Haihuwa Da Hanji Page 37 Hausa Novel
Bayan ta tashi daga baccin da ya dauƙeta tun bayan Sallar asuba wanka tayi ta shirya cikin wata doguwar riga mai hannun roba purple da ya amsheta ta ɗaura dankwalin a kanta sai ta nufi sashen mammi don gaisheta, da sallama ta sanya kanta ciki ta ga mammin kwance a kan sallayar da tayi sallah ta ɗora kanta saman pillow tasbihi take a hankali tana ta maimaita “Allahumma inni As’aluka husnal khatima, Allahummar ruzuƙnee taubatan nasuha qablal maut, Allahumma ya musalibbal quluub thabbit qalby ala dinika, ya musarrafar quluub sarraf quluubina ala ɗa’atik..!”Abin da ta lura kusan kullum a kwanakin ya zama tasbihin Mammi kenan, a ganganta ta zauna “Mammi…kina lafiya?”Tayi tambayar hankalinta na kan mammin gabaɗaya ganin yanayinta kaman marar lafiya lumshe idanu mammin tayi ta buɗe kan ta ce a hankali “Afeefah je ki buɗe bedside za ki ga wani kwali ki ɗauko”Miƙewa tayi taje ta buɗe ta ɗauko ta dawo tana zama riƙe dashi “Mammi gashinan!”Mammin bata motsa daga kwancen ba don bata jin zata iya tashi tace a hankali “Afeefah ki buɗe ki gani menene ciki?”Buɗewa tayi sai ta ga set ne na dankunne sarka da abin hannu da kuma zobe, daga gani ka san ba ƙarami bane don ma bata san gold ba da sai ta ce wannan ɗin gold ne babba ma don yadda yayi wani irin kyau ga ɗaukar ido.”Set na sarka ne Mammi””Masha Allah, sadakinki kenan da na yi amfani dashi na saya miki wannan kadarar, ki riƙe a wurin ki naki ne halak malak ban baki tsabar kudin bane don na san ba zai ajiyu ba amma wannan ko shekara nawa zai yi a zaune babu abin da zai yi sai ma darajar shi ya ninku”Rasa bakin godiya Afeefah tayi sai hawaye ya shiga ziraro mata “Mammi kin yi min komai a wannan duniyar ba ni da abin da zan saka miki face Adu’ar Allah ubangiji ya baki lafiya, Allah ya yaye miki wannan ciwo ya kawo mana karshensa mu ga kema kin warke kaman kowa, Allah ya sa kaffara kika yi””Ai lafiyar ta zo ma Afeefah”Ta faɗa tana rufe idanu jin yadda take jin ciwo mai tsanani a ciki da ma jikinta gabaɗaya.”Mammi…!”Sai ta ga wani irin zufa na karyo mata numfashinta na fita da kyar da kyar har chasbin hannunta na zamewa da kanshi, wani irin tashin hankali ne ya ziyarce ta da gudu ta miƙe ta fito sai tayi side ɗinsu kaman za ta kifa haka ta tura kofan ta same shi tsaye gaban madubi, ba zata ce ga yadda ta riske shi ba ita dai ta san ta isa gabanshi tare da riƙe hannunshi”Mammi…! Mammi..””Me ya sameta?”Ya faɗa hankalinshi na tashi lokaci ɗaya, ganin duk ta ruɗe yace “Je ina zuwa”Fita tayi da sauri shi kuwa ya ɗauki boxers kawai ya saka da jallabiya tare da zaran keyn mota kafafunshi ma silifas ce ta wanka ya fice da hanzari, yanayin da ya sameta sai da ya ƙara ɗaga masa hankali haka ya ɗauketa Afeefah na ta kuka suka nufi Asibiti duk ma’aikatan hankalinsu ya tashi da sauri aka karɓeta sai oxygen aka sanya mata sun yi iya kokarinsu har numfashinta ya ɗan daidaitu, Rayyan dai ya kasa aikata komai don ba karamin girgiza yayi ba duk tashin ciwonta bai taɓa ganin kaman wannan ba, bai zaci za su iso asibitin da ranta ba jikinshi rawa kawai yake yana tsaye daga gefe yana kallonsu a sadda zuciyarshi ke cigaba da bugawa kaman zai fashe, idanunshi sun rine sai adu’a yake yana roƙon Allah akan ya bata sauƙi a ranshi.Ganin ta dawo daidai oxygen ɗin na tafiya a hankali ba kaman daga farko ba da in ta ja kaman ba zata sauƙe ba ya isa gangarta ya riƙe hannunta kawai ya zauna, a jikin gadon ya ɗaura kanshi yana danne abinda yake ji na taso mishi, ina ma da zai iya kuka da yayi ko don samun sassaucin abinda yake ji a ranshi da ma kwakwalwanshi!Ba zai ce ga adadin lokutan da ya ɗauka zaune a wurin cikin wannan yanayi ba chan dai ya ji kaman ana shafa suman kanshi da ɗan hanzari ya ɗago sai suka haɗa idanu tana ta kallonshi, gyara zama yayi yana kirkiro murmushi mai nauyi ya ce “Mammi na! Kin farka? Ya jikin?”Ta sake yin murmushi a hankali ta nuna mishi oxygen na hancinta sai ya cire yana jin yadda take sauke numfashi a kai akai “Mammi ki yi saving energy ɗinki kar ki yi magana kin ji?”Ta sake yin murmushi “Ina so na ji abin da ke bakin ka! Ka ba ni labari…tun jiya na lura kana son min magana amma kana riƙe wa menene?”Shiru ya ɗan yi “Speak up Saraki, yanzu ne kake da lokacin magana da ni anjima kaɗan kila sai dai matarka ko ‘yan uwanka”Da sauri ya ɗan kalleta tana ta murmushi, kanshi ya duƙar a hankali ya fara furta “Mammi ki daina irin wannan maganan don Allah””Toh na daina Saraki!”Ta faɗa tana lumshe ido, hannunshi dake cikin nata ne ya ƙara yin sanyi she can feel the nervousness a cikin tafin hannunshi zata iya cewa yana cikin yanayi ne marar fasaltuwa sai dai da yake namiji ne kuma jarumi yana iya shanye damuwarshi kaman babu komai.Idan Mammi ta tafi ba tare da ya sanar da ita menene a ƙasan Ranshi ba tabbas zai yi nadama mai girma, tunaninsa ya dinga rarrabuwa har yana jin kaman zai zauce idan ya cigaba da zurfafa a cikin muguwar tafiyar rayuwarshi…iya tunanin kaɗai kan karya duk wani guntun karsashinsa.*****A hankali yake buɗe idanunshi har ya ware su akan Mommy da su Sadiqa dake zaune a ɗakin jugum jugum.”Saleem! Ka farka? Sannu ko mu je asibiti ne?”Girgiza kai yayi yana Miƙewa zaune jikin gadon ya kalli mommy da ita ma take kallonshi a hankali yace “Mommy na tuba! Mommy ki yafe min wallahi….””Shhhh Saleem na sani, na san ba da saninka ka aikata hakan ba na san baka cikin hankalinka a lokacin da komai ke faruwa, laifina ne wlh laifina ne ka yafe min Saleem son zuciya ɓacinta, hakika na yi amfani da son zuciyata wurin ɗaiɗaita maka rayuwa don Allah ka gafarceni”Ta roka yafiyarshi tana kuka su ma duk su sadika suka shiga bashi hakuri, anan ya zauna yana jin yadda komai ya kasance… Hakika mommy ta yi kuskure Afeefah ce ta faɗo mishi a rai ko tana cikin wani hali yanzu? Ko ya rayuwa yayi da ita? Allah masani ******”Mammi..!”Ya sake ƙira a karo na biyu ba tare da ta buɗe ido ba tace “Uhmm””Zan faɗa miki ne, zan faɗa miki wanene ni…”Da sauri ta buɗe ido ta kalleshi cikin yanayin jin jiki ta zura mishi idanun a hankali ya cigaba da cewa “Ban manta komai ba, na ƙi faɗa ne saboda wacce daraja da ƙimarta suka zama ƙololuwa a gare ni ta yi fatali da hakan ta ɗauke ni ta yasar tamkar tsumma a cikin al’ummar da ba ni da masaniyar yaya suke bare ya rayuwarsu take, ya al’adarsu take ko ya imaninsu yake, ba tare da ta damu da zan ci ko bazan ci ba, shin rayuwata za ta inganta ko za ta yi lalacewa marar iyaka? kafin na haɗu da ke na zaci uwa masifa ce ga ‘ya’yanta ta kan nesanta su da farin ciki ta saya musu wahala, ta kan zama tamkar ginin ƙasa da muddin ɗa ya jingina da ita sai ya faɗi, a maimakon ta kasance garkuwata sai ta zama ita ce a farkon cutar da rayuwata, na kasance a koyaushe bana rufe idanu na buɗe ba tare da na ga sadda take cire hannayenta daga cikin nawa ba tare da tura ni cikin dattin juji…ta tafi! Ta tafi da rayuwata da dukkan farin cikin da ya taɓa wanzuwa cikinsa ta tafi da rai da ruhi na…”Shiru yayi yana cije lip ɗin shi na ƙasa da har su ma rawa suke yi.”Ke ce kika ba ni hope na rayuwa, a kan ki na yarda uwayen ma suna suka tara Mammi kin zame min gata a sadda na kasance cikin wahala, kin ba ni duk wani kulawa da gata ba tare da tsammanin lada ba kin bani kaunar da bata taɓa yankewa ba, kin zame min rayuwa, rahama da kyautatawa da bata da iyaka. Mammi Sunana Sameer…”Lumshe ido tayi a hankali hawaye na sauka mata ya sa hannu ya share mata.A hankali ya cigaba da bata labarin da kafin ya gama jijiyoyin kanshi sun yi raɗa-raɗa, idanunshi tamkar garwashi muryarshi har yankewa yake amma Dukda haka jarumtarshi ta ƙi barin ruwan hawaye ko guda ya diga bisa fuskar shi ko zai samu salama cikin rai da ruhinshi, ba zata iya Miƙewa ba da zata iya da ta rungumeshi ta rarrasheshi da ta nuna mishi komai na duniya mai wucewa ne, da ta tuna mishi da irin girma da darajar da Allah ya ba uwa don kalamanshi sun yi tsauri sossai a kanta, bata san dalilin ta na yin hakan ba amma ta san babu uwar da zata so tagayyarar ɗan ta, ɗan ma mai tarin gata, daraja da martaba irin Rayyan.”Ka zama mai haƙuri da rayuwa! Ka zama mai afuwa Saraki haƙiƙa an cuce ka an kuma ɗauki alhakinka mai yawan gaske amma ina roƙon ka da ka bari komai ya wuce kaman ba’a yi ba, ka yi uzuri ga mahaifiyarka ka waiwayi gida…”Shiru tayi sai ta ɗan yunkura kaman zata tashi ta koma ta kwanta tana shaƙuwa.”Ka min alƙawari Rayyan!”Girgiza kai yayi yana ɗago rinannun idanunshi gareta sai ya ji tana ambaton Allah da salati ɗauke a Bakinta a kan idanunshi, hannunta na a cikin nashi Mammi ta ja numfashinta na ƙarshe da ya tafi da duk wani ƙwarin gwiwanshi, ya tafi da duk wani haske da yake tunanin da shi yake amfani wurin haskaka tarin duhun dake mamaye da shi, gigice wa ya nemi yi sai ya manta da cewa shi ɗin ma likita ne, ya kasa yanke hukuncin cewa ta tafi ya kasa yardar wa kanshi cewa da gaske ta tafi ta bar shi… “Innalillahi wainna ilaihi rajiun…”Shine kalaman da ya fito da kyar ya ratsa harshenshi har ya fita sarari.Ya fi mintuna ashirin a zaune a haka baya iya ko da kifta idanun kirki, kila mafarki yake, kila bacci tayi za ta buɗe idanu kila zai iya ganin kirjinta ya motsa ya cigaba da bugawa kila za ta ja numfashi ta ce mishi wasa take… Shigowar wani likitan ne ya tabbatar mishi da cewa da gaske ya rasa Mammi rasawa ta har abada haƙiƙa ɗaci da raɗaɗin mutuwa ba za su faɗu ba ba kuma za su misaltu ba.A chan reception kuwa Su jannah da Afeefah ne zaune cikin damuwa mai yawa don tunda suka shigo Afeefah bata daina zubar da kwallah ba, ta san mutuwa kuma ta ga mutuwa daban daban bata fata ya kasance a kan Mammi nan kusa Dukda ta san da cewa mutuwar dole ce ga dukkan mai rai, su uncle Musa da iyalan shi da Abeeha ta ƙira ta sanar musu jikin Mammi babu daaɗi duk suna cikin asibitin a lokacin da wannan likita ya fito ya sanar musu da rasuwar gigice wa suka yi suka fice daga hayyacinsu, Jannah ce ta yanke jiki ta faɗi sai jini ya fara fita mata Abeeha kam rasa ma ya zata yi tayi sai da uncle Sanusi ya riƙo ta yana ta maimaita salati ta kankanmeshi ta fara kuka mai tsuma zuciya shikenan sun zama marayu babu uwa babu uba, Mammi ta tafi lallai dukkan mai rai mamaci ne.Afeefah kam ba zata ce ga yanayin da take ciki ba, Dukda ta kaɗu iya kaɗuwa sai dai ko motsi ta kasa yi daga inda take hawayen idanunta ma kafewa suka yi, wata cousin ɗin su Abeehar ce ta riƙe mata hannu sai ta firgita tana kallonta idanunta duk a waje…”Wai cewa suke Mammi ta rasu? Ko kunnuwana ne basu ji da kyau ba?””Sai haƙuri Afeefah, sai haƙuri…”Wasu irin hawaye ne suka shiga zubo mata masu zafi da raɗaɗi, da kyar take iya maimaita innalillahi wainna ilaihi rajiun….A lokacin Rayyan ya fito hannunshi na tura gadon da mammin take kai a hankali yana tafiya ne ba tare da ya san inda yake jefa kafafunshi ba, Uncle Sanusi ne da matarshi suka taho da sauri suka saka mishi hannu don kaman zai kifa, idanunshi sun zama wani iri jikinshi na rawa zuciyarshi a bushe haka suka fice yana gaban motar da Mammi ke ciki wacce amblance ce aka dauko ta a baya har cikin gida, a ɗakinta aka sanyata babu wani jinkiri Matar uncle Musa dattijuwar malama da taimakon wasu malamai mata aka yi mata wanka aka yi mata sutura, kan kace mene gidan ya dinke da mutane masu kuka na yi masu yabon kyaun halinta na yi, Jannah dai tana asibiti don ɓari tayi ba tare da ta sani ba. Abeeha da Afeefah banda kuka da du’a babu abinda suke yayinda Rayyan na a parlorn shi a zaune wane mutum-mutumi tasbihi yake yi amma ba zai iya cewa ga abin da yake cewa a ciki ba, Saleem ne ya shigo Dukda ba ƙarfin jiki ya samu ba sai dai labarin mutuwar ya dugunzuma hankalinshi.”Rayyan!”Ya kira sunan. Jajayen idanunshi ya buɗe ya zura mishi ba tare da yayi magana ba “Sannu! Allah ya gafartawa Mammi Allah ya haskaka makwancinta ya sadata da annabin rahama”Da kyar ya iya furta “Ameen”Idanunshi na kan hawayen da Saleem ɗin ke yi ina ma zai iya? Ina ma ya san ta yadda zai nemo hawayen? Ina ma zai iya cire zuciyarshi ya yasar? Da yayi hakan ko zai huta raɗaɗin da ke gasata wane wuta.”An gama shirya ta ayi alwala a fita gabatar da sallah don samu a kaita makwancinta!”Wannan kalma ta Uncle Mansur ya zama kaman zuban wuta a jikinshi, shikenan fa yanzu ko? Shikenan zai rabu da Mammi rabuwa ta har abada? Saleem ne ya ja hannunshi har zuwa bayi yayi alwala suka fito a tare zuwa ɗakin Mammi aka ɗago makarar aka nufi fita da ita haraba inda kuka ke tashi, kowa idanunshi na kan Rayyan ne da yake ta focusing akan hanyar da yake takawa kar ya faɗi riƙe da gawar Mammi da yayi mata sallama na ƙarshe da qulhuwallahu ahad! A tare da shi aka yi mata Sallah aka kaita makwancinta na gaskiya, shine ya ba da ghdumuwa wurin sakata a rami kuma shi ne ya fara zuba mata ƙasa kan yayi baya baya zai faɗi aka tare shi su Uncle Mansur ne da Saleem, ɗagowa yayi yana kallonsu kila su basa jin abinda yake ji tunda gashi suna hawaye! Har aka gama binne Mammi aka kamo Rayyan zuwa mota baya gane fari ko baƙi don duk wanda zai ji mutuwar Mammi a bayan Rayyan ne…. Innalillahi wainna ilaihi rajiun 😭 Allah ka sa mu yi kyakyawar karshe!


