Uncategorized

Ɗan Pantami ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane sa’o’i 24 bayan sace shi

Ali Isah Ali, ɗa ga Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki ta Fasahar Zamani, Isa Ali Pantami, ya shaƙi iskar ƴanci, sa’o’i 24 bayan da a ka ce an sace shi.

Jaridar Nation ta rawaito cewa an tsinci Ali, ɗan shekara 14 a wani shingen binciken jami’an tsaro a Ƙaramar Hukumar Dambam, Jihar Bauchi.

Nation ta jiyo cewa an yi garkuwa da Ali ne a kan hanyar shi ta dawowa gida bayan an tashe su da ga makarantar islamiyya, inda masu garkuwar su ka yi awon-gaba da shi a kan babur.

Jaridar ta ce babu wani cikakken bayani kan yadda yaron ya kuɓuta, inda ya ke zaune wajen mahaifiyarsa a Bauchi bayan da a ke zargin sun rabu da Pantami.

Nation ta ƙara da cewa mahaifiyar taron ma ta tabbatar da kubutar ta sa, inda ta ce tuni ya na gida tare da ita.

Haka shima Babban Limamin Masallacin Juma’a na Isa Ali, Imam Hussain ya tabbatar da cewa Ali ya kuɓuta kuma ya na wajen mahaifiyarsa.

Jaridar ta ƙarar da cewa da a ka tuntuɓi Kwamishinan Ƴan Sanda na Jihar Bauchi, Ahmed Mohammed Wakil, ya ce bashi da masaniyar sace yaron sabo da ba a kai rahoton ga ƴan sanda ba.

Ya ce ya tuntuɓi caji-ofisoshi cikin garin Bauchi amma duk sun ce basu da masaniya kan lamarin.

Back to top button