Description/Story:
Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1! Written By Aisha Aliyu Garkuwa
Description Of Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1
Nakasarsa bata zama kasawa a gareshi, domin hausawa kance Babu nakasasshe sai kasasshe!
Y kasamce mai zarrar da ko lafiyayye marar nakasa bashi da irinta, Rayuwarshi madubine ga dukkan nakasassu, kana abar birgawace ga dukkan lafiyayyu kana abin so da sha’awar ko wanne bawa mai imani a zuciyarshi yadda sunanshi yake haka zahirinshi da bad’irinshi yake *SAIFUDDEEN* Muhammad Ahmadu managarci ne salihi mai yawan fasaha da tawakkali kekyawane irin ken da ke tsantsar haiba.
苼iggiren tushe da asalinsu Saifuddeen.
Asalin su FULANIN DUKKU NE NA JIHAR GOMBE.
DUKKU wani yankine daga yankunan Gombe wanda ya kasance yankin fulanine masu tsananin kyau uwa uba fulanine masu fafutukar neman ilimi na bank茩are biyu duka wato ilimin Arabic da kuma Boko.
Al’ummar Dukku sunyi fice da zarra tako wanna sashin shiyasa, suke ko ina cikin mutane masu daraja masu kima da cikar kamala.
DUKKU diyam sad’i na kosam
Malam Ahmadu shine kaka gasu Saifuddeen.
Malamu Ahmadu asalin bafullatanin Dukku ne gaba da baya, nannen tushensa iyaye da kakanni, babban Malami da babu kamarshi a fad’in Dukku a waccan lokacin.
Mafi akasari yaran garin a gunshi suke karatu, dan yanada tsankgaya mai girma , sai dai shi baya tara al’majirai, kowa yazo yayi karatu kana in an tashi kowa ya koma gida, shiyasa yaran anguwannin nesama suke zuwa karatu, kamar yaran Sirinkiyo, Katafila, Fada, da nan Dugge, kai wasu daga shabewa ma suna zuwa makarantar, wanna yasa ya shahara a cikin Dukku domin masarautar Dukku da kanta tanaji dashi, domin shine limamin masallacin fada.
Allah ya azirta shi da kadararorin filayen cikin garin Dukku da tarin gonaki wanda yawan cinsu ya gajesu ne a wurin mahaifinshi wanda sune suka sari dajuka da tsaunikan Dukku da kewaye kasan cewar wancan lokacin ba’a saida gonaki saida ka shiga daji ka sari fili ka gyarashi shike nan ya zama naka wahalakar ya mallaka maka shi.
Malam Ahmadu yanada matarsa d’aya mai suna Bintu Allah ya azurtasu da yara uku.
Babban d’ansu sunanshi Muhammad Bella shine mahaifinsu Saifuddeen, sai mai binshi Aliyu sai autarsu Aisha suna kiranta Dada.
Sun taso cikin had’in kai da tausayin juna, babu raini ko kad’an sai girmamawa da tausayawa.
Yayiwa yaranshi maza aure.
Bello mahaifinsu Saifuddeen kenan mutun ne mai mutunci da kamala yanada nitsuwa shiyasa aka had’ashi aure da d’iyar goggonshi mai suna Fatima amman ana kiranta da Bisije, yaranta ku su Saifuddeen suna kiranta Ummi.
Ummi kenan, wacce mahaifiyarta k’anwar Malam Ahmadu ne, Ummi marainiyace dan rana d’aya ta rasa iyayenta saka makon gobara da ya cisu dere d’aya, ita kuma lokacin an kaita yaye gidan kakunsu, shiyasa ta tsira, ba nisa tsakaninmu kakanin nasu suka rasu, shiyasa rik’onta ya dawo gidan Malam Ahmadun kawunta kenan.
Bello ya rayu da matsalar makarai tattare dashi, wanda yakan tashi time to time yana matuk’ar wahal dashi shiyasa, iyayenshi suka zab’i a had’ashi da Bisije Ummin kenan anaga tunda yar uwarshi ce zatayi hak’urin zama dashi, bayan an gama yin komai na buk’atun hidimar aure, sannan akayi auren Bisije da Bello, anyi biki lfy an watse lfy.
Ranar da aka watse abokan Bello na shirin rekoshi gidanshi inda yayi gina cikin asalin family house in nasu. kawai sai suka sameshi ya toni rami mai zurfi kana ya had’a k’irarai ya shirga itatuwa ya hura wuta, wai zai fad’a ciki,
nan abokanshi Ashiru da Hamisu sukayi kanshi da gudu suka kamashi, sai fizgewa yakeyi wai su barshi zai fad’a cikin wutar yana me ce musu.
Wai a k’asan wutan al’jannace su barshi ya fad’a ciki.
Wannan abu ya tada hankali yan uwa da abokan arzi a daren ranar dole Hamisu da Ashiru,
a gidanshi suka kwana don in an barshin zai kashe kansa, sabida makaranshi ne suka motso, k’aninshi Aliyu da Dada kuwa sai rarrashin Amarya suke, wacce taketa kuka.
To mafarin bak’in cikin Ummi kenan tun randa aka watse bikinta ta fara shiga toskun rayuwa sabida.
Daga ranar duk bayan wata biyar sai cutar Bello ta tashi wani lokacinma yakan tashi sau uku a shekara, sai dai Alhamdulillahi abun baya sashi duka ko fad’a sai dai yakan tashi tsakiyar dare yayita yawo yana zagaye cikin garin Dukku, kana duk inda ya samu masallaci sai ya tsaya yayi sallah raka’a biyu.
Sannan yana tafiya yana karatun qura’an da k’arfi.
Kafin gari ya waye sai muryarshi ta disashe, kana sawunshi su kumbura.
Mahaifinshi Malam Ahmadu dama yan uwanshi kab suna nema mishi mgn amman Allah baisa anyi dace ba.
Haka shekaru sukayi taja Ummi tana ta hak’uri da d’an uwanta mijinta, koda kawunta yayi yunk’urin raba auren sai tayi ta kuka tace ita kam a barta dashi, acewarta in ita ma ‘yar uwarshi ta gujeshi wa zai zauna dashi, dole Malam Ahmadu ya barsu yana mai ci gaba da yiwa d’anshin addu’ar samun lfy.
Har tsawon shekaru da dama, inda Allah ya azurtasu da yara shida uku maza uku mata.
Nuruddeen shine babba sai Rahma, kana Saifuddeen sannan Raihana sai Raliyya sannan Auta Hayatuddeen sakalin Ummi da Hamma Saifuddeen.
K’anin Bello Kuma Aliyu har yau matarsa bata tab’a koda b’ariba.
Su Nuruddeen na kiranshi Bappa Ali, kana Dada ma tayi aure suna kiranta Goggo Dada.
Ita kuma tunda tayi haihuwar fari bata kumaba, Ahmad shine sunan d’an nata kuma sa’an Saifuddeen ne.
Ana cikin haka ne kuma Allah yayiwa Malam Ahmadu rasuwa.
Mahaifinsu Abba kenan daga ranar kula da d’aliban ya dawo hannun bappa Ali, da kuma Abban in yana cikin haiyacinshi.
Kafin bintu ta fita takaba ne itama Allah ya mata rasuwa sakamakon cutar murd’a na dare d’aya.
Daga nan Abba da bappa Ali da goggo Dada suka k’ara ruggume juna bisa amana da gsky da tausayawa d’an uwan nasu.
Yara kuwa sun fara girma ciwon mahaifinsu na ci musu tuwo a kwarya musamman Nuruddeen da Raihana sai Saifuddeen wanda a lokacin yakeda shekara goma sha uku kana ya gama primary school inshi, har yaci gaba da secondary school inda yake JSS 1 shi kuwa Nurruddeen tuni yayi nisa yana Ss 3 Raihana Ss 2 da yake tsakaninsu da Saifuddeen akwai ‘yar tazara, a gefen Arabic kuwa tun sunada shekara goma sha bbbiyu sukayin sauk’an al茩ur’an mai girma.
So tuni Saifuddeen ya sauk’e Qur’an tun shekarar data gabata lokacin kanninsu na raye dan yanada 12 years yayi sauk’a kamar sauran yayunshi tuni ya meda hankalin kan hadda da sauran littafai da ake musu a isilamiyarsu.
Saifuddeen yana ta murnar zai tafi JSS two wata rana kwatsam ya tashi da wani irin azabebben zazzabi mai tsananin zafi, kwana yayi yana firgita, da safe kuwa yana tashi sai mura ba tari amman yanzu yanzu hancinshi na zubda ruwa kana hancin yayi jazazir hakama idanunshi,
ganin haka Ummi ta kama hannunshi taje ta nunawa wata makociyarsu tsohuwa iya shatu kakar Salisu abokin Saifuddeen, tana nuna mata jikin Saifuddeen d’in.
Tana gani tace k’end’ace bak’on daurane zata fito mishi ga kuma azabebben zazzab’in sank’arau daya rufeshi, haka yasa ta nemi tsink’aro da gero ta barzasu ta jik’ashi da ruwa sannan ta kurba sai ta fesa mishi a jikinshi,
cikin ikon Allah kafin dare duk Sun feso sun fito birjink a jikinshi har cikin tafin k’afafunshi zazzabin sank’arau kuma tamkar zai hallakashi.
Koda dare yayi Ummi ta d’aukeshi suka koma side inta,
abu kamar mafarki koda gari ya waye sai aka samu jikin Saifuddeen yayi sumut duk bak’on dauran nan ya b’ace ya koma cikin jikinshi ya k’ume yaro sai karkarwa yakeyi dan zafin zazzabi ga kuma sank’arau da ya hanashi sukuni wanda har cikin kunnenshi yakeji yana bada sautin dummmm,
ba irin mgnanin da ba’a bashi amman sunk’i su kuma fitowa a lokacin kuma ba’a wani damu da batun asibitiba ko riga kafinshi ba’a fiye yiba a garin.
haka dai Saifuddeen yayi ta shan wahalar sheretuwannan da zazzafan zazzab’in sank’arau daga k’arshe yayi sanadin kuram tashi.
Wannan al’amari ba k’aramin girgiza family ensu yayiba don Saifuddeen yarone mai shiga rai, gashi da nitsuwa da al’kunya
iyaye da da ‘yam suna matuk’ar sonshi ran da aka gane Saifuddeen ya zama kurma a ranar anga tashin hankalin Bello Abba kenan hakama Nuruddeen daya dawo makaranta aka gaya mishi, kuka yayi tayi dan duk k’annenshi yafi k’aunar Saifuddeen Hayatuddeen kuwa lokacin shekaranshi 4 so baisan meke faruwa ba yakan dai yi kuka in yaga suna kuka.
A Daren ranar jikin Abba ya tashi a wannan ranar ne karo na forko da ya rink’a ihu tamkar yaro k’arami.
K’arfe biyu dai-dai na dere ya kama hannun Saifuddeen dake bacci ya mik’ar dashi, kana ya jashi suka fito haka ya rink’a janshi koro-koro duk inda suka samu masallaci sai ya sashi suyi Al’wala suyi nafila raka biyu kana suci gaba da tafiya.
Saida akayi sallan asuba sannan suka dawo gida, nanma dan yaga Saifuddeen d’in yanata kuka.
Suna dawowa Ummi ta jawo d’anta ta ruggumeshi cikin kuka take tambayarshi ina sukaje, baki ya bud’e da nufin ya kuma gwada yin mgna amman ina ya kasa, hakan ya sashi kife kanshi jikin gini yana wani irin gurnanin azabebben kukan da duk mai imani sai ya tausaya mishi babu mai sanin zafi da kun’an da yakeji a ranshi sai wanda ya tab’a shiga irin wannan halin ace an haifeka lfy ranatsaka nakasa ta sameka, so yake ya bud’i baki ya yiwa Umminshi bayanin yadda yakeji amman ina Allah bai bashi damar hakanba ganin ya kuma kife kanshi jikin ginin ya sake zazzafan shesshek’an kukane yasa Yayanshi mik’ewa ya nufi inda yake.
Da Sauri Nuruddeen ya kamoshi,
hannu yasa ya tallabe kanshi cikin tsananin kuka da tausayawa k’anin nashi murya na rawa yace.
“Saifuddeen…!!!
File Name | Nakasa Ba Kasawa Bace 1… Hausa Novel Doc. |
Title | Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 |
Author | Aisha Aliyu Garkuwa |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Fiction Story |
Published Date | 07/08/2024 |
File Size | 1020KB |
Format Size | TXT |
Book Price | 500 |
Phone No | 09097853276 |
Download Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 By Aisha Aliyu Garkuwa
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.