Sirrin Rike Miji

Abubuwan da suke haddasa fitar farin ruwa a gaban Mace daya kamata ku sani domin magance su

Farin ruwa wanda a turance ake kira da (white discharge) wanda ke fitowa daga Farjin Mace ko Azzakarin Namiji, a lokacin sha’awa ko da lokacin jima’i ko bayan jima’i, akwai farin ruwan da yake fita daga farji domin taimakawa Mace wajen jima’i.

Misali akwai wani nauyin farin ruwa da ake kira da (cervical mucus) shi idan ya fita yana wanke farji tare da kara masa santsi, ya zama kamar an shafa masa wani mai me yauki.

Karanta>>> Hanyoyin Da Ya Kamata Matan Aure Subi Domin Kara Inganta Zaman Aurensu: Malama Juwairiyya

Sannan akwai wani ruwa wanda ake kira da (Penile fluid) wanda ke fita ta cikin bututu daya da fitsari yana fita hanya daya da fitsari.

Wadannan ruwaye idan aka ga sun fita ba komai bane lafiya ce, wasu lokuta fitar ruwan yana nuni da cewa mutum ya kamu da cutar infection ne, amma in sha Allah zan danyi bayani akan wanne ne na cuta wanne ne na lafiya a cikin su.

Karanta>>> Maganin Karin Hips Mai Sauki Ga Mata

Akwai fitar farin ruwa a lokacin da Mace taji sha’awa:

Sha’awar jima’i shine sanadin farin ruwa da farjin mace mafi yawanci lokaci, kuma wannan ruwa yana fita fari mai haske.

Wannan ruwan yana tsaftace da bata kariya ga farji lokacin da mace daji sha’awar jima’i, wannan ruwan yana karuwa tare da fitowa daga gaban ta kuma indai mace ba zafi take ji wajen jima’i ba wannan ruwan fitar sa ba komai bane face lafiya.

Karanta>>> Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi

Sai kuma fitar farin ruwa a lokacin da Al’ada tazo wato haila:

 

Ba matsala bane mace taga farin ruwa a lokacin da al’ada tazo ko kuma a karshen al’adar tata a lokacin ovulation lokacin da kwan haihuwar mace ke fita, farin ruwa na fita daga gaban mace kalar sa kuma kamar farin dake cikin danyen kwai.

Karanta>>> Matsi Ga Sabbin Amare Kafin Kije Gidan Miji.

Sannan idan akai jima’i a wannan lokacin na ovulation za’a iya ganin wannan farin ruwan hatta akan Azzakari.

Ganin farin ruwa a lokacin da aka gama jima’i:

Karanta>>> Domin Dawo Da Martabarki Cikin Sauki.

Idan mace tana ganin farin ruwa bayan an gama jimai da ita to wannan lallai tana da infection a tare da ita.

A takaice wadan nan sune wasu daga cikin lokutan da mace zata iya ganin farin ruwa yana fita daga gaban ta, ina fatan kuma ‘yan uwa sun karu da wannan dan takaitaccen bayani nawa.

Karanta>>> Yadda Zaki Hada Sabulun Da Zai Sa Ki Dinga Kyalli, Santsi, Kamshi Da Kuma Maganin Kuraje

Back to top button