Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 26 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                            TWENTY-SIX📍

       Girgiza kai Deen yayi ya shiga kakkabe jikinsa data bade da kura yana lissafin yanda zeyi tracking dinta, kamar yasan wani abu ze faru ya dauki tracker a gidansa yasa a motar da wata manufar daban sai gashi abun ze masa aiki a inda baya tinani, kawai yarinya tayi gaba da mota kamar ta ta, ji wani audacity dan Allah?…. Abu daya ne ze hanashi nemo inda take a darennan and that’s because he’s not with his phone dake tracker din is linked to his phone, yanzu dole sai ya koma prison tinda wayar na chan though yana da plan din komawa a yau kafin securities din su farka daga suman da basu san sunyi ba, yanzu kam saidai yasan yanda zeyi ya dauki phone dinsa ya sake gudowa……. 

          Driving take a haukace har securities din unguwar saida sukayi kokarin tareta amma taki tsayawa, ganin kamar zata bi takansu ne yasa suka matsa mata da sauri after jotting down the plate number……

Ta dade tana shawagi akan titi kafin Allah yasa tayi shawarar zuwa school, school din da tafi sati nawa bata jeba, if she’s not mistaken ma kamar exam is starting on Monday gashi ko tests batayi, dage kafada tayi alamun ko oho idanma tayi failing……

      Suna zaune suna dan hirarsu yanda suka saba duk dare idan suka dawo daga library kasancewarsu yan till day break duk inda 9 tayi sungama karatunsu sun dawo hostel, basa taba karatun dare……

       “Nidai wannan unknown girl din ta tsayamin arai wallahi”…..

Cewar eesha dake zaune tana shan tea….

       “Ni bansan yaushe kika zama so concerned about someone’s life ba, kina kulata tana wulakantaki amma kin kasa hakura”……

Cewar Umaima dake kwance tana game a waya….

 Dariya tayi tace:

      “And if you ask me why I can’t say, I think I just like her and she kinda looks like……”

Bata karasa ba sukaga an turo kofar dakin a hankali kamar ana tsoron taba kofar……

Wani tsalle eesha tayi saura kadan ta zubar da tea din hannunta cikin ihu tace;

     “Yar halak, yanzu muka gama maganarki, where have you been zaa fara exam in the next three days, kinyi tests kuwa? Gosh you’re so beautiful wallahi, dan Allah ki dena rufe fuskarki”……

Lumshe idanunta da take jinsu kamar gaurashi tsabar yanda suke mata zafi tayi tana jingina da bango, all she need right now is to sleep, gashi wannan tazo tana mata surutun da ko word daya bata tsinta a ciki ba…..

Tun bayan datayi parking a gaban hostel ta balli usuals dinta tasha bata kara gane kanta ba, she’s got so high burinta kawai ta zube a ko ina ne tayi bacci…..

      “I need to sleep”…

Fatima zainab ta fada tana ruko hannun eesha batareda tasan tayi hakan ba……. 

 Rukota sosai eesha tayi tana fadin;

     “Oh Ohk muje ki kwanta, we’ll talk tomorrow ko?”…..

     “Yeah”….

Taimaka mata eesha tayi har kan bed dinta ta kwanta sannan ta rufe mata spot dinta yanda taga tanayi har lokacin bata dena mamakin maganar data mata ba, ba ita kadai ba har sauran mutanen dakin mamaki suke ganin ta kulata yau, so suke suyi magana akan incidence din amma kowa ya kasa summoning courage, tsit kake ji kamar ba kowa a dakin…..

A hankali billy ta dawo kusa da eesha, kasa kasa tace;

     “Dama haka take da kyau? Why is she always covered toh?”….

    “If you ask me who I go ask? Yanda kika ganta haka nima naganta”…..

    “Kinji muryarta kuwa? Subhanallah!”…..

Wani harara eesha ta mata tana dan tureta tace;

      “Don’t even go there! Mayya kawai”….

Dariya tayi tana shafa fuskar eesha tace;

     “No loud am, amma gsky ina ciki”….

     “In kin ganni a lahira kaini akayi, tashi min daga bed zanyi bacci yar iska kawai”…..

Eesha ta fada tana janye hannunta daga fuskarta….

      “Dama baa abin arziki dake, kwantar da hankalinki ni fita ma zanyi yanzu”…..

     “Allah ya raka taki gona”…….

       Saida yayi tafiya me nisa kafin ya fita daga district din, cab ya tsaida ya fadamasa inda ze kaisa..

      Tun bayan an saukesa a prison din yake tsaye yana tinanin yanda ze shiga ya dauki wayarsa ya fito sannan yaje yayi abinda zeyi ya dawo batareda sun sani ba…….

 Yanke shawarar haura katanga kawai yayi hakan yasa ya nufi bayan building din, luckiky for him ginin bashida wani tsawo sosai, nan da nan ko ya haura sai gashi a compound din…..

Da sanda ya shiga har ya karasa section din da yake, kamar yanda ya zata haka ya gansu yanda ya tafi ya barsu kamar matattu… 

Sadap sadap ya shiga duba wayarsa a inda yake tinanin suna ajyewa, saida ya dade yana dubawa kafin Allah yasa yaga wayar….

Daukan wayar yayi ze fita kenan yaga kamar wani ya motsa a cikinsu, da sauri ya matsa gefe yana boye wayar a aljihunsa…….

Sai daya tabbatar  babu wanda yake motsi sannan ya sake fita ya kuma haurawa ta inda ya shigo yabar prison din gabadaya……

Saida ya bar area din sannan ya kunna wayar amma taki tashi saboda rashin charji……

      “Shit!”….

Deen ya fada yana dafe kansa….

Ganin bashi da yanda ya iya ya shiga tsaida cab dan ya tafi Transcorp yayi charji….

Haka akayi kuwa saidai ko kafin ya isa Transcorp Hilton shadawa ta kusa, dole ya hakura ya bari sai washe gari zuciyarsa cike da taraddadin yanda mami zasuji idan sukaje basu gansa ba, be gama fita daga wannan ba ya sake daukowa kansa wani, duk abinda ze faru ya faru kawai…..

        Karfe ukun dare ta farka as usual, alwala ta dauro tazo ta tada sallah kamar yanda ta saba duk dare…. Hawaye take sosai tana addu’ar Allah ya yaye mata damuwarta kaman yanda ta saba duk sanda zatayi addu’a, gashi ko zaa kasheta batasan meye damuwarta ba, tasan dai tana cikin damuwa sosai…

Tana zaune tana karatun qur’ani har aka kira sallar asuba, tashi tayi tayi sallah sannan ta dora da azkar… 

Mikewa tayi tana ninke sallaya bayan ta idar, haka kawai taji tanasan komawa bacci ranar abinda bata saba ba…. 

Har zata kwanta wata zuciyar tace ta tashesu suma suyi sallah, bed din eesha ta nufa dan batajin zata iya wahalar tashin sauran dan tasan bata lokacinta kawai zatayi ba tashi zasuyi ba…..

A hankali ta janye blanket din eesha ta dan bubbuga kafarta….

Bude ido eesha tayi tana kallonta tace;

    “You want something?”….

     “Sallah!”

Ta bata amsa tana mikewa….

Tashi tayi tace;

   “Shiyasa nayi missing dinki wallahi, harna manta when last nayi sallar asuba da wuri”…..

Fatima zainab batace komai ba ta koma ta kwanta eesha na cigaba da surutunta…. 

Itama sallah tayi tazo ta kwanta kamar tacewa fatima zainab yau bazata fita da wuri bane tadai ja bakinta tayi shiru…..

        9am dot haka agogon dakin ya nuna, farkawarta kenan ta fito tana shirin yin wanka…

Sai 10am sannan ta gama shiri, shirye take tsap cikin wani maroon abaya me ratsin gold, kanta sanye da wula golden, sosai tayi kyau kamar ka saceta ka gudu….

Tana jin ido na rakata duk inda tayi amma tayi kamar batasan sunayi ba, gabadayansu sun kasa dauke ido akanta kadama billy taji labari, ita kadai tasan me takeji aranta, ta maimaita dama haka take aranta yafi sau a kirga…..

Sosai take jinta wani iri yau kamar wacce aka chanja, abu daya ke damunta irin kallon da ake binta dashi baga yan hostel din ba baga yan dakinsu ba, ta rasa mene a jikinta da ake kallo? Saidai kuma abinda taga dama shi zatayi, sanda take lullubinta waya sata? Babu! Toh yanzu ma da taga damar denawa ba wanda ya isa ya hanata….

Dan karamin veil din abayar ta yafa sannan ta dauki car key ta fita…..

  

        “Kutumar uba wannan daga wani duniyar tazo?”..

Cewar umaima kamar jira take ta fita….

      “Hmmm kedai bari wallahi an tashi kaina, yo akanme bazata dinga boye kanta ba, eesha kinga abinda nagani kuwa?”……

    “Ai dama kinfi kowa ganin abubuwa, toh me kika gani?”…..

    “Yanzu idan na fadi abinda nagani sai kicemin yar iska, but seriously I need a hookup with her, wallahi ko nawa ne zan biya”……

     “Umaima ana magana dan wannan zance yafi karfina kinga wai ko nawa ne zata biya”……

    “Bar yar is wannan tafi karfin tsohonki yarinya bare ke yar iskar karshen zamani, if e sure for you kije ki sameta ki fada mata, mu ba ruwanmu”….

   “Ya isa kar ki kuskura ki sako min uba a wannan lamari inba hakaba sai insa a dauremin ki yarinya inga uban da ze iya fito dake, kuma duk yanda zanyi in sameta sai nayi kawai ku zuba ido kusha kallo”….

Tana fadin haka taja tsaki ta fita daga dakin………

      Tun asuba Mami tazo tashinta tayi sallah, tafi minti goma tana knocking ba’a kulata ba hakan yasa tayi sallama tashiga…. Saidai me? Kamar ba’a kwanta a gadan ba, murmushi tayi tana tinanin maybe tana toilet, probably irin mutanennan ne masu gyara gado kafin suyi alwala, tinanin haka yasa ta fita kawai…… 

Wata maid aka tura taje ta kirata suyi breakfast around 10am dake sun makara ranar……

Suna zaune basu taba komai ba suna jira tazo, sai ga maid din ta dawo tace musu bakuwar is no where to be found….

     “This is a joke!”….

Cewar Umm tana mikewa da sauri Mami na mara mata baya……

Babu kalan binciken da basuyi ba a gidan amma babu ko alamarta, sosai suka daga hankalinsu tuninika iri iri a ransu, wani abu ne ya fadowa Mami tasa a tara mata duka ma’aikatan gidan including me gadi dan tayi interrogating dinsu……..

     “Dakai zan fara because you’re in charge of the gate, jiya munzo da bakuwa gidannan kaga fitarta?”…

A rude yace;

     “Eh hajiya ta fito nace mata idan zatayi aike ga Isa nan ta aikeshi amma tace sako zata karba yanzu zata dawo”……

     “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, tun karfe nawa kenan?”…….

Cewar Umm data keta salati

      “Tara ta wuce sosai”…..

    “Amma ya zaka bar Yarinya around wannan time din ta fita? Basai kazo ka tambaya ba?”….

Mami ta fada dan ta rasa me zata dafa taji sanyi a ranta…..

Dafata Umm tayi ta kalli mutanen gurin tace;

     “You all can go”

     “It’s not his fault, bamuce kar a bari ta fita ba”….

Umm ta sake fada bayan sun fita….

Numfashi mami ta sauke tana fadin;

     “Toh yanzu meye abunyi? Why am I feeling like she’s not safe?”……

     “Same here, could it be abinda Saif ya fada gsky ne? Dayace aljanun basu gama fita jikinta ba?”….

    “I’m beginning to think of that too, lamarin yarinyar nan na bukatar babban malami sosai”….

Cikin damuwa da tausayawa Umm tace;

      “You’re right! Yanzu ta ina zamu fara nemanta?”…

      “Dole a gurin Saifuddeen zama samu information”…

    “Hakane, mu shirya muje prison din, bawan Allah he’ll be so heartbroken in yaji bata gidan, tsap zece mune bamu kula da ita ba”…..

    “Ke kike ta tashi, ni damuwata kawai muga yarinyar, menene ma sunanta?”…..

     “Fatima zainab tace!”….

   “Ikon Allah, mushirya mu fita toh”….

          Driving take hankali kwance dariyar mugunta kwance  akan fuskarta, “kifi daga sama gashasshe”, ta fada tana cigaba da dariyarta, ashe haka motar keda dadi bata sani ba? Dake jiya bata cikin hayyacinta shiyasa bataji ba?, dama ance abinda ba naka bane yafi dadi, itako ta samu motar yawo a bagas…….

Horn tayi a gaban gate din me gadi ya taso ya bude mata da sauri yana gaisheta, bata amsa ba tace;

    “Kar a rufe motarnan da ita zan koma”…..

     “Angama hajiya”…

Ya fada yana rufe gate bayan ta shiga….

     Direct part din daddy tayi bayan tayi parking motar, sosai take san magana dashi akan auren da suke shirin yi, tinda bukatarta ta riga ta biya bataga dalilin auren tsoho ba, idan auren ne gwara ta auri khaleel ya fiye mata ubansa……

Knocking daya tayi daddy dake zaune a parlour ya taso ya bude kofar….

Saida mood dinsa ya chanja daga ganinta, kallo daya zaka masa kasan ba karamin jindadin ganinta yayi ba, irin ka dade kana neman mutum sai yau Allah yasa ya ganshi……..

 Kallonta yayi daga sama har kasa yace;

     “Welcome dear, yana ganki haka yau?”….

Cikin ko in kula tace;

     “Daddy meka gani?”…

    “Not covered as usual?”

   “And so?”…

   “Nothing, come in”….

Ya fada yana murmushi……

Shiga tayi ta samu guri ta zauna, shima zama yayi a kujerar dake facing dinta yace;

     “What would you like to have? Nasan bakiyi breakfast ba!”…..

     “Nayi! Magana nazo muyi!”

   “Ina jinki? Nima ina nemanki dama!”….

    “Aurennan nake so a fasa!”….

Ta fada kai tsaye…….

Zaro ido daddy yayi cikin dan rudewa yace;

     “Wani auren??!”

    “Namu ni dakai, a fasa! Zan dawo maka da duk abinda na karba, ko ka barshi kawai a madadin danka khaleel, dama shiya kamata in aura!”….

     “You must be kidding! Kinsan plan din danayi akan aurennan kuwa, harfa hafsah na saka!”….

    “Wannan kuma matsalarka! Nina saka ka saki matarka? In banda abinka me zanyi da tsoho kamarka? Sannan ni bazan iya cin amanar khaleel ba…Banyi expecting zamuna dragging akan wannan maganar ba! Kamata yayi kayi farin ciki da nace na fasa tinda nina maka dole tin farko!”….

Saita kansa yayi ganin idan ya biyo mata ta haka bazasu daidaita ba yace;

     “Hakane daughter I don’t even know what came to my mind, you deserve khaleel not me gaskiya, forgot to even tell you khaleel na kwance a asibiti bashi da lafiya sosai because he couldn’t reach you”…..

      “Subhanallah, wani hospital yake?”….

Ta tambaya tanajin tausayin khaleel karo na farko a rayuwarta….

     “National Hospital, Abuja”

   “Zanje in dubashi Insha Allah”….

Ba daddy ba har ita da kanta tayi mamaki dataji tana son zuwa dubashi, daga jiya zuwa yau jinta take kamar different person……

     “Ok, ya bani sako in baki, let me get it”

Yana fadin haka ya haura sama……

Daddy na sakkowa daga steps bayan ya dauko sakon wayarsa ta shiga ringing, ganin me kiran yasasa dauka da sauri yana sawa a speaker, gabadaya ya manta da mutum a parkour……

Tinda ya fara wayar hankalinta ke kai, hakanan ta samu kanta da bawa wayar dukkan nitsuwarta…..

   

      “Alhaji habibu nawa, ni kuma na Allah”….

Cewar daddy yana dariya….

 Daga daya bangaren akace;

     “Hmmm kaidai bari mutumina, aikin gurina ya kammalu, na gama da tsegaran yaronnan dan gidan Alhaji Abdallah”…..

      “Ahh kace anyi nasara kenan”….

    “Sosai ma, take taken uwarsa justice fatima ne keban tsoro, naga alamun tana neman gano bakin zaren shiyasa jiya na aika yarana suka kaiwa gurin hari, maganar da nake maka yanzu an kona prison din kurmus”…..

   Dariya daddy yayi ya shiga komawa sama yana fadin;

     “Kai kai abu yayi kyau gaskiya amma na tayaka murna, hankali kwance zakayi harkannan yanzu kabar alhaji abdallah da jimami kasan ba karamin ji da munafukin dansa yake ba”…

 

 Daganan bata karan jin abinda sukace ba amma hankalinta ya tashi, duka taji sunayen da aka fada saidai bata sonsu ba bare tace zata taimaka musu, toh wani taimako ma bayan ance an kona inda suke?… Ta dade da sanin daddy is doing something illegal saidai batasan abin nasa ya kai haka ba…..

Tana cikin wannan hali daddy ya sauko, da sauri ta saita kanta kamar bataji komai ba, shima be damuba dan beyi tinanin taji ba…..

 Mika mata zobe yayi yace;

    “Gashi yace dan Allah idan na baki kisa”…,,

Karba tayi tasa a hannunta sannan tace;

    “Thanks”…

Murmushi yayi sosai yace;

     “You’re welcome, now will you marry me?”…

       “Yes”…

Ta fada itama tana murmushi…..

    “Good, when?”….

      “Ko yau kace”…

Dariya yayi yace;

    “Ai komai saida shiri, mudai bari gobe kafinnan nayi wasu abubuwan da suka dace!”

   “It’s ok, I’ll be on my way”….

    “No prob, basai kinje kin duba khaleel ba kinji koh?”….

    “Ok”

Ta fada tana mikewa…..

    “Sannan kar kiyi nisa kisani nemanki, kizo da safe gobe dan dole sai kinanan aurennan ze yiwu, kinji ko?”……

      “Insha Allah, sai goben”….

Ta fada tana fita daga gidan……

     

        Yanda yaga rana haka yaga dare ranar, duk yanda yaso ya rintsa kasawa yayi dukda yayi tracing din inda akayi parking motar yaga bakin hostel hakan kuma ya tabbatar masa school ta tafi kenan, zuwanta school din ya fiye masa kwanciyar hankali amma ya rasa meyasa ya damu sosai, hakanan yakeji kamar something isn’t normal and it’s about her, abun mamaki sai gashi ya dauro alwala  ya shiga sallah akanta yana mata addu’ar Allah ya kareta, abinda ko kansa bayama addu’a sai gashi yau ya bata night dinsa akan wata shakatafi dan shi dai be taba sata a jerin masu hankali ba, har aka kira sallar asuba hankalinsa be kwanta ba…..

Yaso ya fita tunda asuba amma dayake bacci barawo ne sai ya sace sa, bashi ya farka ba sai after 9….

Da sauri sauri ya shirya yana duba tracker ko tabar hostel……

       Parking tayi a Hilton idonta na sauka akan disposable nose masks dake center motar, zaro guda daya tayi kai kace nata ne ta fito tana kokarin daura wa, kamar ance juyo tagansa few inches away from her, batasan sanda ta saki nose mask din a kasa ba irin kayiwa mutum abu ya kamaka red handed yanz..

  Tun kafin ta fito yake tsaye a gurin tun tana kokarin zaro nose mask, badan yasan motar bane cewa zeyi ba ita bace ba, he has always imagine how she’ll look under that hijab, ashe haka take, very very breathtaking? Could it be the reason why she’s always covered? Besan ya yar da wayarsa a kasa ba saida yaji tace;

     “Mallam bani hanya in wuce, ba abunda ka iya sai tarewa mutane hanya”…..

Sai a lokacin ya dawo daga suman wucin gadin dayayi ya shiga kallonta sosai tundaga sama har kasa, sosai yaji ransa ya baci ganin yanda abayar ke nuna shape din jikinta, dan kallon gefe yayi yaga ko akwai wa’yenda suke kallonta….. Nannauyen ajiyar zuciya ya sauke ganin ba mutane a harabar gurin……

Sai ya dawo da idonsa kanta, ya haderai sosai yace;

     “Ko kunyar kin sace min mota bakiji ba? Saima wata magana da kike fadamin?”…..

   “So nawa zan fada maka abun kunya gaba na basa ba baya ba?”….,

Kwafa yayi ya duka ya dauki wayarsa da screen din ya dan tsage kadan yace;

    “Ni bama wannan ba meya hanaki sa hijabi yau?”

      “Haka naga dama”…

   “Just know that you’re not adding an inch from here a haka”….

     “Sai kazo ka hanani motsawa mallam!”….

     “Karki kara cemin mallam, calla Yaya Deen or Yaya saif or better still Yaya Saifuddeen, be respectful!!”……

     “Respectful my foot! Da in cemaka yaya wallahi gwara nacewa mage anty”…..

Sosai maganarta ya basa dariya ya daure yakiyi dan da gaske bayasan rashin kunya, dole kuma ya saita ta tana bashi respect……

     “Zan saita ki very soon! And what took you to Alhaji Ibrahim’s house?”…..

    “Wannan kuma kaika san shi!”….

    “Zanyi maganinki, sannan zaa fara exam next week, I don’t think kinyi test ko guda daya, wata kalan unserious student ce ke?”….

Murmushi tayi da saida ya jingina da motar dake gefensa aranshi yana ce mata“seductive bitch” sannan tace;

     “Sai yau kasani? Banyi test ba exams dinma idan naga dama bazanyi ba and I’m not gonna fail any course!”……

Harararta yayi yace;

       “Maybe you have some business with sauran nonsense lecturers din, just know that ko kinyi karatu bazakiyi passing course dina ba, and I’ll make sure you fail every courses”….

 Cikin rashin damuwa da maganar exam din tace;

     “Matsalata dakai ka cika surutu, now you’re already giving me headache, can you excuse me?”

Ta fada tana kokarin bin ta gefensa ta wuce, a daidai lokacin idonsa ya sauka akan zoben hannunta, abinda ya dauke masa hankali kenan harya kasa bata amsar dayayi niyar bata, zoben looks familiar amma ya kasa tuna a hannun wa ya taba gani, kamo hannunta yayi yace;

     “Waya baki zobennan?”

     “It’s none of your business sakemin hannu”

Ta fada tana kokarin janye hannun….

Be kulata ba ya shiga kokarin zare zoben, kokawa suka soma shi yanason ya cire zoben dan haka kawai yaji be yarda da zoben ba sannan a hannu wanda yaga zoben ne ya kara sasa rashin yarda da zoben,ita kuma tanaso ta janye hannunta……..

 After lots of janye janye yayi succeeding din cire zoben, yana shirin sakin hannunta yaji mutum a jikinsa, da sauri ya tareta kafin takai kasa yana fadin;

     “Nashiga uku ta suma? I hope she’s not trying to set me up again? Ke tashi!!”….

Domin sauke cikakken Littafin ku dannan bulun Rubutun dake kasa 👇👇

https://www.aihausanovels.com.ng/2023/01/wace-ce-ita-chapter-19-complete-hausa.html

 

~Uniquebarakancy~

Back to top button