Hausa novels

Abban Sojoji Chapter 63 Book 2 Complete Novel

Abban Sojoji Chapter 63 Book 2

The Fatjer Of Soldier

Written By: Hafsat Bature

Abban sojoji paid book ne,ga duk maison karanta cigabanshi zai biya 300 ne za’a tura mashi nabaya har inda muka tsaya,ga mai buƙata direct zaiyi mun magana ta whatsapp ɗina 08103884440, pls banda phone calls,Mijina ya hana ana kira na awaya🤭🤫

 

 

❤🤍❤

 

 

Gaba ɗaya farin ciki ya lullu6e Marshal Omar da kuma major,tunda su kaji bayanin Jahad suka tabbatar da cewar ba shakka Itace ƴar uwartasu da take magana akai,

“Jahad,wannan maganar ba anan ya kamata muyi ta ba,mu shiga daga ciki”

buɗe motar Omar yayi tun kafin major ya buɗe mashi,fitowa jahad tayi itama,sannan shima major ya fito,duka dae a tare suka ɗunguma izuwa cikin gidan,har lokacin jikin jahad rawa yake yi,saboda tsabar doki da kuma zumuɗin ganin cewa Sehrish ce yarinyar da Omar ke magana akai,

 

Lokacin da suka shiga cikin palour ɗin atare,hosana na a kwance saman 3 seater,tasha kuka harta gaji shine ta ɗan kishingiɗa nan,bacci ya kwashe ta, ko uniform din bata cire ba,bin ta da kallo Omar yayi bakomai ya faɗo mashi a rai ba,face abunda yayi ƙoƙarin aikata mata,tausayinta ne ya kama shi sosae,tsayawa yayi atsaye ya zuba mata ido ko kyaftawa baiyi,

“Ya Omar,ka zauna mana,”muryar jahad ce ta katse mashi kallon da yake ma hosana,

Wuri ya samu saman 2 seater ya zauna,jahad kuma ta zauna asaman 1 seater,mayar da idonshi yayi kan major ganin ya tsaya daga tsaye yace”bismilllah mana,ave seat,” ya nuna mashi gefen shi,murmushi major yayi tare da ƙarasawa ya zauna daga gefen Marshal,

“Jahad,inaso kiyimun bayani sosai yarda zan fahimta game da ƴar uwarku,taya akai kuka rabu da ita har tsawon wannan lokacin’? Omar ne ya jefa mata tambayar,gaba ɗaya suka zuba mata ido suna sauraron jin abunda Jahad zata ce,

“Ya omar ba da son ran mu muka rabu da ita ba,ƙaddara ce ta rabamu da ita,amma muna son junan mu sosai…..’dakatawa tayi da maganar yayin da idanunta suka cicciko da kwalla,

Anatse taci gaba da magana”ƴar uwarmu tana son mu sosai,tasha wahala akanmu,a lokacin baya Dani da hosana an ta6a kwantar damu asibiti,za’ayi ma hossana aiki,ana neman kuɗi kusan dubu ɗari tara da za’ayi mata aikin,bamu da ko sisi,bamu da mai taimakon mu sae Allah,mu kaɗae muke rayuwarmu tare da wata tsohuwa wadda take ruƙon mu a wurinta,wannan dalilin ne yasa sehrish ta nemi aikatau,don ta biya kuɗin aikin hosana da kuma na maganin da za’a siyamun,babu yarda muka iya alokacin wannan kaɗae ce mafita,muna ji muna gani ƴar uwarmu ta tafi neman kuɗi saboda ta nema mana lafiyarmu,ya Omar Sehrish tayi duk wata gwagwarmaya akanmu,damu da ita duk kanmu ɗaya,amma ita tamkar uwa take a wurinmu,tamkar yaya take a wurinmu,bamu da tamkarta aduniyar nan,rishi har ranta zata iya sadaukarwa saboda mu,nayi kukan rashinta sosai,nayi baƙin cikin yin nesa da ita……..tun muna yara muke tsananin son junan mu,rayuwarmu a wulaƙance mukayi ta sakamakon mugun uba da muke dashi wanda bai ta6a nuna mana soyayya ba……..’fashewa tayi da matsanancin kuka,

Gaba daya jahad ta gama kashe masu jikinsu yayi sanyi,

dakyar ta tsagaita da yin kukan taci gaba da magana”bayan sehrish ta tafi aiki,cikin sa’a ta samu kuɗin aikin hosana ta biya,lokacin da aka sallame mu daga asibiti,muka koma gidan tsohuwar da take kula damu,anan muke rayuwarmu,kullum muna kiranta awaya mu gaisa da ita,ita ma kuma tana kiran mu awaya taji ya lafiyar mu take,akwai wani lokaci da maganin hosana ya ƙare,ciwonta ya soma dawowa ta dinga hauka tana ƴan buge buge,hankali na ya tashi,gashi bamu da kuɗin da za’a siya mata wasu magungunan,shine na yanke shawarar sanar ma rishi halin da ake ciki,don ta taimaka mana dana magani,na tura mata saƙo ta waya,sai gashi ta turo mun da amsar cewa mu tura mata da acct number,cike da zumuɗi na zura hijabi na shiga gidan makwabtanmu wurin ɗiyar matar,don ta rubutamin acct number ɗinta tun da mu bamu da ita,ashe lokacin da na fita daga gidan,hosana tafarka daga bacci tana son shiga toilet,shine ta ɗauki wayar dana bari saman jakar kayanmu ta shiga toilet da ita,kafin nadawo cikin gidan hosana ta jefar da wayar cikin masan,wannan shine silar da muka rasa sehrish gaba ɗaya,saboda ba mu da wata hanyar da zamu iya magana da ita,sae ta wannan wayar…….’ƙarasa maganar tayi tana faman share kwallar da ke kwaranyowa daga idanunta,

sunnar dakai omar ya ɗanyi,yayin da yake jin zuciyarshi wani kala ba daɗi,haka shima major duk tausayin yaran ya kamashi,musamman ƴar uwarnan tasu sehrish,yarinyar tayi bajinta sosai,

ɗagowa omar yayi tare da kallonta yace”Jahad,inaso ki faɗamu taya akai kuka shiga hannun ƴan sanda?wane laifi kuka aikata ne”?

Cikin shessheƙar kuka tace”bamu aikata laifin komai ba ya Omar,sharri ne akayi mana,abunda ya faru bayan hosana ta jefar da wayar acikin rami,sae ga tsohuwar nan da take rainon mu ta shigo cikin gidan,anan ta same mu ni da hosana muna faɗa akan wayar da ta jefar mana,sai take tambayar meya faru ne muke faɗa,shine na sanar da ita abunda ya faru,hankalinta ya tashi sosai akan wayarta da mukayi mata asararta,rai a6ace ta shige cikin ɗaki ta rufe ƙopa,duk bamuji daɗi ba lokacin saboda bata ta6a nuna mana 6acin ranta ba irin na ranar,atsaye muka kwana muna bata haƙuri akan ta buɗe mana ƙopa mu shiga ciki,saboda a gidan ɗaki biyu ne,amma ɗaya ya rushe saboda ruwan saman da aka ta6ayi mana mai ƙarfi,ya Omar aranar waje muka kwana har ciwon hosana ya tashi,kafin washe gari kuma taji sauƙi,koda muka farka munyi tsammanin zata buɗe mana ƙopar amma abun mamaki sae muka ga ƙopar adatse,tun muna sa ran zata buɗe mana kopar har muka fidda rae,a ƙarshe agidan makwabtan mu muka shiga yin sallar asuba,anan ma muka ci abinci,da mamansu yarinyar ta tambayemu meya faru,muka sanar da ita duk abunda ya faru,shine yarinyar gidan ta rakomu har gidan mu,muka haɗu tare da ita muna babbuga ƙopar,a ƙarshe hosana ce tayi ƙoƙarin 6alle ƙopar……anan muka samu gawarta,ashe tun daren jiyan ta mutu…….mutane kuma suka daura mana laifin kisan nata,saboda sun gano cewa guba aka bata taci,wannan ne dalilin da yasa ƴan sanda suka kaimu police station,bayan an gama tattara hujjojin da za’a miƙa mu kotu dasu,sae kuma ciwon hosana ya tashi acikin cell,wannan ne farkon fitarmu daga cikin cell aka kai hosana asibiti,Ya omar kaji yarda akai muka kasance a hannun ƴan sanda….. “Ƙarasa maganar tayi yayin da hawaye ke ta faman sintiri a fuskarta,

“Ina mahaifiyarku take ne”?omar ne ya kuma tambayarta,

Jahad tace”bamu san inda take ba,bani da tabbacin cewa tana a raye kota mutu,abu ɗaya nasani koma a wane hali take yanzu indae tana araye to bata acikin hankalinta,”

Jinjina kai Omar yayi kafin yace”Insha Allah zan bincika komai a sannu zan gano duk wanda yayi sanadiyar shigarku cikin wannan halin,bazan ƙyaleshi ba,koda uban da ya haifeku ne,zan yanke mashi hukunci daidai da zunubin da ya aikata,’

major yace”wannan gaskiya ne,yalla6ai Allah ya taimaka kuma yayi jagora,nidae yanzu babban burina shine ƴan ukun nan,su kasance a ƙarƙashin kulawar family ɗinku,”

 

Omar yace”abun ya ɗaure mun kai major,kaji wani iko na Allah nan,gaba ɗaya yaran su ukun suna a ƙarƙashin kulawar family dinmu,duka Allah ya haɗasu awurinmu batare da saninsu ba,kuma batare da sanin mu ba,ita ɗayar ƙaddarar aiki ce ta kawota gidan mu,yayin da su kuma su hosana da jahad,ƙaddarar zaman asibiti ce ta haɗani dasu a lokacin da hosana ke hauka hannunta ruƙe da bindiga,Major abun akwai wata sarƙaƙiya acikinshi,tabbas akwai abunda Allah yake nufi da waɗannan yaran!akwai wani abu da Allah ke son bayyana mana shiyasa ya haɗasu duka awurin mu!”

Zuba mashi ido jahad tayi tana kallonshi ita kanta abun ya ɗaure mata kai,

Shi kanshi major ya shiga kokonton cewa Anya yaran basu da alaƙa dasu Marshal Omar?juyawa yayi ya dan kalli fuskar marshal sannan ya mayar da idonshi akan hosana,sae lokacin ya dinga ganin wata irin kamanceceniya atsakaninsu sosae,tabbas akwai wata alaƙa ta jini a tsakaninsu,shiru kawai yayi baice komai ba,

Kowa ya tafi duniyar tunani hafsat bature ma,ta ɗan ajiye typing tana tunanin wannan abun daya ɗaure mata kai tamau…,

“Ya Omar,”gaba dayansu sukayi firgit suna kallon Hosana dake kwance tafarka tana faman mutsistsike idanunta,jin muryar Omar yasa ta ambaci sunan shi,

Murmushi ya dan saki tare da ambaton sunanta “Hosana”,

miƙewa tayi zaune tana ƙare masu kallo gaba ɗayansu,tashi Omar yayi ya koma gefenta ya zauna yana kallonta,

lokacin da ta tabbatar cewa shine saita fashe mashi da kuka tana cewa”Ya omar fushi nake dakai,meyasa ka tafi kabarmu kadaina zuwa wurin mu?laifin me mukayi maka da har kayi mana wannan horon”?

Lallashinta ya shiga yi yana cewa”Am really sorry hosana..pls stop crying and wipe ur tears,komai ya wuce yanzu muna tattaunawa ne game da ƴar uwarku Sehrish…… ‘

Tunda ya ambaci sunan sehrish hosana tayi tsit ta nemi kukan da takeyi ta rasa la66anta har rawa sukeyi wurin cewa”Anganta ne ya omar?”

Murmushi Omar ya saki tare da cewa”An ganta hosana!ƴar uwarku da ku ka jima kuna nema,ashe itace yarinyar dake yi mana aiki agidan……”bai ƙarasa maganar ba hosana ta fashe da kukan murna tana cewa”Ya omar tana ina?ina rishi ɗinmu take?inaso naganta!tana ina,wayyo Allah na….’

Yarfa hannunta tashiga yi saboda tsabar farin ciki bakinta yaƙi rufuwa hawaye na zuba fuskar kuma ɗauke da dariyar farin ciki,

Itama jahad farin cikin ne tsantsa afuskarta yau takasance babbar rana agaresu rana mafi girma arayuwarsu ranar da Allah yasa suka gano inda ƴar uwarsu sehrish take,dole suyi farin ciki,bama su kaɗai ba,hatta masu karanta labarin rayuwarsu da kuma marubuciyar data zauna ta tsara labarin ita da kanta tana taya su farinciki,Ya Allah ka ƙara danƙon ƙauna atsakaninmu da ƴan uwanmu masu son mu,Allah ka bamu ikon faranta ma juna da kuma taimakon junanmu,a gudu tare kuma atsira tare❤

 

Omar ya jima a wurinsu hosana kamar karya tafi ya barsu haka yaji,abunda yasa bai tafi dasu yau ba saboda Yarinyar gidan tasu da ba’a gani ba,yafi son sai sun ɗauko yarinyar sannan ya kaisu gidan nasu don suga ƴar uwarsu ido da ido,zai so yaga wannan farin cikin a fuskokinsu,

Bayan tafiyar su Marshal Omar,jahad da hosana duk sun bi sun ruɗe saboda tsabar murna ko abincin rana basu ci ba,sai faman sintiri sukeyi acikin babban falon nasu,aƙagare suke dasu ga sehrish,zuciyarsu sae faman azalzalarsu take akan son ganinta kamar suyi hauka.

 

💋BOSS BATURE💋

 

Ga wani tashin hankalin kuma,duk yadda sojojin nan suka so su kama sehrish abun yaci tura domin kuwa sehrish ta kubce masu,babu irin neman da basuyi mata ba,amma babu ita 6at ta 6ace kamar al’jana,abu kamar wasa har bayan sallar La’asar basu ganta ba,

Niko sehrish ina kika shiga ne!kai jama’a daga antaro nan sae kuma nan ya ruguje,

 

tunda Abbansu ya sanar mashi game da zuwan Aunty azeema,jiki na rawa junaid ya fito daga dakin Abbansu da gudun gaske ya nufi ɗakin da aka saukar da ita,faɗawa cikin ɗakin yayi ko sallama babu saboda tsabar ɗoki,a lokacin tana daga zaune saman gadonta tana daddana wayarta,sam bata lura dashi ba,bata ji shigowarshi ba,sae dae kwatsam taji faɗowarshi jikinta,gaba ɗaya ya ƙanƙameta sosai,yana yi mata kukan shagwa6a wai yayi missing ɗinta sosai,

Dariya sosai hajiya Azeema tashiga yi tana cewa”Oh ni junaid,tun ɗazu nake ta tambayar ina babynmu yake ina babyn mu yake,duk na ƙosa naganka naso ace ina shigowa cikin gidan nan kaine mutun na farko da zaka fara tarbata da wannan sumbatar taka,”

ta ƙarasa maganar tare da ɗago shi daga jikinta tana bin shi da kallo tace”Masha Allah,junaid kaine ka koma haka?ka ƙara girma sosai kyakkyawan yarona,nayi missing ɗinka sosai,”

murmushi junaid ya sakar mata tare da cewa”mommy azeema ina tsarabata?me kika kawo mun”?

Dariya tayi tana girgiza kai tace”Tsarabarka na nan junaid,wannan karan nazo maka da abun ban mamaki,inaso inga farin cikin da zakayi idan nabaka tsarabar nan,”

cike da zumudi junaid yace”tana ina,”

Harara ta ɗan watsa mashi tare da cewa”Shine damuwarka?ka manta baka bani kiss dina ba,”

matsawa junaid yayi tare da kai bakinshi gefen fuskarta ya manna mata kiss sannan ya ɗago yana kallonta yace”yanzu sai aban tsarabata ko”?

Dariya tayi tace”ɗaukomin trolley ɗin kayana,”tayi maganar tana yi mashi nuni da trolleyn da Kanal yousouf ya jingine mata ajikin wardrobe,

jiki na rawa junaid ya saukko daga saman gadon ya taka izuwa wurin wardrobe din ya ruƙo trolleyn tare da janyoshi har wurin gadon ya miƙa mata shi,sannan ya zauna daga gefe ya zuba ido yana jiran ganin tsabar da tayi mashi,

hannu tasa ta buɗe trolley din ta curo wani ɗan kit ƙarami sai faman ƙyalƙyali yake yi yadda kasan da gold akayi jikinshi,tunkan ta buɗe shi junaid ke ta faman haɗiye yawu yarda kasan yaga abunci,

Murmushi ta danyi tare da kallon fuskarshi tace”close ur eyes,”

Rufe ido junaid yayi kamar yarda ta umarta,

Murmushi ta kuma yi tare da buɗe akwatin tace”Now Open ur eyes,”

A hankali junaid ya buɗe idanunshi kai tsaye suka sauka akan danƙareran Zoben diamond ɗin da ta siya mashi tare da agogonshi,sae faman ƙyalli suke suna ɗaukar ido,diamond bana wasa ba,wanda aƙalla price ɗinsu yayi miliyan ɗari uku,

Waro ido waje junaid yayi yana bin su da kallo saboda tsabar farin ciki ya gaza rufe bakinshi,hannunshi na kerma ya kar6i akwatin yana ƙare masu kallo,

Cikin tsantsar farin ciki yace”aun…aunty..wannan duk nawa ne”?

dariya Azeema tayi ganin yarda yabi ya rikice ta wani 6angaren kuma ba ƙaramin daɗi taji ba,saboda bata da wani burin daya wuce taga ta faranta mashi,tana son ganin farin cikin junaid sosai,yaron tun yana ƙarami take tsananin son shi,

“Junaid duk naka ne wannan,Na musamman ne nasa akayi maka shi,duk duniya babu mai irin shi sae kai kaɗae,ni da kaine na bada sample ɗin yadda za’a haɗa maka shi,ka duba a jikin zoben ka gani,Harafin J ne ajiki wato farin sunanka,”

Wani irin farin ciki ne,ya cika junaid,a ƙarshe daya rasa abun cewa kawai sae ya fashe mata da kuka Yana cewa”mommy azeema,narasa da wasu kalmomi zan iya gode maki,babu su abakina,kin sanyani farin ciki sosai da wannan kyautar da kika bani.

 

Hannu tasa tare da shafo gefen fuskarshi izuwa cikin sumar kanshi tace”kasan dae babu godiya atsakaninmu ko?nayi maka wannan ne saboda inga farin cikin ka,kuma Alhamdulillah nagani kuma naji daɗi sosai,abu ɗaya zakayi mun yanzu shine ka share hawayenka,bana son ganinsu suna zuba,”

Cikin sauri junaid ya sanya hannunshi tare da goge hawayenshi duka,sannan ya mayar da hankali yana kallonta,

Cigaba da magana tayi a natse”junaid kana addu’a kuwa”?

gabanshi ne yaji yayi wani irin bugu jin tambayar da Aunty azeema tayi mashi,baisan dalilin dayasa tayi mashi wannan tambayar ba,

A ɗan ruɗe yace”Mommy meyasa kikayi mun wannan tambayar”?

shiru ta ɗanyi kamar mai nazarin wani abu kafin taci gaba da cewa”junaid bibiyar rayuwarka akeyi!”

Hankali atashe junaid yace”Ni kuma mommy azeema,to meyasa ake bibiyar rayuwata?su wanene ke bibiyar rayuwata,me nayi masu?kuma me suke so atare dani?”gaba ɗaya ya gama ruɗewa,

“Just calm down ur mind,ba wani abu bane na tashin hankali ba,banaso ka sanya damuwa a ranka junaid,amma ya zama dole na sanar dakai,akwai wata baiwa da Allah yayi mun,duk in nayi mafarki yana xama gaskiya,bawan da yasan da hakan sai ni,abubuwa da yawa kafin su faru acikin gidan nan,ni nake fara ganinsu acikin mafarki na,Allah yana nuna mun…’ajiyar zuciya ta dan sauke tana kallon junaid daya kasa kunne yana sauraronta,

kafin taci gaba da cewa”Nayi mafarki akan ka junaid,mafarkin ya tsoratar dani sosai,wannan dalilin ne ma yasa na nace akan saina zo,ba don komai ba sai don na ganka naga wani hali kake ciki……’

gaba daya hankalin junaid yayi mugun tashi muryar shi na rawa Yace”Mommy azeema,dan Allah ki fahimtar dani wani kalar mafarkine wannan?wani mummunan abune zai faru dani ne?mutuwa zanyi ko?dama najima ina ji araina cewa bazanyi tsawancin kwana ba………’bata bari ya ƙarasa maganar ba,tasa tafin hannunta ta rufe mashi bakinshi,tsit junaid yayi jikinshi na rawa,zuciyarshi naci gaba da bugawa da ƙarfi da ƙarfi,

Cikin sanyin murya tace”Junaid,babu wanda ya isa yayi maka abunda Allah baiyi maka ba!tabbas rayuwarka na cikin hatsari sosai saboda duk wani dake son ganin bayan zuri’armu ta wurinka zai biyo junaid,dole sae da kaine za’a iya cutar damu junaid saboda kaine lagwon kowannanmu,kaine farin cikin mu gaba ɗaya…..’ ƙarasa maganar tayi tare da zame hannunta daga bakinshi,

Jikin junaid yayi mugun sanyi,bakomai ya faɗo mashi aranshi ba face wannan ɗigon jinin dake ɗigowa daga hancinshi,da kuma daren ranar nan daya farka tsakar dare yaga wani baƙin hayaki ya fito daga cikin madubin ɗakin Abbansu,ya tunkaroshi ya shiga ta ƙopar hancinshi,a lokacin bayan ya farka washe gari,duk tunaninshi mafarki ne yayi ba gaske ba,amma yanzu da Aunty azeema tayi mashi wannan maganar sae wani tunanin ya faɗo mashi aranshi,tun daga daren ranar da hayaƙin nan ya shiga ta ƙopar hancinshi,a washe garin ranar jinin nan ya soma ɗiɗdigowa daga hancinshi,tabbas akwai wani 6oyayyen abu dake shirin faruwa dashi,

Download>>> Anya Baiwa Ce Complete Novel Document

  Tuna wannan abun yasa junaid ɗagowa idanunshi awaje yana kallon mommy azeema yace”Nashiga uku!mommy ina cikin tashin hankali!mutuwa zanyi bazan rayu ba…kashe ni zasu yi….bazasu bar ni da raina ba ..zasu rabani da Abbana’

Ganin yarda junaid yabi ya gigice yasa ta ruƙo hannunshi sosai tace”Ka natsu junaid!ba kayi imani da Allah bane?

Cikin shessheƙar kuka yace”nayi Imani da Allah mommy azeema,amma ni bana so na mutu yanzu,inaso na rayu ko don nacika ma abbana burinshi da kuma burin da nake dashi…  ‘

Katse shi tayi da cewa”tunda kayi imani da Allah,to inaso kasa aranka cewa babu wani mahaluƙi daya isa ya cutar dakai a faɗin duniyar nan face da izinin sa,sannan inaso ka dage da addu’a na sanka junaid baka ba addu’a mahimmanci sosai,kuma ita addu’a da kake gani takobin mumini ce,ka tashi tsaye ka dage da addu’a ka yaƙi duk wani wanda ke son ganin bayanka,kayi mun alƙawarin hakan,nima kuma zan tayaka da addu’ar,sannan zanyi ma abbanku magana akan ya dinga tashin ka tsakar dare kunayin sallah atare koda ace shi bai tashi ba,in har ka farka to ka shiga toilet ka dauro alwala kayi sallarka,sannan kuma zan sanar ma sauran ƴan uwanka duk zanyi masu magana akan su tayaka da addu’a Allah ya tsare mana babynmu,’

Wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyarshi,kalaman Aunty azeema ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya su kayi ba,ya samu ƙwarin guiwa sosai awurinta,har ya daina jin damuwa a ranshi,

“Kana da budurwa”?cike da zolaya tayi mashi maganar,don ta kawar da damuwar dake aranshi,

Sunnar da kai junaid yayi tare da cewa”am…um….eh..’

Dariya Aunty azeema tayi tana cewa”wai kunya ta kake ji ne?dalla faɗamun ni inji,”

Hannu yasa yana ɗan sosa ƙeyarshi yace”mommy azeema,akwai wadda nakeso sosai,kuma itama tana sona sosai,acikin gidan nan take,tare da Aunty azmee suke aiki,yau ta sanyani farin ciki sosai mommy,ta kar6i soyayyata,aure kawai ya rage yanzu inyi ma Abbanmu magana…..’kasa ƙarasa maganar yayi ganin yarda Azeema ta saki baki galala tana kallonshi,

Cike da jin kunya junaid ya kifa kanshi asaman laps dinta yana faman tiƙar dariya,

Suna cikin wannan rahar,wayar Hajiya azeema ta shiga ruri,tsagaitawa tayi daga yin dariyar da take,sannan takai hannu tare da ɗaukar wayar dake ajiye gefenta,ta duba mai kiran nata,a fili tace”Abbanku ne ke kirana,bari na ɗaga naji me zaice mun,”ta ƙarasa maganar tare da kara wayar a kunnanta,

Lamo junaid yayi kwance saman laps ɗinta,ba komai yake tunawa ba face soyayyar da suka sha tare da rishi ɗinsa acikin mota,soyayyarta ƙara ninkuwa takeyi acikin zuciyarshi,musamman da ta kar6i soyayyarshi hannu bibbiyu kuma ta amince zata aure shi,yanzu bai da sauran damuwa,dama itace damuwarshi kullum fargabarshi taya zai tunkareta da zancen soyayyar,zata amince ko bazata amince ba!?

Yana cikin wannan zancen zucin nashi yaji muryar azeema tana cewa”Alhamdullillah!Alhamdulillah mun gode ma Allah daya sauke su lafiya,ba don na tara gajiya ba,da ba abunda zai hana nima na biku Airport din mu tarboshi ..’

cike da farin ciki junaid ya ɗago yana cewa”Mommy,Uncle ɗinmu ne ya ƙaraso nigeria”?

Fuskarta dauke da murmushi tace”Eh,yanzu Abba ke sanar dani cewa sun shirya zasu tafi airport ɗauko shi,jirgin nasu bai kaiga ƙarasowa ba,amma kafin su isa airport din zai ƙaraso da yardar Allah,

Cikin sauri junaid ya sauko daga saman gadon jikinshi na rawa yace”Mommy azeema,ki ajiye mun gift ɗina a wurinki,zanzo na kar6a anjima,inaso zanje airport ɗin nima tare dasu Abbanah,’ko amsarta bai saurara ba,ya fuce da sauri da sauri,

Murmushi Azeema tayi yayin da take bin bayanshi da kallo har ya fuce,

 

Goggon katsina

 

Da gudun gaske ta fito daga cikin ɗakinta,hannunta ruƙe da wayarta saboda tsabar farin cikin jin zuwan Abusufyan ɗinta da abbansu junaid ya sanar mata,

Adai dai lokacin Saude da dr haris suna manne da juna saman 3 seater a falo suna shan soyayya,yana ƙoƙarin manna mata kiss asaman wuyanta,kwatsam sai ga goggon katsina ta faɗo cikin falon tana murna ganinsu yasa ta aza hannu akai tana cewa”La’haula masalli ila!acikin gidan nan ake wannan baɗalar?

A firgice suka ɗago suna kallonta hankali tashe,kamar yarda itama take kallonsu hankalinta atashe,

sunnar dakai ƙasa sukayi suna ƴan kame kame,

Jinjina kai tayi tare da cewa”munafukan Allah,yau asirinku ya tonu,dama abunda kuke aikatawa kenan duk in nashige cikin ɗaki ko?cike da tuhuma tayi masu maganar,.

Download>>> Boddiya Complete Hausa Novel Document

   buɗe baki saude tayi da niyar tayi magana,goggo tayi mata dakuwa da hannunta tace”Ungo nan,ja’ira dama kar nake kallonki,munafuka ashe shiyasa kullum nace zan maidaki rugarku sae kiyi mun narai narai da ido kamar na mujiya kina cewa bakison ki koma kiwon shanu,ashe kina nan kin kama wani shanun kina ta tatsa,ina nan sake da baki,Allah kaɗae yasan me kuke aikatawa,ni ban yarda daku bama Allah,ka fadamun gaskiya Harisu iya shinshine-shinshinen kuka tsaya ko kun zarce nan? Tayi maganar tana wurga mashi harara,duk kunya ta gama rufe shi,

Cike da jin kunya suka sunnar dakai ƙasa atare suna sauraronta,sae da takai aya sannan Dr haris yace”Mommyna ni fa ba abunda ya shiga tsakanina da ita,wannan ma da Allah yasa kika gani sharrin shaiɗan ne, ba yin kanmu ba……’bai ƙarasa maganarba,goggo ta tsige kallabin dake kanta,ta wurga mashi shi kafin ya ƙarasa saman fuskarshi,cikin sauri saude ta tarbe kallabin goggon a hannunta,

 

Baki asake goggo tace”Saude! don tsabar iya rashin kunya da tsageranci akan idona kike kare mashi don na jefe shi da kallabina?wato ya saba baki kina sha shiyasa kika raina ni ko”?

Waro ido waje Saude tayi tana kallonta hankali atashe tace”nashiga uku goggo,me kike nufi daya saba bani ina sha”?

Harara goggon katsina ta watsa mata tana murguɗa mata baki tace”nima bansani ba,nasan dae kina bashi kuma shima yana baki,Allah ya shiryeku in masu shiryuwa ne,sae yanzu nagane kuskuren danayi na barin ki acikin gidan nan,batare da an shafa fatihar Auranku ba,gashi yanzu kuna ƙokarin haifo min ɗan gaba da fatiha…..’fashewa tayi da kuka,cikin shesshekar kuka taci gaba da cewa”Allah sai kin bar gidan nan saude…bazan cigaba da zama dake ba,kina lalatamin yarona,kafin zuwanki gidan nan harisu ko kalmar kiss baisani ba,amma sae gashi yau na same shi yana ƙoƙarin manna maki kiss kamar wani maye,yabi ya kanenayeki don tsabar jaraba irinta ƴaran zamani,acikin gidajen iyayensu ma bazasu iya kame mutuncinsu ba,ni bandamu ba duk abunda zakuyi kuyi,amma ba agaban idona ba…..’

Atare Dr da saude suka kalli juna cike da mamakin jin abunda goggo tace,wato komai zasuyi suyi amma ba’a gaban idonta ba,tashin sense,

Miƙewa haris yayi tare da takawa inda take ya ruƙo hannunta,cikin lallashi yace”Goggo pls komai ya wuce,kuskure ne mun riga da munyi,kuma bazamu ƙara ba,kiyi haƙuri kinji mommyna”

fisge hannunta tayi daga cikin nashi tace”kada ma Allah yasa ku daina,ni wannan ba damuwata bace,yanzu ni bani da sauran damuwa zan tattara nabar maku gidan,idan kunga dama kuyi aure,in baku ga dama ba ku cigaba da abunda kuka saba,Allah dae na kallon mutun,’

Tayi maganar tana wurga ma saude harara,haushinta takeji kamar ta rufeta da duka,

“Mommyna,ina zakije ne?naji kina cewa zaki bar mana gidan”?cike da damuwa yayi maganar

Murguɗa mashi baki tayi tare da cewa”gidan Abba mana,zanje inga Abusufyan ɗina ne,yanzun nan zan shirya in tafi,’

“Mommyna pls ki bari sae gobe zan kaiki da kaina har can ki ganshi,amma yanzu marece yayi fa,naji kamar ana kiran sallar magriba ma,dare zai yi mana a hanya,’cikin lallami yake yi mata magana,don yasan halinta bamai iya mata,

Turo bakinta tayi tana gunguni kamar wata ƙaramar yarinya tace”Allah bamai hanani zuwa,sai naje naga Abusufyan dina tare da ƴa’ƴanshi,’

ɗaure fuska babban likita yayi tare da cewa”Muddin kikasa ƙafa kika bar gidan nan,akwai karnukan layi na nan suna ran gadi acikin anguwar nan,da zarar sunyi arba dake hmmmmmm Allah kaɗae yasan mai zai biyo baya,

tunda taji ya ambaci sunan karnuka,nan take jikinta ya shiga kerma,saboda mugun tsoransu take ji,bata ƙara tanka masu ba,jiki na rawa ta wuce bedroom ɗinta,

Ajiyar zuciya Dr haris ya sauke tare da juyawa ya kalli saude dake ta faman sakin murmushi yace”wlh naji kunya sosai,mommyna bata da saiti,komai yazo bakinta faɗinshi takeyi,yadda kasan rakwa6a66iyar motar da burki ya kwace mata,’.

Fashewa da dariya sukayi,daga bisani Saude ta tsagaita da yin dariyar tace”babyna,addu’a yakamata muyi mata akan Allah ya bata lafiya,idan tadawo dai dai mu kanmu zamuji daɗi sosai,saboda goggo tana da kirki sosae,’

Murmushi Dr haris ya kuma yi tare da cewa”insha Allah zamu cigaba dayi mata addu’a Akan Allah ya bata lafiya,’

 

_💋Boss Bature💋_

 

 

Wuraren ƙarfe 6:30 jirginsu Abusufyan yayi landing a Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja,

gaba ɗaya su Abba sun gama hallara a airport ɗin suna jiran saukowarsu daga cikin jirgin,kowannansu a ƙagare yake daya ga fuskar Abusufyan da suka jima basu sanyashi a idanunsu ba,nikaina wlh amatse nake dana ga wannan Abusufyan ɗin da kowa yake ta ɗokin ganinshi,

 

Gaskiya namatsu,namatsu namtsu, inga wannan ɗan tahalikin,

 

daga cikin waɗanda suka hallara domin tarbar shi akwai Abbansu tare da junaid,kanal yousouf da kuma Irfan,jabeer,khaleed da kuma fawan,bayansu kuma akwai Twins suma duk suna zazzaune asaman waiting seats na airport din suna jiran ƙarasowarshi,suna zaune suka ji ana annoucement din ƙarasowar jirgin daya zo daga ƙasar turkey,

 

Tsantsar farin cikine ya bayyana a fuskokinsu,duk suka zuba ido suna jiran 6ullowarshi,

 

 

Passengers ne suke ta fitowa daga cikin jirgin kowannansu fuskarshi asake,sae bullowa sukeyi ta ko’ina,

Sannu a hankali ya aza kafarshi asaman matattakalar benen,masha Allah sae dae muce tabarakallahu ahsanul khaliqin,

giant ne yana da tsayi da kuma cikakkiyar sura mai jan hankali,ta ko’ina Allah ya hore mashi,a launin fata kuwa chocolate colour ne,kala mai tsada,fatar nan tashi taji hutu ko a ido ka kalleta sae kasan cewa ba ƙaramin hutu taji ba,jikinshi na sanye da Suit maroon colour launin glass ɗin dake manne a fuskarshi,wani irin daddaɗan kamshi ne ke fesowa daga jikinshi,hannunshi na sanye da tsadaddan agogo na diamond,

A hankali ya ɗaga hannunshi tare da kai shi saman fuskarshi ya zame glass ɗin da ke manne a fuskar,lumshe idanunshi yayi tare da waresu a hankali yana kallon mutanen dake shawagi a wurin,

Yayi kewar ƙasar shi sosai,shekara kusan goma sha wani abu,bai taka ƙasar ba,sai yau Allah ya dawo dashi,

“Ƙaddara ta sake dawo dani wannan ƙasar” ya furta hakan yayin da yake ƙara ruƙe trolley ɗin hannunshi,jan shi ya shiga yi yayin da yake ci gaba da saukowa daga saman matattakalar jirgin,

Dirar shi ke da wuya,yaji an ambaci sunan shi da wani irin sauti yaji ance”Uncle Abusufyan! “firgit yayi tare da kai idanunshi wurin da yaji an ambaci sunan,

Waro ido yayi waje fuskar nan dauke da farin ciki ya ambaci sunan Junaid,

Da gudun gaske junaid ya ƙarasa tare da faɗawa saman faffaɗan ƙirjinshi,ya kankame shi sosai kamar zai shige jikinshi,

Download>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel

  sosai Abusufyan ke sakin dariyar farin ciki yana ƙara bubbuga bayan junaid da hannunshi yana cewa”WOW MASHA ALLAH MY BABY BOY KAINE KA KOMA HAKA,GASKIYA NAYI MISSING ƊINKA SOSAI JUNAID,AM REALLY GLAD TO SEE U ……..’

ya ƙarasa maganar tare dasa hannunshi ya ɗago junaid daga saman kirjinshi yana kallon fuskarshi,yayi mamakin girman yaron lokacin da daya tafi yana ɗan ƙaraminsa ya barshi,

 

ganin hawaye na sauka asaman fuskar junaid yasa shi cewa”meya faru junaid?kai da zan ga kana farin ciki sae kuma naga hawaye a idanun ka why?

Cike da shagwa6a junaid yace”uncle bakaine ka tafi kabarmu ba,shekara da shekaru ka manta damu,ba ka damu da kazo ka ganmu ba,”

ƙayataccen murmushi Abusufyan ya saki tare da cewa”Am really sorry my boy,nasan ni mai laifine ayimun afuwa pls,shiyasa nadawo nigeria don in goge laifina….’

Yana cikin maganar tashi sai ga su Abba sun ƙaraso wurinsu tare dasu kanal yousouf,

Gaba daya suka ƙarasa one by one suna rungume shi ajikinsu cike da nuna farin cikin ganinshi,

Sae da ya kammala rungumarsu,sannan ya ɗago yana kallon ɗan uwan nashi daya tsaya gefe guda,yana kallon shi fuskarshi aɗaure alamar fushi yake dashi,

Tunkarar shi yayi zai rungume shi,cikin sauri Abba ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga mashi hannu yace”karka kuskura ka ƙaraso nan,bana son ganinka,ni banma san ya akai nazo airport ɗin nan ba,”

Hannu uncle abusufyan yasa tare da kama kunnan shi yana cewa”Am sorry my bro,ayi mun aikin gafara nasan nayi laifi,amma zan gyara kuskure na,yanzu dae ka barni in rungumeka kona ji sanyi araina,’

Buɗe mashi hannu Abba yayi alamar ya taho,faɗawa jikin shi abusufyan yayi sosai suka rungume junansu,tuni hawaye suka cicciko a idanuwan kowannansu

muryar abbansu junaid tamkar zaiyi kuka yace”Hakanan ka tafi ka barni batare da sani na ba,me yasa kayi mun haka abusufyan?duk irin son da nake maka,ka tafi ka barni da raɗaɗin rashin ka acikin zuciyata,abun ba ƙaramin ciwo yake yi mun ba,”

ya ƙarasa maganar a lokacin da yake ƙoƙarin raba jikinshi daga na Abusufyan,

Jikin shi yayi mashi sanyi,duk sai yaji ba daɗi,kuma bai kyauta masu ba,

daƙyar yace”Ka yafe mun ɗan uwana,na cutar dakaina,na raba kaina da ƴan uwana,bawai don bana son kasancewa atare da ku ba……’

Kasa ƙarasa maganar yayi saboda wani abu daya tuna a rayuwarshi daya ta6a faruwa dashi…,

Jinjina kai kawai Abbansu junaid yayi tare da ruƙo hannunshi yace”Komai ya wuce,tunda kadawo nigeria,kuma inaso ka sani bazan ƙara bari kabar ƙasar nan ba,komai kakeso ka faɗamun zanyi maka shi,in ma akwai wani abu dake damunka duk ka sanar mu,zanyi ƙoƙari wurin ganin na share maka hawayenka,dama ni sae da raina ya bani cewa bada son ranka kabar ƙasar nan ba,akwai wani abu dake faruwa wanda kaƙi sanarma kowa…..’

“Abba,uncle fa ya gaji sosai,ya kamata muyi hanzarin wucewa gida tare dashi,idan ya kwanta ya huta sae mu ƙara gaggaisawa dashi,”

Kanal yousouf ne ya katse mashi hanzarinshi,

murmushi abba yayi tare da janyo hannun abusufyan suka kama hanyar fitowa daga airport din,gaba dayansu suka ɗunguma izuwa wurin da suka ajiye motocinsu,murmushi kawai Abusufyan keta saki yana kallon ƴan uwan nashi kamar ya haɗiyesu haka yake ji,saboda tsabar son da yake yi masu.

 

Finally Uncle Abusufyan ya ƙaraso nigeria,saura mommynsu junaid da kuma Ammi,su muke jira,

 

Koda suka ƙaraso cikin gidan,anan main palour din suka zazzauna ana ƙara gaisawa da juna,a ƙarshe abba ya ruƙo hannun ɗan uwan nashi yakai shi izuwa cikin bedroom ɗin da aka tanadar mashi,katafaren ɗakinsa da zai zauna aciki,sae da abba ya tabbatar da cewa Abusufyan ya shige cikin ɗakin sannan yaja mashi ƙopar ya rufe,

Gaskiya zanso kuga irin farin cikin da ahalin nan suke yi na zuwan Uncle dinsu Abusufyan,

 

Wuraren ƙarfe 11 na dare lokacin komai ya lafa,junaid ya nufi bedroom ɗin sehrish yana nemanta ganin bata fito ba,lokacin daya je,ɗakin nata ya shiga wayam yaga babu kowa,jiki na rawa ya wuce ɗakin azmee yana tambayarta ina reesh take,azmee tace”tun ɗazu dana kai mata lunch ban ƙara sanyata a cikin idanuwana ba,”fitowa junaid yayi daga ɗakin azmee hankalinshi a matuƙar tashe,saƙo da lungu na gidan ya dinga bi yana dubawa bai ganta ba,lokacin daya tabbatar da cewa sehrish bata acikin gidan,jiki na rawa ya wuce ɗakin Abbansu anan ya same shi zaune shi da Uncle abusufyan suna ƙara tattaunawa a tsakaninsu,

Ganin yarda junaid ya faɗo masu ba sallama yasa suka shiga tambayarshi ko lafiya,hankali tashe yace”Abba,sehrish nake nema,na duba ko’ina acikin gidan nan bata nan,’

cike da mamaki abusufyan ya maimaita sunan Sehrish abakinshi,

Abba kuma yace”tun yaushe tabar gidan?baka je ɗaukota daga school bane”?

“Abba naje,dakaina na ɗaukota kuma na kawota acikin gidan nan,amma yanzu na duba ko’ina babu ita,”

Jin wannan maganar ta abba yasa shi miƙewa daga zaunen da yake gefen gadon ya nufi junaid yana cewa”muje wajen,”

Juyawa junaid yayi suka fuce atare,yayin da suka bar Abusufyan azaune cikin ɗakin,

 

Hankalin kowa fa ya tashi,abun sai ya baka mamaki,ashe ba ƙaramin so sukeyi ma yarinyar ba,duk wanda akace mashi Sehrish ta 6ace ba’a ganta ba,sae kaga ya fito daga bedroom dinshi yadawo falo cike da damuwa,gaba daya sae da kowannansu ya hallara banda Sgr,saboda tun ɗazu yabar cikin gidan,

Hankalin Marshal omar ba ƙaramin tashi yayi ba,jin ana neman Sehrish,sam ya manta da bata a cikin gidan,tunda junaid yayi musanyarta da jahad,ya tura sojojin nan don su nemo mashi jahad,su kayi arba da yarinyar saboda kamanceceniyar dake atsakaninsu yasa sukayi tsammanin Jahad ce,yayin da suka bi ta da nufin su kamata ita kuma ta watsa aguje,tabar masu school bag ɗinta a ƙasa,babu irin neman da basuyi mata ba,amma babu ita ba alamarta 6at ta 6ace masu………Shin Ina sehrish ta shiga ina!?

 

“Abba wai meke faruwa ne naga kunyi curko-curko anan,kamar kuna cikin damuwa,”hajiya azeema ce ke tambayarshi a lokacin da take ƙarasowa inda suke tsaitsaye,duk sun hallara gaba dayansu kowa yana cike da zullumin abunda zai biyo baya game da yarinyar da ta 6ata,

Download>>> Dr Bobby Complete Novel

  “Yarinyar dake taya azmee aikice ta 6ace,an nemeta an rasa babu ita acikin gidan nan,”ya bata amsa fuskarshi cike da damuwa,

Fawan yace”Abba ita yarinyar bata da waya ne”?

junaid ne ya bashi amsa da cewa”akwai waya a hannunta,amma na kira layinta a kashe,tun ɗazu nake trying still switch off,

Hajiya azeema tace”gaskiya akwai matsala,yakamata ayi hanzarin binciko inda yarinyar take,”

Gaba daya duk sun shiga damuwa,musamman junaid hada ƴan hawayenshi,

Gyaran murya Marshal Omar yayi suka mayar da hankalinsu akanshi,sannan yace”kada ku damu,insha Allah za’a ganota,na zuba sojoji acikin garin nan suna nan suna bibiyarta,kuma insha Allah zasu gano mana ita,”

Abba yace”naji daɗi sosai Omar,Allah yasa su gano mana ita,hankalina bazai ta6a kwanciya ba in har yarinyar nan bata dawo cikin gidan nan ba,’

Ya ƙarasa maganar tare da kallon su fawan yace”kuje ku kwanta,insha Allah za’a gano ta,”

Har suna haɗa baki wurin cewa”Abba,ba zamu iya runtsawa ba,in har ba’a ganta ba,zamu zauna anan ne mu jira har Allah yasa ta bayyana,’

Abun ba ƙaramin mamaki ya ba Abbansu ba bai ta6a tunanin cewa sun damu da yarinyar ba,sae yau,abunda ke faruwa ita mace ce,kuma matashiya dole kowa yayi zullumin ina ta shiga,waya dauketa,sace ta akayi ko kuma cutar da ita akayi,?

Back to top button