Hausa novels

So Da Buri Page 3 Complete Novel

So da Buri

003

A hankali Mama ta bud’e idanunta da suka d’an kumbura ta juyo tana kallon fuskar Hudan kafin ta kai hannun a hankali ta shafa kumatunta tausayinta yana sake shigar mata zuciya.Nasarawa GRA, Kano. Wani dogon dattijo ne ke tsallako titin da sauri had’e da d’an gudunshi,hannunsa na dama rik’e da agwaluma guda uku a cikin farar leda,na hagun kuma yana amfani da shi wajen mayar da y’an chanjin sa cikin aljihun gabar rigarsa,da alama agwalumar ya tsallaka siyowa.K’ara saurin gudun nasa yayi sakamokon ganin har motocin da ya hango sun iso bakin mahaukacin gate d’in makeken estate d’in.Da saurinsa ya zaro wani d’an k’aramin makulli a cikin aljihun gefen wandonsa ya isa gaban wata had’add’iyar k’ofa wadda ke a ta gefen makeken gate d’in wadda colour d’inta da design d’in exactly irin na gate d’in ne, cikin sauri ya zura mukullin a ramin mukulli sannan ya murza k’ofar ta bud’u ya tura da sauri ya shiga har yana tuntub’e, shigarsa ke da wuya waennan motocin da ke jiransa a ta wajen gate d’in suka fara danna masa horn babu k’akk’autawa…tashi d’aya duk ya bi ya rikice hakan yasa ya yi sauri ya fad’a d’akinsa na mai gadi ya d’aga k’asan pillow ya d’auko mukullin babban gate d’in ya fito yanata sauri ya k’araso jikin gate d’in ta baya ya bud’e padlock d’in sannan ya bud’e wani lock kafin ya durk’usa k’asa ya zare wata makekiyar sakata tukunna ya mik’e ya fara k’ok’arin tura gate d’in jikinsa duk yana rawa kana ganinsa ka san a rikice yake gashi an k’ara rikita shi da uban horn d’in da ake ta maka masa babu k’akk’autawa… ,Bai kai ga k’arasa tura gate d’in ya bud’u duka ba motar farko k’irar benz G wagon Bak’a wuluk! ta danno kai da mugun gudu ta biyun na binta a baya, ba don ya yi hanzarin barin wajen ba da babu abunda zai hana gilashin motar tafiya da y’ar sharar jikinsa.Ganin motocin sun shige ne yasanya shi K’arasowa bakin gate d’in ya fara turawa domin rufewa, da kyar yake iya turawa saboda tsabar girma da nauyi.Wani gate d’in motocin suka nufa a cikin jerin gidajen estate d’in da a kalla sun kai 15 kuma gaba d’aya ginin gidajen yanayin tsarin 3D ne masu hawa biyu,tsayuwa fad’an haduwar ginin gidajen b’ata lokaci ne.Wani kakkauran mutumi ne zaune a bakin gate d’in da suka nufa,sanye cikin uniform d’in sojoji,da alama shi ke gadin wannan particular gate d’in, mik’ewa ya yi sakamokon hango motocin sannan ya shiga ta k’aramar k’ofa ya bud’e musu gate d’in wanda hakan ya bawa farfajiyar gidan damar baiyyana..mahaukacin makeken mansion ne yanayin tsarin ginin 3D shima…Ma sha Allah aljannar duniya kenan domin kuwa ya had’u har ya gaji da had’uwa da tsaruwa ga kyau ga girma duk ya had’a.Wajen da aka tanada domin ajijiye motoci suka nufa sannan suka yi parking.Wani mutum ne ya bud’e motar farko,ta wajen mazaunin driver ya fito ya zagayo ta wajen owners corner da d’an saurin shi ya bud’e murfin motar ya koma gefe ya tsaya …..K’afarshi ta dama wadda ke sanye cikin had’add’en black d’in covershoe mai tsananin tsada ya fara zurowa waje, kafin ya sauk’o da d’ayar sannan ya mik’o ya fito gaba d’ayansa, ba matashi bane ba ko magidanci ko kuma dattijon Alhaji, tsohon mutum ne ,tukuf da shi!!Sanye yake cikin wasu zazzafan suit,ash colour, kai kana ganin yanayin kayan ka san ya kai kud’in jarin mai k’aramin k’arfi,idanunsa sanye cikin wani farin glasses wanda kana gani ka san na k’arin k’arfin gani ne,walking stick d’in dake rik’e a hannunsa for sopport ma kanta abar kalloce!! Ka na gani ka san an zuba mak’udan kud’ad’e wajen siyar ta,ga wani had’add’en Rolex watch a hannunsa, Tsohone amman skin d’insa glowing yake yi wanda kana gani ka san tsabar hutune..to cut it short dai,every part of him is screaming ‘I’M RICH!!’.Sandar hannunsa ya d’aga domin yin tafiya har ya d’an tura k’afarsa gaba sai kuma ya yi amfani da ita ya juyo ya tsaya yana kallon motar da suka shigo tare.Wani kyakkyawan saurayi ne ya fito daga mazaunin driver da alama shi ya tuk’o motar da kansa, yana d’an fizgen kama da tsohon sannan kalar fatar su iri d’aya ce.Ganin da Auwal ya yi kakan nasa ya kafeshi da idanune ya sanya shi K’arasowa wajensa da d’an sauri, tukunna ya d’an rissinar da kansa yana mai kallon k’asa kafin yace”Garanpa,u need something??.”Ya yi masa tambayar ba tare da ya kallesaba .Juyawa Grandpa d’in ya yi ba tare da ya sake kallonsa ba,har zuwa lokacin da drivern d’insa ya d’auko suitcase d’inshi ya gama rufe motar yana taka mishi baya….yana tafiyar ba tare da ya tsayaba cikin muryarsa ta tsofaffi yace”Go and give iliyasu 50k,ask him to leave this house foreva,he is fired!!Sannan ka cewa Daniel ya nemo sojan da ya san zamu shirya ni da shi,ya fara gadin main gate,within 3 hours.”Yana magana yana tafiya ko sake waigowa bai yi ba balle ya amsa Auwal wanda yake cewa”Ok Granpa consider it done”.Ya shige.Wani shu’umin murmushin jin dad’i Auwal d’in yayi, daman shi ya tsani Malan iliya, domin kuwa kamar gadin sa shi kad’ai yakeyi a gidan,ya saka masa ido dayawa, kullum idan ya dawo dukda kuwa motarshi tinted glass gareta sai Malan iliya ya san yadda yayi ya d’an lek’a ta gaban dukdan ya ga shi kad’ai ya dawo ko kuwa tare da wata yake,sannan bai isa yayi dare ba,yana wuce 12 zai fara ganin kiran Daddyn sa ko da kuwa Daddyn nasa baya gari,ko me yayi in dai malan iliya ya gani to a kunnen Daddynsa, kuma sai an hukuntashi hukunci mai tsanani, ya zame masa kamar wani cctv camera sam ya hanasa sakat duk dan kawai idan ya kai wa Daddyn nasa rahoto yana bashi kud’i da kaya, and the most annoying part of it Daddyn nasa ya hanashi ko da hararar mallan iliya ne,balle wata banzar magana.Yana wannan nazarin da murmushi akan fuskarsa ya k’arasa bakin gate d’in granpa ya fad’awa Daniel sak’on granpa sannan ya nufi main gate wajen mallan iliya. Daniel kasa b’oye zumud’in sa yayi , a take ya d’au waya ya kira wani abokinsa solomon wanda ya san irin halinsu d’aya, nan da nan kuwa Abokin nasa ya amince bayan Daniel ya fad’a masa nawa ake biyan malan iliya, yace masa ya jira zuwanshi nan da 2 hours yanzunnan zai sallami mamanshi da sistern shi ya taho.Shikuwa Auwal yana isa maingate ya sanar da malan iliya sak’on granpa,tsabar mugunta dubu hamsin akace ya bashi amman yabashi dubu ashirin,kayansa kuwa kala uku ya bari ya d’iba waenda ya zo gidan da su,ragowar kuwa yace “ba zai d’auka ba ai ta wajen Daddynsa ya samu ta hanyar kai gulmarsa.” Sai da ya tabbatar ya bar gidan tukunna ya k’ulle kayayyakin da ya hanashi tafiya da su ya jefar a babban garbage bin na Estate d’in, ya koma ciki abinsa. Cike da annashuwa ya nufi wani Triplex a cikin jerin gidajen estate d’in, kamar yadda kowanne yake gate d’inshi daban da compound haka shima wannan, knocking ya yi sannan ya d’an ja ya tsaya, cikin y’an seconds wani tsohon mutumi ya bud’e y’ar k’aramar k’ofar gefen gate d’in gidan ya d’an lek’o, ganin waye a tsaye ya sanya tsohon saurin bud’e k’ofar sannan ya d’an rissina yace “Barka da yamma.”“Lafiya” kawai Auwal d’in yace dashi daga haka ya kutsa kai ya nufi cikin gidan wanda yake zagaye da flowers kala kala,an shafe k’asan compound d’in gidan da interlock, ta tsakiyan compound d’in kuwa wani k’aramin roundabout ne,ta left side na roundabount d’in wani k’awataccen garden ne wanda yake d’auke da su porch swing,hammock chairs da k’ananun kujeru domin hutawa sannan ga shuke shuke kala kala, ta right side kuma parking space ne, sai ta gaba hanyar shigowa,gate kenan,sannan ta bayan roundabout d’in kuma anan ne k’ofar shiga gidan ta main parlour take.Kasancewar gidan a zagaye yake..idan ka wuce main door d’in ka yi hanyar baya akwai k’aramar k’ofar kitchen ta shiga kitchen da wajen wanke wanke da d’an k’aramin fili.Yadda ginin gidan nan yake haka gaba d’ayan gidajen estate d’in suke apart from gidan granpa ,wanda ya fi kowanne girma da tsaruwa.Karasawa yayi ya shiga y’ar k’aramar varander da aka dan zagayeta da k’arafuna da flowers,sannan ya isa bakin k’ofar parlourn ya danna doorbell.Wata farar budurwa wadda ba zata wuce shekaru goma sha biyar bace ta bud’e k’ofar,hannunta rik’e da waya kirar iPhone tana daddanawa tana murmushi,da alama chatting d’in da takeyi ya tafi da hankalinta, dan bata ma lura da waye ta bud’ema k’ofar ba,kawai ta juya ta nufi k’aton parlourn nasu mai d’auke da set d’in kujeru uku da katon dining area ,sai staircase biyu.Juyawa Auwal yayi ya rufe k’ofar sannan da d’an sauri ya biyota ta baya yasaka hannu ya warce wayar,da sauri ta juyo suna had’a ido da shi ta saki wani sassanyan murmushi.B’ata rai ya yi sannan yace “da wa kike chattn haka??”Ya yi mata tambayar yana maida idanunsa kan wayar domin ganin da waye take chattn d’in. Zaro ido ta yi sannan da sauri ta kai hannunta kan wayar da niyyar warcewa amman sai ya yi saurin kama hannun ya rik’e da d’an k’arfi har sai da ta yi k’ara,ganin k’ok’arinsa na ya karanta mata chat ne ya sanya a karo na biyu ta sake yunk’urin karb’ar wayar tata cikin shagwabarta tace “Ya Auwal dan Allah ka bani waya ta.”Murmushi ya yi ganin chat d’in nata ita da wata friend d’inta ne, tana bata labarinsa, expressing how much she loves him, har tana ce mata ta fi son smile d’insa saboda hakan yana fitar da dimples dinsa,sake fad’ad’a murmushin nasa yayi sannan yace “D’ago kanki mana ,ungo wayarki.”Shiru ta yi,sai hannunta d’ayan da bai rik’e ba da ta d’ago da niyyar karb’ar wayar amma sai ta ji ya had’a da nashi hannun da wayar ya rik’e, da sauri ta d’ago kanta ta yi kalar tausayi tace “Da zafi fa,ka bani wayata mana.”Yanayin kallon da yake yi mata babu ko kyaftawa had’e da murmushi ne ,yasanya ta yi saurin mayar da kanta k’asa. Taku d’aya ya yi ya matso daf da ita,sannan ya yi k’asa da murya a hankali yace “Da gaske kina son dimples d’ina?”D’aga masa kai ta yi alamar ‘eh’. Sannan ta d’an yi taku d’aya ta yi baya Sake takowa ya yi kamar d’azun ya matso da gefen fuskar sa kusa da tata yace “Tou bara in goga miki,kema ki zama mai dimple, kinga sai mu Haifa Yara masu dimples hud’u.”Yayi maganar yana matso da gefen fuskarshi har yana gogar kumatunta,ba ta san ya akayi ba kawai ta ji ya sakar mata light peck a gefen fuskartata,tana k’ok’arin matsawa taji ya yi saurin ruk’ota ta hanyar rik’e mata gefen cikinta.“AAIMA!!!”Suka ji an fad’a cikin tsawa,Da sauri ta juyo,a tsorace. Karkarwa jikinta ya fara yi sakamokon had’a ido da tayi da yayaynta ransa a mugun b’ace.Sak’k’owa ya fara yi daga benen cikin sauri mai had’e da d’an gudu,yana tafe yana k’ok’arin kwance belt d’in jikin wandonsa, kafin ya k’arasa sak’k’owa kuwa har ya k’arasa zaro belt d’in ya rik’e ta a hannunsa,gadan gadan ya yi kansu.A take Aiima ta fasheda kuka tun kan a daketa,ta fara kiran “Mammy!!” da k’arfi.Mammy da anty Adama da suke kitchen ba su ji shigowar Auwal ba amman tun lokacin da ARSHAAD ya kwala kiran Aiima sukaji suka fito da saurin su.Ganin Arshaad ya yi kan Aiima da belt ne ya sanya Mammyn k’arasowa da sauri ta shiga gabanta ta tsaya tace”Arshaad meye haka?lafiyarka kuwa?”Anty Adama kuwa ganin Auwal a tsaye yasa ta kafeshi da idanu kafin ta ce”mai ya faru?”Sai a lokacin ma shi Arshaad ya lura da Anty Adama a wajen dan gaba d’aya idanunsa sun rufe ransa ya yi mugun b’aci!! Ya so ace yau ya damk’i Yarinyar nan wallahi da sai yayi mata mugun dukan da sai ta yi jinya tunda ya lura kunnen k’ashi gareta kuma ta raina shi, ba sau d’aya ba ya sha ja mata kunne ya hanata shiga harkar Auwal amman ta k’i yarda inda ace Aslam ne ya yi mata magana ya san da tuni ta bari……Maganar Anty Adama ce ta katse masa tunani,jin ta sake cewa “Wai kai Auwal ba da kai nakeba?mai ya faru wai?me kuka yi mata take kuka??”Saurin katse ta Auwal yayi yace”Nooo,Mom bani baneba!!”ya yi maganar cikin d’aga tafukan hannayensa biyu kamar za a yi arresting nashi yana tab’e baki,alamun shi fa ba ruwanshi,kafin ya ci gaba da cewa “ta yaya zan sakata kuka? Zance na zo fa.D’azu da muka yi waya da ke kika ce mini kun dawo,shine nace bara inzo in ganta kuma in gaida Mammy,kin ganni daga office wallahi ko wanka banje na yi ba na zo nan mu gaisa,shine fa yana hango mu tare ya zaro belt ya yo kanmu zai dakemu!”Kallon mamaki Arshaad ya tsaya yana yi mishi ganin yadda ya d’aure sa da jijiyoyin jikinsa,dukda kuwa yadda ya san halin Auwal sarai na iya juya al’amari….haka yake tun suna Yara kamar mace wajen iya makirci,kaf cikin mazan estate d’in sai da ya san yadda yayi kutun kutun ya kawar da kowa ya zama na right hand d’in granpa,yanzu haka shine MD , granpa ya d’aurasa a kan komai saboda shi sai end of the month yake shiga office , ko kuma in akwai Manyan Bak’in da suka zo ya kanje ya gansu, ko kuma wani important meeting,shima still Auwal d’in yana nan manne da shi baya barin kowa ya je jikinshi sosai, idan ma ya ga kuna shiri da granpa d’in to sai ya san yadda yayi ya had’a maka gurmi an maka fata fata.“Wai Arshaad sai yaushe za ka bar wannan mugun abu daka d’aukarwa kanka ne?”Ya ji muryan Mammy cikin fad’a, da alamun maganar Auwal ta yi tasiri akanta har ta kai ga b’ata mata rai.Anty Adama ce ta kalli Arshaad da duk kunyarta ta rufesa,gashi shi mutum ne mai kawaici ba zai iya fad’i a gabanta abinda ya ga Auwal d’in yayi ba .Takowa ta yi ta zo gaban sa ta tsaya sannan ta sa hannunta ta kamo nashi, cikin yin k’asa da murya tace“Son, please ku zauna lafiya kai da d’an uwanka mana,kowa yana son had’in nan nasu shi da Aiima ko dan zumunci ya k’ara k’ulluwa, but if there’s anything da kake gani ya sanya baka san Auwal d’in a tare da sistern ka just name it,I promise zanyi putting into consideration and if kanada gaskiya I’ll support u 100%.”“Bafa shi da wani reason da zai baki,kawai ke kin san halinsa ai tun suna Yara ba shiri sukeyi ba,abu kad’an sai fad’a,shine har yanzun basu san sun girma ba!!!ki barni da shi na san maganin sa”inji Mammy. Ganin bashi da niyyar yin magana ne yasanya Anty Adama ta cika hannunsa ta kalli Auwal tace masa “lets go””Mammy za mu k’arasa tattaunawa a waya.”“Ok” kawai Mammy tace mata…bayan sun fita ne ta maida hankalinta ga Aaima wadda ke durk’ushe a k’asa har yanzun tana gunjin kuka,Kamo ta tayi ta mik’ar sannan tace mata “goge hawayenki,daina kuka kinji auta wuce ki tafi d’akin ki.”Da saurinta ta zo ta wuce ta gaban Arshaad dan gani takeyi kamar zai kamota. Juyowa Mammy tayi ta kallesa sannan tace “Ko ba komai ni na haifeka atleast idan ka so abunda nakeso zan ji dad’i,ko dan Adama da zumuncinmu ya kamata ace ka yi hak’uri ka zauna lafiya da d’anta. Dukda na san taurin kanka da kuma yadda ka raina ni ba lalle ya bari ka yi abinda nakeso baamman ni dai ba zan gaji da fad’a maka gaskiya ba.”tana gama fad’in haka ta wuceshi…har ta d’an tsaya kamar za ta sake yin magana sai kuma ta juya ta nufi hanyar kitchen,suka barshi a tsaye a wajen…..Su Auwal suna shiga main parlour ya yi hanyar staircases d’in da yake a hannun dama,da alama ata nan side d’insa yake.“We’re not finished.”Ya ji muryan Mom d’insa.Juyowa ya yi ya kalle ta sannan yace “Let me freshen up first,Ina zuwa . Ya fara hawa stairs d’in da d’an sauri.“What did u do??”Ya ji ta sake tambayar shi. “A peck.”kawai yace mata, da ga haka ya ci gaba ta tafiyar sa ba tare da ya juyo ba. BULAMA✍️

Back to top button