaba, ki dinga shafawa fuskarki minti biyar kafin ki shiga wanka, idan kuma zakiyi wanka dashi Zaki dinga wanke fuskarki.

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

SABULUN WANKA NA BAKAR MACE

🍯 Sabulun salo ko

🍯 Sabulun Ghana

🍯 Magiji.

🍯 Zuma

🍯 Lemun tsami.

🍯 Zaitun

a hada sabulun Ghana da magiji a dake a zuba Zuma a matsa lemun tsami kadan a saka man zaitun cokali daya a bada a kwaba, bakar mace da bata son tayi fari sai ta dinga wanka da shi, zai sa tayi kyau.

Karanta>>> Maganin Jinnul Ashiq (Aljani Mai Saduwa Da Mace)

 GYARAN FUSKA AMMA NA SABULUN 

🧽 Sabulun salo.

🧼 Sabulun Zuma.

🧽 Zuma.

🧼 Aloevera.

🧼 Man zaitun.

🧽 Kwakwa.

a Samu sabulun salo ko sabulun Ghana kamar girma sabulun giv guda biyu, a Samu sabulun Zuma guda daya idan ba’a sameshi ba asa aloevera soap, a daka sabulun ko a goge asa ruwan ganyen aloevera cokali uku, Zuma cokali uku,an zaitun cokali daya, man kwakwa cokali daya, a hada a kwaba, a dinga shafawa a fuska, bayan minti goma ko sha biyar sai a wanke fuskar yana saka kyan fuskar tayi shaining tayi kyau.

🔵 Sabulun Gyaran Fata 🔵

Ana bukatar ababe kamar haka:-

🔳 Sabulun Diyana.

🔳 Sabulun Salo.

🔳 Lalle.

🔳 Majigi.

🔳 Zuma.

🔳 Garin darbejiya.

🔳 Dawa’ussabuni.

🔳 Sabulun Premier Antiseptic.

🔳 Kurkur.

🔳 Sabulun zaitun.

🔳 Dudu osun.

🔳 Dettol.

Za ki daka sabulun duka ki zuba a Container ki zuba lalle da majigi a kai da zuma da kurkur ki juya shi sosai garin darbejiya kuma ganyen zaki samun ki shanya ki daka ki tankade ki hada akan sabulun ki sak ruwa kadan ki juya yadda zai hade jikinsa zaki ga yadda fatarki zata canja sirrin kyaun jikin ki ya kadu, sai an gwada dai za a tantance.

Ga kuma gyaran jiki da fuska gaba daya fata tayi laushi da sheki.

Zaki tanadi ababe kamar haka:

1. Man Zaitun

2. Lalle

3. Kur-kur

4. Madarar ruwa (peak)

Za ku hade wadannan kayan hadin guri guda sai ku kwaba su ku shafe jikinku da fuskar ku, za ku yi wannan hadin kafin ku shiga wanka idan ya bushe a jikin ku sai ku murje sannan sai ku shiga wanka, wannan hadin ya na sa jiki yayi kyau da sheki insha Allahu.

Za ku iyayin wannan ma:

1. Kur-kur

2. Dilka

3. Zuma kwai

4. Lemon tsami

Za ku hade su a guri guda ku samu ruwan ku kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma ya fi kwabin lallen ruwa, sai ku shafe fuskanku, idan kuma har da jiki kuke so, sai ku shafa harada jiki bayan awa daya sai ku shiga wanka za k ga yadda jikinku zai goge. Das da izinin Allah. Domin wannna hadin shi ake kira Dalleliya.

Ga kuma wani hadin har wayan na gyaran fatan jiki zaku tanadi:

1. Lalle

2. Kwaiduwar kwai 3

3. Manja cokali 3

4. Kur-kur

Sai ku kwaba su guri guda ku shafe jikinku zuwa awa guda, sai ku yi wanka da ruwa zalla sai ku jika duka da ruwan dumi ku shafe jikin da ita sai ku kuma yin wanka. Allah ya taimake mu.

Karanta>>> Maganin Sanyi Na Maza Da Mata

Idan kuma gyaran fuska ku ke so sai ku tanadi:

1. Dettol

2. Sabulun Ghana

3. Garin Zogale

4. Farar albasa.

Sai ku hade su guri guda ku kurba su a turin ku mulmula ku rinka wanke fusku za ku ga yadda fuskarku za ta y i kyau.

Wannan kuma hadin yanasa fuska ya yi haske ya yi kyau da annuri ya kuma kore kurajen fuska za’a tanadi abae kamar haka: Bawon kankana sai a runka goge guska da shi yana gyara fuska ya yi sumul.

Ga kuma wani hadin duk na gyaran fatar jiki shi ma wannan hadi ne na musamman wanda ya ke sa fatar mace ta zamo tana tare da shauki da laushi kai har ma zaki ji jikin ki yana wani damshi damshi wannan hadi ne da yawanci amare ka wai ake yi wa shi. Za ku tanadi ababen kamar haka:

1. Ayaba

2. Lemon tsami

3. Tataciyar madara

4. Kwai daya

Za ku sami ayaba mai kyau ku bare k matse da hannuku, ko ku markada a blenda ya yi laushi, sai ku zuba tataciyar madara ku fasa kwai kamar guda daya amma farin zaku zuba sai ku matse lemoun tsami ku gauraye shi ku shafa a jikin ku ya samu kamar tsayin awa daya, sai uk yi wanka da ruwan zafi, idan har kuka lazinci yin haka kamar kwana uku za ku sha mamaki.

Back to top button