Kuka ummie ta fasa tana faɗin
“Kana kallon abunda yaron nan ke gaya min amma kayi shiru Alhaji?, daga tambayar ba’asi? shikenan irin sakayyar da Abdul ze min kenan?”
Cikin fushi Abbah ya ce
“Dakata min Hajiya Asiya, bana son wani tashin tashi na, ni duk a tunani na makamantan irin maganganun nan mun baro su can a rayuwar baya, banga dalilin da zesa kuma a dawo da su ba”
Su Fauza da sukai carko-carko a wajen suna kallon iyayen nasu da mamaki, dan kaf a tarihin rayuwar su basu taɓa ganin iyayen nasu a wannan yanayin ba.
Kallon junan su sukai, sannan suka ja ƙafafun su suka bar palourn,
Wajen da suka fara cin abinci suka hau gyarawa, ba wanda ke tanka ɗan’uwan shi, ko wanne da tunanin da yake a cikin ranshi.
Abbah na ganin fitar yaran shi, ya kalli ummie dake ta haɗiyar zuciya yace
“Kin kyauta kenan da abunda kike shirin yi? ko ba komai yanzu yaran nan sun san bake kika tsugunna kika haifi Abdul ba, ko da ga jin kalaman bakin ki dole mutum ya gane, ballanta na su Fauza da ba yara bane”
Be tsaya jin abunda zata ce ba ya ci gaba
“kuma kinfi kowa sanin waye Abdul, bamu taɓa kama shi da abinda nasan kema sheɗan ne ke miki saƙar shi a cikin ran ki ba,
To miye ribar ki in kin jefe shi da wannan abun?”
Shiru ummie tayi ta sadda kanta ƙasa, ranta na daɗa baci
Da dai Abban ya san ba tankawar zatai ba, tunda bata da abun faɗa, ya fita ya bar mata ɗakin yana jin wani iri da kewar Murjanatu a can ƙasan ranshi.
Tunda Abdul ya bar wajen su ummie ya koma ɗaki,
Yana ta nazarin maganganun ummie murmushi kawai yayi yace
“Allah sarki Ammah kin tafi kin barni da kewar ki, bani da kafaɗar da zan dafa nai kuka”
Da dai Abdul yaga tunani na neman kaishi ƙasa,
Wayar shi ya janyo, kai tsaye yallaɓai ya kira.
Bugu biyu yallaɓai ya ɗaga.
Cikin girmamawa Abdul yai mishi sallama, bayan sun ɗan taɓa hira Abdul yace
“ina son zanyi resuming aiki ranar monday sir”
Cikin fara’a yallaɓai yace “kai amma da ka kyauta kuwa, muna da buƙatar ka sosai-sosai, Allah ya kaimu monday”
Da “amin” Abdul ya amsa, daga bisani sukai sallama.
Abdul be aje wayar ba, ya maida akalar kiran wayar ta shi zuwa numbar muslim, haka tai ta ringing muslim be ɗaga ba.
Huci me ɗan ɗumi ya fesar daga bakin shi, aje wayar yayi, a hankali yace
“shima ina gaf da rasa shi, koma na rasa shin”
***********
Tana tsaka da kashi ta tuna ta bar magunan ta a cikin jaka bata fito da su ba
Da gudu Zainab ta fito daga banɗakin
shaf ta manta da su
Da gudun ta tashiga ɗakin, har Iya da ƙanin Abie dake zaune suka so firgita
Tsayawa Zainab tai tana wurwurga idanu taga ta inda zata gano jakar tata.
Takaici da ya ishi Iya ta wawuri kofin robar dake kusa da ita ta wurga ma zainab, tace
“kiji min yarinya, haka nan kin sa hantar ciki na ta kaɗa, ubanwa ya biyo ki? ina kin ce min kashi zakiyi?
ko kuma a banɗakin ne kika ga abinda ya firgita ki ni Dije!”
Iya ta ƙarashe maganar tana riƙe haɓa haɗe da kallon Zainab da tai wiƙi-wiƙi da idanu.
Zumɓura baki Zainab tayi ta ƙarasa shiga ɗakin,
Uwar ɗaka ta wuce ta dudduba kan gadon iya da gefe-gefen kujeru duk bata ga jakar ba
Sake fitowa palourn tayi tace
“Dan Allah iya baki ga jakar da na shigo da ita ba ɗazu?”
Iya tace
“jakar da kike ta wani ƙunbiya-ƙunbiya da ita kamar warce ta ɓoyo kan mutane a ciki?”
Ido ƙwal-ƙwal Zainab ta gyaɗa kai.
Iya tace “humm, ki duba a inda kika ajiye, ni ko tashi a wajen nan banyi ba”
Kaf seda zainab ta birkice ko ina na ɗakin amma bata ga jakar ba, tunanin duniyar nan tayi shi amma kanta ya kasa tunaso mata a inda ta aje.
Haƙura tai ta koma ta zauna tana ta wani cicci magani, ita duk a tunanin ta iya taga magunan ta cire su a jakar.
Ba’a wani jima can sosai ba, ƙanin Abie yai ma Iya sallama ya wuce.
Yana tashi Zainab ta koma inda ya tashin, tana zama ta tuna ana fa ta aje jakar, hada ɗan kara musu pilo kafin ta shiga banɗaki.
Wani salati me ƙara da yasa iya zabura Zainab ta doka tana tashi a firgice.
pilon ta janye sannan ta ɗago jakar da ta gama laƙumewa kamar ba komi a ciki, tace
“Na shiga uku ni Zainab, wayyo Allah na!!”
Hannu biyu Zainab ta ɗora a kan ta, tana ta zabga salati
Da ƙyar iya ta yunƙura ta miƙe,
taro ta tayi tace
“ke lafiyar ki kuwa, miye a cikin jakar?”
Zainab batace komi ba se hawaye da ke ta ɓulɓulowa daga idanun ta, hannun ta duka biyu a bisa kanta, ta zuba ma jakar idanu
Kallon idanun Zainab ɗin iya tayi taga inda take kallo,
Ba tai wata-wata ba ta janyo jakar taga mene a ciki da har zainab ɗin ke ta zabga salati.
Iya na zuge zip ɗin jakar taga maguna ƴan ƙananu se uwarsu dake gefe duk a mace,
Wurgi iya ta yi da jakar tana ja da baya, itama da yake gwanace wajen tsoro, ido warwaje tace
“Na shiga uku ni Dije, a ina kika samu maguna Zainabu?
Zainab bata ce komi ba se ma matsawa tayi kusa da jakar ta tsugunna tana leƙen magunan
Tattaɓa su tayi, ta tabbatar da sun mutu dukan su,
Rushewa da sabon kuka Zainab tayi, kuka me sauti,
Ɗaya bayan ɗaya ta rinƙa ɗaukan magunan tana ajewa.
Sororo Iya ta tsaya tana kallon ta, tunani take dama wai magunan na a cikin jakar tunda ta shigo ko ko ya abun yake ne?
Daga can bakin ƙofar shigowa palon Iya ta tsaye, ido a waje, hannu a kan ƙirji take kallon yarda jikar tata ke ta ɓarzar kuka a gaban gawarwakin magunan
Jarumta Iya ta aro ta yafa ma kanta ta matso kusa da Zainab ɗin
Dafata tayi tace
“a ina kika samu maguna?”
Cikin sheshshekar kuka Zainab tace
” nawa ne fa Iya”
Tagumi Iya ta zabga tace
“kuma ɗazu da kika shigo dasu kika shigo?”
“eh” Zainab tace
Cikin damuwa Iya tace
“shikenan yanzu alhakin ransu a kanki kenan?
Wani kallo Zainab ta wurga ma Iya, tsabar takaici bata ce komi ba ta ci gaba da kukan ta.
Suna nan a zaune sun tasa maguna a gaba, Zainab na kuka Iya kuma na jimamin anyi kisa a ɗakin ta
Suna a hakan, su ka ga ɓaƙar magen da Zainab ɗin bata so a cikin su ta fara motsi,
Dakatar da kukan Zainab tayi tana kallon ikon Allah,
Iya ma na daga gefe taga ɗaya ta fara motsi
Kabbara me ƙarfi Iya tayi, tace
“ikon Allah, ita wannan tana da rabon shan ruwa a gaba, yanzu duk uban maka-makan mazaunan Ibrahim da ya maka musu kinga ita ta tsira”
Duk da halin da Zainab ke a ciki, seda maganar Iya ta saka ta dara wa.
Rungume ta tai tsam a jikin ta,
Tausayin ta gaba ɗaya ya kama ta,
Gaba ɗaya soyayyar da take ma sauran ta ɗauka ta ɗora ma ƴar baƙa kacokam (ƴar baƙa ta saka ma magen).
Sun kwashi drama sosai, kafin Iya ta yarda aka binne magunan a gidan ta,
ita a cewar ta sedai a kai su bola karnuka su samu abinci,
ita kuma zainab ta kafe da ƙunata akan se dai a rufe su anan cikin gidan.
Da ƙyar Abdul ya samu ya fito da muslim daga gida,
har yanzu da a kwai sauran tsoro a ranshi, haka nan dai ya dake ya fito
tun daga ranar be ƙara yarda yai sakaci da azkhar ba
Suna tare da Abdul ɗin fa, amma bakin shi bai dena motsi ba
Ɗan waigowa Abdul yayi ya kalle shi, murmushi kwance a fuskar shi yace
“wai me kake cewa ne guy?”
Seda muslim ya gyara zaman shi da kyau yace
“Ayatulkursiyu nake hadda” ya ƙara muskutawa yace “ko na maka ƙarya na san za’a faɗa maka ai”
Dariya Abdul yayi ya kaɗa kanshi,
dai-dai zasu karya kwanar babban layi Abdul ya hango ta rungume da wani abu baƙi a hannun ta.
Cak Abdul ya taka burki ya tsaya, har seda muslim ya sake kallon shi
Kallon ta yake ta mirrow ba ko ƙyaftawa,
Tana tafe cikin nutsuwa kamar ko da yaushe, fuskar nan ɗaure ba alamun wasa a tattare da ita har tazo ta gifta su be dena kallon ta ba.
A hankali Abdul ya shafa kanshi bayan Zainab ta ɓace ma idon shi yace
“Tayi kuka!”
Galala Muslim ya yi yana kallon Abdul, da mamaki ƙarara a fuskar shi,
in baze manta ba suna da shekara talatin cif a duniya, amma be taɓa ganin Abdul ya tsaya ya ɓata lokacin shi akan kallon wata ƴa mace ba,
Har yana faɗin wai “tayi kuka”
Kasa shiru muslim yayi seda ya tambaya
“wacece ita Guru?”
Murmushi kawai Abdul yayi be ce komi ba, sema ci gaba da tuƙin shi da yayi
Sun ɗanyi nisa kaɗan muslim ya kasa haƙurin maganar dake cin shi a rai yace
“karka sa ƴar mutane a matsala fa”
Seda Muslim ya faɗi haka, ya tuna haɗuwar shi da mutuniyar shi,
A firgice yai maza ya ɗora hannun shi akan leɓan shi ya riƙe su gamm, hada ƙoƙarin faɗin “astagafirullah” kamar wanda yai saɓo.
Sabon kuka Zainab ta shiga gida tana yi,
Da sauri mama ta taso ta tarbe ta tace
“me ya faru, ni mamaki kike bani wallahi, kuka sam baya miki wahala ke kam”
Cikin shashshekan kukan take ba mama labarin mutuwar magunan nata
Allah ya kyauta kawai mama ta iya cewa, tana leƙen ƴar baƙa dake hannun ta tana barcin wahala.
Ɗaki Zainab ta shige ta shimfiɗe ƴar baƙa akan gadon ta sannan ta cire hijabin ta,
Fitowa tayi ta haɗa mata madara, sannan ta koma ɗakin.
Ɗukan ta tayi ta fara bata a hankali, da kamar ba zata sha ba, daga baya ta fara sha,
har cikin ran zainab taji daɗin yarda ƴar baƙa ta buɗe ciki tana shan madarar
Seda ta ƙoshi sosai sannan ta maida ta kan gadon ta shimfiɗe ta.
Ido kumbure Zainab ta fito daga ɗakin ta iske Abie da Mama a palon shi yana cin Abinci
Ƙarasawa tayi da sallama, zama tai kusa da Abie ta gaishe shi sannan ta matsa gefe tana ɓata rai
Inda haka nan banza ne hannu zata saka suci tare
Ɗagowa Abie yai ya kalle ta yace
“Auta na ya akayi ne? me ya samu idon ki”
Kamar me jira, ta fara share hawaye
Tsaki mama tayi tace “wai magunan ta ne suka mutu fa”
Abie yace “Ashsha, garin yaya?”
Tas mama ta bashi labarin da Zainab ɗin ta bashi,
Dariya sosai ke cin Abie, amma haka nan ya daure yai mata ta’aziya😂
Se daga baya yace
“Banda abun Auta, ya za’ai ki saka maguna a jaka har ki manta da su”
Zumɓura baki Zainab tayi tace
“Ni fa mancewa nayi, se da ina kan masan Iya na tuna na barsu a jaka, ko da na fito na iske Baba Bashir ɗare ɗare a kan su”
Abie yace “ayi haƙuri to, Allah ya raya ita guda ɗayar, ke kuma Allah ya baki haƙurin rashi”
Dariya sosai mama ke kwasa, yarda Abie yaci magani yana mata ta’aziya duk da tasan shima ɗaure tashi dariyar ya ke yi.
Fushin beyi wani tsawo ba ta zauna suka ci gaba da cin abincin tare da Abie, (Zainab bata fushi da abinci sam)
Seda tai nak tai Hamdala tukun ta kalli mama tace a shagwaɓe
“Wallahi mama na san zaman da nake da ke, baki man ta’aziya ba”
Pilon dake kusa da ita ta ɗauka
Zainab na ganin haka tasan kanta za’a jefo, da gudu ta tashi tai waje tana dariya.
Zainab na fita daga ɗakin mama ta kalli Abie tace
“Ni nayi murnar mutuwar magunan nan, tunda aka haife su kwata-kwata Zainab bata da sukuni, kulum tana zarya zuwa siyo musu madara,
Ɗan aikin gidan data saba taya ni ma shima duk an dena, rannan fa da na matsa mata akan shara, se ce min tai “wai jego take”
Dariya sosai Abie ke yi, mama kuma na ci gab da bashi labarin shaƙiyanci irin na zainab
Seda Abie ya gama kwasar dariyar shi yace
“Ai kina takura min yarinya da yawan aikace-aikace”
Murshi mama tayi tace
“to malam in bata koya a yanzu ba se yaushe? in na biye ma zainab to ba abunda zatai a gidan nan”
Abie yace “Hafizar tawa? ni dai na san bada ga baya ba indai wajen aiki ne”
Tashi tai ta fara gyara wajen da Abie ya gama cin abinci, sannan tace
“ai indai wajen janyo Aya da hadisi ne, to ba baya ba, amma aikin gida kam se nayi da mugun gaske”
Nan dai sukai ta firar su akan Auta zainab, sukai ta kwasar dariyar iyashegen ta.
******
Wajajen ƙarfe biyu da rabi na dare, iske me ƙarfi ta fara kaɗawa, sakamakon hadarin da ya haɗu yai baƙinƙirin yana rugugin zabda ruwa
A dai-dai wannan lokacin Abdul na kwance a ɗakin shi ido biyu yana tunane-tunanen rayuwar shi.
Ƙarfin iskar hadarin ne ya farkar da Abbah da shima be jima da yin bacci ba
sakkowa daga gadon yayi ya nufi window inda har feshin ruwa ya fara ɗan shigowa
Har Abba yajawo window ɗaya ze jawo ɗayan idon shi ya kai saitin ɗakin Abdul da gaba ɗaya mujiyoyi farare da baƙaƙe sun yi yama-yama,
tun daga saman rufin ɗakin har izuwa ƙasa, sun yi jere sahu-sahu kamar a sahun sallah.
Da sauri Abbah ya ɗan ja baya, ya saki labulen
Laɓewa yayi yana leƙawa a hankali,
ƙuri yaga ɗaya daga cikin manyan fararen mujiyoyin tai mishi tana kallon shi
Ƙara lafewa Abbah yayi, Zuciyar shi ta ce mishi “ƙara leƙawa, ƙila idanun ka ne”
Kamar sakarai Abbah ya bi umarnin zuciyar shi ya leƙa
Aikuwa kamar a cikin ɗakin yaji ance
“KAI JARIRI, JE KA SAKAYO MA SIRIKI NA TAGAR SHI, BAN KUMA CE KA KALLE SHI BA”
Abbah na jin haka ya kwasa da uban gudu ya shige ɗakin ummie da fushi yasa basu nemi junan su ba
A sukwane Abbah ya danna kanshi cikin ɗakin,
idon shi rufe ya ɗanna ƙofar ɗakin da iyakacin ƙarfin shi, jikin shi nata karkarwa
A firgice ummie ta farka, itama ta diro daga kan gado
Kan Abbah ta yo da gudu itama,
Ido warwaje tace
“Ɓarayi ne? ta ina suka shigo? ba’a rufe gidan bane?”
Riƙe ta Abbah yayi ganin tana neman finshi firgicewa
Addu’oin neman tsari ya fara karantawa, gaba ɗaya babu inda baya rawa a jikin shi tsabar firgita da yayi
Tun yana yi a zuciya bakin shi kawai ke motsi, ya koma yana yi da ɗan ƙarfi
Sototo ummie tayi tana kallon mijin nata da gaba ɗaya ya haɗa zufa sharkaf
Magana ta fara mishi, amma ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu.
Gefen gado ta koma ta zauna ta zuba uban tagumi tana kallon yarda Abbah ke ta zuba karatu
Jikin shi tun yana rawa har ya koma ya dena.
Ya ɗau gogon lokaci yana karatu kafin daga bisani ya fara jin sanyi da wata nutsuwa na ratsa shi
Tun da Abbah ya fara jin nutsuwar nan ya tsaya da karatun, yaci gaba da baza idanu yana tuna kallon kallon da sukai da mujiyar nan
Kallon ummie Abbah yayi yace
“ki koma baccin ki”
Da mamaki ummie tace
“Haba Alhaji, wani irin in koma bacci bayan na ganka a firgice, kuma baka sanar da ni komi ba”
“hummm” kawai Abbah ya iya cewa, ya tashi daga zaman dirshen ɗin da yayi ya shiga toilet ɗin dake nan cikin ɗakin ummie
Alwala yayi tukun ya fito,
A hankali ya rarrafa ya haye gadon ummie yai kwanciyar shi
Tashi ummien tayi itama ta shiga bayin ta kama ruwa tukun ta fito
Jin sanyin da ɗakin ya ɗauka yasa ummie ta nufi wajen window dan ta rufo shi
Kamar walkiya se jin Abbah tayi a bayan ta ya cafko ta ƙam,
ya janye ta daga jikin windon
Ƙara kallon shi tai da mamaki tace
“Lafiyar ka kuwa Abbahn Abdul?”
Murya da ɗan rawa Abbah yace
“ki bar windon, zo mu kwanta kawai”
Badan Ummie ta so ba ta haƙura tabi shi suka kwanta,
Riƙeta yai ƙam dan ma kar ta tashi bayan ya saki jiki.
Da saƙe-saƙe kala-kala bacci yai awon gaba da ummie.
Abbah kam, har aka kira sallah idon shi biyu
se a sannan yake tuna kiran da malam Hamza yai mishi da shaf ya sha’afa, abunda ba halin shi ba kenan mantuwa.
Tunani fal a ran Abdul ya dawo gida daga sallar asuba
Ya manta when last Abbahn shi yayi missing sallar asuba a cikin jam’i
Da ya shigo gidan yaso ya wuce ciki ya dubo Abbahn,
amma ya fasa ganin akwai sauran duhu a garin
Ɗakin shi ya wuce, dan zuwa 8 ya ke son ya tafi office
Yana shiga kamar ko da yaushe ɗakin shi na ta zuba ƙamshi, kuma ko ina a gyare fes, komi na a inda yake,
Be bi ta kan wannan ba saboda kwana biyu ya saba da hakan, dan wani lokacin ko wanka yake yi se yaji ta tana cuɗa mishi baya,
Haka ze ta faman faɗa da abunda ba gani yake ba,
Wani lokacin kuma in taso iskancin ta se tai hanging soson wankan can saman rufin bayin taita ƙyalƙyala mishi dariya, ita wai nan wasa take mishi
Ko kuma in yana tsaka da wanka,
irin ko da shower ne, se ta bari ya gama mulke jikin shi da kumfa, se ta kashe shower ɗin
In taga ya ɓata rai ko kuma ya ƙule se ta sure shi ta dire shi a cikin kwamin wankan, ita ala dole se ta wanke shi
Kamar zararre haka ze ta magana yana cewa
“Bana son abinda kike min, ki fita ki bani waje”
Yayi ta ihu shi kaɗai, ita kuma tai ta kwasar dariya.
Wankan shi yayi tas, ya fito ya shirya cikin ƙananun kayan da suka karɓe shi ainun, briefcase ɗin shi na gefe, se kuma farar rigar da zaku ga likitoci na sakawa a saman kayan su a gefe
Anan ya bar komi ya fita zuwa dubo Abbahn shi
Yana shiga da Ummie ya fara cin karo ta fito daga kitchen zata nufi dining,
Cikin girmamawa kamar yarda ya saba ya gaishe ta,
amsawa tai ba yabo ba fallasa tai gaba
Shima wuce wa yayi hanyar da zata sada shi da palourn Abbah
a zaune ya iske Abbahn waya kare a kunnen shi suna magana da Abie, inda yake ta bashi haƙurin rashin zuwan da beyi ba, da mantuwar da ta kama shi
Har abunda ya gani a daren jiya sedai Abbah ya ba Abie labari,
Ganin shigowar Abdul ɗinne yasa Abbah ya yanke maganar da niyar ze je har gida su ƙarasa maganar.
Kusa da shi Abdul yaje ya zauna
Kanshi a ƙasa yaca
“Barka da asuba Abbah”
Abbah dake kallon ɗan nashi yana ƙara nazartar shi yace
“Lafia lau Abdul”
Ɗan kallon shi Abdul yayi yace
“Lafia kuwa Abbah naga ban ganka ɗazu a masallaci ba?”
Tausayin Abdul ƙarara zaku gani a fuskar Abbah yace
“Banji daɗi bane jiyan, kuma bacci ya ƙwace min ne shiyasa” Abban yace “yauwa, saƙon me mlm Hamza yace ka faɗa min ranar?”
Abbah na lura da duk wani yanayin Abdul ɗin
Kuma yaga sauyi da Abie ɗin yace ze gani in yayi mishi tambayar
kan Abdul a ƙasa, yace
“kayi haƙuri mance wa nayi”
Abdul yayi niyar ya zauna har yayi breakfast tare da Abbahn, amma a lokaci ɗaya yaji kamar ana janshi daga palon
Murya can ƙasa Abdul ɗin yace
“Zan wuce wajen aiki Abbah”
Badan Abbahn ya gaji da jin ɗan nashi a kusa da shi ba yace
“Allah ya bada sa’a, Allah kuma ya tsare min mutuncin ka”
(IYAYE MU DAURE MU RINƘA KALAMI ME DAƊI WA ƳAƳAN MU, BAKIN MU NA TAKA MUHIMMIYAR RAWA GAME DA RAYUWAR YARAN MU)
“Amin” Abdul yace sannan ya ma ummie sallama ya fice
Hanyar ɗakin shi ya nufa dan ya ɗakko tarkacen shi, yaji tace
“NA RUFO KOMI SANNAN GA KAYAN NAN A CIKIN MOTA, IN MA BA ZAKA IYA TUƘIN BA SE IN KAIKA DAGA KAI HAR MOTAR”
Cak Abdul ya tsaya, shiru yayi, yana jin hannuwa barkatai a kafaɗar shi,
Hannun shi ya ɗaga da niyar ze make hannayen ta dake yawo a jikin shi yaji ta riƙe hannu ƙam
yi hannun yayi kamar ya riƙe, daga baya kuma ya ji ya sake
Kamar mutum mutumi sarauniya Aziza ta juya shi, yana cogewa tana kwasar shi, a kunne ta raɗa mishi
“SIRIKI NA YANA KALLON KA TA TAGAR PALON SHI, IN KA KUSKURA ZAN ƊAGA KA CAK AKAN IDANUN SHI IN KAI KA MOTAR,
KAGA ABUN BA ZE ƘARE DA KYAU BA IN YA GANI”
Ɗaga idon shi ya yi yaga ilai Abbahn nashi na tsaye ta window yana kallon shi
Haka nan ya haƙura ba dan yaso ba taja hannun shi har cikin mota,
seda ya zauna, ta rufo mishi motar, sannan yaji zaman ta a kujerar gaba ta kusa da shi
Motar ya ja ya fice daga gidan,
Be tsaya ko ina ba se a ƙofar gidan su muslim, sunyi dama ze je ya ɗauke shi su wuce tare
Horn yayi mishi,
Ko minti uku muslim beyi ba ya fito a shirye shima fes,
Sit ɗin baya ya buɗe ya saka jakar shi ya rufe
Buɗe ƙofar gaba yayi ze shiga, Abdul yace mishi “ka zauna a baya guy”
Kallon Abdul muslim yayi da mamaki,
Be ce komi ba kawai ya bude bayan ya shiga
Abdul yaja suka tafi
Suna tsaka da tafia Aziza tace ma Abdul
“BAKA GABATAR DA NI A WAJEN ABOKIN NAMU BA AZIZ”
Cikin fushi Abdul yace
“Ki dena firgita musu ɗa na gaya miki”
Ƙuuuuuuuuu haka cikin muslim ya bada sauti, ido warwaje yake kallon Abdul dan sam Aziza bata bari muslim yaji muryar ta ba..
Ta mirrow Abdul ya ke kallon muslim da zufar tsoro ta rufe shi ruf yana ta ƙwalalo idanu,
duk yanayin da ya shiga be hana shi addu’a ba
Daria Abdul yayi yace
“Guy wasa fa nake maka, maganar zuci ce ta fito fili”
Banza da shi muslim yayi yaci gaba da karanto addu’oin shi na neman tsari
Tsayawa da tafiyar Abdul yayi yace
“ka dawo nan, wallahi ban san maganar ta fito ba guy”
Buɗe motar muslim yayi, kamar da gaske gaban motar ze koma, yana fita ya ɗauki jakar shi a hannu ya rufe mishi ƙofar shi
Seda ya ɗan ba motar tazara kaɗan ya buɗe baki da ɗan ƙarfi yace
“Kar ka ƙara zuwa ɗauka ta, na yafe!”
Dai-dai nan ɗan kekenapep yazo wucewa, muslim ya tsaida shi ya shige ya bar Abdul da baki sake yana kallon shi.
***Tunda ummie ta gama jera wa Abbah breakfast ta zauna tana tambayar shi tace
“na kasa gane kanka tun jiya Abbahn Abdul, wai meke faruwa ne dan Allah?”
Numfasawa Abbah yayi ya kalli ummie da ta wani marairaice fuska yace
“Ba wani abu Asiya, kawai ku rinƙa addu’a sosai, kuma ki faɗa ma yaran nan dukan su”
A hankali ummie ta sauke tagumin da tayi tace
“Humm, Ruƙayya ma na kasa gane kanta tun shekaran jiya, ɗazu da safe da na leƙa ɗakin su naga tana haɗa kayan ta, wai zata koma gidan su”
Se yanzu tunanin Abbah ya kai kan Ruky,
A cikin zuciyar shi yace
“yarinyar nan ƙila fa abinda na gani ne itama tai gamo da shi”
Dafa cinyar shi ummie tai,
Firgit Abbah ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula
Kallon shi ta ƙara yi tace
“Abbahn Abdul, ba dai zaka gaya min me ke damun ka ba, gashi ƙiri-ƙiri ina kallon ka a cikin damuwa, maganar da nayi akan Ruky itama kamar baka jini ba”
Abbah yace
“Na jiki Asiya, ki barta ta tafin, in ta huta nasan zata dawo”
Shiru ummie tayi, a tunanin ta Abbah ze taya ta lallashin Rukyn akan ta yi haƙuri ta zauna, amma se yai mata wata maganar daban kuma
Da ƙyar Abbah ya tsakura abincin ya barshi
Be wani ɓata lokaci ba ya shirya yai ma ummie sallama bayan ya bata kuɗi ta ba ma Ruky kuɗin mota,
ba wani ƙwaƙƙwaran bayani yai mata sallama ya fita
Abbah na shiga mota ya kunna karatun ƙurani, a memakon labarun safe da ya saba ji duk safiyar Allah
Be tsaya ko ina ba se a ƙofar gidan Abie
Ya daɗe zaune a cikin mota ko Allah ze sa yaga fitowar wani daga cikin gidan, yasan mafi akasari gidan baya rabuwa da jama’a
Ikon Allah har yana neman yafi awa da zuwa bega kowa ba
Wayar shi ya ɗauka ya danna kiran layin Abie, dama girmamawa ce yasa be kira shin ba
Bugu biyu Abie ya ɗaga da bakin shi ɗauke da sallama.
Cike da girmamawa suka gaisa, anan Abbah ke sanar mishi da yana a ƙofar gida
Abie na zaune a palon shi dama yana ma Zainab ƙarin fashin baƙi akan tambaya da tai mishi game da rabon gado a musulunci kiran Abbah ya shigo mishi
Kallon Zainab Abie yayi yaga yarda ta maida hankalin ta kacokam akan littafin gaban ta tana ƙara nazartar shi, yace
“Auta, je ki buɗe ma baƙo na palon baƙi na babban soro”
Da “to” ta amsa bayan ta saka alama a inda ta tsaya, shi kuma ya shiga cikin bedroom ɗin shi
Shiga ɗakin ta tai ta ɗauki hijabin ta, har zata fito daga ɗakin, idon ta ya kai kan inda ta aje ƴar baƙa bata ganta ba
Har ta juya zata duba ta tuna aiken da Abie yai mata, ta fasa ta fice
Key ta saka ta buɗe ɗakin sannan ta kunna wuta da na’urar sanyaya ɗaki
Daga can kusurwar ɗakin ta hango ƴar baƙa kwance tana bacci
Da mamaki zainab ke kallon ta, tambayar kanta da kanta tayi tace
“how comes?”
windon ɗakin da ya shiga har cikin gidan ta duba taga ashe windon a buɗe yake, kuma ta san ƴar baƙa zata iya shigowa ta nan
Kamar zata ɗauketa ta tafi da ita, ta fasa a cewar ta wai zata katse mata bacci.
Tana fitowa daga palon Abbah na kunno kai ciki, da sauri ta matsa gefe ta sunkuyar da kanta ƙasa
Seda ta bari ya shige tukun ta tsugunna har ƙasa ta gaishe shi
Fuska sake Abbah ya amsa mata, har da tambayar sunan ta
Da sallam Abie ya ƙaraso cikin palon shima,
Tashi zainab tayi ta fita
Tana shiga cikin gidan ta shiga kitchen ta haɗo mishi ruwa da lemo se kuma shayi
Tasan indai Abie yace a buɗe babban palo to tabbas baƙon nada muhimmanci, shiyasa batai wani tunani na biyu ba.
Gab da zata ƙarasa ƙofar shiga palon taji muryar Abbah na cewa
“Basu rabu da shi ba gaskiya, jiya na gani da idona, hankalina ya tashi malam, bacci gaba ɗaya ya ƙaurace ma idanuna, har yanzu ji nake na kasa kula da amanar da murjanatu ta barmin kafin mutuwar ta, a da nasan nayi babban kuskure ko ince sakaci, amma Allah ya sani ba a son raina bane hakan ya kasance, kuma a lokacin Allah ya temakemu munci nasara da temakon ka, ni duk a tunani na komi ya wuce, amma tabbas abubuwan da Abdul keyi a yanzu abun dubawa ne malam”
Da sallama zainab ta ƙarasa shiga palon, in da sabo ta saba jin proɓlems na mutane da yawa an kawo ma Abie
Har ƙasa ta tsugunna ta aje tray ɗin hannun ta
Abie ya kalle ta yace
“Sannu da ƙoƙari Auta, Allah yayi albarka”
Da “amin” ta amsa, sannan ta tashi zata fita
Kiran ta Abbah yayi yana sa hannun shi a aljihun rigar shi, yace
“Zo nan ɗiya ta”
Jiyowa tayi ta koma,
Abbah sake cewa
“ya sunan ɗiyar tawa?”
Kanta a ƙasa tace “Zainab”
murmushi Abbah yayi yana ƙara yaba tarbiyar ta, yace
“kice tsohuwace, ungo nan” ya miƙa mata ƴan ɗari biyar-biyar guda ashirin
Kanta a ƙasa, ta karkaɗa kai alamar a’a
Abbah yace
“gidan ku, ni ba Abbahn ki bane? karɓa”
Hannu biyu ta saka ta karɓa sannan tace
“nagode Abbah”
Murmushi Abbahn yayi yace “Allah yayi albarka”
Shiru Abie yayi yana nazarin maganar Abbahn,
sannan kuma yana tuna kashedin da hatsabibiyar tazo tai mishi jiya tsakar dare
Can Abie ya numfasa yace
“Bata aure shi ba, amma zata iya auren shi duk in ta samu sa’ar hakan, abinda za kai yanzu shine, kayi ma yaron ka aure, su aljanu suna da tsananin kishi matuƙa, in dai akai nasarar yi mishi aure to tabbas an rufe wata ƙofa”
Shiru Abbah yayi yana nazarin maganar
Beyi nisa a nazarin shi ba Abie ya ƙara cewa
“ga wannan” garin habbatussauda ya miƙa mishi ya ɗora da “ka turara ɗakin na shi dama gidan naka gaba ɗaya, sannan kasa shi ya daure ya rinƙa kwana da karatun ƙur’ani,”
Hannu biyu Abbah yasa ya karɓa yana godiya,
Abie ya ƙara da “karkayi wasa da maganar auren nan, a daure kar ya ɗau lokaci”
InshaAllah, malam, nagode ƙwarai da ƙoƙarin ka gareni da kuma iyalai na”
Har mota Abie ya raka Abbah dake ta zuba godiya
Fasa zuwa office ɗin Abbah yayi, gida ya wuce direct, yana nazarin abubuwa da daman gaske
Tun kafin ya isa gida ya kira ummie a waya yace ta haɗa mishi rushi gashi nan zuwa,
Nan ummie ta ƙara shiga mamaki akan wanda take a aciki,
Kafin Abbah ya isa gidan ta haɗa rushin
Parcking kawai ya daidaita ya fita ɗauke da habbatussaudan da Abie ya bashi
Ummie najin shigowar shi dama ta fito
Ko ƙarasawa inda take beyi ba ya ɗaga murya yace
“ɗakko min rushin”
Da sauri ta juya ciki, kasko ta ɗauko ta ta zubo rushin sannan ta fito
Tana fitowa Abbahn ya amsa kaskon yai hanyar ɗakin Abdul
Binshi tai abaya tana tambayar shi lafia
Da ƙyar Abbah ya samu ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga, dan har ya so ya haƙura tinda taƙi buɗewa…
COMMENTS AND SHARE PLS
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU.