Hausa novels

Wace ce ita Chapter 56 Complete Novel

NOTEWORTHY WRITERS ELITE✍️

Unique Barakancy🌹

*WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)*

FIFTY-SIX📍

Juyowa tayi taga daya daga cikin me aikin gidan tashigo parlourn, suna hada ido ta koma da sauri batareda ta dauki abinda aka aiko ta ba, dawo da kallonta kan Deen tayi da har lokacin yaki sakar mata hannu, kamar zatayi kuka tace;
“Dan Allah ka bari mana”….
Dagowa yayi ya kalleta tayi saurin yin kasa da kanta, sake rungumota yayi ya maida yatsun cikin bakinsa ya cigaba da tsotsa kamar wani jariri, idan ya saka guda biyu ya tsotsa sai ya cire ya saka wasu, haka ya dinga tsotson duka yatsun goma, sosai ta fita hayyacinta gashi takasa janyewa saboda tsattsauran rukon daya mata, tsabar jaraba hannun har zugi yake mata ga wani ja dayayi, har gane hakan akeyi ta spaces din da aka bari ba lalle dake lallen irin me yankan celotape dinnan ne…..
Sai da ya tsotsi yatsun son ransa sannan ya saketa a hankali yana sakin hannun….
Saida ta tsorota da suka hada ido dashi saboda yanda idonsa yayi ja ya chanza kamanni, mikewa tayi da sauri tana shirin guduwa idonsa ya sauka akan lallen kafarta, ba shiri ya mai da ita inda ta tashi yana zama a gabanta, kawai sai jin saukar bakinsa tayi akan yatsun kafarta, rintse ido tayi tana jin kamar kanta ze rabe gida biyu tsabar tsoro ga wani zirr da takeji kamar ana mata tafiyar tsutsa, shi ko besan ma tanayi ba dan abinda yasa a gaba shi kawai yake gani….
Sosai ya shayar da ita ruwan mamaki dan bata taba tunanin ze iya stooping low haka ba, tana ganin kazantar lashe mata hannu dayayi shine ze nuna mata bataga komai ba…..
Tana cikin wannan tunani taji lashe lashensa ya fara haurowa saman kafarta, ai batasan sanda ta hankadashi ba Allah ya taimaketa lokacin ya sassauta rukon daya yiwa kafar, ta kwasa a guje tayi hanyar sama, saida ta ganta ta fara hawa stairs sannan ta daga murya da karfi yanda zeji tace;
“Maye! Kazami kawai!”…..
Yajita sarai amma ko motsi ya kasa saboda yanda mararsa ta wani irin rikewa, kwanciya yayi a kasa hannunsa dafe da mararsa…….
Besan minti nawa ya kwasa a haka ba, sai jin muryar umm yayi akansa;
“Lafiya ka kwanta a kasa haka?”….
Tashi yayi zaune cikin muryarshi da bata fita sosai har lokacin yace;
“Lafiya umm, sannu da zuwa”……
Guri ta samu ta zauna tana fadin;
“Yauwa, baka da lafiya ne?”….
“Lafiya lau nake umm, kawai bacci ne ya kwasheni, yaushe kuka shigo?”…
“Tin dazu, muna dayan building dinchan nawa kasan bakin dayawa dole muka bude chan din ma, ka tafi part dinka ka kwanta mana”….
“Banajin baccin kuma, amma umm it’s the taron necessary?”…..
“Anna da bappa insisted”….
“But….”…..
“Shhhhh! Yanda anna da bappa keso haka za’ayi! You can excuse me!”……
Mikewa yayi da niyar tafiya kamar yanda ta umarta, saidai ko kafin ya kai bakin kofa yaji murya mami cikin masifa tana fadin;
“Dawo! Dawo! Dake kasan baka da gaskiya zaka gudu”…..
Dawowa yayi mamaki dauke akan fuskarsa na rashin gaskiyar da akace yayi…..
Hannun baby tee mami ta dago tana nunawa umm tace;
“Kalli hannunta dan Allah , ya za’ayi da girmansa da komansa ya ciji yar yarinya, wannan wani kalan mugunta ne?”…..
Baki sake umm ta kalli hannun tace;
“Cizo? A duka yatsun? Tadai fadi gaskiya ko abu me nauyi ta dauka hannunta yayi ja”……
“Bawani abinda ta dauka, dududu yaushe muka shigo gidan? Kuma ko kwaso kaya ba’ayi a mota ba haryanzu, kawai muguntarsa ce, ai babu abinda baze iya ba”…..
Unbelievably umm ta kalli Deen tace;
“Saif dagaske kai kama yatsunta daya bayan daya ka ciza?”…..
Dagowa yayi yana kallon baby tee mamakinta na kara kasheshi, shi ya rasa gane meke damunta, wauta ce ko makirci ne, wato bazata kyale ba shine taje ta fadawa mami ya cijeta sai kace yaro karami, ita kuma mami dake ta riga ta masa bakin penti ta hau ta zauna akai, girgiza kai yayi yace;
“Umm I have no idea what she’s talking about, nida nake bacci anan”….
“Nima abinda nagani kenan, I met him sleeping here, yanzu nace ya tafi ma”…
Umm ta fada tana kallon mami….
Karap baby tee tace;
“Kafin ya fara bacci fa ya cijeni, tundazu fa nashigo”…..
“Umm karya takeyi ni ban cijeta ba”….
“Wallahi ya cijeni, har a kafa ma”….
“Ta ina ake cizan mutum a kafa?”…
“Ta inda kabi ka cijeni mana”….
Tsawa umm ta daka musu tace;
“Dalla kuyiwa mutane shiru! Wa kuka maida shashasha daze zauna yana sauraron shashancinku, sa’anki ne da zakina masa rashin kunya? Yana fada kina fada a gabanmu? Kai kuma jiya kazo kace ta fita munje munga tana bacci, ke kuma yau kinzo kin fadi abinda hankali baze dauka ba, wai ya cijeki a duka yatsu da kafa, toh duk ku kama kanku wallahi sannan daga yau zan baku last warning, kar wanda ya sake zuwa ya tunkaremu da shirmensa, ku wuce ku bawa mutane guri, marasa da’a kawai!”…..
Barin parlourn sukayi dukansu, Deen yayi hanyar waje ita kuma baby tee ta haura sama sai kumbure kumbure take……
“Gaskiya ki dena min haka umm, yarinya da gaskiyarta zakiyi disregarding abu”…..
Mami ta fada tana zama gefen umm….
“Bawani gaskiya a maganarta, ki dena biyemusu dan Allah, wayen’nan biyun sai su sawa mutum hawan jini”…..
“Bawani nan, ni dai ina bayan namesake”….
Mami ta fada tana dariya…..
Murmushi umm tayi tace;
“Au abun hakane? Nima sai in koma bayan saif dina”…..
“Hahaha dama ai a bayansa kike tintini, jiya daya kawo kara ai kin binshi kingani, sai yau za’a gwale min ya”…..
“Lamarin baby tee ne harda rashin kunya mami, ni kuma banasan haka shiyasa kikaga ina tsawatar mata, kuma shima saif din ai na hada dashi”…..
“A duki mutum a hanashi kuka ba, wani rashin kunya tayi? In shi be zubar da girmansa ba ai bazata renashi ba”…..
Umm zatayi magana kenan wayarta ya fara ringing…..
“Ameen ne ke kira, ko sun karaso ne”…
Ta fada tana amsa wayar…..
Sauke wayar tayi da farinciki a fuskarta ta kalli mami tace;
“Sun karaso fa, amma sunyi transit a kano, yanzu zasu karaso abuja”…..
Dariya mami tayi tace;
“Masha Allah, yau anna zataga dan autanta”…..
“Wallahi kuwa, bari ince saif ya fara shirin daukosu kafin su karaso”…..
“Eh yaje ya jirasu kawai”….
Kiranshi umm tayi a waya ta sanar masa, amsawa yayi da toh sannan ta kashe wayar….
Tana kashe wayar kiran Abby ya shigo mata, silencing wayar tayi ta sakata a do not disturb batareda mami ta sani ba…..
Saida umm da mami suka kara inspecting gidan suka tabbatar komai is in place kafin suka tafi shiryawa, saida mami ta biya ta bedroom din baby tee tace ta sake wanka ta shirya itama dake lokacin ankawo kayanta daga fashion house din mami….. Wanka tayi ta shirya cikin wani newly designed abaya daya burgeta, sosai kayan suka amsheta kuwa kamar dan ita akayi…….
Saida Deen ya kira umm ya sanar da ita kafin ya tafi, kamar tace su tafi da baby tee wata zuciyar tace kar suje suyita rigima, kawai ta mishi Allah ya kiyaye hanya ta kashe wayar…..
Tinda suka kira Deen yace musu sun shigo layin gidan suka fito suna jiran isowarsu a harabar gidan, dake yan maiduguri sai bayan isha zasu karaso, kana kallon fuskar kowannensu kasan suna cikin madaukacin farinciki har da baby tee da ranar zata fara ganinsu itama, gwarama umm dake ko last year sunje gurinta a England, mami ko tafi 5 years bata gansu, anna da bappa har sun gaji da complain din ameen yaki zuwa da iyalinsa…
Horn akayi me gadi ya tashi ya bude gate da sauri, tun kafin Deen ya daidaita parking suka karasa parking space, fitowa sukayi su twins sukayi kan baby tee suka rungumeta kamar sun santa, rungumesu tayi itama tanajin sonsu aranta tashin farko….
Hada umm da mami uncle A yayi ya rungumesu, cikin zolaya yace;
“Bari in fara rungume yan kannena tinda twins sun kanainayemin ya”….
Mintsininsa mami tayi tace;
“Dan rainin hankali zakaga kannenka kuwa, ni sakeni mu gaisa da ruwaida”….
Sakesu yayi sukaje suka rungume kyakkyawar matarsa ruwaida suna mata sannu da zuwa….
Sultan da yake kaninsu twins, shekara daya taakaninsu ya janye su twins daga jikin baby tee sannan ya rungumeta yana fadin;
“Ku kadai zakuyi hugging dinta ne, I miss you so much sis”…..
A take baby tee taji ya shiga ranta shima, rungumeshi tayi itama tana dariya tace;
“I miss you too bro”….
Dariya duka yan gurin suka sa ganin yanda sukayi kamar sun dade da sanin juna, banda deen daya rintse ido ya shige ciki…..
“Come hug me too baby”….
Uncle A ya fada yana bude mata hannu…
Sakin sultan tayi ta tafi ta rungemeshi…
“Nifa daughter?”….
Mamansu twins ta fada tana dariya…
Rungumeta tayi itama sannan suka rankaya suka shiga ciki sai hirar yaushe gamo suke, fadan irin farinciki da dukkaninsu keyi ma bata lokaci ne….
Suna shiga baby tee ta ja twins suka shige dakinta dayake duk sa’anni suke, sai labarin dubai suke bata, tana dai jinsu amma bata wani tofawa dukda ta taba zuwa dake bata da wani surutu, amma ba karamin shakuwa sukayi ba a dan kankanin lokaci…..
Bayan sun kimtsa sunyi komai akace kowa ya sakko ayi having appetizer kafin su anna su iso ayi dinner gabadaya….
Saida kowa ya hallara a parlourn sannan sukaga babu deen, uncle A ne yace;
“Ina mutumin nawa ya shiga ne?”….
Kallon baby tee mami tayi tace
“Yana part dinsa baby tee je ki kirasa”….
“Okay”…
Ta fada tana kokarin mikewa….
Sai kuma ta sunkuya daidai saitin kunnen hassana kasa kasa tace;
“Hassy zo ki rakani please”….
Kasa kasa hassy ta maida mata da fadin;
“A’a jeki ke kedai dan Allah, ni bansan abinda ze hadani da masifaffen mutumin chan”….
Batace komai ba ta sunkuya ta gefen hussy zata mata magana kenan umm tace;
“Kus kus din me kukeyi haka, je ki kirashi ki dawo mana”…..
Fasa yiwa hussy magana tayi, ta fita kamar zatayi kuka, aranta tana fadin ashe kowa ya sansa da masifa…..
A hankali tayi knocking a kofar part dinsa gabanta sai faduwa yakeyi, inda tana da yanda zatayi ma da komawa zatayi tace yace bayaci, ko dazu da ta kai kararsa gurin mami tayi niyar fadamata gaskiyar abinda ya mata, sai kawai taji kunyar tace ya sha mata hannu da kafa kawai tace cizonta yayi, sai bayan umm tayi magana ne tagane gaskiya abinda ta fada beyi making sense ba…..
Knocking ta sakeyi amma shiru ba’a amsa ba, turo kofar tayi fortunately ta sameta a bude, zagaye parlourn ta hau yi tana tabe baki take aranta fadi take ‘a haka kamar me tsafta amma kazami ne’…
Tana cikin zagayenta ta hango kofar wani daki a bude, batareda tunanin komai ba ta nufi dakin…
Deen na kwance a cikin bargo yayi rub da ciki yana kallon hotunan daya mata jiya, dama yana tashi da safe yasa akazo aka karbi wayar aka kai gyara, dazu da ze tafi dauko su uncle A kuma aka kawo masa, yana shigowa kuma yasa hotunanta a gaba da kallo yanajin wani nishadi aransa, hakan sai ya gushar masa da wani bacin rai daya shigo dashi….
Tinda tashigo parlourn turerenta ya masa iso har inda yake, ya rasa ina ta samo wannan fitinenne tiraren me shegen kamshi da cika guri, yana sane ya kara rapkewa dan yaga me tazoyi dama kuma yana nemanta….
Tsayawa tayi a bakin kofa tana bin kan gado da kallo, ko ba’a fada mata ba tasan shine saidai tayi mamakin yanda ta ganshi a cikin bargo, haka kawai zuciyarta ta bata bashi da lafiya ne, sai ta karaso ta tsaya daidai kansa tana kallonsa ta cikin bargon……
Yana jin duk motsinta akansa amma yaki motsawa hannunsa dauke da wayarsa yana zooming lips dinta ta cikin hoton…..
Hannunta tasa ta yaye bargon ta saitin fuskarsa a hankali, yanajin haka yayi saurin kwantar da wayar yayi kamar yana bacci, tsugunawa tayi tana kallon fuskarsa tace;
“Kamar fa bashida lafiya?”….
Sai kuma ta dora hannunta akan girarsa tace;
“In kana bacci kanada kyau kadan because you look peaceful, kana tashi kuma sai ka koma mummuma”….
Sai kuma ta dungure masa kai tace;
“Masifaffe kawai kazami”…
Ta manta hakan ze iya sa ya tashi koda baccin yake…..
Kawai ji tayi anyi cikin bargon da ita, ko kafin ta gane me yake faruwa taji mutum a samanta, ihu ta saka jin nauyi kamar ze kasheta, dakyar tace;
“Wayyo kirjina, dan Allah ka dagani”…
Sake sakar mata nauyinsa yayi yace;
“So nake kirjin ya fashe ai, badai nine kazami ba?”……
Kuka ta fashe dashi jin lamarin yafi karfinta cikin shesshekar kuka tace;
“Wallahi a’a, ba kai bane kazami ba, ni ce”….
Kwafa yayi yana rike dariyar da take so ta kubcemasa tin dazu da take surutanta akansa yace;
“Zaki kara gayawa su mami idan na miki abu?”….
Da sauri hawaye na zuba a idonta tace;
“A’a, ko kaina bazan kara fadawa ba”….
Dariyar da beyi niya ba yayi sannan ya sake gimtse fuska yace;
“Bakida hankali kika rungume sultan dazu? Ban hanaki rungume maza ba?”…..
Cikin fitar hayyaci tace;
“Wallahi ka hanani, bazan sake ba, har mata ma bazan rungume ba, dan Allah kayi hakuri”….
“Good for you, sannan wannan turaren naki karki kara sawa, zan baki turaren da nakeso kina sawa bana mahaukata irin wannan ba”…..
“Toh naji, dan girman Allah da annabi ka dagani”……
Ta fada tana zuko numfashinta”…..
Sake sakar mata nauyinsa yayi yanda zata shiga taitayinta da kyau yace;
“Ai bangama ba, ki saurareni da kyau kiji abinda zan fadamiki, kika saba ko guda daya ne zakiga abinda zan miki wallahi”…..
“Zan kiyaye, wallahi bazan saba ba”….
Ta fada tun kafin ya kai karshe…….
“Good, daga yau gidannan ze cika da mutane kala kala masu halaye daban daban, wallahi kika sake na ganki da matsattsun kaya na lahira sai ya fiki jindadi, sannan banyarda in ganki kin zauna kafada kafada da wani kato ba, sannan duk wacce kikaga tana mammanne miki a cikin matan ki gayamin inci uban ko wacece, wallahi ko gashin gaban goshin ki nagani a bude sai kingane kuranki, idan kinga dama kije ki gayawa mami abinda na miki yanzu, zaki iya tafiya”…..
Yana gama fadin haka ya sauka akanta, a daddafe ta mike tsaye, fashewa da kuka tayi jin takasa jan kafafunta, tashi zaune yayi ze sake kamota, tana ganin haka ta fita da sauri batasan daga ina strength yazo mata ba, ficewa tayi daga part din ko tina ta fadamasa abinda ya kawota batayi ba….
Sai da ta tsaya a bakin part din mami ta sha kukanta ta koshi sannan ta goge fuska tashiga…
Tana shiga sukaci karo da hussy da akace taje ta dubata shiru daga aike tun dazu, komawa ciki sukayi tare, suna karasawa dining kamar ance ta kalli gefe ta ganshi a zaune, wani irin ihu ta kurma ta zube kasa a sume!!!…

Back to top button