Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 7/8
https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share
________________Ihu jauro ya kurma mai Æ™arfin gaske ya faÉ—i can gefe yana burbura tare da rikan “wayyo haroji jaurota zai cinyemin ka taimakeni zan mutu wayyo maciji “ya Æ™arasa faÉ—a da kyar sakamakon wata danÆ™a mai Æ™arfi da macijin nan yayiwa jauronsa har saida numfashinsa ya É—auke .
Haroji kuwa ya mugun tsorata ganin halin da jauro ke ciki,ga wannan ƙaton macijin daya kanannadeshi yana ƙoƙarin karya masa ƙasusuwa.
Cikin kiɗima ya rarumo wani ƙaton dutse yayi kan jauro da wannan macijin,yana zuwa baiyi wata wata ba ya ɗaga dutsen ya kwaɗawa macijin nan abayansa.
Aikuwa nan da nan bayan macijin ya fashe jini yayi tsartuwa har kan fuskar haroji,wani ihu haroji ya kwala ,sakamakon sauƙar jinin macijin nan akan fuskarsa ji yayi kamar an watsa masa ruwan batir,nan da nan gurin ya sale kamar wanda ya ƙone sai turiri gurin yake.
Jifa haroji yayi da dutsen hannunsa yana ihu yana faÉ—in”wayyo Allah idona bana gani wayyo kwayar idona ta zazzage na shiga ukuna “abinda yake daÉ—i kenan yana ihu da tsalle.
Shikuwa macijin nan silalewa yayi daga jikin jauro ya koma gefe guda tare da kwantar da kansa akasa ,dan kuwa sosai haroji ya kwada masa dutsen nan,kuma da alama ya shige shi .
Gaba ɗayan abinda ke faruwa akan idanun fattu ,tana kwance tana kallon ikon Allah,tabbas zuwa yanzu ta gama yarda cewa macijin nan bashi da biyar cutar da ita ,saima taimakon ta da yake,shin wanene wanan macijin?meye alaƙarta da shi?me yake nema agurinta?anya ma MACIJINE wannan ?kodai aljanine yake zuwa mata asiffar macijin? Wadanna sune tarin tambayoyin da fattu ke yiwa kanta tana daga kwancen wanda bata da amsarsu.
Saidai kuma gaba ɗaya hankalinta ya tashi ganin yadda macijin nan ya kwanta lamo kamar ya mutu.nan da nan tsoro ya mamaye zuciyarta ,cikin dauriya da jarumta ta yunƙura ta miƙe tsaye tana yamutse fuska,hannunta mai ciwon yana riƙe aɗaya mai lafiyar.
Gurin macijin ta nufa gabanta na ci gaba da faɗuwa,dan tsoro take kar ita kuma yayi mata wani abu.tana ƙara sawa ta durƙusa ahankali dai dai inda haroji ya buga masa wannan dutsen ,hannu ta sanya ahankali ,cikin karkarwa jiki ta ɗan shafa gurin ciwon.ai tana ɗora hannunta agurin macijin nan yayi wata irin juyowa tare da fasa kai kamar zai sareta, cikin tsoro da fargaba ta cire hannunta tare da matsawa baya da sauri tana zare ido tana kallon macijin.
Shima yana juyowa yaga fattu ce ,sai ya tsaya yana kallon ta,tare da komawa yadda yake ,wato ya sassauta fusatar da yayi ,kawai ya tsaya yana kallon ta.
Itama kallonsa take cikin tsoro da bugawar zuciya,ahankali macijin ya fara tahowa ,har ya zo gareta ,runtse idanu tayi tana karanta addu’ar Allah ya tsareta.
Ga mamakinta kawai saitaji macijin ya hau kan cinyarta ya kanannaÉ—e jikinsa ya dora kansa a saman gammon da yayi da jikinsa.
Ahankali ta buÉ—e idanunta tana kallonsa,shima ita yake kallo saidai idanunsa na zubar da hawaye kuma na jini .
Jikinta kawai rawa yake cike take da tsantsar tsoron abinda zai faru .juyawa tayi tana kallon haroji dake ta faman ihu yana yaÉ—uwa kasa.sannan ta kalli jauro wanda yake kwance ba alamun numfashi atare dashi,ga jauronsa nan tayi wani irin kumbura na ban mamaki sai jini ke zuba .
Tsorone ya ƙara kamata cikin azama ta yunƙura tare da mikewa tsaye, ture macijin tayi daga jikinta ta kwasa da gudu tayi gida tana kuka .
Koda taje gidan, da sanÉ—a tayi saurin shiga É—akinta tana kuka,zama tayi akan tabarmarta tare da kife kanta a tsakanin cinyoyinta tana kuka.damuwace fal cikin ranta,wai meke shirin faruwa ne da rayuwarta?wacece mahaifiyarta?waye wannan macijin da yake É—aukan hukunci akan duk wanda yayi nufin cutar da ita?tanasan sanin wannan macijin waye shi,kokuma waye ya aikoshi gareta.tana cikin kukanta ne kawai taji abu yana hawa jikinta silililili!!! Afirgice ta É—ago kanta tana kallon macijin daya gama hawa jikin nata. kansa ya É—ora akan wuyanta yana fidda wani irin huci ,shiru tayi tana sauraron yadda macijin ke huci,sanan jikinsa yayi wani irin zafi sosai.duk yadda akayi bashi da lafiya ,kuma dukan da haroji yayi masane solar hakan.
Tausayinsane taji yayi mugun kamata,ahankali cikin tsoro ta miƙa hannunta tare da riƙo saitin wuyansa ahankali ta janyoshi, ko motsi baiyi ba bare ya hanata abinda yake yi ɗin.
Akan tabarmar ta É—orashi tare da ci gaba da kallonsa,cikin muryar kuka tace “bawan Allah kai waye?meke tafe dakai?waya aikoka zuwa gareni?meyasa kake Æ™oÆ™arin daukar mataki akan duk wanda ya zalumceni?dan Allah karka cutar dani, bani da kowa sai baffana,dan Allah kayi tafiyarki ,idan mutanen garin na suka farga da kai zasu kasheka ,bazan so hakan ba dan Allah na roÆ™eka ka tafi”ta Æ™arasa maganar tana haÉ—a hannunta cikin kuka.
Shidai macijin nan ko motsi baiyi ba sai huci da yake yi sosai,
Ahankali ta kalli gurin da yaji ciwo dazu sai taga gurin yana turiri kuma yayi wani fari fat.shiru tayi tana kallonshi ,yanzu ya zata yi masa ne?dan da alama fa yana jin jikine, data rasa abinyi kawai saita lulluba zanin sallarta ta fara karatun Alqur’ani mai girma.cikin abinda bai wuce sakwan biyar da fara karatunta ba kawai macijin nan ya fara wata irin murmurÉ—ewa yana sauya kala, da farko yayi jajur dashi,sai kuma yazo yayi baÆ™iÆ™irin sosai ,wani irin hayaÆ™i na fita daga jikinsa .
Duk abinda yake sam fattu bata kulaba ,dan ta É—aga kanta sama ne tana karatun ,kuma idanunta na zubda kwalla.
Shikuwa macijin nan burburwa ya ci gaba dayi yana murɗewa jikinsa na turiri tare da sauya kala.can kuma ya fara wani irin ƙara mai kama da gurnanin zaki.cikin tsoro fattu ta dawo da kanta ƙasa tana kallon macijin , sakamakon wannan sautin ƙara da taji yanayi.sai lokacin hankalinta ya kai kanshi taga abinda ke faruwa.
Tsorone ya kamata Æ™arara “innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”shikenan ta tabbata wannan ba maciji bane tabbas aljanine ,ko kuma aljanine ya shiga jiki sa,na shiga uku ni fattu ya zanyi da rayuwata?meke shirin faruwa dani” ta faÉ—a cikin muryar tsoro da shiga ruÉ—u.
Shikuwa macijin nan tana daina karatun saiya daina burburwar da wanann gurnanin,ahankali kuma jikinsa ya dawo yadda yake . Ya jima kwance lamo kafin ya fara motsi,kansa ya É—ago tare da fasa kan yana kallon fattu,gaba É—aya idanunsa sun koma baÆ™iÆ™irin dasu sannan wasu irin Æ™ananan layoyi suka bayyana kusan guda uku aÆ™asan kanshi, sai wani irin motsi suke kamar ya’yan tsutsa.
Karkarwa jikin fattu keyi kamar an saka mata shokin, lamarin ya matukar bata tsoro ,meye wannan É—in haka suka bayyana jikin macijin nan? Me yasa daga fara karatun Alqur’ani gaba daya ya sauya kama?tabbas akwai wani boyayyen al’amari game da wannan halittar dake gabanta,kuma zata ci gaba da bibiyar macijin nan sannu kan hankali har saita gano menene tattare dashi.
Tana nan maƙale jikin katangar karanta kamar ƙadangaruwa dan tsabar tsoro da shiga shock ,idanunta ƙuri akan macijin ,wanda shima ita yake kallo ,kusan minti biyar suna haka ,taga macijin ya sulale ya bar ɗakin ta wannan hanyar tashi.
Rarraba idanu ta farayi tana dafe da Æ™irjinta ,yau kam tana ganin ikon Allah kala kala ,anya kuwa bata janyowa kanta masifa ba?waima meye alaÆ™arta da wannan halittar ne?ko dai baffanta zata sanarwa halin da ake ciki ne?kai a’a ba yanzu ba tukunna ,ya kamata ta zama jaruma tayi wanann aikin koba komai zata taimaki rayuwar macijin,dan ta fahimci akwai boyayyen al’amari atareda shi.
Su haroji kuwa gaba É—aya ya fice daga hayyacinsa sai ihu yake yana faÉ—uwa Æ™asa ,ahaka ya nufi gidan lamiÉ—on garin ,wanda shine mahaifin jauro ,yana ihu yana tumami, har yaje gaban lamiÉ—o ya faÉ—i yana “wayyo idanuna ,wayyo fuskata lamiÉ—o ka taimaka min.
RuÉ—ewa lamiÉ—o yayi wanda yake tsaye jikin wata sanuwa yana bata ciyawa, lamiÉ—o bashi da imani ,azalumine sosai ,kuma mutanen garin suna matuÆ™ar tsoronsa, dan haka yake mulki na zalumci agarina,ganin halinda haroji yake ciki”kai haroji menene hakan ?ina jauro?me yasameka?sune tambayoyin da lamiÉ—o ya jerowa haroji
Cikin azabar ciwo da fitar hankali haroji yace “jauro ya mutu maciji ya cinye masa jauronsa yana bakin rafi”
Ai dajin wannan batu hankalin lamiÉ—o ya tashi ,nan da nan yayi kan haroji yana faÉ—in wane macijin ?me kake cewa ?jauro ya mutu?Æ™aryane badai agarina ba ,ba wanda ya isa ya zo garina ya kashe min É—ana.”lamiÉ—o na gama faÉ—in haka ya kira mazan garin ,ya sanar dasu maza aje bakin rafi ataho da jauro.
Aikuwa cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗauko shi kamar gawa .
Nan da nan lamiÉ—o ya nemi haroji ya sanar dasu abinda ya faru .
Nan ya sanar dasu iya abinda idanunsa suka gani,dan shima yana cikin mugun halin mutuwa ko rayuwa dan tuni gurin da jinin nan na macijin ya taɓa ajikinsa yayi wani irin kore shar yana zubar da wani yallow ɗin ruwa .
“LamiÉ—o fattu ce ta Turo mana macijin nan ,shine ya kashe jauro”abinda haroji ya faÉ—a kenan ya sume.
Nan da nan mutanen gurin suka fara maganganu Suna faÉ—in da “da hansai ta faÉ—a tace mayyace yarinyar ,tunda har ta fara kashe mutane ba zasu yarda ba sai an hukunta itama.
Ran lamiɗo ya ɓaci sosai ,dan dama yana jin haushi yarinyar da ubanta,ya shirya neman aurenta amma sam taƙi yarda wai karatu take,yanzu kuwa dama tasameshi da zai hukunta su ita da tsohon nata.dan haka cikin bada umarni yace lallai lallai aje ataho da fattu da ubanta .
Nan da nan fusatattun maza suka nufi gidan malam bukar dan aiwatar da Æ™udurin lamiÉ—o……..
Masu karatu meke shirin faruwa ne ?
Wane hukuncin lamiÉ—o zai zartar akansu fattu?
Mai zai far nan gaba?
Muje zuwa yaki ce dai anty mammy
Mrs babi💘💘💘
Share and comments fisabilillah.
More comments
More typing.