Harijin Sarki Page 35 Romantic Hausa Novel
Rana ta kai kwana biyar bayan haihuwar Rayyan amma Sultan bai samu natsuwa ba.Ko da yake bai bayyana wa kowa ba tun daren da jaririn ya zo duniya yake jin wani irin nauyi a ƙirjinsa kamar ana tura masa numfashi daga wani wuri da ba shi gani Daren yau, bayan sallar isha’i, ya zauna a cikin ɗakin madubin sarauta ɗakin da babu wanda ke da ikon shiga sai shi da wani bawa tsoho mai suna Rifaa, wanda shi ne mai gadin asirin masarauta Madubin nan yana rataye a bango, girmansa ya kai mutum biyu, kuma a duk lokacin da aka kalle shi, sai ya nuna wani irin ruwa mai motsi ba kamar madubi na duniya ba Sultan ya yi kallo sannan ya furta kalmomi da ya gada daga kakanninsa“Ya madubin ƙaddara, ka buɗe min hanyar da nake neman sanin gaskiya” A lokaci guda, haske ya fara fitowa daga cikin madubin Sai ya ga wani yaro sanye da farin kaya yana tafiya cikin duhu Cikin mamaki, ya ɗaga murya“Kai waye kai yaro?”Amma kafin ya samu amsa, sai muryar Rifaa ta yi ƙasa kamar tana rawar jiki ta ce:“Ranka ya daɗe, wannan ba mafarki bane wannan shi ne yaron da aka haifa cikin haske Idan ya girma, zai gaji wani ɓangare na ikon da aka mallaka maka, amma ya fika tsarkaka” Sultan ya juyo da mamaki“Wato kana nufin wannan jariri da aka haifa shi ne na gani?”“Eh” in ji Rifaa da rawar murya “Madubin ba ya nuna haske sai idan akwai wanda Allah Ya zaba don ya gyara abin da duhu ya lalata.”Sultan ya juya ya kalli madubin, numfashinsa ya yi nauyi Sai kuma hasken ya dushe, amma kafin ya ɓace gaba ɗaya, sai ya ga hoto na Ameer ɗan uwansa da ya ɓace shekaru da dama.Idonsa ya faɗa, ya furta cikin tsoro:“Ameer….. ka dawo ne?”Madubin ya fashe da ƙara, haske ya watse har cikin ɗakin.Wani ƙamshi ya buso kamar turaren ƙabari. Rifaa ya faɗi ƙasa, yana riƙe kirji yana cewa:“Ya Sultan… alamar komawar duhu kenan. Ka tuba domin wannan lokaci ya zo” Sultan ya dafa bango, yana jin jiri.Ya furta da ƙaramin murya“To idan wannan yaro ne mai haske, ni fa, wane ne ni?” A gefe guda kuwa, Samha ta taso daga bacci tana jin kamar ana kiran sunanta daga wani nisa.Rayyan yana cikin kwanciyar sa, amma hannunsa ya riƙe yatsunta ƙarfi kamar wanda yake tsoro Ta ɗaga kai ta ga haske ya cika ɗakin ba na rana ba kuma ba na fitila baSai kawai ta ji muryar wata tsohuwa tana cewa “Ke Samha, ki kare wannan yaro da addu’a, domin hasken da yake jikinsa yana jan zuciyar duhu. Ki nemi Allah kaɗai, domin madubin da aka buɗe a daren yau ya haɗa sararin haske da duhu.”Kafin ta yi magana, hasken ya ɓace.Sai kawai Rayyan ya farka ya fara kuka, amma kukansa yana da irin sautin da babu yaro da zai iya yi kamar ana karanta Ayatul Kursiyyu cikin muryar jariri.Samha ta firgita, ta rungume shi cikin firgici ita wannan lamari ya fara damunta matuƙa meyesa yaronta ya zama daban da sauran yara? “Subhanallah! Ya Allah ka tsare min wannan jariri” A cikin duhu kuma Ameer yana cikin wuri mai kunshe da ƙanshin ƙasa.Ya buɗe idanunsa yana kallon madubi da ya ƙone a gefensa, ya murmusa “Na ganka, ɗan uwana. Kuma na ganshi wannan yaron da ke haskaka zuciyarka. Amma ka manta, haske yana buƙatar inuwa domin ya yi tasiri.”Ya sa hannunsa cikin ƙura ya ɗebo wani farin lu’ulu’u.“Lokaci ya yi Duhu zai dawo cikin gidan haske. Kuma madubin da ya buɗe ba zai sake rufewa ba” Ya busa ƙurar cikin iska iska ta canza launi zuwa baƙar ruwan toka…….Watanni biyar kacal kenan da haihuwar Rayyan, saidai babu wanda ya taɓa ganin jariri irin sa Yana dariya da safe, amma idan dare ya sauka sai haske ya cika ɗakin Samha kamar ranaKo bata kunna fitila ba fitilar tana haskaka kanta idan ya fara motsawa. Samha ta fara tsoron kanta, amma duk lokacin da ta riƙe shi, sai zuciyarta ta nutsu kamar ruwa bayan iska.A kullum tana karanta masa Suratul Ikhlas da Ayatul Kursiyyu.Wata rana, Granny ta shigo ɗakin ta tsaya cak tana kallon hasken da ke fita daga jaririn.“Samha…” ta ce cikin muryar mamaki, “wannan hasken yana fitowa daga cikinsa ne ko daga sama?”Samha ta kalli jaririn cikin tausayawa, hawaye na sauka daga idonta.“Na kasa bambanta Granny. Amma duk lokacin da yake kuka, idan na karanta bismillah sai na ga fuskarsa ta canza ta zama kamar mai dariya.”Granny ta zauna a gefenta cikin tausasawa, ta dafa hannunta.“Rayyan bai zo duniya kamar sauran yara ba, kina ganin haka?”“Na gani Granny” ta amsa “amma tsorona shi ne duniya zata iya jure shi?”Granny ta yi shiru na ɗan lokaci, ta ɗago kai tace “Abin da Allah Ya halitta da hikima ba zai lalace ba. Ki tsaya da addu’a domin duhu yana fara motsi” A gefe guda, Sheikh Zayyad wanda Rashid ya gayyata ya iso gidan domin ganin jaririn.Yana kallon Rayyan, sai ya yi murmushi ya furta“Subhanallah… wannan yaro yana ɗauke da ayoyin ikon Allah. Saidai akwai wani abu a jikinsa kamar an yi ƙoƙarin rufe shi da duhu, amma hasken bai yarda ba”Rashid ya ƙara matsowa cikin damuwa:“To Sheikh, me zamu yi?”“Ku ci gaba da karatu, ku tsarkake gidan da Yasin da Falaq da Nas Amma ku sani wannan yaron ba a yi masa tsafi ba, an haife shi da amanar haske”Yana kai wannan magana sai iska ta buso cikin ɗakin, fitila ta yi walƙiya ta kashe kanta Rayyan ya fara dariya, sai ƙamshin furanni ya mamaye ɗakinSheikh Zayyad ya kalli Samha da Rashid cikin murmushi “Wannan dariyar ba ta jariri bace kawai wannan dariyar alama ce ta tsarki”

