Budurci: Dalilin Da Ya Sa Mata Da Dama Ba Sa Ganin Jini A Daren Farko A Gidan Miji
Budurci: Dalilin Da Ya Sa Mata Da Dama Ba Sa Ganin Jini A Daren Farko A Gidan Miji
Ba za ka iya kirga adadin aurarrakin da suka mutu a sakamakon rashin fitar jini daga gaban amaryar da angonta ya aureta a matsayin budurwar da shi zai buɗe ta. A yadda muka dauka shi ne, sai ango ya ga amaryar sa kaca-kaca cikin jini a daren su na farko, shi ne zai tabbatar masa da cewa amaryar tasa bata taɓa sanin wani namiji ba.
Ita kanta amaryar cike ta ke da fargaba na ko angon nata zai tono jini ko kuma a’a ko da kuwa ta san ba ta taɓa aikata lalata da wani namiji kafin aur ba. Ba sabon labari bane ba a wasu zamaninnika da suka gabata cewa, har jefar da amaryar a ke yi da zarar mijinta ya yi saduwar farko da ita kuma jini bai fita ta gabanta ba.
Karanta>>> Yadda Ake Hada Sabaya Don Murjewar Jiki Da Kuma Tayar Da Nonon Da Ya Zube Ko Ya Kwanta
Har farin kyalle ake shimfidawa akan abin kwanciyar amarya da ango a darensu na farko don a tabbatar da zubar jini daga gaban amaryar, kuma cikin alfahari za a yi ta yawo da ƙyallen ana nunawa manya fa cewa “Wance bata zub da mutunci ba kafin ta yi aure.
Wannan dabi’a ta fitar jini daga farjin mace a daren farko ba mu kadai ke da ita ba. Mutanen Pakistan, Indiya, Bangladesh, Afghanistan da sauran ƙasashe, na da irin wannan tunani na cewa dole sai jini ya fita daga gaban mace a jima’inta na farko. Kuma idan har ta sadu da namiji a matsayin saduwar farko, kuma bai ga jini ba, to lalle ta taba saduwa da wani kafin shi kuma a wancan saduwar da ta yi, jini ya fita.
Karanta>>> Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku BiKi
Ganin Jini A Daren Farko Na Aure:
Wannan batu namu ya zo ne da nufin ƙaryata wancan tunani da ke cewa wajibi ne macen da ba ta taɓa saduwa da da namiji ba ta fitar jini ta gabanta a yayin saduwarta da da namiji a daren farko. Wannan ko kusa ko alama ba gaskiya bane. Batun shi ne, ba kowace mace ce ke fitar da jini a lokacin da namiji ya kawar mata da budurcinta ba, Wasu na fitarwa, wasu kuma basa fitarwa, kuma hakan ba ya na nufin lalle ba wankakkun ‘yan mata bane don basu fitar ba.
Domin fahimtar dalilin da ya sanya wasu mata ke fitar da jini wasu kuma akasin haka a daren su na farko, ya kamata mu fahimci cewa akwai wata fata ko tantani wacce ba tada kwari da ke rufe farjin mace tun daga haihuwarta. Fatar ba wai tana rufe kafatanin farjin mace bane. Hasali ma dai, ba kasafai a ke samun macen da farjinta ke lullube da tantanin budurci ba.
Karanta>>> Maganin Toilet Infection Da Kuma Rashin Sha’awa Ga Mata
Wani abu da ya kamata mu ƙara fahimta a nan shi ne, ba dukkanin mace ba ce ke da wannan tattani na budurci a lullube a gaban farjinta. wasu mata ke dauke da fatar a lullube da gabansu, wasu ‘yar kadan ce, wasu rabin farjinsu, wasu kaso biyu bisa uku da dai sauransu. A saboda haka, mace mai tantanin budurci mai kauri (wanda ya lullube gabanta gaba daya) dole za ta fitar da jini a daren farko sakamakon sai namiji ya fasa wannan tantani kafin ya samu ya shigeta.
Ita kuma mace mai matsakaicin tantani, dole jinin da za fitar ba zai kai na wancan ta farko ba. Haka abin zai kasance har zuwa kan wacce sam ba ta da tantanin budurci. Ita wacce ba ta da wannan tantani, ba ta fitar da jini ko a daren su na farko.
Karanta>>> Sakonnin Soyayya Na Mata Na Barka Da Shan Ruwa Ga Samarinsu 2023
Ga yawancin mata, wannan tantani na ficewa da kansa sakamakon yin abubuwa na motsa jiki kamarsu tuƙin keke, sukuwa a kan doki, wata ma daga yin rawa ko kuma ta hanyar yin amfani da ƙyalle a maimakon auduga a yayin al’ada. Wannan na faruwa ga mace da ke dauke da tantanin budurci wanda bai da ƙwari.
Yana da kyau mu fahimci cewa, tantanin budurci na shafewa da kansa bisa dalilin girman mace. Anan muna nufin, mace mai ƙarancin shekaru (kamar shekaru 16 ko kasa da haka) na da yiwuwar fitar da jini a jima’i na farko sama da ‘yar shekaru 25 zuwa sama.
Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata
Ya kamata maza su fahimci cewa, sau tari ba ma tsagewar tantanin budurci ke haifar da jinin da mace ke fitarwa a daren farko ba, a’a, wasu mazan kan gaza yin haƙuri ne su bi matan a sannu a hankali ta yadda za su shiga matan har su kai ga yi musu rauni a gabansu wanda shi ne a lokuta da dama ke haifar da fitar jini.
Da’a ce maza da dama na fara yin wasa da mace na tsawon lokaci ta yadda har sai ta kamu ko ta buƙatu, da da dama ba a za ga fitar jini ba a gaban mace ko dai ta hanyar yi mata rauni ko ta hanyar fasa tantanin budurci.
Karanta>>> Amfanin Zobo Ga Lafiyar Jiki Da Kuma Illolinsa
A takaice dai, babu wata hanya takamaimai da mutum zai iya tabbatar da cikar budurcin mace ko akasin haka. Fitar jini ba hujja ba ce, saboda fitar jini ya danganta ne ga irin tantanin budurcin da mace ke ɗauke da shi tun daga lokacin da aka haifeta. Akalla, kaso 63 na matan duniya ba za su fitar da jini ba a lokacin daren su na farko. Kaso 37 ne bisa hasashe za su fitar da jini a daren farko bisa bincike mai inganci da aka wallafa a wata mujallar lafiya ta kasar Ingila.
Samun ilimin budurci na da matukar amfani ga maza da mata, musamman ma maza. An zargi mata, an wulakantasu, an ci zarafinsu, aurensu ya mutu, a shekaru da dama da suka gabata ma an jefe mata kawai don ba su fitar da jini ba a daren farko. Wannan ilimi ko shakka babu zai taimaka wajen kare mutunci da muhibbar mata, tare da fitar da su daga zargin mazajen aurensu, iyayen su da danginsu.
Karanta>>> Maganin Kowacce Irin Cuta Da Izinin Allah.
Mu kiyaye, ba duk wacce bata fitar da jini a daren farkonta ba ce, wacce ba ta da budurci. Don Allah a yaɗa don al’ummata ta amfana. Allah ta’ala yasa mudace, ƴan mata a kwantar da hankali a bar tsoron Daren farko.
sai dai kuma kada ki yi amfani da wannan damar wurin bin maza ko lesbian sanna ki fake da wannan.
Kai dai kayi addu’ar samu mace tagari sannan a cire son zuciya da makauniyar soyayya.
Karanta>>> Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi