Uncategorized

Kishi Da Aljan Chapter 9 Complete Hausa Novel

 

A takure waje ɗaya yayi baccin wannan ranar, 

Sanda ya tashi gaba ɗaya wuyan shi a ƙage, saboda be kwanta a dai-dai ba, seda yayi ta streaching wuyan sannan ya ɗan ji dama-dama, har ya iya shiga toilet ya samu yayi wanka da ruwa me ɗumi sosai.

Sauri-sauri yayi shirin tafia office, yaso ya ɗan makara ma

Seda ya kai komi mota, tukun ya wuce cikin gidan nasu

Amal da fauza ya fara cin karo da su, a ɗan ɗarare fauza ta gaishe shi, 

Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa, yasan sarai da tsoron da suke mishi

Sosai Amal ke tausaya ma yayan nata, itama fuska cike da tausayi tace

“Yaya Abdu, yanzu nake shirin kawo maka breakfast, gashi har ka fito”

Murmushi ya ɗan sakar mata yace

“Ina da patients da yawa suna jira na, naso na makara ma”

Murya a sanyaye tace

“Allah ya bada sa’a to”

Da “amin” ya amsa, yayi gaba ya gaishe da ummie 

Sannan ya wuce palon Abbah ya gaishe shi shima, tukun ya fito ya wuce wajen aiki.

***

Binta ki ce ta shirya ga Abubakar nan zuwa ya kaita asibiti.

Da “to” mama ta amsa, ta tashi ta shiga ɗakin da zainab ke kwance tana murƙususu

Mama tace

“Tashi ki ɗan ɗauraye fuskar taki, duk kin bi kinyi laushi, 

Ki saka kwalli ma a idon naki ko ya rage hasken nan da yayi”

Da ƙyar Zainab ta tashi, maman ta temaka mata ta kimtsa, sannan suka fito palo inda Iya ke zaune tana jan carbin ta da kwata-kwata bata rabuwa da shi a yanzu.

Mama na ajiye ta, taci gaba da ayyukan gaban ta.

Iya se satar kallon zainab ɗin take, se tayi yunƙurin mata magana, se kuma ta fasa taci gaba da lazimin ta.

Zainab na lura da ita, can dai ta buɗe baki tace

“Iya ta, yanzu na lura sam kin dena so na kamar da”

Taɓe baki Iya tayi, ta ɗan karkato kaɗan saitin zainab ɗin tace

“Kina a rai na ƴarnan, kawai dai ina jan mutumci na ne kar ya zube,

Dan naga wani lokacin rikiɗa kike, gara nayi gefe tunda ba tantance lokacin da kike dai-dai nake ba”

Murmushi zainab tayi, duk da yara take jin jikin nata, be hanata yunƙurawa ta matsa kusa da Iya ba,

Iya na ganin zainab ta matso kusa da ita, ta waro idanu tana kallon ta, da sauri tace

“Kinga koma inda kike, ba fa wani abu daban nake nufi ba, kin sanni da suɓutar baki dai”

Ta ƙarashe maganar tana ƙoƙarin miƙewa tsaye

Ƙwal-ƙwal zainab tayi kamar me shirin kuka tace

“shikenan Iya, tunda haka kike so”

Zainab ta san halin Iya na tausayi sosai, ita sam bata son taga mutum na kuka koda kuwa bata sanshi ba, nan da nan itama hankalin zaka ga ya ta tashi.

Dawowa tai ta zauna, amma a fakaice seda ta kalli ƙafar zainab ɗin ta tabbatar da lallai ita ɗin ce tukun ta ɗan saki jiki

Ganin Iya ta zauna yasa Zainab ɗin ta ƙara marairaicewa tace

“Dan Allah Iya muje dake asibitin, kin san halin yaya Abubakar yana iya sawa a ɗirka min allura wallahi”

Shiru Iya tayi, can dai tace

“To bari in kimtsa kafin ya ƙaraso, banda ma ina tsoron sharrin kishiyar ki ai ko gidan auren ki da tare zamu tafi wallahi”

Can dai Iya ko me ta tuna? tace “Humm, bari nayi shiru dai, nima wani lokacin na cika neman ba’asi”

Dariya sosai ke cin zainab, a hankali mood ɗin ta gaba ɗaya ya sauya e zuwa tunanin shi

Can cikin zuciyar ta take tambayar ta da

“Yana lafia kuwa?, yanzu a wani hali yake a ciki?”

Bata da me bata wannan amsar, ajiyar zuciya ta sauke, tana tuna lokacin da ya maƙe mata kafaɗa dan tace ya tashi ya tafi gidan su.

A fili ta furta

“Hummm, dole ne abun yayi mishi yawa wallahi, ga kurum ta ga kuma tirken aljanu”

Can kuma ta murguɗa baki ita kaɗai, ta ƙara cewa

“Ba ma dole bataliyar aljanu su tirke akan ka ba, mutum se shegen kyau kamar jikan su”

Dai-dai sanda take murguɗa baki, Iya ta ƙaraso palon, akan idon ta komi ya faru, baya ta ja da sauri tana ɗaga hannaye sama tace

“kin ga matsala ta dake ko? innace kin fara rikiɗewa se kiyi tunanin na dena ƙaunar ki ne, alhalin kuma gaskiya nake faɗa”

A hankali Zainab ta ɗaga kanta ta kalli Iya da ta kasa ƙarasowa tace

“me kuma nayi miki?”

Kafin Iya ta bata amsa, yaya Abubakar ya shigo yace “tashi mu je”

Kallon shi Zainab tayi tace 

“Tare da Iya zamu tafi”

“ku muje” kawai yace ya juya ya fita

Kamar Iya zata fasa zuwa,

Haka nan dai ta yi shahada ta saka hijabin ta suka fita

Iya akwai son shiga gaban mota, 

ba ruwan ta, ita ko ma da waye za’a fita indai da itane, to kowa sedai ya shiga baya ya barmata gaban motar, acewar ta an fi ganin komi

Zainab tasan hali dama, suna fita ta buɗe bayan motar ta shiga, Iya ta zauna a gaba

Kai tsaye khadeja special hospital Abubakar ya wuce, duk da dai yasan zainab bata da file a asibitin,

Zainab na kallon sun ɗauki wata hanyar bana asibitin da suka saba zuwa ba tace

“yaya Abubakar bafa nan ne hanyar ba”

Idon shi na kan titi yace

“na sani, kafin muje can mun wahala, yau garin a cunkushe yake”

Bata ƙara cewa komi ba har suka ƙarasa.

Parcking yayi, suka fito dukan su

Kama zainab tayi suka ci gaba da tafia har ciki

Da yake wannan hospital ɗin iyalan shi ke zuwa yasa yai amfani da hakan.

Mutum biyu ne a gaban ta, suna a haka zaune ɗaya ya fito, ɗayar dake kusa da zainab ɗin ta tashi tana wani yauƙi ta shiga

Yatsina baki zainab tayi tace

“wannan ba ciwon kike ji ba, tun da har kika iya zuba kwalliya haka kina wani yauƙi.”

Ta ɗan jima kaɗan itama ta fito,

Da ƙyar zainab ta yunƙura ta tashi, a kasalance tace

“Kizo ki kamani Iya”

Seda Iya ta gyara ɗaurin zanin ta sannan ta kama ta suka shiga ciki

Kan zainab a ƙasa ta ƙarasa ta zauna a kan kujerar da aka tanada don marasa lafia, Iya ma ta zauna a ɗayar

Be ɗago da kan shi ba, ya janyo katin da sunan ta ke rubuce a kai, 

idon shi na akan katin yace

“me ke damun ki”

Kafin tai magana Iya tace

“Yi magana mana Zainabu”

Yana jin muryar ta ya sheda ta, da sauri ya ɗago kan shi ya kalle su

Gaf da Iya zata ɗago kanta yayi sauri yaja facemask ɗin fuskar shi ya gyara.

Zainab bata kalle shi ba tace

“Ciki ne ke ciwo,”

Ƙur yayi mata da ido yace 

“Ta ina?”

ta cikin hijabi take nuna mishi, kauda kai yayi kamar be gani ba yace

“ki shiga can, akwai gado ki kwanta se in duba ki”

Shiru Zainab tayi tana kallon gefe, can dai ta miƙe tsaya

Baki sake IYA ke kallon Dr da kuma Zainab ɗin da ta riga ta tashi, tace

“Ba dani za’ai wannan shashancin ba, matar da aka riga aka karɓi sadakin ta za’ace ta kwanta a duba ta? to wallahi ba da ni ba, bari na kira yayan ta, in ni raina ni kayi”

Da hanzari ta fice daga office ɗin tai waje

Tana fita Abdul ya cire facemask ɗin fuskar shi yace

“Da gaske ke matar aure ce ashe?”

Ɗago kan da Zainab zatai sukai ido huɗu da shi 

Da sauri ta ja da baya tana ƙara ƙwalalo ido waje, da mamaki ta nuna shi da yatsa, tace

“Kaine?”

Murmushi me ƙayatarwa yayi mata, ido ɗaya ya kanne mata yace

“Kinga ɗan kurman ki na magana ko?”

Da sauri zainab ta rufe idanun ta, jin yace wai “ɗan kurman ta”

Yarda tayi ɗin ba ƙaramin dariya ya bashi ba, aikuwa ya dara ɗin

Suna a haka, zainab ta rufe fuska shi kuma ya kafe ta da idanu yana ta zuba murmushi Iya ta banko ƙofar da iyakacin ƙarfin ta.

Ido huɗu sukai da Abdul

Da ƙarfin gaske ta hau salati jikin ta na kyarma tana nuna Abdul dake tsaye yana kallon ikon Allah

Salatin ta yasa zainab sauke hijabin ta da sauri ta yi kan Iya da ke ƙoƙarin juyawa ta fice da gudu

Gam zainab ta riƙe, faɗi take “nitsu mana IYA, bafa a gida muke ba’

Murya ƙasa-ƙasa IYA tace 

“Tuna min addu’ar nan zainabu, kaina ya fara juyewa, nasan sarai baki ga abinda na gani ba”.

Iya ki nutsu mana dan Allah, kar ki tara mana mutane a wajen nan.

Abubakar da ke  riƙe da ita ta ɗayan ɓangare  yace 

“Wai me ta gani ne?”

Karaf Iya tace

“Tunda ku baku lura da abinda na gani ba ku saita min hanyar waje na fita, dan na kasa gane ta inda na shigo”

Murmushi Abdul yayi ya kalli yaya Abubakar yace

“Ka kaita office ɗin muslim, ina jin ya gama ganin patients ɗin shi, se ta zauna a can kafin in gama duba ta”

Hakan akayi kuwa, ya Abubakar ya fice da Iya, 

Abdul da kanshi ya tura ƙofar, sannan ya jingina bayan shi da ƙofar.

Kallon ta yake tun daga sama har ƙasa,

 Gaba ɗaya ji take ina ƙasa take ta shige, 

Gaba ɗaya kunyar abinda tayi mishi a gidan su ne ke dawo mata

Kamar yasan abinda take tunani yace

“mara kunya, muje in duba ki”

Da sauri ta karkaɗa mishi kai tana kakkama gefen hijabin ta tace

“wallahi ya bari ma”

Dariya sosai Abdul keyi, yarda take abu yanzu kamar ba itace ke tsiwa ba rannan

Da ƙyar ya tsaida dariyar da yake ya nuna mata wajen zama da hannun shi,

Shima ya zagaya ya zauna a kujerar shi.

“To gaya min, ciwon ciki ta ina ne yake miki?”

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi ta na wasa da yatsun ta, uffan bata ce ba, se marmar da baki kamar me shirin cewa wani abu.

Be sake ce mata uffan ba ya janyo telephone ɗin gaban shi

Daddannawa yayi sannan ya ƙara a kunne, ana ɗauka daga can ɓangaren yace 

“Come pls” Ya aje wayar yaci gaba da kallon ta.

Yana aje wayar, ko minti biyu beba akai knocking ƙofar sannan wata nurse ta shigo, 

“Gani sir”

 “Ai mata test ɗin maleria da typhod”

Zainab na jin an ambaci test ta fara zaro idanu waje, tana ƙyafƙyaftawa

Ta gefen ido yake kallon duk wasu actions ɗin ta

Nurse ɗin na fita ta dawo ɗauke da syringe da kuma robar da zata ɗaure mata hannun

Tana shigowa Zainab ta miƙe tsaye, tana rarraba idanu,

Kafin kace me idanun ta sun tara ƙwalla, ƙiris suke jira su fara gangarowa

Kallon ta Nurse ɗin tayi tace

“Matso madam”

Gallara mata harara Zainab tayi, ba tace komi ba kuma bata matso ɗin ba.

Fuska ɗaure nurse ɗin ta kalle ta taƙara cewa

“Ina da abun yi malama ki matso ko inyi tafiya ta”

Murguɗa mata baki Zainab ta ƙara yi, ta buɗe baki tace

“A daɗi na ai, ba wanda ya riƙe miki ƙafa ai” ta ƙara maganar tana juya mata baya

Waigawa nurse ɗin tayi wajen Abdul da niyar magana,

Kafin tace komi ya ɗaga mata hannu, alamar ta bashi syringe ɗin

Taɓe baki tayi, sannan ta miƙa mishi tai ficewar ta.

Kallon ta kawai yake, yama kasa ce mata komi

Be yi tunanin jarumtar da ya gani a tattare da  ita ba, kuma daga baya ya ganta tana tsoron a ɗiba jinin ta

Motsin tashin shi da taji ne yasa ta juyo da sauri tana kallon shi, 

Matsowa ya yi yace

“Tun muna mu biyu kizo na ɗauka cikin sauƙi kafin insa wannan ɗirkekiyar matar da kika gani zaune a waje ta riƙe min ke”

Shiru tayi tana tuna warce tai ma dariya kafin su shigo office ɗin

A zuciyar ta tace 

“caɓ, wannan in ta zaune ka ai se ka nemi numfashin ka karasa”

“Kina ganin kamar da wasa nake ko?”

Hanyar fita taga ya dosa

Da ɗan gudun ta tasha gaban shi tace

“Karka kirata dan Allah”

Tsayawa yayi yace “to muje ki bani na ɗauka”

Kafin Abdul ya ɗau jinin ba ƙaramin wahalar da shi tayi ba, daga ƙarshe dai ya ɗauka, sannan ya sake kiran nurse ɗin ta tafi da shi lab

Sosai idonta ya cika da ƙwalla, saboda zafin da wajen ke mata, ciccijewa kawai tayi ta hana ƙwallar zuba, acewar ta dan kar ya rainata.

Yana zaune a kujerar shi ya zuba uban tagumi yana kallon yarda take wani mazewa

Can, murya ƙasa-ƙasa kamar me son yayi raɗa yace

“Abinda na taɓa ganin kukan naki, yanzu ma kiyi abunki ba wanda zan faɗa ma”   yayi maganar cikin zolaya

rufe fuskar ta tayi ta waiga gefe.

Suna a haka nurse ɗin ta dawo ɗauke da result ɗin ta bashi

Buɗe takardar yayi ya duba

Tana zaune itama tana kallon takardar.

Yana ɗagowa suka haɗa idanu, tai maza ta kauda nata ta maida su ƙasa

Shafa kanshi yayi yana kallon ta,

A hankali yake ɗan bubbuga pen ɗin a laɓɓan shi, yace

“Typhod ne kawai, muje in karɓan miki magani se ku wuce, kafin Hajiya IYA ta tara mana mutane”

Ambaton sunan Iya da yayi seda ta ɗan murmusa, kafin ta tashi ta biyo bayan sa.

Can gefe ta tsaya ta jira shi har karɓo magungunan sannan ya dawo,

Wayar shi ya zaro ya danna number Abubakar sannan ya kara a kunne

Bugu biyu ya ɗaga, Abdul yace

“Ku fito, na gama duba ta”

Banji me akace daga can ba, kawai dai naga murmushi a fuskar shi, can naji yace ” to shikenan”

Kallon zainab yayi da gaba ɗaya hankalin ta na kan ɗirkekiyar matar da yace ze kira ta danne ta,

Zungurin ta yayi da ƙafar shi,

Da sauri ta waigo,

 murguɗa baki tayi badai tace komi ba

“Muje na sauke ki a gida, wai Iya taƙi yarda a jira ki, sun riga da sun tafi”

Ledar maganin ta ya miƙa mata yace

“bari in tarkato kaya na se mu wuce”

“Humm” kawai tace, juyawa yayi ya shiga office ɗin shi, mintuna kaɗan ya fito ɗauke da shirgin shi, ya ƙaraso inda take, yace

“Mu tafi”

Kallon hannun shi tayi taga kayan sun mishi yawa, bata ce uffan ba, hannun kawai ta miƙa ta ɗora akan ƴar madedeciyar jakar dake hannun shi

Kamar sakarai, haka Abdul ya sakar mata jakar yana jin wani irin nishaɗi na kama shi can ƙasan zuciyar shi.

Tana karɓa tayi gaba, bata lura da kallon da yake ta aika mata ba, shi kaɗai yake kiɗan shi.

Seda ta kusa kaiwa ƙofar fita daga reception ɗin tukunna shima ya taka da sauri yabi bayan ta.

Cak Zainab ta tsaya daga tafiyar da take, ita bata waigo ba ita kuma bata ci gaba da tafiya ba.

Shima tsayawar yayi yaga me ya tsayar da ita

Waigawa yayi yaga be ga komi ba,

Ƙarasa wa saitin ta yayi, kafin yace komi tace

“Bana son kallo, kayi gaba zan bika a baya”

Murmushi Abdul yayi, ya ce

“Allah ma yasa ba haramun nayi ba”  Yayi maganar yana basarwa shima kamar yarda tayi ɗin

Can dai da Abdul yaga bata da niyar tafiya, kuma ga dukkan alamu tana ɗan jin jiki, ga kuma rana yasa yayi gaba sannan yace 

“Ki tawo to”

Sit ɗin baya ya saka duka kayan hannun shi, sannan ya karɓa na hannun ta ya saka a ciki

Tana a tsaya batai wani yunƙurin shiga motar ba, da kan shi ya zagayo ya buɗe mata gaba yace

“Bisimillah Ranki shi daɗe”

Yarda yayi ɗin seda abun yaso bata dariya, daurewa kawai tayi ta shiga bata dara ba

Suna tafe yana ɗan sako mata fira sama-sama duk da shi ɗin ma ba sabawa yayi ba

Mafi akasarin firar tambaya ce, ita dai kanta na a ƙasa tana wasa da yatsunta, daga eh se a’a, kawai take cewa

Karaf taji ya kama hannun ta yana lalubar yatsar ta da ƴar baƙa ta ciza 

Daga shi har ita seda suka ji ɗan yammm haka a jikin su.

Duka yatsun ya hau dubawa, amma ko alamar me ciwon be gani ba

Ƙwace hannun ta tayi da sauri tana zumɓuro baki gaba, 

Kallon ta yayi sannan ya sake maida idon shi ga titi yace

“wani yatsa ne ta cije ki?”

Sarai ta gane me yake nufi, amma ta basar ta nuna ita ba wanda ya cije ta fa

Kafin ya ƙa ra cewa komi, Zainab da se yanzu hankalin ta yakai inda suke tace

“Ina zaka kaimu ne wai?”

Bece uffan ba, sema wata kwana da ya ƙara shiga

Sosai zainab ta waigo ta kalle shi, gaba daya idon shi ya kaɗa yai jaa, jijiyoyin kan shi sun fito sunyi ruɗu-ruɗu

Kallon shi take ko ƙyaftawa babu.

Murya a tausashe ta sake cewa

“Bafa nan ne hanyar gidan ba”

A hankali Abdul ke gangarawa ƙasa, har seda ya samu waje yayi parcking, 

Ɗora kanshi yayi akan  steering ɗin motar yayi shiru yana maida numfashi da sauri da sauri

Ƙwale Zainab tayi da ido tana kallon shi, 

hannun ta na ɗan rawa kaɗan ta ɗora a na shi hannun, murya ƙasa-ƙasa tace

“Lafia kuwa?”

seda ta maimaita hakan kusan so biyu, amma bece uffan ba, 

Gaba ɗaya Abdul baya jin ta ballanta na yasan me take faɗa, sarewar nan ce kawai ke tashi, yarda yake jin ta a yau tafi ta ko yaushe ma.

Leƙa fuskar shi ta yi taga idanun shi a lumshe, amma jijiyoyin kan shi na nan a waje ruɗu-ruɗu.

Komawa tayi ta jingina da kujera tai shiru, 

Daga ƙasan zuciyar ta  taji maganar Abie na dawo mata

“YANA DA MATSALAR JINNU!”

Da sauri ta sake kallon shi, murya ƙasa-ƙasa tace 

“sun bugar da shi ne kenan?”

Gyara zaman ta tayi, ta jingi na da murfin motar tana fuskantar shi, lumshe idanun ta tayi tai shiru, can dai tai

Gyaran murya, sannan ta fara da bisimillah

Cikin zazzaƙar muryar ta da ƙira’a me daɗi ta fara karanto fatiha, sannan ta shiga baƙara

Tiryan-tiryan take zubo karatun ta, ba wani ɗar ko tsoro a tattare da ita, sema wani tausayin Abdul ɗin dake mata shiga farat ɗaya cikin zuciya.

Tunda zainab tai nisa a cikin karatun ta, Abdul ya fara jin sarewar na rage ƙara,

 kaifin sautin karatun Zainab na dakushe sautin sarewar da Abdul ke ji,

A hankali da kaɗan kaɗan, sautin muryar zainab ya gauraye kunnen shi har cikin ƙwaƙwalwar shi

A mugun kasalance Abdul ya buɗe idanun shi da gaba ɗaya akan fuskar zainab suka sauka

Shiru yayi yana kafe bakin ta da kallo,

 kallon yarda bakin ta ke ba ma duk wani harafi haƙƙin shi yake, 

A hankali ya gangara da idanun shi saitin nata idanun da suke a lumshe, gashin idanun ta a jiƙe, alamun idon ta taf yake da ƙwalla

Lumshe nashi idon yayi yana jin wata nutsuwa da kuma ƙarfi-ƙarfi na shigar shi,

Sautin muryar ta na mishi wani maganiɗisu ƙara  kusantowa gare ta

Yarda ya ke jin ya wuce tunanin shi, murya can ƙasa ya furta

“Ya salam!”

Da sauri Zainab ta buɗe idonta jin muryar shi, duk da dai ƙasa-ƙasa yayi maganar, amma da yake Allah ya bata kaifin ji yasa taji

Idanun ta akan nashi idon ya sauka, da sauri ta kauda nata idon gefe,

A kasalan ce yace

“Kiyi haƙuri, na kasa gane gidan ne shiyasa, nake ta zagaye dake a waje ɗaya”

Da mamaki ta waigo tana kallon shi, badai tace komi ba sema gyara zama da ta sake yi.

Sarai yaga kallon tambayar da tai mishi, murmushi kawai yayi yace

“Nasan ba lale ki yarda ba, amma wallaahi gidan ɓace min yake, se inmance wani layi zan shiga, kin san na kai wajen sati kullum se na fito gida da niyar inzo wajen ki, amma se in nemi layin in rasa, se in ta mai-maita layi har dai da ga ƙarshe in haƙura”

Da mamaki sosai Zainab ke sauraron Abdul,  abun ma se yaso bata dariya, wai “se yayi ta maimaita layi”   seda ta murmusa, sannan tace

“To ka kalla yanzu da kyau, ba wannan layin da keke shirin shiga bane, layin gaba ne”

Ba musu ya fasa shiga layin farkon ya shiga na gaban, suna shiga se ga gidan su Zainab daga gefe,

Kallon shi tayi ta ɗage gira ɗaya, irin ya ka gani ɗin nan?

Sosai ɗage girar yayi ma Abdul kyau, har seda ya ɗan dara, duk da kasalar dake damun shi.

Buɗe motar tayi ta fito,

 sauke glass ɗin side ɗin shi ya yi, yace

“Zanzo anjima da dare in ƙara duba jikin naki”

Murmushi kawai zainab tayi, a ranta tace

“Kar dai kaje kai ta bin layi, nidai ba ruwa na”

Kallon ta ba ƙaramin nishaɗi ya ke saka shi ba, can dai yace

“ki shiga gida ki huta akwai rana, se nazo ɗin, kuma kice ma wannan tsohuwar ina gaishe ta”   ya ƙarashe maganar yana murmushi

Wannan karon kasa riƙe dariyar ta zainab tayi, seda ta dara, amma cikin nutsuwa, tace

“IYA, sunan ta fa”

Shima dariyar yayi yace 

“To ace ma IYA ina gaisheta se nazo da daddare”

Zainab tace “zan gaya mata da na shiga ciki”

Har ta juya ta fara tafia, ta waigo da sauri, karaf suka haɗa idanu, 

Ɗan basar wa tayi tace 

“kar ka manta da addu’a dai, kar ka fito asaka kai ta maimaita layi”

Ta ƙarashe maganar tana toshe bakin ta.

Murmushi Abdul yayi ya kaɗa kanshi, yace 

“ki shiga gida, se nazo”.

Tana saka ƙafar ta a soron gidan sukai ido huɗu da Abie

Ga dukkan alamu ya jima tsaye a wajen

Wata almurar kunya ce tazo ta rufe Zainab,  kafin Abie yace wani abu, tai saurin cewa

“Wallahi tawowa sukayi suka barni a can Abie”

Murmushi kawai Abie yayi, ganin yarda take wani kame-kame, 

Dan ya ƙara kunno ta yace

“Amma ya naga kun daɗe Auta?”

Fuska a marairai ce ta kalli Abie, tas abinda ya faru ta gaya mishi, har yarda gidan ke ɓace mishi in yayi niyar zuwa.

Shiru Abie yayi, yace

“to ƙarasa ciki, Allah yayi miki albarka”

Da ɗan gudun ta taƙarasa cikin gidan, 

IYA na zaune tana ta bitar addu’ar da mama ta tuna mata suka ji faɗowar Zainab ɗin

Kallon ta sukai duka, yarda ta faɗa kan kujera ta cumimiye kanta

Tsaki mama tayi tace

“Meye haka wai, ko duk ciwon ne?”

Ɗan buɗe fuskar ta tayi kaɗan tace

“wallahi duk kunya ce ta addabeni mama, Abie ya kamani ina ta zuba ma wancan mijin aljanar murmushi, kamar wata doluwa wallahi”

Me mama zatayi inba dariya ba, 

Taɓe baki IYA tayi tace

“Na gaya miki ai binta, zainabu ta fara rikiɗewa itama, yo miye abin burgewa a wajen wannan?”

Da sauri IYA ta kama bakin ta, tai gummm, sannan taci gaba da bitar addu’ar ta.

Alhamdulillah malam, komi ya kammalu, se a turo mata suzo suga wajen in ba matsala.

Daga can ɓangaren Abie, murmushi kawai yayi yace

“Ba wani buƙatar se mata sunzo, kawai gaya min yawan ƙofofin gidan da na windo, 

Anjima zan turo masu saka komi inshaAllah”

Badan Abbah ya so ba ya lissafa ma Abie yawan ƙofofin da windunan, 

Yaso ace shi yayi ma zainab komi, saboda halarcin shi gare shi

Amma ƙiri-ƙiri Abie ya nuna be yarda ba, ba yarda Abbah ya iya, se ya sakar mishi.

Cikin girma da mutunci sukai sallama da junan su, kowa ya aje waya.

Cike da farin ciki Abbah ya ƙarasa shiga gidan na shi, duk wanda ya ganshi ze san lallai yana a cikin farin ciki

Memakon ya wuce palon shi yarda ya saba akoda yaushe in ya dawo

Waje ya samu a nan palon Ummie ya zauna, 

Abinci da komi duk a nan yaci, seda ya ƙoshi yayi hamdala tukun ya kalli ummie da fuskar ta ba yabo ba fallasa yace

“me da me zaku buƙata na taron?”

Shiru ummie tayi na wasu ƴan sakonni, can dai tace

“Taro za’ayi ne sosai?”

Da mamaki Abbah ke kallon ta, baya so sam ya sauya daga mood ɗin farin ciki da yake ciki i zuwa ɓacin rai, yace

“Ya kika gani ke?”

“Kawai ayi cefanen komi da komi, tunda an riga da an ɗaura aure ai an gama taro Abbahn Abdul”

“Shikenan” kawai yace mata, ta tashi ya tattara keys da hular shi da ya aje akan kujera ya hanyar palon shi.

Amal da Fauza na daga gefe, sunji sarai abinda ummien nasu tace

Amal na ganin Abbah ya shige ta sakko ƙasa kusa da ummie tace

“Ummie, ba amsar da ya dace ki bama Abbah kenan ba gaskiya, ni wallahi kwana biyu se inga kamar ba ummien da na sani bace”

Sororo ummie ke kallon Amal da tai ƙwal-ƙwal da idanuwa kamar zata fashe

“Gaya min yarda za’ai to?” ta zuba mata idanu

Murya a tausashe Amal tace

“Kin fimu sani ummie, komi a wajen ki fa muke koya, 

amma ni a gani na yarda kike son yaya Abdul be kamata ace auren shi yazo ba kuma ki nuna halin ko in kula akai, 

gaba ɗaya yanayin Abbah ya sauya daga maganar da kika yi ummie, dan Allah ki bishi ki bashi haƙuri se ku ƙarasa maganar”

Shiru Ummie tayi tana nazarin maganar Amal,

Tabbasa tasan gaskiya ta ke faɗa, amma ita ba wai tana ja baya bane saboda wani dalili can daban, kawai bata son ta saka kanta cikin matsalar jinsin da ba naka ba

Kuma dai ai ance tsoro halal ne.

Numfashi ta ɗan fesar me ɗan huci, tukun ta yunƙura ta miƙe,

Kafin ta wuce tace

“ku gyara min wajen nan” sannan ta kalli fauza tace “ke kuma ki ɗora min girkin dare kafin na fito”

Dukan su da “to” suka amsa mata, sannan ta wuce palon Abbahn kai tsaye.

***Tunda sun maka komi guru, kai ka samu kayi wannan da kanka gaskiya, nan zasu gane lallai ka gode da abinda sukai maka

Shiru Abdul yayi, gaba ɗaya rabin hankalin shi na kanta, daɗin muryar ta, dariyar ta da kuma tsokanar ta

Shi kaɗai se zuba murmushi yake, baki sake muslim ke kallon shi, dan gaba ɗaya a ƴan kwanakin nan baka isa kayi magana ɗaya zuwa biyu da Abdul ba, batare da yayi shiru na wasu ƴan daƙiƙu ba, a shirun da yake yi ɗin yai ta zuba murmushi yana kallon waje ɗaya.

Su a tunanin su ko Aziza ta fara taɓa shi ne, amma basu san mamar ƴar baƙa ce a ran nashi ba.

Da dai muslim yaga abun ba na ƙare bane, ya sa hannu ya zungure shi, yace

“magana fa muke yi guru”

“ina jin ka guy, yanzu ya kake tunanin za’ayi?”

Muslim yace “ya za’ayi me”?

Ɗan yatsina fuska yayi yace

“Haɗa kayan mana”

Shafa kanshi yayi, ya fesar da iska daga bakin shi yayi shiru, kafin daga baya yace

“Ni duk bam san waɗan nan abubuwan ba wallahi, bana son in tunkari ummie da komi yanzu, naga itama yanzu wani tsoro na take ji sam bata ƙaunar ina raɓar su, 

Abbah kuma ba zan iya maganar da shi ba gaskiya guy”

Tausayin Abduk sosai zaku iya gani akan fuskar muslim, 

Murya a sanyaye yace

 “muje da kanmu mu haɗa komi, in muka ce  lefe zamu haɗa, tunda sana’ar su ne zasu san abunda ya dace ai”

Murmushi Abdul yayi, ya kalli muslim a ido yace

“nagode daka tsaya mun duk da kaima kana da hujjar da zaka iya guje min guy”

Banza da shi muslim yayi, ya shige toilet kamar wanda ze yi wani abun,

Seda ya tsaya ya share hawayen da ya kasa riƙe su, tukun ya wanke fuskar shi sannan ya fito yace “muje muyi komi da wuri”

Basu shawarci kowa ba, da shawarar su kawai sukai aiki,

Wani babban store suka samu suka shiga,

Inda suka ce lefe zasu haɗa, shagon akwai mata da maza, 

Wasu mutum biyu me shagon ya haɗa su da su yace  “ku taya su haɗa lefe”

Da “to” suka amsa, sannan Abdul suka bisu.

Wani saitin akwati me kyau ya gani, yace su yake so

Tas akwatuna shidan nan seda aka cika su da kaya, abu biyu ne ya ja musu delay, rashin sanin size na bra da pant

Da matar ta tambaye shi size ɗin amaryar shiru yayi ya rasa me zece

Muslim na gefe yana zuba mishi iya shege

Ganin zasu ɓata lokaci yasa matar tace

“ka kirata a waya ne ka tambaye ta sir”

“minti biyu” Abdul yace mata sannan ya fita daga waje

Yana fita yayi shiru, yana tunanin ta inda ze fara ma

A fili yace “Tabɗijam!”

“Ni da bani da number ta ma ta ina zan fara tambayar?”

Yaya Abubakar ne ya faɗo mishi a rai, beyi ƙasa a gwiwa ba ya zaro wayar shi yayi dialing number shi.

Bugu biyu ya ɗaga haɗe da sallam, yace

“Ango, kuma siriki na”

Dariya sukai gaba ɗayan su, sannan Abdul yace

“Godiya nake siriki na, ya aiki ya kuma iyali?”

“lafia lau suke”

Bayan gaisawa da sukai, daga ƙarshe dai da ƙyar Abdul ya iya tambayar shi number zainab.

Seda yaya Abubakar ya gama mishi iyashege tukun ya tura mishi number.

Tsura ma number ido yayi ko ƙyaftawa ba yayi

kafin ɗan wani lokaci ya ɗauke ta tsaf a kan shi, 

Abdul akwai kwanya, shiyasa yaci sunan “GURU” a wajen abokan shi da yanzu gaba ɗaya babu ko ɗaya se Muslim kawai.

Har ya danna ma number kira yayi maza ya kashe, a ranshi yace “to ta ina zan fara ni kam”

A hankali ya ƙarasa in da sukai parcking, ya buɗe mota ya shiga ya ja sit baya

Ya kai kusan minti goma yana nazarin yarda ze tambaye ta, daga ƙarshe kawai yayi shahada ya danna mata kira

Gaf da wayar zata tsinke zainab ta ɗaga,  murya a tausashe tace

“Assalamu alaikum”

Gaba ɗaya tsiga jikin shi ta tashi jin muryar ta,

Shirun data ji yasa ta sake maimaita sallamar ta

Dakewa yayi ya amsa mata sallamar

Shiru zainab tayi jin muryar shi, da farat ɗaya ta gane waye

Daga ɓangaren shi yace

“kina lafia, yasu IYA da Mama?”

Sunan IYA da ya ambata, seda ta murmusa, a hankali tace “IYA daru kenan”  Sannan tace “suna nan kalau”

Rasa me ze faɗa yayi yace

“Abdul ne fa”

Abun ma dariya yaso ya bata, tace “na gane fa”

Itama ta saka “fa” ɗin kamar yarda ya saka shima

Yarda tayi ɗin abun ya bashi dariya, tana jiyo sautin dariyar shi ta waya

“kin iya tsokana yarinyar nan” be jira amsar ta ba yace 

“ehhm, dama tambayar ki zanyi”

“tohm, Allah yasa na sani”

A ranshi yace “kin sani mana”

Yana ɗan ciccijewa yace

“Dama size ɗin bra da pant aka ce na tambaye ki wai”

Shiru Abdul yaji, ya duba waya yaga wayam bata a kan layi

Shiru yayi can kuma ya ƙyalƙyale da dariya, yace

“nasan za’ai haka yasin”

Ta ɓangaren Zainab kuwa, kafin ya gama ƙarashe maganar ta latse wayar gaba ɗaya ta mutu, 

A guje ta kwaso tayi kan IYA ta cumimiye ta tana ɓoye kanta a rigar ta

Da sauri Iya tace

“a’uzubullahi minashshaiɗanirrajim, aniyar kowa ta bishi”

Mama na sallame sallah ta kalli zainab dake neman komawa cikin IYA, Itakuma IYa na ta ƙoƙarin hankaɗera daga jikin ta, tace

“wallahi banga ranar da zaki nutsu ba zainab, ke kullum se anga kamar kinyi hankali, se aga kuma abu ya dawo baya”

Da ƙyar zainab ta fito da fuskar ta tace

“Kunya ce wallahi ta addabeni mama, na rasa a ina zan ɓoye, gashi ke kina sallah, ga ƴar baƙa ta tafi biɗiɗi shiyasa na ɓoye a rigar Iya tunda itace a zaune”

Takaici da ya gama cika IYA, ta kalli zainab tace

“A ina kika je kika jiyo kunyar, banda dai iyashegen ki”

Ido a rurrufe tace

“Wai fa tambaya ta yayi size ɗina”  tana gama faɗa ta ƙara duƙunƙune IYA.

Tsaki mama tayi ta juya abinta

IYA kam, bata gane ma me zainab ɗin tace ba, 

Ranƙwashi ta sakar mata akai tace

“me aka tambaye ki? memakon su kije can ki musu tsiyar zaki zo nan mu da kika raina ki mana”

can gefe zainab ta matsa tana sosa inda Iya ta ranƙwashe ta, tace

“Yo in banji kunya ba me zan ji?, cewa fa yayi wai meye awon rigar nono na da ɗan kamfai na  fa”

Salati Iya ta sake bugawa tana tafa hannaye, 

Hannu ta miƙa ma zainab tace

“matso zainabu na, ai tun farko bayani zaki min in fahimci halin da kike a ciki, wannan kam abun jin kunya ne wallahi”

Rigar ta taɗaga ta janyo zainab ɗin tace

“shige, har se kunyar ta sauka, ko ni nan da ba ni aka tambaya ba neman ƙasa nake na shige wallahi”

Ya jima zaune yana jujjuya wayar hannun shi, 

Sosai ya kwashi dariya, a fili yace

“Ashe tana da kunya haka”

Muslim da ya gaji da jiran shi ya biyo bayan shi, 

Zaune ya iske shi ya tasa waya a gaba yana ta zuba murmushi

Kallon wayar hannun na shi muslim yayi, ya ƙara maida kallon shi ga Abdul, sam bega wani abun da za’ai wa murmushi ba

Zungurar shi yayi yace

“Kafa aje mu wallahi, daga tambayar size ka wani zo ka zauna kana ta zuba murmushi”

Murmushin ya sake yi yace

“Taƙi faɗa min wallahi, kashe wayar ma tayi gaba ɗaya,

Amma bari na kira Amal naji nasu, dan nasan bazata wuce su ba”

Size 37 suka ɗauka kawai, aka haɗa musu komi da komi sannan ya biya

Ɗakko su suka yi, aka saka wasu a can baya, wasu kuma a sit ɗin baya, sannn suka wuce

Suna tafe a hanya Abdul ya kalli muslim dake waya da juwairiya yana bata labarin auren Abdul ɗin, yace

“Can gidan nasu zamu wuce akai?”

Aje wayar muslim yayi yace

“Bafa haka ake ba, ka fara kaiwa gida su gani, daga can se ai deciding yarda za’aiyi’

Murya a sanyaye yace

“Ai ban sani ba guy, thanks”.

Ummie na zaune tana waya da sistern ta akan taron da zatai, Abdul da muslim suka fara shigo da akwatunan suna ajewa anan tsakiyar palon.

har suka gama, a sannan itama ta gama wayar da take

Kallon kayan tayi sannn ta maida kallon ta ga Abdul tace

“Daga ina kuma wannan?”

Ba wani tunani na biyu Abdul yace

“Daga shago suke ummie”

ƙara kallon shi tai tace  “ban fahimta ba Abdul, wai kana nufin da kanka kaje ka haɗo lefen ka?”

Bata jira cewar shi ba ta ɗora da “salan ka ja min zagi a gari ace ina zaune kana abu da kanka? gaskiya baka kyauta min ba”

Bece uffan ba har seda ta kai ƙarshen zancen ta sannan yace

“Ayi haƙuri” ya tashi ya fita, tunda muslim ya taya shi kawo kayan be zauna ba ya koma cikin mota yayi zaman shi

In da ace da ne, da ɗakin Abdul ɗin ze shige yayi kwanciyar shi, acewar shi wai ɗakin yafi ƙarfin shi yanzu.

Abdul na fitowa, ummie ta ƙwala ma su Amal kira suka fito

Kafin ta yi magana Amal tai caraf ta zauna gaban kayan tace

“Laa, ummie har an kawo kayan?”

Tsawa ummie ta daka mata, seda ta tsorata tai baya, 

“Dan ubanki karki janyo mana bala’i, salon ki buɗa ki nuna murnar ki kema ta cinno miki nata ƙanin ko wani ɗan’uwan ya maƙale miki?”

Shiru Amal tai tana ja da baya, fauza kam taɓe baki tayi tace

“ummie kenan”

Kafin ma ummie ta waiga kanta, har ta shige ɗaki.

Ɗaga murya tayi yarda fauzan zata iya jiyo ta tace

“Wallahi in baki fito ba se na shigo ɗakin nan na lallasa ki”

Fitowa tayi ta tsaya badai tace komi ba, kallon su ummie tayi tace 

“ku ɗauki akwatunan da bisimillah, ɗaya bayan ɗaya ku kaisu palon Abbahn ku, ku gama kuzo ku ɗakko min su hishma daga makaranta”.

Rai a jagule suka ja akwatunan suka shigar da su, na ƙarshe da Amal ta kai seda ta ɗan buɗe kaɗan ta gani, ba  dai ta taɓa komi ba tai maza ta maida ta rufe shi a yarda yake, sannan ta fito palon.

Abbah yaji daɗin ganin kayan nan, gaba ɗaya shi beyi wani tunanin  haɗa lefe ba, hankalin shi sam be kai nan ba, kallon Abdul yayi yace

“Allah yayi maka albarka Abdul, Allah ya sa wannan auren sanadiyar yayewar dukkan wani ƙuncin ka ne”

Kanshi a ƙasa yake amsawa da “Amin”

Ummie na daga gefe, list ɗin abubuwan da zata buƙa ta miƙa ma Abbahn tace

“Wannan sun isa, abun kamar wasa, masu kira na zasu zo naga suna da yawa fa”

“Humm” kawai Abbah yace ya karɓi takardar.

Hankalin shi ya sake maidawa kan Abdul dake zaune idon shi a kan Tv, yace

“Zan kira Aliyu da sayuɗi se su kai anjima bayan magrib”

Kafin Abdul ya amsa, ummie tai karaf tace

“Nasha mata ne zasu kai Abbahn Abdul?”

“A’a” kawai tace yaci gaba da shan bakin shayin shi yana kallon TV..

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU.

Back to top button