Uncategorized

Tubali Book 2 Page 4 Complete Novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

 K’ofar falon ta tura ahankali tare dasa k’afarta na dama ta d’an shigo cikin falon, bakinta d’auke da siririyar sallama, wanda ba kowane zai iya jin amo da kuma sautin muryar natan ba.

Ahankali tad’an sake kofar, tare da k’arasa shigowa, wanda hakan ya bawa kofar daman rufewa.

Shiru ta d’anyi na y’an wasu sakanni, kafun daga bisani ta soma yawo da Idanunta acikin, had’add’en falon wanda kaitsaye za’a iya k’iransa da suna Aljannar duniya, badon komai ba kuwa face saboda tsananin had’uwarsa, duk da cewar babu wani tarkace aciki, amma falone daya amsa sunansa falo.

Ahankali ta d’an lumshe Idanunta, tare da shak’an daddad’an k’amshin dake tashi acikin falon, wanda ya had’u da sanyin A/C da kuma, fitinannen turaren air conditioner mai k’amshin strawberry.

Daddad’an k’amshin da d’adinsa kan iya saka mutum jin bacci ta zuk’a, tare kuma da d’an bud’e lumsassun Idanunta, b’angaren dama da kuma hagunta ta kalla, inda taga d’akuna guda biyu, sai kuma kitchine dake can gefe guda, gefe dashi kuwa wani had’adden dining table ne, mai kyaun gaske. 

Gefen damanta ta kuma kallo, kasancewar ance mata bedroom din nasa, ab’angaren dama yake.

Ahankali kuma Cikin nutsuwa ta nufi, kekkyawan kofar da take da tabbacin cewa, nanne d’akinsa, hannunta rike da tray.

Kowani taku zatayi kuwa sai tafukan k’afafunta sun amsa, da wani irin sanyi da kuma taushin dake tashi ak’asan tiles din dake malale acikin falon.

 

Acan b’angaren Rayyern kuwa, akasalance yaja wandon nasa sama, cikin yanayin gajiya da kuma kosawa da tsayuwan da yayi.

Idanunsa yadan lumshe Ahankali adai-dai sanda ya kawo wandon saman kugunsa, duk da cewar bai gama jan wandon ya haura masa can sama ba, hakan kuwa shiyasa duk shatin saman mararsa ya bayyana. 

Akasalance ya jawo short sleeve ya saka ajikinsa, saboda yanayin da yake ciki ne kuma, yasa ko gama had’e bottum din rigar baiyi ba,   hakan kuwa shiya saka kwantattun gargasan dake kwance akan kirjinsa suka Dan bayyana. 

 Haka ma gargasan k’afarsa saboda wandon daya saka din, ya tsaya iyaka guiwarsa ne, wannan shi yasa duk wani lallausan bakin gashin dake kwance a jikinsa suka bayyana.

Duk da cewar akwai rama ajikinsa, kuwa amma hakan baihana kyawunsa bayyana ba, musamman ayanzu daya saka kayan da suka k’ara fito masa da kyaun surarsa. 

Ahankali ya sauke wani irin numfashi mai dauke da ‘alamar gajiya, cikin kosawa da tsayuwar da yakeyi din kuma, ya d’an juya tare da jawo wata had’add’iyar kujera dake gefen gadonsa.

Zama yayi akan kujera tare da  fesar da numfashi mai dumi, Jin kansa yake ya gaji sosai, wanda kuma yasan hakan bai rasa na saba, da rashin karfin jiki da bashi dashi sosai.

Idanunsa ya lumshe tare da maida kansa ya daura ajikin kujeran, akai akai haka yake fitar da numfashi.

A dai-dai lokacin kuwa Jannart ta k’ara masowa jikin k’ofar d’akinnasa, tsayawa tayi ajikin k’ofar tare dayin shiru, zuciyarta cike da tunanin yanda zatayi ta shiga cikin dakin.

Sake gyara rikon tray din dake hannunta tayi, kana Ahankali ta d’an matso, hannunta na dama tasa ajikin kofar tare da soma knocking, cikin kuma tattausan muryarta tace.

“Assalamu Alaikum!”

Shiru taji babu alaman za’a amsa mata, gashi kuma ta kasa ci gaba da knocking din.

Daga can b’angaren kuwa sam Rayyern baima jita ba, saboda tunaninsa daya tafi izuwa wani waje na daban.

Itakuwa Jannart sanin da tayi cewar tana da raunin ji, ba lallaine ma taji koda ya amsa mata ba, hakan yasa Ahankali ta d’an murd’a handle din kofar.

Cikin sa’a kuwa kofar ta bud’e, wanda hakan ya bata daman d’an tura kanta ciki ta shigo ciki bakinta dauke da sallama.

Rayyern kuwa Jin alamun bude kofar ne yasa shi dan bud’e idanunsa Ahankali,  inda ya sauke ganinsa akanta,  ganin ita dinne kuma yasa shi maida idanun nasa ya lumshe, ba tare da ya bari sunyi ido hudu ba.

Jannart kuwa sauk’e idanunta da tayi akansa ne yasa ta d’an tsaya, tare da sauk’e ganinta akan kyakkyawar fuskarsa,  Ahankali  ta dan soma yawo da idanun nata akansa,  har dai ta sauke ganinta akan lallausan sajen dake kwance agefen fuskar tasa, sajen nasa da kuma wuyansa ta d’an k’urawa ido, saboda yanda taga tsaruwa da kuma k’awatuwarsa, ga kuma wani irin haske da taga cikin jikin nasa ke dashi.

Sak ayanayin nasa da mai bacci yayi mata kama, domin hakanne ma yasa ta d’an tsaya kallonsa na d’an wasu sakanni.

Ahankali kuwa ta kauda kanta tare da janye Idanunta daga garesa. 

Cikin sanyi da nutsuwa ta k’arasa shigowa cikin d’akin, tare kuma da nufo inda yake.

Anutse ta d’an rusuna adai-dai gabansa, inda wani glass stull ke aje anan gefensa, sunkuyawa tayi tare da soma kokarin ajiye tray din dake hannunta. 

Batare kuma da takai ga ajiye tray dinba, ta d’an d’ago da kanta ta kuma Kallon fuskarsa.

“Ina kwana.”

Ta fad’a asanyaye, duk da kuwa bata da yakinin cewar zai amsa mata.

Hakan kuwa akayi domin shiru yayi bai amsa mata ba, saidai taga kwayan idanunsa sun d’an motsa, wanda kuma hakan shiya tabbatar mata da cewar ba bacci yake yi ba.

D’agowa tayi daga ajiye tray din, still kuma cikin muryarta dake bayyana sautin nutsuwa tace.

“Sannu Ya jiki?”

Akaro na biyu kenan daya d’an motsa, tare kuma da jan wani dogon numfashi, kana ya bud’e maraitattun idanunsa, masu cike da kasala, gajiya, had’i kuma da bayyana yanayi irin na marassa lafiya.

Inda ya saukesu acikin nata idanun.

Da sauri tayi kasa da kanta, saboda har abada bazata tab’a iya jurewa Kallon cikin idanunsa, a irin wannan yanayin ba.

Shikuwa Rayyern Jajayen labbansa masu sheki ya motsa.

“Da sauki.”

Ya amsa mata cikin muryarsa da bata fita sosai.

Kasan cewar ta kasa kunne kuma hankalinta na gareshi yasa taji,

Jin yanda sautin muryar tasa ke fita ne kuma yasa, Jannart d’ago Kanta ta kalleshi.

Gaba d’aya ya rame sosai, labbansa sun sakeyin ja, Yayinda idanunsa duk suka bayyana ramar fuskarsa, tabbas kallo daya zakayi masa kafahimci cewa ya matukar jin jiki sosai,  saboda yanda komai nasa ya sanja,  amai makon yayi muni kuma sai ramar ta k’ara masa kyau.

Wato atakaice dai Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara irin mutanen nanne, da a kowani irin yanayi suka samu kansu suna kyau,  badon komai ba kuwa, sai dan kyau din a jininsu yake.

Idanunta ta d’an kawar daga kallonsa.

Akaron farko kuma kenan  da ta tausasa muryarta sosai, cikin nuna kulawa tace.

“Allah Ya baka lafiya.”

“Ameen Idan da gaske kike.”

Ya fad’a akasalance, cikin kuma kauda Kai daga Kallon ta. 

Jin abunda ya fad’a d’inne kuma yasa Jannart din, girgiza kanta batare da tace masa k’alaba ta maida hankalinta wajen had’a masa tea.

Acikin zuciyarta kuwa cewa tayi.

“Mai Hali dai baya sanja halinsa, ko bashi da lafiya sai yayi.” 

Ta k’are zancen zucin nata, tana me sauke Idanunta  akan fararen legs d’insa, wanda gargasa suka yi musu k’awanya, ba kuma irin normal gargasa da kowa ya sani ba, gargasane dogaye kuma masu taushin gaske, wanda suka kwanta lub-lub ajikin fatar nasa.

Kauda kanta daga Kallon k’afan nasa tayi, adai-dai lokacin kuma ta kammala juya masa tea d’in.

Tea spoon ta sanya acikin cup din tare kuma da d’ago kanta ta kalleshi.

“Ga Tea din.” Ta fad’a tana me mik’a masa cup din.

Ahankali ya d’an jujjuya mata kai, tare da karyar da wuyansa gefe.

Alamun bazai shaba.

Idanunta tad’an zuba masa, saboda wani irin tausayinsa da taji, sanin kuma halin marassa lafiya da kin son cin abinci ne yasa, cikin tausasawa da kuma kwantar da murya tace.

“Bazaka sha ba?”

Kansa ya kuma jinjina mata, alaman “Eh.”

“To Meyasa?” Ta tambayeshi da wata irin murya, kana kuma cikin yanayin da ita kanta batasan tayi ba.

Fararen hakwaransa yasa ya dan danne lipsl d’insa, cikin wata iriyar fitinenneyar murya yace.

“Banaso!! Bsnaso! banassso!!!”. 

Idanu ta zuba mishi tana mai jin yadda tsikar jikinta ke zubawa sabida yadda yayi mata mgnar like ɗan yaye mai shogoba.

Kai ta ɗan kwantar kana cikin murya da bata san ta yaya ya ziyarci harcentaba tace.

“Bakason me?”.

Kwaɓe fuskarsa tayi tamkar zaiyi kuka yace.

“Banason tea me madara empty zaki baneeee.” 

Yayi maganar cikin sake yin kasa da murya, saboda gaba daya baya wani jin dadin jikinsa, ga kuma rashin karfi dake damunsa, wanda hakan yasa maganan ma wahala yake basa.

Jannart kuwa jin abunda ya fad’ane yasa, ta d’an kwantar da kanta gefe, tare kuma da Kallon kayan tea din da ta shigo dashi. 

Ajiyar zuciya ta d’an sauk’e, kana cikin sanyi tace.

“To bari naje na d’auko wani cup, saina had’a maka empty din.” 

Ta k’are maganan tana me mik’ewa tsaye,batare kuma da ta jira wani abuba kaitsaye ta fice daga Cikin d’akin.

Direct falon nasa ta dawo, harta kawo bakin kofar fita daga falonne kuma sai ta hango, kofar dake gefe da dining area d’insa,  da dukkan alama kuma nanne kofar kitchine din dake Cikin falon nasa.

Ahankali ta k’arasa jikin kofar tare da turawa ta kutsa kanta ciki.

Idanunta tad’an ware saboda ganin yanda kitchine din nasan ya tsaru, da komai na zamani, domin wani irin kitchine carbinet akayi na musamman acikinsa, ga kuma plates da cups hadi da sauran kayan aiki masu kyau kana Kitchen din nada girma ga kuma kofar store ta ciki.

Jinjina kanta tayi saboda yanda ta yaba da kyawun kitchine din.

Wani cup ta d’auka tare da k’arasawa gaban sink ta wankesa.

Juyowa tayi Anutse ta dawo cikin d’akin.

Yana nan zaune a inda ta barsa dan ko motsawa baiyi ba, saidai idanunsa daya sake lumshewa.

A ranta tace.

“Ga kafiya faɗa ga kuma raki da sakalci”.

D’an durk’usawa tayi, agaban stull din tare da d’aukan lipton ta saka acikin cup din, sai kuma k’wayan shugar guda hud’u da ta d’auka acikin k’wali, bayan ta saka shugar’n ne kuma ta saka ganyen lemongrass leaves wanda already dama tazo dashi akan tray din, murfin flask ta bud’e tare da zuba ruwan zafi acikin cup din,  kana tasa cokali tadan jujjuya.

Ganin sugar din ya narke ne kuma yasa ta, d’ago cup din tare da mik’a masa cikin kulawa tace.

“Gashi.”

“Ki ajiye.”

Yafad’a agajarce tare kuma da gyara zamansa,  wanda kuma daga yanayin maganarsa kad’ai zaka fahimci cewar bayajin dadin komai. 

Ajiye cup din tayi agefensa kamar yanda ya fad’a. Cikin nutsuwa kuma ta mik’e tsaye, tare da d’aukan tray din.

Ahankali batare kuma da ta sake ce masa komai ba, ta juya ta fice daga cikin dakin, tare da mayar masa da kofar ta rufe. 

Kaitsaye k’asa ta nufa.

Shikuwa Rayyern jin alamun fitanta ne yasa shi sake lumshe idanunsa.

Ahankali ta gama sauk’owa daga kan steps din.

 Ganin babu kowa acikin main falon ne kuma yasa kaitsaye ta wuce kitchine.

Dan aciki ne takejin motsin Mamy.

Tana shiga kuwa ta samu Mamyn nata aikace aikace.

“Sannu da aiki Mamy.”

Ta fad’a tana me ajiye tray din dake hannunta.

Mamy kuwa jin muryar Jannart abayanta ne yasakata sakin murmushi, cike kuma dajin dadin d’an jimawan da taga Jannart din tayi a sashin Rayyern din tace.

“Yauwa sannu dai Jannart.”

K’asa Jannart din ta d’anyi da kanta, kana anutse tazo kusa da Mamyn tare da k’arb’an aikin da Mamyn keyi ta soma Taya ta.

Hakan yasa cikin yan mintuna suka kammala had’a komai na breakfast.

Bayan sun zuba komai acikin food flask ne kuma, Jannart takai kulolin kan dining Table.

Mamy kuwa na Abba ta d’auka takai masa zuwa part d’insa.

Dai-dai lokacinne kuma Ramadan da Riyyam nsra suka shigo.

Jannart dince ta bawa Riyyam nsra food flask din su Baba Maud’o ya Kai musu.

Koda ya dawo kuwa anan falon suka zauna su dukansu, atare sukayi breakfast, inda suna cin abincin Riyyam-nsra nata zuba musu surutu, wanda kuma bashi da wani labari saina y’an tiktok.

Suna ahaka ne kuma Dr. Sulaiman da kuma Baba Maud’o suka shigo cikin falon. 

Fuska d’auke da fara’a suka gaisa, dasu Mamy dai-dai lokacin kuwa Abba ma ya fito daga nan part d’insa. 

Bayan Abban sun gaisa da Dr. Sulaiman ne kuma yayi musu jagora zuwa sama. 

Ahankali Abba ya tura kofar dakin Rayyern din ya shiga bakinsa dauke da sallama,  Yayinda su Baba Maud’o ke biye dashi abaya.

Rayyern dake dan kishingid’e kuwa jin muryar Abban nasa ne, yasa shi dan yunkurawa ya tashi zaune.

Akusa dashi Abba da Baba Maud’o suka zauna, cikin kulawa Baba Maud’o yace.

“Rayyern ya jikin naka?”

Murmushin karfin hali ya d’anyi, tare da gyara zamansa, kana cikin tausasawa yace.

“Alhamdulillah jiki da sauki Baba Maud’o.”

Kai Abba da Baba Maud’o suka jinjina, cikin kuma danjin dadi suka had’a baki wajen cewa.

“Allah ya baka lafiya.”

Da “Ameen.” ya amsa.

Inda Dr. Sulaiman kuwa ya zauna akan bedside drawer, cikin nuna  kulawa ga abokin nasa yace.

“Sannu Dr Rayyern ya jikin naka? da Fatan ka d’anji k’arfin jiki.”

Idanunsa ya d’an lumshe kana Ahankali yace.

“Alhamdulillah, nasan komai zai dawo dai-dai soon.”

“Insha Allah, amma fa kasan dole saika dage, musamman wajen cin abinci, domin yanzu  ma haka akwai magungunan dana kawo ma, amma dole sai kaci abinci kafun kasha su.”

Cewar Dr. Sulaiman yana me fito da wasu magunguna daga aljihunsa. 

Rayyern kuwa Ganin magungunan ne yasa shi d’an yamutse fuska, tare da komar da kansa ya kwanta. 

Sanin da sukayi cewa Koda lafiyarsa, bayason yawan surutu, bare kuma yanzu da bashi da cikakken lafiya ne, yasa su mik’ewa tare dayi masa Allah ya sauwake,  kana duk suka fice daga cikin dakin, Dan ayanayin da suka gansa kamar ma bacci yakeson yi. 

Atare suka sauk’o k’asa dukansu.

Anan cikin falon suka zauna, inda Dr Sulaiman ya d’ago kansa ya kalli Mamy.

Cikin girmamawa yace.

“Mamy akwai wasu magunguna dana kawowa Rayyern, To amma kuma dole akwai buk’atar sai yaci abinci kafun yasha su, saidai kuma  na lura kwata kwata Rayyern bayason cin abinci.”

Ajiyar zuciya Mamy ta sauk’e, cikin kuma yanayin sanyi tace.

“To ya zamuyi Sulaiman, kafasan halin Rayyern komai nasa dabanne dana kowa, amma Insha Allah Zamuna kokari akan cin abincinsa.” 

Kai Dr Sulaiman din ya jinjina, domin kuwa yasan halin Rayyern din Sarai.

Jannart kuwa dake zaune anan dining table din, ahankali ta ajiye spoon din dake hannunta, tare kuma da d’aukan tissue ta goge bakinta.

Ganin alaman ta kammala cin abincin ne kuma yasa Mamy, kallonta cikin kulawa tace.

“Yauwa Jannart tunda kin kammala cin abincin naki, ga food flask nan d’auka  ki kaiwa Rayyern nasa abincin, ki kula dan Allah ki sashi ya d’anci ko kad’anne, sai ki bashi magungunan kinji.”

Mamyn ta k’are maganan cikin sigar kulawan, da tasaka Jannart yin kasa da Kanta.

Ahankali kuma Cikin nutsuwa tace.

“To Mamy.”

Mik’ewa tsaye tayi, tare da gyara mayafin dake jikinta, kana ta d’auki d’an tray ta saka food flask da kuma cups, din da aka gama had’a masa duk breakfast din nasa aciki.

Cikin nutsuwa da kuma d’abi’arta na hankali kaitsaye ta nufi saman.

  Ganin tafiyan Jannart dinne kuma, yasa Ramadan d’an gyara zamansa, tare da fuskantar su Abban nasa, cikin tausasawa da kuma yanda yasan zasu fahimcesa yace.

“Alhamdulillah wannan karon ba ayiwa Hamma Rayyern allura ba, saboda likitotin China sun sanja masa magani, wanda iya maganin ya wadatar basai an had’a masa da wannan, alluran mai matukar kashe jikin ba, sun kuma ce typhoid ne ke causing stomach pain din nasa, wanda kuma dama tuntuni munsan cewa akwai cronic typhoid ajikinsa, wanda ayanzu harya fara tab’a masa hanjinsa, shiyasa ma yake yawan sa masa ciwon ciki, amma yanzu likitotin can din sun bamu magunguna wanda, zasu na taimakawa wajen wanke masa hanjin nasa, dama kashe duk wata cuta dake cikinsa,

shiyasa ma suka sallamemu, amma hakan fa bawai yana nufin shikenan bane, sunce akwai yiwuwar dole za’ayi masa aiki, amma Idan anyi dace, magungunan zasu iya wanke duk wani cuta dake damunsa, Insha Allah zai samu sauki, akwai watarana na zuwa da Hamma Rayyern zaiyi bankwana, da wannan ciwon bazai sakeyi ba da Yardar Allah.”

Ajiyar zuciya duk su Abba da Baba Maud’on suka sauk’e,  saboda bayanin da Ramadan din yayi musu, yasa sun samu gamsuwa sosai.

Cikin samun nutsuwar zuciya Abba yace.

“Allah yasa Ramadan, Allah Ubangiji ya yayewa Rayyern wannan ciwon, Insha Allah ma basai anyi masa aikin ba nasan zai warke, ai waraka ta Allah ce.”

“Sosai kuwa, da yardar mai duka watarana komai zai wuce, Allah dai ya yaye masa.”

Cewar Baba Maud’o.

Da “Ameen.” Duk suka amsa.

Inda Ramadan kuwa ya gyara zamansa, tare da sake Kallon su Abban nasa murya araunace yace.

“Amma Abba fa Doctors din sun tabbatar mana cewar, harda yawan shan zak’in da yake ma, domin shi zaki kana shansa yana taruwa maka aciki ne, bazai tashi yi maka illa ba kuwa, sai ya samu wani ciwon dazai tashi maka, zai iya had’ewa da wannan ciwon ya cutar dakai, batare da kasan da hakan ba,  kuma shi kansa Hamma Rayyern ya sani, amma bansan yaushe ne Hamma Rayyern zai sanja ba, bansan yaushe ne zai daina maida abun zaki abun sonsa ba.” 

Shiru duk su Abban sukayi saboda acikinsu babu wanda baisan halin Rayyern dason zaki ba sai dai sun sani laifinsune sune suka rainesa da zaƙin dan yawan soyyaya.

Saidai Abba ya kud’urtawa ransa cewar.

“Insha Allah zai dage tukuru wajen ganin ya raba Rayyern din, da yawan shan zakin da yakeyi.” 

Haka dai suka d’an tattauna, kafun daga bisani Abba da Baba Maud’o suka fice, haka shima Dr  Sulaiman.

Acan b’angaren Jannart kuwa ahankali, ta murd’a handle din kofar ta shiga bakinta d’auke da sallama.

Kwance yake akan lallausan gadonsa, Yayinda yayi kwanciyarnan irin ta rub da ciki.

Jin sautin muryarta ne kuma yasa shi, lumshe idanunsa dake bud’e. 

Ita kuwa Jannart k’arasa shigowa cikin d’akin tayi, tare da  ajiye tray din dake hannunta.

D’an Kallon yanda ya bawa kofar shigowa dakin baya tayi, cikin sanyi da kuma tausasa murya tace.

“Ga abincinka nan.”

“Nak’oshi.”

Ya fad’a atakaice saboda ayanzun Sam bayason takura.  

“Katashi kaci abinci inji likita.”   

Jannart din ta fad’a tana me bud’e food flask din, tare da d’aukan spoon ta zuba Coastarian breakfast dish din, gyara zaman plate din akan table tayi, tare da d’ago da Kanta ta kalleshi.

“Please ka tashi, Mamy ne tace kaci abinci sai kasha magani kaji ko.”

Tayi maganan cikin sanyin murya, da kuma zallan yanayin shagwab’an da ita kanta batasan tayi sa ba.

Idanunsa ya d’an rumtse ahankali, tare kuma da sa hannayensa duka biyu, ya sake matse pillow’n dake kirjinsa. 

Kwata-kwata bayason yawan damuwa, bawai kuma dan bayajin yunwa ba, no kawai dai bayason yaga Jannart din akusa dashi har haka ne, musamman ayanzu daya fahimci wani abu, adangane da ita, shine tana da wani special Mood wanda yafahimci ita kanta batasan tana dashi ba tana kuwa yiwa zuciyarsa raraka.

Sake gyara kwanciyarsa yayi, cikin kuma nuna halin ko inkula yace.

“Kije zanci.” 

Idanunta ta d’an zubawa faffadan bayansa, tare da kama waist dinta ta rik’e, dama tasan halinsa, ta kuma san cewar bazai tab’a daina wa ba.

“Nifa bawai na wani damu dakai bane, Dan kawai kaga Ina baka attention dina, saboda baka da lafiya ne kawai Malam, baya ga haka me mazaisa nazo wajenka.”

Ta fad’i hakan acikin zuciyarta, tare kuma da murgud’a bakinta gefe.

“Da kika tsuramin ido haka wani abu ne zaki bani? Ko cinyeni danye zakiyi!?” 

Rayyern din ya fad’a, batare daya juyo ba.

Saurin kawar da kanta gefe tayi, tare da turo dan karamin bakinta gaba, cikin yanayin Mood din shagwab’a tace.

“Ni ai ba kallonka nake ba kuma ba kai nake kalloba”.

A hankali yace.

“Toh wa kike kallo”.

Baki ta ɗan turo.

“Ni babu”.

Dan gajeren tsaki yaja tare da cewa.

“Mayya”.

Yayi mgnar a hankali so batajiba.

Sai ta d’an kwab’e fuska tare da cewa.   

“Kuma ni Mamy ce ta aikoni, Dan Allah katashi mana katashi ka tashhhhhi….”

Ta kare maganar tana slowdown da muryarta.

Hakan kuwa shiya sanya, Rayyern din d’an juyowa akaron farko ya kalleta.

Karab kuwa kyawawan idanunsu suka had’e acikin na juna, da sauri Jannart din ta kawar da kanta gefe. 

Shidinma kuma janye kallonsa daga gareta yayi, inda ya sauke ganinsa akan Coastarian breakfast dish din.

Idanunsa ya d’an lumshe akasalance, kuma cikin muryarsa da tayi sanyi yace.

“Give me the water.” 

Kallon d’an madaidacin bakinsa dake motsawa tayi, sai kuma Ta kau da kanta, tare da rusunawa ta zuba masa ruwan swan acikin cup.

Mik’a masa ruwan tayi.

Ganin hakanne kuma yasa shi d’an yunk’urowa ya zauna. 

Karb’an cup din ruwan yayi, tare dayi masa kurb’i d’aya ya ajiye. 

Kyawawan yatsun k’afarta ya zubawa ido, cikin sauk’e numfashi yace.

“Naji zanci amma ki tafi, nima zan iyaci da kaina, banason abunda za’amin wanda baikai zuci ba, dan ni bana son abun zuciya biyu da manufa.”

Ya k’are maganar still yana me Kallon yatsun k’afar nata.

Idanu Jannart din ta d’an tsura masa, saboda har yanzu tana mamakin wasu kalamai da yake yawan jifanta dasu, wanda batasan me hakan suke nufi ba ta dai fahimci tabbas bai yarda da ita bane zarginta yakeyi.

Pink lips dinta ta d’an turo, tare da soma motsasu tana mamul mamul dasu, tamkar dai Wacce takeson fad’an wani abu.

Lips din nata ya kalla, ganin yanda suke motsawa ne kuma yasa shi kauda kansa gefe.

“Da wani k’aramin bakinta kamar na tsuntsu.” 

Ya fad’i hakan acikin zuciyarsa, Yayinda afili kuwa idanunsa ya lumshe tare da cewa.

“Zagina kikeyi ko?”.

Da sauri ta zaro ido tare da cewa.

“Ni dai a’a”.

Kana ta juya, tana me wasa da y’an yatsun hannunta ta nufi hanyar fita daga cikin dakin. 

Har takai bakin k’ofar d’akin nasa kuma saita tsaya tare da juyowa,  cikin sanyi da kuma muryar dake nuna lallashi tace.

“Kaci abincin dan Allah sai kasha magani.”

Batare kuma da ta jira abunda zaice dinba ta fice daga cikin dakin tana mgnar zuci.

“Sherri kayan kolba, wannan ai yafi Yah Junaid neman sababi da hujja wai na zageshi”.

Bayanta yabi da kallo harta fice din.

Idonsa ya lumshe tare da sauke wani irin sassayan numfashi,

Kana a hankali ya buɗe su,

Anutse ya jawo plate din abincin, cikin sanyi da kuma yanayi irin na marassa lafiya, ya soma dan tsakalan abincin.

Baiwani ci sosai ba kuma ya ture plate din gefe, tare da d’aukan tea yasha,  bayan yasha tea dinne kuma ya b’alli magungunansa yasha.

Yanasha kuwa ya koma ya kwanta.

Jannart kuwa Koda ta sauk’a k’asa, Bata samu Mamy ba, Riyyam nsra kawai ta samu, da shidinne kuma suka sha hira, kafun daga bisani kowannensu ya tashi ya tafi.

Alhamdulillah yau kwanan su Rayyern, uku da dawowa daga China, Masha Allah kuma ciwon cikin nasa yayi sauki sosai, saidai jikin nasa ne baigama samun karfi ba, har yanzu.

Kulawa kuwa yana samunshi sosai daga wajen ahalin nasa, Abba, Baba Maud’o, Mamy, Ramadan Riyyam, da kuma Dr. Sulaeman harma da Usman P.A duk suna iyaka kokarinsu wajen bashi kulawa, saidai kuma har yanzu bai iyacin abinci sosai.

Wanda kuma hakan al’adarsa ce ta tuntuni.

Yau ne kuma Barrister Kabir da kuma Dr Sajo suka shirya musamman dan zuwa duba Rayyern din. 

Koda suka Iso gidan tarba na musamman, Abba da Mamy sukayi musu, bayan sun gaisa dasu Mamy da Jannart ne, Abba yayi musu jagora zuwa  part din Rayyern din.

Koda sukaje akwance suka iske shi, duk da cewar bayajin karfin jikinsa, amma daya gansu ya d’an sake sunyi hira. 

Yanzun kuma saukowarsu k’asa kenan.

Dr Sajo ne ya kalli Abba, cikin kulawa yace.

“Amma Alhaji Bashir me zai hana baza’a sake maida Rayyern din, hospital ba tunda naga har yanzu jikin nasa bawani karfi sosai.”

Mamy dake zaune acikin falonne, ta d’an gyara zamanta, tare da fuskantar Dr Sajon, cikin bayyana damuwarta tace.

“Ai bawai wani abune matsalar ba, bayason cin abinci ne kwata kwata, komai aka basa sai yace a’a, Koda an matsa masa kuwa, bai wuce yayi loma biyu ko uku ba, sai yace ya koshi, bashi da wani abinci sai tea, nan ma yanzu ne yake d’an shan tea din da madara, da bayason ko madaran saidai empty, shiyasa bayi da karfin jiki.”

Kai Dr Sajo ya jinjina, cikin gamsuwa yace.

“Eh to kin san dama duk inda dan adam yayi ciwo abinci yake fara tsana.

Tabbas kuwa bazai samu wadataccen karfin jiki ba, harsai in ya dage da cin abinci, amma ana tambayansa ko yana da buk’atar wani abu, sai anayi masa.”

“To.”

Mamyn tace.

Yayinda Abba kuwa cewa yayi.

“Idan naga abun nasa yaki karewa ai, dolensa na daukesa na maidashi hospital, yasan duk wani illar rashin cin abinci, amatsayinsa na Dr amma baya kiyayewa.”

“Hakane kam sai hakuri da majinyaci, Allah dai ya bashi lafiya.”

Cewar Barrister Kabir.

Da “Ameen.” Duk suka amsa.

Basu wani jima ba kuma, Abba yayi musu rakiya suka tafi.

Bayan suntafi dinne kuma Mamy ta haura saman.

Azaune tasa meshi yasaka Laptop d’insa agaba, yana Dan lallatsata.

“Rayyern.”

Mamy takira sunansa da kulawa.

Jin sautin muryar Mamyn nasa ne kuma yasashi d’ago kansa Ahankali ya kalleta.

“Na’am Mamy.”

Ya amsa adan kasalance.

Karasa shigowa cikin dakin Mamyn tayi, tare da matsowa kusa dashi, cikin kulawa da kuma nuna tausayawa agareshi tace.

“Meyasa ne haka Babana? Meyasa kwata kwata bakason cin abinci? kasani fa bazaka samu isashshen karfi ba, har sai inkana cin abinci, yanzu fad’amin mekakeson ci, ko meye saina dafa maka.”

Fuskarsa yad’an kwabe tare da marairaicewa.

Cikin yanayin sakalci yace.

“Nifa Mamy bana sha’awan komai, kawai dai abincin yanzunne baya min, nafison abu me d’an melting da kuma tsami, like Chinese dishes dai, ko Mamy amin irin kunun ranan.” 

Ya k’are maganan yana langwabar da kansa gefe.

Murmushi Mamy tayi tare da cewa.

“To za’ayi maka kunun kaji kada ka damu.”  

Mamyn ta fad’a tare da juyawa ta fice daga cikin dakin.

Direct kasa Mamyn ta sauk’o, inda ta samu Jannart ta gaya mata, cewar Rayyern yana son ayi masa irin kunun ranar.

“To.” Jannart din tace, babu musu kuwa ta wuce kitchine, Anutse ta soma had’a kunun kamar yanda ya buk’ata.

Tsab ta gama had’a kunun, da yayi kyau sai tashin kamshi yake, juye kunun acikin flask tayi, tare da daura flask din akan tray ta daura cups agefe, sai kuma madara da zuma wanda suke cikin wani abu mai kaman glass. 

Fitowa falo tayi rike da tray din ahannunta.

Mamy dake zaune afalon kuwa Ganin Jannart din harta kammala ne yasa, cikin jin dadi tace.

“Masha Allah Jannart har kin kammala, Allah Dai yayi miki albarka, ki kai masa nasan yana nan yana jira.”

Murmushi Jannart din tayi, tare kuma da dan sunkuyar da kanta, cikin nutsuwa ta nufi saman.

Tafiya take Ahankali, Yayinda tayi kyau cikin riga da wandon pallazon dake jikinta, wanda ta yafa mayafi. Dan babba akan shigar nata, saidai duk da hakan ga wanda yayi mata Kallon k’urulla, tsab zai iya hango tsararren cikakken hips dinta.

Ga kuma rigar shirt din da yayi mata cibcib ajikinta, cikin tan nan alafe yake, tamkar babu hanji acikinsa.

Karasowa bakin kofar falon nasa da tayi ne kuma yasa ta, tura kofar ahankali, bakinta dauke da sallama ta kutsa kanta ciki.

Babu kowa acikin falon hakane yasa ta nufi, Bedroom nashi,

a hankali ta tura ƙofar tare da sallama a bakinta.

Still nan ɗin ma babu shi,

Cikin mamaki ta ɗan ware idanunta tare da jujjuya kanta, tana mai kasa kunne wai ko zata jiyo mostinsa a Bathroom,

jin shirune ba motsin komai, harta nufi kofar dakin dan fitowa falon nasa ne kuma, saita hangosa zaune acikin wani balcony wanda labulayensa keta kaduwa saboda iska. 

Kaitsaye wajen ta nufa tana isa wajen kuwa, idanunta suka sauka akansa.

Da sauri tayi kasa da kanta, saboda ganinsa ahaka da tayi,  domin yau dinma ba wani kayan kirki bane ajikinsa, singlet ne da kuma gajeren wando. 

Shikuwa Rayyern jin sallamanta ne yasashi dago kansa, ya sauke idanunsa akanta.

Tashin farko kuwa idanunsa suka sauka, akan lafaffen cikinta, wanda ta daure kasansa da adon igiyan wandon dake jikinta.

Janye idanunsa yayi daga Kallon nata, tare da maida kallonsa gefe.

Anutse ta karasa isowa inda yake, tare da Dan dukawa ta ajiye tray din dake hannunta.  

Cup ta d’auka tare da zuba masa kunun, kana ta saka masa madara da zuma aciki.

D’an d’agowa da kanta tayi, hade da mik’a masa cup din.

Cikin sanyi tace.

“Gashi.”   

Tayi maganan tana me sauke idanunta, akan lallausan beard d’insa. Wanda yake matukar yi mata kyau.      

Ahankali ya juyo da kallonsa zuwa gareta,  lokaci daya kuma ya sauke idanunsa akan kyakkyawar fuskarta, da kuma dan karamin lips dinta, dake shining din lipgloss.

Hannunsa yasa ya karb’i cup din, Ahankali kuma ya dan motsa lips d’insa,  saidai kuma ita kanta bataji mai ya fad’a ba.

Kan Wani had’add’en rug dake gefensa ta zauna, tare kuma da rike flask din ahannunta. 

Saurin kallonta yayi, saboda baiyi tunanin zama zatayi ba, kamar zaice wani abu kuma sai ya fasa,Ahankali kuma ya janye idanunsa da suka sauka akan waist dinta. 

Cikin nutsuwa ya soma sipping kunun, yana me lumshe idanunsa saboda yanda yakejin dadin kunun.

Itakuwa Jannart gaba daya kallonta ta mayar k’asa, inda take hango Riyyam-nsra da Baba Maud’o wayanda suke zaune abakin gate.

Kallonsu takeyi sosai, musamman ayanzu da taga Riyyam din na waya,  ba tare da taga ya jima yana wayan ba kuma ya mikawa Baba Maud’o.

Hannayenta duka biyu ta had’e tana kallonsu.

Yayinda acan kasan kuwa.

Mammy ce takira tana tambayan Riyyam din jikin Rayyern . 

Nan Riyyam din yake shaida mata cewar jikin da sauki,  Koda ta nemi ta gaisa da Rayyern dinne kuma, Riyyam yake sanar mata cewa, baya kusa da Hamma Rayyern din,  ananne kuma Riyyam din yace.

“Mammy  Ina tare da Baba Maud’o bari na bashi ku gaisa.”

“To.” Mammyn tace.

Yayinda Riyyam-nsra kuwa ya mikawa Baba Maud’o wayar.

Karb’an wayan Baba Maud’o yayi tare kuma da karata akan kunnensa, Cikin nutsuwa yace.

“Assalamu Alaikum.”

Acan Ethiopian kuwa Mammy dake zaune akan kujera, Jin amo da kuma sautin muryar daya daki dodon kunnenta ne, yasa taji zuciyarta tayi wani irin bugawa, take kuma tsikar jikinta suka shiga wani irin mimmikewa, cikin wani irin yanayi ta mik’e tsaye, tare da sake sauraran muryar dake kan wayar.

“Assalamu Alaikum.”

Baba Maud’o ya sake maimaita sallaman nasan, saboda Jin shiru da yayi.

Komawa Mamyn tayi ta zauna, tare kuma da sanya hannu ta dafe kirjinta, cikin rawar murya tace.

“Wa’alaikassama.”

Zumbur haka Baba Maud’o ya mik’e tsaye daga zaunen da yake, tare kuma da d’an zazzaro idanunsa waje,  lokaci daya wani irin yanayi ya bayyana atattare da Baba Maud’on.

Wanda hakan yasa Riyyam dake zaune kallon Baba Maud’on, Cikin yanayin mamaki yace.

“Baba Maud’o lafiya?”

Kallonsa Baba Maud’on yayi, tare kuma da komawa Ahankali ya zauna, saidai kuma har yanzu jikinsa bai daina tsuma ba.

Daga can b’angaren kuwa cikin rawar murya Mammy tace.

“Ina wuni, ya maijiki?”

Hannu Baba Maud’on ya d’an dunkule cikin wani irin abu dake dukan zuciyarsa yace.

“Lafiya mai jiki kuma Alhamdulillah.” 

“Masha Allah Allah ya kara sauki, mungode sosai Baba Maud’o nasan kuna nan kuna fama da rigiman Riyyam, Allah ya bada lada.”

Mammyn ta fad’a cikin sanyin murya. 

Baba Maud’o kuwa murmushi ya aro ya sakawa muryarsa, kana shima cikin sanyi yace.

“Ameen summa Ameen, ai Riyyam kam babu wani rigiman da yake yi mana, harma mun saba dashi kwannan yana ta cewa kin matsa ya komo mu kuma bamu son rabuwa dashi.”

Murmushi Mammyn tayi, cikin kuma karfin hali da danne bugun zuciyar da takeji, tace.

“Shikenan to Baba Maud’o ahuta gajiya.”

“Yauwa.”

Baba Maud’on ya amsa, tare da zare wayar akan kunnensa, cikin sanyi da kuma wani irin tunani dake dukan, kwakwalwarsa ya mikawa Riyyam nsra wayan. 

Karb’an wayan Riyyam-nsra yayi tare da Karawa akan kunnensa.

Jin muryar Riyyam dinne kuma yasa, Mammy sauke wani irin nannauyar Ajiyar zuciya.

Cikin sanyi tace.

“Riyyam ka had’ani video call da Rayyern, inason naga ya yanayin jikin nasa.”

“To Mammy zan hadaku amma maybe sai gobe, saboda nasan yanzu haka yana sama, kuma Idan magriba ta kusa bayason yawan magana.”

Riyyam din ya fada atausashe.

Daga can b’angaren kuwa Kai Mammy ta jinjina, tare da cewa.

“Shikenan to badamuwa Allah ya kaimu goben.”

“Ameen”

Riyyam din ya amsa kana sukayi sallama da Mamyn.

Duk abunnan da sukeyi kuwa Jannart na kallonsu, saboda gaba daya hankalinta ya tafi garesu ne ma, yasa har yanzun take nan bata tafi ba.

Shikuwa Rayyern tuni ya shanye kunun da ta zuba masa din tas.

 Ganin bata da niyan kara masa ne kuma yasa shi, dagowa ya kalleta.

Akaron farko kenan daya tsaya ya k’are mata kallo,  idanunsa ya dan tsayar akan fuskarta, saboda yanda yaga hankalinta ya tafi izuwa wani waje na daban.

Ajiye cup din dake hannun nasa yayi,  Karan ajiye cup dinnasa ne kuma yasa hankalinta dawowa garesa. 

Ahankali ta juyo da kanta zuwa garesa, karab kuwa idanunsu suka sarke acikin na juna.

Sunkuyar da kanta k’asa tayi, tare da sauke numfashi, cikin silent voice dinta tace.

“Nak’ara maka ne?”

Kansa ya d’an girgiza mata, tare da lumshe idanunsa, cikin wani irin yanayin daya saka zuciyarta harbawa yace.

“Um um nakoshi.” yayi  mgnar yana jin dadi bakinsa yayi masa wasai yawunsa ya sinke alamar dandanon bakinsa zai dawo.

Kallonsa tayi, haka kuma shid’inma.

Kasa tayi da Idanunta tare da matsowa ta durk’usa, tray din ta ke kokarin dauka.

Dan kusancin da sukayi ne kuma yasa, daddad’an kamshin turarenta ratsa cikin hancinsa. 

Idanunsa ya dan lumshe, Yayinda itakuwa tray din ta dauka Anutse ta juya ta tafi. 

Kaitsaye kasa ta sauka, bayan takai kayan kitchine ne kuma ta wuce dakinta. 

Shikuwa Rayyern kiran Sallan magriba ne ya tadashi awajen.

Washegari.

Yau dinma kunun da Jannart din tayi masa jiya ya kuma sha, sai kuma abu mai romo da Mamy tasa ta dafa masa, babu laifi kuma  yaci sosai.

After 3days.

Mamy ce tsaye agefensa, Yayinda shikuwa ke zaune akan daya daga cikin kujerun falon. 

Murmushi Mamyn tayi tare da dubansa cikin danjin dadi.

Tace.

“Masha Allah Babana Lallai jiki yayi sauki, tunda har ka iya fitowa  falo.”

Murmushi ya d’anyi tare da Kallon Mamyn nasa, cikin sanyi yace.

“Mamy yunwa nakeji sosai, kuma nafison abu mai dan tsami, please Mamy roasted fish da ruwan lemon tsami nakeso, ko kuma miyan da akayi ranan nan pls Mamy.”

Murmushi Mamyn tayi tare da cewa.

“To Rayyern amma ni bansan yanda akeyin miyan ba, rannan ma bani nayi ba Jannart ce tayi, amma bari na turo maka ita saikayi mata bayani.”

Fuskarsa yadan kwabe cikin shagwaba yace.

“Eyyah Mamy kifada mata mana, dole sai ni?”

“Eh mana bakaine kakeso ba.”

Mamyn ta fad’a tana me nufar dakin Jannart.

Ramadan dake zaune agefe kuwa, Kallon Hamman nasa yayi, tare da mik’o masa magungunan daya b’are.

Cikin kulawa yace.

“Please Hamma Rayyern karb’a maganinka kasha.”

Fuskarsa yadan yamutsa, kamar zaice a’a sai kuma ya karba yasha.

Bayan yasha maganin ne kuma Ramadan ya Mike ya tafi, domin dama hospital zai tafi, ya tsaya bawa Hamman nasa maganine.

Already Abba kuma dama ya tafi company, Riyyam-nsra kuwa yana waje .

Jannart kuwa dake falon ta zaune take, inda tayi kyau cikin wani fitted gown na maroon lace dake jikinta, sosai rigar tabi jikinta ta zauna, saboda yanda dinkin ya fita sosai.

Bak’aramin kyau yau Jannart din tayi ba, musamman da ta watsa jelan  gashinta haka bata kitseshiba, tare dasa dan siririn mayafi daga kanta zuwa kirjinta.

Shigowar Mamy ne kuma yasa ta d’agowa, fuskarta dauke da murmushi.

Itama Mamyn murmushi tayi, tare kuma da Kallon Jannart din Cikin kulawa tace.

“Jannart kije mijinki yana kiranki.”

Kai Jannart din ta d’an sunkuyar kasa, cikin sanyi kuma tace.

“To.”

Juyawa Mamyn tayi ta tafi, Ganin hakanne kuma yasa Jannart din mikewa, Cikin yanayin nutsuwarta ta nufi part din nasa.

Ahankali ta murd’a handle din kofar ta shiga, bakinta dauke da sallama.

Saidai kuma dan ja baya tayi, ganinsa da tayi yana waya, hakan yasa ta matsawa jikin kujera ta d’an zauna, wanda hakan yasa suka zama suna fuskantar juna.

Ahankali ta dan saci kallonsa, musamman yanda taga yayi kyau cikin shigar riga da wandon DG dake jikinsa. 

Ahankali ya ajiye wayar tare da d’ago kansa ya kalleta.

K’asa tayi da Idanunta, cikin sanyi tace.

“Ina kwana.”

Idanunsa ya sauke akan labbanta zuwa kan kirjinta, wanda dinkin jikin nata ya masifar fitar da shape din samansu.

Kauda kansa yayi batare da ya iya amsa mata ba

Itakuwa Jannart jin bai amsa mata dinbane yasa ta cewa.

“Ya jiki.”

“Da sauki.”

Ya amsa mata da wani irin murya, wanda yasa ta dago ta kalleshi.

Ahankali kuma tace.

“Gani Mamy tace kana kira na.”

Idanunsa ya dan marairaice cikin sanyin murya mai hade da zallan shagwab’a yace.

“Yunwa nakeji sosai, kibani abinci, but mai dan tsami kawai kinji….”

Yaja maganar tasa cikin wani irin yanayi, tare dasa hannunsa ya shafa cikinsa. 

Hakan kuwa shiya sanya Jannart ta d’ago Kai ta kalleshi, lokaci daya kuma taji wani irin tausayinsa ya cika mata zuciya. 

Ahankali Cikin yanayin ta itama dake kama da shagwab’a tace.

“To meye kakeso? Miya ko kuma abinci?.”

Idanunsa dake lumshewa ya rufe, tare da bud’e labb’an sa ahankali yace.

“I don’t know kimin komai kawai, ko miyan da kika tab’ayi ranan mai ɗan sami.”

“To.” Tace asanyaye tare da juyawa ta nufi hanyar fita. 

Koda ta fito daga dakin nasa, Anutse ta soma sauka daga kan steps din.

Dai-dai lokacin kuma Riyyam-nsra yake haurowa saman, hannunsa rike da waya.

Ganin Jannart dinne kuma yasa shi sakin murmushi, Cikin kulawa yace.

“Good morning My Aunty ya jikin Hamma Rayyern.”

Murmushi tayi tare da dubansa, cikin sakin fuska tace.

“Jikinsa da sauki Riyyam, yanzu ma na sameshi afalo.”

Murmushi Riyyam din yayi tare da cewa.

“Masha Allah, bari naje na sameshi.”

 

Riyyam din ya fada, Yayinda ita kuwa Jannart kaitsaye kasa ta wuce, inda ta nufi kitchine Dan fara had’a masa abunda zaici.

Riyyam kuwa direct falon ya wuce, yana zuwa zuwa kuwa ya zauna akusa da Hamman nasa.

Tare da dan rankwafar dakai cikin sanyi, yace.

“Hamma Rayyern Mammy tanason yin magana dakai, tace kuyi video call saboda taga ya jikin naka, na kirata please?”

Idanunsa ya dan lumshe, akasalance kuma ya d’an gyad’awa Riyyam din Kai alaman “Eh.” 

Murmushi Riyyam din yayi cikin, Jin dadi kuma ya zaro wayartasa tare da dannawa numbern Mammy kira video call.

Ring kadan kuwa wayar tayi Mammy ta d’aga.

Tana d’agawa kuwa Riyyam yayi murmushi, tare da Kallon Mammyn nasa Cikin kulawa yace.

“Mammyna Barka da safiya, ga Hamma Rayyern dinnan ku gaisa.”

Ya k’are maganan yana me mik’awa Rayyern din wayar. 

Kasancewar kuma kan Rayyern din yana dan jingine ne yasa, Riyyam cewa.

“Hamma Rayyern ga wayan.”

Ahankali ya d’an juyo tare da kai dubansa ga fuskar wayar, wani irin bugawa yaji zuciyarsa tayi da karfi, wanda hakan ya sashi zabura tare da yunkurawa ya gyara zamansa, inda ya sauke ganinsa akan fuskar…….

Matar da hoton fuskarta ya cika fuskar wayar.

Wani irin harbawa yaji zuciyarsa tayi da karfi, wanda har saida hakan yasa shi zaro idanunsa waje.

Da matukar mamaki yake Kallon fuskar matar, Wacce bata da wata maraba da fuskar Ramadan, domin kuwa tsananin kaman Ramadan daya hango akan fuskarta ne ma, ya sanyashi jin wani irin bugun zuciya. 

Lokaci daya kuma yaji wani irin nauyi, da kuma dattakun matar ya cika idanunsa, Yayinda daga cikin zuciyarsa kuwa, wani irin girma, kima, karamci, martaba da kuma haibar matar ne ke hauhawa cikin duk harbawar da zuciyarsa keyi.

Ganin fuskar matar ne kuma yasa, kowanne kofar gashi dake jikinsa budewa, take yaji wani irin sanyi na ratsa shi tako Ina, Yayinda kuma nutsuwa ke kara saukar masa.

“Mammy Ina kwana!!”

Ya fad’a cikin tausasa murya daga can cikin maƙoshinsa har zuwa kan labbansa.

Daga b’angaren Mammy kuwa da ta tsura masa ido bata ko k’yaftawa, wani irin abu itama takeji acikin zuciya da gangar jikinta, lokaci daya kuma taji zuciyarta tayi rauni sosai, tabbas Kallon fuskar Rayyern din da tayi ayanzu, yana tattare da wasu abubuwa da dama, ciki kuwa harda abunda ke kwance acikin zuciyarta, a mafi rinjayen tsawon shekarun rayuwarta. 

“Lafiya Maud’ona ya jikin ka?”

Mammyn ta tambaya cikin boye rauni, da kuma damuwar dake kwance akan fuskarta yace.

“Alhamdulillah jiki na yayi sauki Mammy.”

Rayyern din ya bata amsa, cikin sanyi da kuma sigar tausasawa.

Riyyam-nsra kuwa dake zaune agefe idanu ya zubawa, Hamma Rayyern din nasa.

Mammy kuwa Daga can b’angaren ta, murmushi ne ya dan bayyana akan fuskarta, cikin tsananin kulawa da kuma muryar tausayawa tace.

“Allah Ubangiji ya karamaka lafiya, ya kareka aduk inda kake, ya tsare gabanka da bayanka, ya kuma nisanta ku da duk wani sharrin mutum da aljan, Allah ya baku zaman lafiya kaida iyalinka, ya albarkaci rayuwarku ya cika haske a rayuwarku Allah yayi maka al’barka!!!.”

“Ameen thumma Ameen Mammy nagode sosai.”

Rayyern din ya fada cikin nuna tsananin jin da d’insa, domin kowacce kalma da Mammyn zata fad’a, jinsa yake yana tasiri acikin zuciyarsa, Yayinda kuma yakejin wani irin farinciki na musamman yana lullub’eshi.

Mammyn ma Ganin farinciki kwance akan fuskarsa ne yasa ta jin dadi aranta, cikin kuma sakin fuska tace.

“Ya Ramadan da Mamyn ku?”

“Lafiyansu kalau Mammy, saidai Ramadan ya tafi wajen aiki, Mamy kuma tana k’asa.”

Ya bawa Mammyn amsa asake, yana mejin Karin nutsuwa na saukar masa sabida mgnar da yakeyi da itan.

“Masha Allah Allah ya taimaka, Ina Surukata Jannart, fatan itama tana lafiya.”

Mammyn ta tambaya da kulawa.

Idanunsa ya d’an lumshe tare kuma da bud’e su alokaci guda, cikin kwarin jikin daya samu yace.

“Lafiya yanzu ta sauk’a k’asa.”

Murmushi Mammy tayi, tare da jinjina kai, cikin farincikin dake da d’a mamaye zuciyarta duk bayan minti guda tace.

“To bari na bawa Zaytoon ku gaisa, gatanan duk ta tsareni da ido.”

Murmushi Rayyern din yayi dai-dai lokacin kuma, Mammyn ta mikawa Zaytoon dake gefen ta wayar.

Karb’an wayar Zayton tayi, tare da fadada fari’ar dake kan fuskarta, cikin muryarta mai dan sanyi tace.

“Hamma Rayyern.”

Saurin d’ago idanunsa yayi, ya kalli kyakkyawar yarinyar da ke magana acikin wayar, wanda muryarta tayi masa sak da wata muryar da yaji kwanannan , idanunsa ya Dan bud’e da kyau, tare kuma  da zaro su waje, badon komai ba kuwa saidan Ganin still kamanin yarinyar sak na Ramadan ga kuma kamannin muryarta da waccar tsohuwar kamar dai yadda kamannin Muryar Ramadan Riyyam-nsra da ita Zayton ɗin a can wani sashin na zuciyarshi kuwa kamarsa da Riyyam-nsra ne ya fado masa “Yah salam”.

Yace a ransa a zahiri kuwa,

Idanu ya dan zubawa yarinyar, har na tsawon minti daya, kafun daga bisani ya fadada fara’ar dake kan fuskarsa, cikin sakewa yace.

“Na’am Zayton.” 

Murmushi Zayton din tayi, kana cikin jin dadi tace.

“Sannu Hamma Rayyern ya jikinka, Ina fatan dai kayi sauki sosai, kuma kana cin abinci sosai ko?.”

Wani irin Murmushi Rayyern din yayi, wanda har saida kyawawan hakoransa  suka bayyana,  tashin farko yaji matashiyar budurwar tashiga ransa sosai.

“Jikina da sauki sosai Zaytoon, amma banason Ina yawan cin abinci saboda kada na zama ɗan lukuti kamarki.” 

Dariya sosai Zaytoon ta kwashe dashi, saboda daga jin yanda yayi maganar ma kasan akwai tsokana aciki.

“Haba Hamma Rayyern ni har wani jiki ne dani, kanaga saboda banida jiki ne ma ai, Riyyam  ya rainani, Hamma Rayyern Ina Auntyna Jannart take?”

Zaytoon din ta tambaya, cike da kulawa.

Murmushi yayi tare da d’an shafa lallausan sumar kansa, cikin muryar tausasawa yace.

“Tana k’asa.”

Kai Zaytoon din ta jinjina, tare kuma da dan rausayar dakai, cikin nuna kulawarta agaresa tace.

“To ka gaishemin da ita kaji, sannan please Hamma Rayyern kana kulawa da kanka kaji, Allah Ya baka lafiya mai amfani.”

Idanunsa ya d’an lumshe tare kuma da sauke Ajiyar zuciya, saboda sosai yaji dadin addu’ar da yarinyar ta masa kana har cikin ransa yake jin sonta a ransa.

Wanda har hakan yasa shi cewa.

“Ameen nagode Zaytoon.”

Kai Zaytoon din ta jinjina, Yayinda shikuwa Rayyern ya mikawa Riyyam nsra dake zaune agefe wayan.

Da sauri Riyyam da zuciyarsa ke cike da farinciki ya karb’i wayan tare da fuskantar screen din wayar, cikin kula dajin dadi  yace.

“Mammyna yau kam kinga Hamma Rayyern dinmu ko.”

Kai Mammyn ta jinjina, cike da jin dadi tace.

“Kwarai kuwa Riyyam yau kam naga Rayyern.”

Tayi maganan cikin kasa da murya, ta yanda Riyyam dinne kadai zai iya Jiyota.

Jin abunda ta fada dinne kuma yasa Riyyam nsra tashi, rike da wayan a hannunsa kaitsaye ya nufi dakin Ramadan.

Shikuwa Rayyern maida kansa jikin kujera yayi, tare da lumshe idanunsa, ahankali yake lumshe idanunsa, yana mejin wani irin nutsuwa na saukar masa.

Mammy da Riyyam kuwa basu wani jima suna magana ba, Mammy ta katse kiran.

Acan Ethiopia kuwa bayan Mammy ta ajiye wayanne, Ta zame daga zaunen da take tare da durk’usawa k’asa tayi sujjada.

Na nunawa Allah tsananin jin dadinta, da kuma godiya agaresa, domin komai da yake faruwa shine ya tsarashi, shine kuma yake bawa ahalinta dama ita kanta kariya akoda yaushe.

Acan b’angaren Jannart kuwa  Anutse ta kammala gasa masa roasted fish, tare da matsa masa ruwan lemon tsami aciki, kamar yanda ya gaya mata yana buk’atar abu mai d’an tsami tsami, bayan ta kammala had’a masa roasted fish dinne kuma, ta soma kokarin yi masa miyan kase kamar yanda ya  buk’ata, saidai kuma kasancewar miyar tana daukan lokaci sosai, shiyasa gama ta ba yanzu yanzu ba.

Rayyern dake zaune afalo kuwa, Ganin almost 1hour ya kare ba akowa masa abincin nasa bane, yasa shi haurawa saman sofa ya kwanta.

Ahankali yake lullumshe idanuwansa, wanda da’alama kuma bacci yakeji, duk da cewar kuma yana jin yunwa, amma hakan baisa baccin yaki daukarsa ba.

Domin yana nan akwance cikin abunda bai wuce 20mn ba, bacci ya d’aukesa, kasancewar acikin magungunan da yake sha akwai mai dan saka yawan bacci. 

2hours later.

Ahankali yake bude idanunsa, wanda suka shafe sama da awa biyu a kulle.

Mik’a ya d’anyi ahankali tare da ambaton sunan Allah acikin zuciyarsa. 

Ahankali ya dan tashi zaune, tare dasa hannu ya shafa kan lafaffen cikinsa, da keyi masa kukan yunwa.

Numfashi ya d’an fesar akasalance kuma, yakai dubansa izuwa babban agogon dake cikin falon.

1:25 pm dai-dai agogon ya nuna masa, wanda hakan ya sashi d’an yunk’urawa ya mike.

Musamman saboda ganin da yayi lokacin sallah yayi.

Hannayensa ya zura acikin aljihun wandon dake jikinsa, kaitsaye kuma cikin tafiyar, dake nuna ya Dan samu karfin jikinsa ya nufi bedroom d’insa. 

Koda ya shiga cikin bedroom din Anutse, ya soma kokarin rage kayan dake jikinsa.

Bayan ya cire trouser’n dake jikinsa ne kuma, ya d’auko wani towel ya d’aura akan waist d’insa.

Direct toilet ya wuce, inda ya had’ewa kansa ruwan wanka mai d’an d’umi.

Anutse yayi wankan nasa tare da d’auro alwala ya fito.

Koda ya fito daga toilet din kuwa wani irin kamshin shower jel ne ke tashi ajikinsa, Yayinda kuma tausassun gashin jikinsa suka kwanta lub.

K’awataccen sajen dake kwance akan fuskarsa kuwa, shek’i take tayi saboda danshin ruwa dake jikinta.

K’arasawa gaban mirror yayi, tare da d’aukan mini towel ya shiga goge ruwan dake jikinsa.

Komai nasa da nutsuwa yakeyinsa.

Hakan yasa duk wanda zai kallesa sai yaji ya burgesa.

Had’add’en body lotion d’insa ya shafa, sai kuma turaren companyn Gucci daya shafa ajikinsa. 

K’arasawa gaban drawern d’insa yayi, inda ya ciro wani riga da wandon companyn Ouchpan masu kyau da taushi.

Rigar irin long sleeve d’innan ne, sai kuma wandon daya kasance tight, Wato mai dan kama jiki, amma kuma irin jeans dinnan ne, masu yanayi da crazy.

Anutse ya zura kayan ajikinsa, tare da d’aukan wasu  simple shoe ya zura akafafunsa.

Masha Allah! Ba k’aramin kyau kayan sukayi masa ba, kasancewar su black colour kuma shiyasa suka k’ara bayyana, hasken da fatarsa ta k’ara.

Ahankali ya d’an ciji jajayen labb’ansa, tare kuma dasa hannunsa ya shafa cikinsa dake kukan yunwa.

Fuskarsa ya d’an kwab’e tare da karyar da wuyansa gefe, Allah ya sani yunwa yakeji sosai.

Domin har wani jiri jiri yakeji.

Wayarsa dake kan gado ya d’auka, tare kuma da nufan falon nashi kaitsaye.

Koda ya fito idanunsa ya sauk’e akan dining table din dake cikin falon,  saidai kuma rashin ganin an ajiye masa abunda zaici ne yasa shi b’ata fuska, tare da d’an rausayar da idanunsa, cike da kasala da kuma yunwa ya nufo main falon nasu kaitsaye.

Acan b’angaren Jannart kuwa bata jima da kammala had’a abincin ba, kasancewar kuma garin ana d’an yanayin zafi shiyasa, Koda ta kammala had’a abincin a tray, kaitsaye part dinta ta koma.

Wanka tayi da sabulun beauty touch, wanda yasa gaba daya jikinta ya d’au sassanyan k’amshin sabulun. 

Bayan ta fito daga wankanne kuma ta shirya kanta, cikin wani had’add’en English wear gown, wanda kwata kwata bashi da nauyi, kasancewar kuma rigar tight gown ne shiyasa ya bayyana duk wani shape din jikinta.  

Harta kan nipples dinta kuwa saida ya bayyana, sosai rigar tayi mata kyau, tare da k’ara bayyana tsararren surar jikinta.

Turaren oud mai kamshin gaske ta shafa ajikinta, bayan ta tubke dogon gashin kanta, wanda yasha kitson da Mamy tayi mata ne kuma, ta yafa wani mayafi mai kauri ajikinta, daya rufe duk wani shape dinta, tayi hakanne kuma saboda sanin da tayi cewa, akwai maza agidan.

Juyawa tayi Ahankali kuma Cikin nutsuwa ta fice daga cikin dakin. 

Kaitsaye kitchine ta nufa, dan daukan abincin da ta dafa din.

Rayyern kuwa Ahankali yake saukowa daga matattakalan steps din.

Cikin nutsuwa da kuma d’aukar hankali yakeyin kowanne takunsa. 

 Ahaka yake saukowa daga kan steps din.

Hannunsa daure akan cikinsa, yana shafawa tare da d’an lumshe  idanunsa.   

“Mamy Mamy!!”

Sunan Mamy yake kira ahankali, cikin kuma muryarsa da tayi sanyi sosai, saboda rashin k’arfi da kuma yunwan da yake fama dashi. 

Adai-dai lokacin kuwa Jannart ta k’araso tsakiyan falon, Jin kamar muryar mutum ne kuma yasa ta d’aga kanta, karab kuwa Idanunta suka sauk’a akansa.

Kyawawan Idanunta ta d’an zuba masa, tare da soma Kallon shigar dake jikinsa, Wacce tayi masa kyau sosai.

Dai-dai lokacin kuma shima ya sauk’e idanunsa akanta.

Ahankali ya zame tare da zama akan steps din karshe dake kan matattakalan, idanunsa ya d’an lumshe tare dasa hannu ya dafe cikinsa,  wani irin numfashi yake sauk’ewa mai d’auke da gajiya, cikin sanyin muryar dake nuna gajiyawarsa ya k’wala kiran sunan Mamy.

“Mamy tana d’akinta.”

Jannart din ta bashi amsa, tare kuma da d’auke Idanunta daga kallonsa.

Idanunsa dake alumshe ya d’an bud’e, tare da k’ara d’aura hannunsa akan cikinsa.

Wanda yayi Dan ƙugin yunwa, har saida Jannart din ta jiyo sautin.

D’an kallonsa tayi, gaba daya duk ya marairaice,  ya wani zama abun tausayi, da dukkan alama Yunwa ce ke wahalar dashi.

“Meye kike wani kallona haka kamar zaki cinyeni, ni yunwa nakeji.”

Rayyern din ya fad’a yana me sauke mayun idanunsa akanta. 

Wanda kuma hakanne yasa tayi saurin dauke Idanunta daga kallonsa.

Batare kuma da tace masa komai ba ta juya, Cikin nutsuwa ta wuce kitchine.

Da idanu yabi bayanta, har saida yaga wucewarta cikin kitchine din kafun ya tashi ya dawo cikin falon.

Jannart kuwa tray da plates ta d’auko, tare da dawowa falon.

Ahankali ta sunkuya dai-dai zata ajiye tray din agabansa ne kuma, mayafin dake jikinta ya zame ya fad’i. 

Saurin ajiye tray din tayi tare da juyawa da sauri dan daukar gyalen nata.

Juyawan da zatayi dinne kuma yasa, Rayyern din sauke Idanunsa akanta.

Ganin inda idanun nasa suka sauk’ane kuma, ya sashi saurin rumtse su, tare kuma da kawar da kansa gefe sabida gani yayi tamkar nimples ɗin ta zasu tsole mishi ido, kasan cewar batasa bra ba yasa breast ɗinta ke tsaye kam nimples ɗin sunyi tsaye cur motsin da take yasa duk ƙirjinta rausayawa kara rumtse idanunshi yayi sabida ganin abin da yakeyi duk da ya rufe idon.

Itakuwa Jannart cikin sauri ta d’auki mayafin nata ta yafa.

Saboda kunyan da taji ya lullub’eta ne kuma yasa ta kasa d’ago kanta ta kalleshi.

Ahankali ta bud’e food flasks din, roasted fish din ta zuba masa, sai kuma miyar kasen shima da ta zuba masa shi, awani plate na daban dasa mishi tuwo kwaya ɗaya.

“Gashi.”

Ta fad’a cikin wata irin sassanyar murya, still batare kuma da ta d’ago ta kalleshi ba.

Akasalance ya d’ago kansa, tare da mik’a hannayensa alaman ta basa plate din.

Sai Alokacinne kuma ta d’ago Kai ta kalleshi, kasancewar kuma tana d’an nesa dashi ne, yasa dole saida ta matsa gab dashi.

Ahankali ta d’an ajiye guiwowinta akan tattausan carpet din dake malale atsakiyar falon.

Hannayenta duka biyu ta sanya wajen Ganin ta mik’a masa plate din.

Ak’ok’arinta nayin hakanne kuma, batare da duk sun Ankara ba, Rayyern din yasanya hannunsa ta k’asa zai karb’i plate din, hakanne kuwa yasa shi sauk’e tafukan hannayensa, akan lallausan fatar hannayenta, masu tsananin taushi tamkar auduga. 

Wani irin abu Jannart taji acikin jikinta, wanda har hakan yasa tsikar jikinta mimmik’ewa, lokaci daya kuma gyalen ta ya zame zuwa kan kafad’unta, hakan yasa lallausar sumar kanta ya bayyana. 

Idanunsa ya d’an zubawa gashin kan nata, Yayinda ita kuwa ahankali ta zame hannunta daga cikin nasa tare da sanya hannu ta jawo gyalen zuwa kanta. 

Dai-dai lokacin ne kuma Mamy ta fito daga d’akinta.

Ganin Rayyern da Jannart din atare ne kuma, ya sakata sakin murmushi Cikin kulawa tace.

“Babana lafiya kuwa Ina sallah naji kana ta rabka min kira.”

D’agowa yayi ya d’an kalli Mamyn, cikin yanayin sigar shagwab’a yace.

“Mamy To ba yunwa nakeji ba.”

Murmushi Mamyn tayi, tare kuma da neman waje ta zauna.

Cikin sakin fuska tace.

“To Rayyern Idan kanajin yunwa, baga matarka ba, komai ita zaka tambaya ba niba, kuma ga abincin ma, Ina naga ankawo ma,  Jannart sannu da aiki.”

Mamyn ta fad’a tana Kallon Jannart, da ta janye jikinta daga kusa da Rayyern din. 

D’an murmushi tayi, batare kuma da tace komai ba, ta dawo kusa da Mamyn nan k’asan sofa ta zauna.

Shikuwa Rayyern d’an k’aramin bakinsa ya taɓe, kana ashagwab’e cikin kuma yanayinsa na marar lafiya, ya soma cin abincin da Jannart din ta kawo masa.

Tun aloman farko da yayi kuwa, ya lumshe idanunsa, saboda dadi da kuma gardin kifin daya ratsa shi, bugu da kari ga kuma ruwan lemon tsamin da taste d’insa, ya hadu dana kifin sai ya bada wani dandano na daban. 

Ci gaba dacin abincin nasa yayi, duk da cewar bata wani sa masa da yawa ba, saboda sanin halinsa da tayi na rashin son cin abinci.

Mamy da Jannart kuwa hira suke d’an tab’awa kad’an kad’an.

Wanda hakan yasa sam basu ma lura da cewar Rayyern din ya cinye abincin ba.

“Bank’oshi ba fa.”

Maganar Rayyern din ya katse su daga hirar da sukeyi.

D’agowa Jannart tayi, karab kuwa idanunsu suka sark’e acikin na juna.

Saurin janye Idanunta daga kallonsa tayi, tare kuma da mikewa ahankali, ta k’arasa inda yake zaune. 

Mamy kuwa Murmushin jin dadi tayi, tare kuma dajin wani sanyi aranta, saboda dama burinsu ne Ganin Rayyern din yaci abinci ya kuma fara sakewa da matarsa.

Jannart kuwa durk’usawa tayi agabansa, tare da daukan plate din, ta soma kokarin kara masa gasashshen kifin.

“Idan ba rowa bama tayaya za’a bawa mutum abunda ansan bazai ishesa ba.”

Rayyern din ya fad’a k’asa k’asa ta yanda, yasan Jannart dince kawai zata iya jiyosa.

Aikuwa karab maganganun nasa, suka sauk’a acikin kunnuwanta kasan cewar tana kusa dashi ainun kuma hankalinta na kanshi.

Hakan yasa Ahankali ta d’ago Idanunta ta kalleshi.

“Malama meye?”

Ya tambaya yana me tsareta da idanu da tsuke fuska.

Fararen hakwaranta ta sanya, Ahankali ta ciji labb’anta, Cikin yanayin sanyi da kuma, yanayinta mai kama da shagwab’a, ta d’an maida bakinta gefe, alaman murgud’a baki.

Idanunsa ya d’an zaro, saboda ganin abunda tayi masa din,  duk da cewar kuwa hakan da tayi din, ba k’aramin k’ara mata kyau yayi ba, musamman saboda yanda lips dinnata suka sha, oil lipgloss. 

“Me bakin rashin kunya.”

Yayi maganan k’asa k’asa, tare da motsa k’afarsa Ahankali,  wanda kuma niyarsa shine ya take mata yan yatsun k’afarta.

Dai-dai nan kuma Abba da Baba Maud’o suka shigo cikin falon.

Hakanne kuwa yasa shi maida k’afartasa.

Jannart kuwa plate din ta tura masa gabansa, tare da komawa baya ta zauna.

“Sannu da shigowa Abba, Baba Maud’o sannu.”

Jannart din ta fad’a cikin girmamawa.

Murmushi dukansu sukayi, kana cikin jin dadin girmamasu da Jannart din keyi, Baba Maud’o yace.

“Yauwa Jannart sannu, ya gidan?”

“Alhamdulillah.”

Ta amsa tana me dukar da kanta k’asa.

Abba ma fuska asake, yana me zama akusa da Rayyern din kuma yace.

“Yauwa Jannart, sannunki .”

Baba Maud’o ne ya kalli Rayyern din cikin kulawa yace.

“Maud’ona ya jikin naka.”

Murmushi Rayyern din ya d’anyi, kana cikin sakin fuska da nuna Jin dadin kulawar Baba Maud’on yace.

“Alhamdulillah Baba Maud’o yanzu kam jikin da sauki.”

“Masha Allah Allah ya kara sauki, dama nace bari nazo na duba ka.”

Baba Maud’on ya fad’a yana me mik’ewa tsaye.

“Ameen Nagode Baba Maud’o.”

Rayyern din ya amsa.

Shikuwa Baba Maud’o juyawa yayi ya fice daga cikin falon.

Hakanne kuma yasa Abba ma tashi yabi bayan Baba Maud’on. 

Dai-dai lokacin kuma Riyyam nsra ya fito falon, hannunsa rike da wayarsa.

Anan kusa da Rayyern ya zauna, Ganin kuma irin delicious din da Rayyern din keci ne, yasa shi dan tand’e baki. 

Cikin dan yanayin zak’uwa yace.

“Gaskiya Hamma Rayyern kana cin dadi, tun Ina sama nake jiyo kamshin abincin kan nan gsky My Aunty kina mana ƴan ubanci.”

Hararan wasa Rayyern din ya d’an watsa masa,  shikuwa Riyyam din wayarsa ya ciro, tare da dannawa numbern Ramadan kira.

Mamy da Jannart kuwa murmushi sukayi.

Bugu biyu kuwa Ramadan din ya dauka.

Cikin zak’uwa Riyyam din yace.

“Albishirinka Hamma Ramadan, yau kada Kaci komai awaje, ka dawo gida Aunty Jannart irin miyar ranan tayi.”

Daga can b’angaren Ramadan yace.

“Ai ganinan ma Ina dawowa, kace Aunty Jannart ta ajiyemin nawa.” 

“To.”

Riyyam nsra din yace, daga haka ya katse kiran.

Rayyern kuwa d’ago kansa yayi ahankali, tare da Kallon Mamynsa cikin sanyi yace.

“Mamy d’azu munyi waya da Mammyn Riyyam tace tana gaidaki.”

Murmushi ne ya bayyana akan fuskar Mamy, cikin jin dadi tace.

“Masha Allah Ina amsawa.”

Juyo da kallonta ta kumayi inda ta sauke idanunta akan Riyyam nsra.

Cikin nuna kulawa tace.

“Ni kam Riyyam baka tab’a had’ani da Mammynka ba ko awaya, bani hotonta na gani mana Idan kana dashi.”

Murmushi Riyyam nsra din yayi, cikin tausasawa da jin daɗin satan amsar da Mamy ta bashi mgnar ta yace.

 

“Ayyah Mamy yi hakuri, amma babu hoton Mammy  awayana sabida randa zanzo na sai sabuwar waya kuma na bar waccar a gida.”

Ya kare maganar yana dan karyar da wuyansa gefe.

“To had’ani da ita mana muyi video call.”

Mamyn ta fad’a tana me kallonsa.

Wani irin bugawa yaji kirjinsa nayi, wanda hakan yasa shi sadda kansa k’asa. 

“Tayaya zai had’a Mamy da Mammynsa video call?”

Yayiwa kansa tambayar.

Mamy kuwa Ganin yayi shiru ne yasa ta cewa.

“Lafiya kuwa Riyyam inayi maka magana kayi shiru, had’ani da ita muyi magana.”

Kansa ya d’an langwab’ar gefe, cikin kuma yarda da k’aryar da zuciyarsa ta tsara masa yace.

“Ayya Mamy d’azu muna waya dasu, naga kiran ya katse, ashe wai Zaytoon ce ta raɗa mata  wayar a ƙasa, dana sake kira kuma baya shiga, saida ga baya Mammy kecemin wai, cameran wayan nasu ya samu matsala, saidai ko voice call.”

D’an Jim Mamyn tayi, kamar me nazartar wani abu kuma saitace.

“To Wayar Zaytoon fa?”

“Ai Zaytoon bata da waya, Mamy ta hana ta rik’e waya, tace wai bayanzu ba.”

Ya k’are maganan yana me waskewa, gudun kada kowannensu ya fahimci cewar bashi da gaskiya.

Kai Mamyn ta jinjina, kana cikin gamsuwa da bayanan nasa tace.

“Ai hakan da Mammyn naka tayi shine daidai, barin waya ahannun y’a Mace budurwa adai-dai wannan lokacin hatsari ne, kodan wannan babbar masifa ta Tiktok dinma, saidai Wacce Allah Ya kare kawai.”

Murmushi Riyyam din yayi, cike dajin dadin yanda karyar tasa ta samu karb’uwa kuma ya samu sun kauda mgnar ma.

Rayyern kuwa mik’ewa yayi, saboda dama ya kammala cin Abincin. 

Anutse ya nufi sama, saboda surutun nasu na damunsa.

Har ya fara haurawa yace.

“Uhum Mamy ai su kansu yara masa basu waya da barinsu yin shuhura a social media babbar masiface, yanzu kigafa yadda Riyyam-nsra yake kamar mazari, wanda  a baɗini kuma Allah ne kaɗai yasan me yake shukawa”.

Ya ida mgnar ya juyowa ya tsurawa Riyyam-nsra ido.

Wanda shi kuwa yayi wani irin firgita dan sai yake ga Hmma nasu ya gane komai da yakeyi ne.

Mamy kuwa cikin yarda da yaron tace.

“A babu ma abinda yakeyi”.

Uhum kawai yace yaci gaba da tafiyarsa.

Tashinsa awajenne kuma yasa ita kuwa Jannart sakewa,  bayan ta gyara wajen da yaci abincin ne kuma ta dawo, suka zauna ita da Riyyam hira suka sha sosai, suna nan zaune dai har Ramadan ya dawo.

Bayan sunyi sallan magriba ne kuma, Jannar din ta zuba musu sauran ragowar abincin Rayyern din sukaci.

After 3day.

Alhamdulillah acikin kwanaki ukun nan, jikin Rayyern ya k’ara sauki sosai, domin babu laifi yanzu ya samu karfin jikinsa.

Domin yana iya fitowa har can compound din gidan, wajensu Baba Maud’o, sannan har motsa jikinsa yana iyayi yanzun.

 

Ab’angaren Jannart kuwa tun ranan bata sake sakashi a Idanunta ba.

Sosai kuma takejin dadin zaman gidan, musamman ayanzu da duk sanda Ramadan  ya dawo, sukan zauna suyi hira sosai, harma game sukeyi.

Ga kuma wayarta dake d’ebe mata kewa, kasancewar ta bud’e Twitter, Instagram, da kuma Tiktok, da wani suna na daban, bawai original account dinta da kowa ya sani ba, sunan da ta bud’e dashi kuwa, ba wai normal sunane da kowa zai gane ba.

Akomai nata da  Unique kawai take using. 

Acan b’angaren gidan su kuwa.

Har dai zuwa yanzu babu wani mai gamsashshiyar nutsuwa acikinsu, more especially Alhaji Idi Sale dakata.

Momy da kuma Abdull, wanda abun ya had’e musu biyu, rashin lafiyar Dadyn da kuma b’acewar Jannart. 

Yanzu ma zaune su Alhaji Idi Sale Dakata, Alhaji Abdu Tababa, Dr. Lukaman, da kuma Barrister Kabir, Alhaji Bala Tamnari suke acikin katafaren dakin ganawa’n Alhaji Idi Saleh Dakata.

D’ago da kansa yayi ya kalli Alhaji Bala Tambarin, cikin dan yanayin damuwa yace.

“Wato Alhaji Bala, har yau ina mamaki kan al’amarin daya shafi yaron nan Rayyern, musamman akan company’s d’insa, akullum hab’aka abubuwan nasa sukeyi, na kuma rasa gano tushe da madafan arzikinsa, saboda ayanzu haka nasa ayimin bincike akan sabon companynsa, ankuma tabbatarmin da cewa, zuwa yanzu ankawo komai da komai na amfani acikin companyn,  kama daga kan engines dama dai sauran abubuwa, saboda har anfara sarrafa kayayyakin abinci, amma naji ance bazasu fara fitar da kayayyakin nasu ba, sai farkon shekara mai kamawa ina mamakin dukiyar yaron dan a iya wannan Company nasa zaikai biliyoyin kuɗi da sunfi shekarunsa yaushe aka haifesa har ya yarasu.”

Kai Alhaji Bala Tambari’n ya jinjina, cikin gamsuwa kuma yace.

“K’warai kuwa nima nasan da haka Alhaji Idi Saleh Dakata.”

Gyara zama Alhaji Abdu Tababa yayi, kana cikin takaici yace.

“Wannan abu ni Ina mamakinsa, amma Meyasa ba zaka dakatar dasu ba Alhaji Bala? Naga Kaike kula da duk wasu harkan filayen da ake gine gine masana’antu, ni har yauma ina mamakin tun farko ma meyasa ka basu takardar izinin fara ginin companyn?”

Murmushi Alhaji Bala Tambarin yayi, saboda shi yasan meya sani, kamar yanda suka kasa gane waye, Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din, to shima  hakane.

Dr. Lukman ne ya cab’i zancen da cewa.

“Gaskiya dai kam, amma ni yanzu sauki na daya, abubuwanshi na harkar asibiti gaba daya sun dakata, yafi maida hankalinsa, akan abubuwan da suka shafi companyn.”

Barrister Kabir dake zaune agefe ne ya saki wani  murmushin jin daɗi. 

Tare da gyara zamansa, Cikin nutsuwa yace.

“Anaka tunanin kenan Dr. Lukman, domin da alama baka da labarin cewa, acikin kwanan nan akwai likitotinsa da ya ware kusan guda biyar dashi na shida, way’anda zasu tafi Russia Mascow yin wani course, baya ga haka kuma Idan sunyi wannan course din sun dawo, akwai ci gaba na musamman wanda za’a samu, a hospital din nasa, domin zasuje suyi course dinne, akan abunda ya shafi dashan k’oda, dana zuciya aikin ƙwaƙwalwa da juyen jini ga masu cutar sikila uwa uba da safarar tunanin kwakwalwar ɗan Adam, dama dai sauransu, kuma Insha Allah zasu kawowa K’asa cigaba.”

Idanu Dr. Lukman ya d’an zazzaro, cikin bakinciki takaici da kuma kunci yace.

“Wallahi kwata-kwata Barrister bani da wannan labarin, kuma ai wannan plant din nima, najima da tsarashi azuciyata, wanda kuma nakeso na aiwatar acikin hospital dina, amma kuma sai next year nakeson haka, why? Why? Wannan yaron ya shigemin hanci, komai zanyi saiya rigani kafin ma in tuna abu shi yayi, na shiga uku Anya zai barni na ci gaba arayuwata kuwa?”

Dr. Lukman din ya fad’i  haka cikin tashin hankali, saboda ya fahimci cewa, duk saurinsa Dr. Rayyern din yana gaba dashi akan komai. 

Boyayyen Murmushi Barrister Kabir yayi, tare da maida kansa ya ajiye ajikin kujera, yayi hakanne kuma saboda yanda yaga, hankalin Dr. Lukman din ya tashi sosai.  

Alhaji Bala Tambari kuwa, gyara zamansa yayi…!

Back to top button