Hausa novels

Harijin Sarki Page 34 Romantic Hausa Novel

A ɗaki Samha tana duba jaririnta wanda yake bacci kamar yana murmushi da karatun da Granny ke yi.Ta sa hannu ta shafi kansa cikin sanyin murya tace “Rayyan, kai ne amsar addu’ar da nake roƙon Allah da hawaye tsawon shekaru. Amma har yanzu zuciyata tana tsoron abin da zai taso”Kafin ta gama, sai iska mai sanyi ta busa tagar ɗakin. Fitilar turare ta kunna kanta da kantaCikin wannan haske ta ga kamar Rashid yana zaune a gefen jariri, amma lokacin da ta kalli Rashid na gaske yana tsaye a bayantaZuciyarta ta buga, ta karanta A’uzu billahi mina shaidanir rajim, amma surar ta tsaya cak lokacin da wannan Rashid ɗin ya miƙa hannu ya ce “Ku kiyaye da Ameer Zai dawo cikin siffar wanda kuke amincewa da shi. Amma yaron nan ba zai mutu ba saboda hasken da ke jikinsa ya fi na sarauta ƙarfi”Hasken ya ɓaceSamha ta durƙusa tana kuka, tana faɗin“ Ina son Rayyan da mahaifinsa Ya Allah ka kiyayesu Rayyan daga sharrin sirri, da tsafi, da munafunci”Rashid ya rungumeta yana ƙoƙarin kwantar mata da hankali daidai lokacin shigo yace“Abin da kika gani wahayi ne ko mafarki, amma duk da haka ba za mu sake saki ba. Zan kira Sheikh Zayyad mu fara karatun ruhi a cikin fadar.” da sauri ta janye tana girgiza masa kai tace “Sultan duk wata kariya tana cikin Kur’ani ka iya karantashi kaje kayi wanka irin na janaba ka ɗauka ka karanta Suratul Baƙara kana me yaƙinin Allah daya saukar da wannan sura yana saman kanka yana sauraronka lallai shi me amsa kiran bayinsa ne” hakan kuwa akayi da sassarfa Sultan ya fara aiwatar da dukkan abinda Samha ta sanar dashi.A can nesa, a cikin duhu Ameer yana cikin wani wuri kamar rami, yana kallo ta cikin wani irin madubi da yake iya nuna masa halin da suke ciki.Ya taɓa fuskar madubin da hannunsa da ke ƙonewa ya ce:“Rayyan… haka sunansa kenan. To ni kuma zan haifi duhu mai sunan Zahim, wanda zai zame masa ƙiyayya. Duniya zata sake zama filin ruhi da jini” Yayi dariya wadda ta haifar da ƙarar da ta sa duhu ya motsa tamkar iska mai kaifi.A wancan lokaci Samha ta ɗaga jaririnta, ta lumshe ido tana furta“Rayyan, sunanka ba zai mutu ba. Kuma daga yau haske ne zai rubuta ƙaddararka”A sararin samaniya a karo na farko tun bayan shuɗewar shekaru da dama, wata ya bayyana da cikakkiyar haske yana nuna cewa wani sabon zamani ya fara…….

_Masu cewa sun kasa gane labarin nan kuyi tsai ku karanceshi zaku fahimta, kuka kasa ganewa Hausar ce ta ɗan jirkita saboda jirkicewar zamani a cikin labarin HARIJIN SARKI.👌🏽_

Back to top button