Zakuna Biyar Page 5 By Princess Teema
Abin da ya sumar da ita kuma shi ne hayakin wutar da su Eagle suka kunna a gidansu. Mu ɗan koma baya kaɗan dan mu ji ya aka yi ta tsira?.A lokacin da Dr ta fita ɗakin da gudu ta nufi room na ƴarta a lokacin shi ma ya miƙe daga gadon, in baku manta ba ai bata yi mashi alluran barci ba, so idanunsa biyu, yana jin dik abin dake faruwa. Fitowa daga room ɗin ya yi ta hanyar dafa bango, dan jikinsa dik babu karfi ko kaɗan, da kyar ma yake iya motsawa, amma saboda yasan musifar da yake a ciki sai ya yi tinanin dik yadda aka yi shi ake nema yasa aka shigo gidan again.Cigaba da tafiya ya yi har zuwa wajen staircase, zai taka stair ɗin kenan su Eagle suka banko parlo door. Ganinsu yasa ya fasa sauƙa, dan jikinsa babu wani karfin da zai iya kwatar kansa, sai ya matsa baya, a maimakon ya koma room ɗin can sai ya kara gaba, a nan ya ci karo da room na ƴarta, buɗe door ɗin ya yi ya shiga ciki. Yana sanya kai daidai lokacin yarinyar ta farka, ta zauna a saman bed tana faɗin. “Mammy I want to dring water”. Laluɓar hanya a cikin duhu ya yi izuwa wajen switch, sai da ya kusa kewaye room ɗin kafin ya gano switch ɗin. Kunna light ɗin ya yi, take haske ya gauraye room ɗin.Da sauri Seraph ta ɗago kanta ganin haske tana faɗin. “Mammy a little water……”. Bata iya karisa maganar ba ganin mutum a tsaye ga bandeji a hannu, bugu da kari bata iya ganin face ɗinsa. Wani irin razana ta yi tare da zazzaro voilet eyes ɗinta a kansa. Wani irin kallo ya bita da shi, wanda ita bata san yana kallon nata ba saboda nose mask ɗinsa, ga p-cap daga cikin hular jacket ɗinsa. Cigaba da zazzare ido a kansa ta yi, tana kallonsa from up to down. A daidai lokacin ya ji motsin mutanen, a tinaninsa suna shigowa room ɗin ne, sai dai kuma a lokacin suka wuce da Dr zuwa ICU ɗinta. Jin motsinsu yasa ya daure tare da takowa izuwa wajen bed ɗin nata. Hannunsa ɗaya mara ciwon nan ya sanya tare da ɗaukar yarinyar, tana ƙoƙarin kurma ihu ya yi amfani da hannunsa mai ciwon ya rufe mata bakda tafukansa. Wajen view ɗinta ya dawo, da kyar ya iya buɗewa, tana ƙoƙarin kwace kanta ya dake suka fita ta view ɗin, a saman wani ɗan dakali a wajen ya zauna da ita a jikinsa. Ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi da iya karfinta, ganin zata iya ja su faɗi kasa tin da wajen ba wani mai faɗi bane, irin dakalin nan ne da ake yi na saman window ɗin toilet ko na ɗaki hakan nan ne, to a wajen window toilet suka zauna, ganin zata ja su faɗi ne yasa ya sanya hannunsa ya zame hular jacket ɗin kansa, ya ɗan kawar da p-cap na kansa gefe dan ta samu damar ganin idonsa, sai ya zame hannunsa daga bakinta ya ɗago haɓart suna fuskantar juna. Wani irin zaro ido waje tai tamkar kwayarta zasu faɗo ƙasa a lokacin da ta ga jajayen idanunsa tamkar wuta, dik da bata kalli face ɗinsa gabaɗaya ba ta wani irin mahaukacin razana, take ta kame waje guda kamar ta sume, dan numfashinta ya ɗauke, idanunsa sun yi wani irin ja tamkar jini ne a ciki, dik wanda ALLAH ya bashi ikon haɗa ido da wannan guy a wannan lokaci ko bai suma ba kaɗan ne zata rage mashi saboda firgici.Ganin ta ɗauke wuta ne yasa ya mayar da hulansa, slowly ya kwantar da kanta a gefen chest ɗinsa, ya ɗan rintse idanunsa saboda tsananin zafin da hannunsa yake yi mashi, alluran kashe zafin ta fara sauƙa, kun san dole akwai zafi. Yana jin motsin yaran Eagle suka shigo room na yarinyar. In takaice maku labari har suka kashe Dr yana wajen da yarinyar, ba zai iya zuwa ya ceci Dr ba, saboda shi kansa taimako yake nema a yanzu. Jin shiru alamar sun bar ɗakin yarinyar yasa ya kokarta ya miƙe da ita, daga alama shahararren ɗan ta’adda ne, yadda yake da dauriya da karfi kamar wani doki, dik yadda aka yi ya sha gwagwarmaya ba kaɗan ba. Da kyar ya lallaɓa ya kama room view suka komo cikin ɗakin, ya so dira ƙasa ya bar gidan, amma ha zai iya dira da ita ba, kunga ga ciwo a hannu, ga kuma nauyinta, jikinsa ba karfi, idan suka dira a tare zata iya jin ciwo koma ta bugu a in da ba zata rayu ba, shi ma kuma haka. So dole ya mayar da ita cikin ɗakin, bata ko motsi. Cikin toile ya kaita, a cikin jaccuzi ya kwantar da ita tare da fitowa, dispenser dake room ɗin nata ya ja zuwa toilet ɗin, da kyar ya ɗaukesa ya ɗaura a saman Jacuzzin, ya rufeta, sannan ya fito, ya koma ta view, ya dinga lallaɓawa a hankali ya sauƙo, a lokacin sun kunnawa gidan wuta sun fita. Shi ma fita ya yi.Yasan da wuya wutar ta kamata, dan a cikin Jaccuzi ya kwantar da ita, ga disperser ɗin da ya ɗaura mata, shiyasa washegari ya tura yaransa su ɗaukota da dik sauran abin da ya rayu a gidan dan ya rama alkhairin mahaifiyarta a garesa, ta sadaukar da ranta a cetansa, yana kwance a gadon asibiti ya turosu.Shi ne suka zo suka ɗauketa, sun sameta sume a cikin Jacuzzin, amma hayakin wutar tai mata illah, ga kuma wutar ta kakkama dik wasu robobi a cikin toilet ɗin ta cinye, ko jami’an da suka zo basu san tana ciki ba saboda wannan rufeta da ya yi…… To kun ji abin da ya faru! Yanzu mu koma kan labarinmu!. Ta jima zaune a wajen tana shan kukanta, tana ganinsa ya sauko ƙasa, ya wuce kitchen ya sauke ruwan da ya ɗaura a pot, ya sanya rariyar tea ya tace ruwan a cup, sannan ya ɗauka ya koma sama ba tare da ya kalli in da take ba. Ganin ba zai kulata bane yasa ta miƙe ta koma cikin room ɗinta cike da kunci, tana son sanin ina mammy ɗinta, meyasa aka kawota wannan irin dream house da take mafarki kullum! Suna da arziki sosai, amma CRYSTAL PALACE ba dik kai ba, sai ta zama ƴar kauye a nan.Saman bed ɗinta ta koma ta kwanta tana cigaba da kukanta babu mai rarrashinta, ga shi bauɗaɗɗen nata ya yi sama abinsa, yana zaune a balcony yana shan tea ɗin da ya dafa cikin kwanciyar hankali da natsuwa abinsa. Bayan ya kammala ya umarci robot dake aiki a gidan da su haɗawa yarinyar abinci, su tabbatar ta ci, sannan su bata magani kamar yadda yake a tsare, kuma su yi mata wanka, yana gama basu bayani ya ɗauki wani tail coat ya sanya a jikinsa bayan ya yi wanka ya cire waɗan can, ya fita ya bar gidan, ita kaɗai a dik wannan girman gidan kamar wata mayya, ba uwa, ba uba, ba kawa, ba aboki, babu kowa sai robot, wannan ma kawai ai tashin hankali, ga shi baƙon waje.Haka robot ɗin nan suka hau aikinsu, tamkar mutane, suka shirya komai suka kai mata, maza ne su biyu. Tana kuka suka iskota. A saman table suka ajiye kayan abinci, ɗaya ya taka zuwa in da take, da hannu ɗaya ya ɗagota, bai direta a ko’ina ba sai a saman sofar dake kusa table ɗin. Tana ta faman faɗin. “I don’t want, please let me go”….. Ina babu wanda ya kulata, dan su ance su tabbatar sun bata abinci, dan haka a baki suka fara tura mata dole, abin da umarni suke karɓa, in kuma suka karɓa sai sun cika ko mutuwa ake yi.Da taga babu sarki sai ALLAH sai ta hakura ta dinga karɓar abinci a natse kawai, ba sai an mata ɗure ba. Sosai ta ci kafin ta ce ta ƙoshi. Sai da suka tabbatar, sannan suka ɗauko magungunar, shi ma a baki suka bata ta sha, sannan ɗaya ya ɗauketa zuwa toilet, dan har da wanka aka ce su yi mata, tana cewa bata so, amma ina, ko a jikinsu, suka haɗa ruwan wanka. Dik tinaninta mutane ne shiyasa take ce masu bata so.Tana ji tana gani yai mata zindir, ya jefata cikin ruwan katafaren glass Jacuzzi tamkar wata kayan wanki. Hannu yasa ya wanketa tas. Ai yau taga ikon ALLAH, kuka ta dinga yi tana kiran sunan Mammy ɗinta, amma ina bata jinta.Dawo da ita ɗakin suka yi bayan sun nannaɗeta cikin towel, a kan gado suka jefata kafin su kwashi kayan abinci su fice, sun gama aikinsu kenan. Fashewa da sabon kuka ta yi, ta kifa kanta da gwiwowinta tare da jawo bargo ta rufe tsiraicinta. Kyakkyawan ash hair ɗinta sai ɗigar ruwa yake yi.Tin sautin kukanta na fita, har ya daina fita, daga karshe barci mai nauyi ne ya ɗauketa a wajen, bata san lokacin da ta kwanta kudundune a cikin bargon ba, ta hau barci, ta ci kuka ta ƙoshi ja’ira. To kun ji halin da Seraph ƴar Dr take a ciki, mu haɗa kayanmu mu koma Barrack. Note, Seraph shekarunta 10 a duniya yanzu, yarinya ce sosai. ————————-🔥GIDA SOJA!. AFTER ONE MONTH.A wannan wara ɗayan dik horon da aka yi masu a farko-farko ne ake ta maimaita masu dan ya bi jikinsu da kyau, ba’a ɗaura sabon horo ba, tin suna iya mantawa har wannan horo na farko ya ratsa jikinsu sosai. Shiyasa na tsallake tin da ba zan yi ta rubuta maimaicin horo ba!.A yau Monday watansu guda kenan a GIDAN SOJA, a yau zasu fara shiga horo sabo kashi na biyu.Kamar kullum karfe 5:30 na asuba, bayan sun yi sallar asuba, dik sun hallara a wannan fili, a yau dai Noor ya fito, dan za su shiga sabon horo, a wata guda da suka wucen nan dik kullum sai Captain ya tashesa da duka, amma yau da yake za’a shiga sabon babi ya daure ya taso.Sun kasance a cikin layi kamar kullum. Cikin zafin nama Captain ya tako, ya iskosu a wajen. Saman stage ya haye tare da ɗan yin gyaran murya. Da sauri suka haɗe natsuwatsu tare da buga kafa, suka sara mashi. Jinnina kai ya yi kafin ya ce. “1, 2, 3 start!” Cikin ɗaga murya.Yana cewa start suka buɗi baki game da ɗaga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA…… “We march through fire, through storm and rain, with steel in heart, we bear the pain, for land and honor, we stand so tall, united as one, well never fall. Oh we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle’s won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground, a thunderous beat, a mighty sound. No chains can break the will we hold, Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom’s call, for justice true, our oath is strong, we’ll see it through. Oh we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle’s won, with fearless hearts, our banners wave, we are the strong, we are the brave!”.Suna kai karshe ya ce. “Kamar yadda kuka sani ne, a yau zamu sabonta maku horo, zamu matsar dashi izuwa matakin gaba, ina fatan kun shirya?”. Ya kai karshe da alamar tambaya. Wani irin kamewa suka yi alamar sun shirya ba tare da magana ba. Rarraba idanunsa a kansu ya ɗan yi kafin ya ce. “A yau zaku fara ne da endurance run for 10km”. Babbar magana, gudu fa ba tafiya ba, na 10Km da matsala. Dayawa daga cikinsu sun ɗan ɗauke wuta, amma ganin babu fuskan wasa yasa suka daure. Maryan Captain ne ya katsesu da cewa. “Lokacinku ya fara daga yanzu, kada ku manta lokacinku yana kirgawa ne! So attention”. Wani irin tsaki Noor ya ja tare da rike kai, har ga ALLAH ya gaji, ba zai iya jura ba fa. Ganin matasan sun fara gudu sun bar shi a wajen ne yasa yai gaggawar bin bayansu da ɗan gudunsa, kada a barsa a baya.Gudu na tsawon kilomita goma ba tare da tsayawa ba. Dik wanda ya yi baya, sai ya sake farawa daga farko. Babbar magana, kuma kun san dik wanda ya yi baya sai ya faro ɗin nan ne, babu tausayi. Haba haka suka zage dantse suka fara gudu babu wasa. Sai dai bayan kamar minti 30, gwiwowinsu sun fara raunata, amma ba wanda ke da damar tsayawa, dan ma wai a wata ɗayan can sun ta maimaita horo sun ɗan samu karfi da kwari ne, da sai yaya kenan?.Noor da ya tabbatar da gaske idan ya yi baya zai sake komawa daga farko, kuma ko mutuwa yake yi ba zasu yafe mashi ba, kilomita goma ba biyu kamar ta baya ba, yaushe zai koma baya ya sake dawowa, ai sai ya zage, yasa dikkan karfinsa wajen gudu. Da yaga kamar ba zai iya bama sai ya kwarara zuciyansa tare da yin shahada ya kama hannun Leo.Ko kaɗan Leo bai kalli in da yake ba, amma da ya fahimci Noor baya son faɗuwa ne yasa ya kama hannunsa sai ya juyar da hannun nasa ya rike Noor ɗin da karfi suka fara gudu sosai a tare, hakan ya yi mugun karawa Noor kwarin gwiwa ba kaɗan ba.Lamarin da ya yi mugun baiwa su Zaysh mamaki kenan, how comes Leo zai kama Noor? Kai kamar a mafarki?. Shi kuwa Leo ganin Noor ya dage sosai ne yasa ya kara kankame hannun nasa.Abin da ba’a taɓa ba wai Noor ya zo na farko, sai yau shi da Leo su ne farkon isa wajen, tsalle ya dinga yi yana murna tamkar wani karamin yaro, kamar ma bai gaji ba fa, dik kuma daɗin Leo ya taimaka mashi ne yasa bai ji wahalar gudun ba. Shi kuwa Leo robar ruwan da aka ajiye masu a wajen ya ɗauko tare da ɓalle bakin ɗaya, tin da ya kafa a ɗan bakinsa bai zare ba sai da ya sanye tas, ya yi jifa da robar, sannan ya sake ɗauko wani, ya ɓalle ya sha rabi, zai rufe rabin Noor ya karɓa ya kafa a bakinsa, tas ya shanye, sai murmushi yake yi ya zo na ɗaya, a ransa yau ya ɗanɗani irin farincikin da ake ji a dik lokacin da aka yi nasara, sai ya ji yana sha’awar ya yi ta yin nasara a rayuwansa. Da bashi da wani tunani a gaba a rayuwansa, amma dalilin wannan abin Leo yasa ya fara tinanin cigabansa.One by one matasan dik suka iso wajen. Wasu sun iso a tare da Captain, wasu a bayansa. Yau babu wanda bai iso a kan lokacin ba, bayin ALLAH sun fara saba horon ne. Captain bai bari sun huta ba, yana isowa ya ce maza su shirya su kama hanya, ya nuna masu wani hanya a wajen, ya ce su je.Ba musu suka kama hanya, da sauri Noor ya bi bayan Leo, a kusa da shi ya tsaya, dik in Leo ya cire kafa a wajen shi kuma zai sanya. A haka suka isa wajen wani katafaren yashi mai kama da ruwa, irin yashi mai mugun laushi dake lumar da abubuwan nan ne. Waro idanu suka yi suna kallon wajen cike da mamaki. Muryan Captain ne ya katse masu kallon nasu da cewa. Zaku rarrafa daga farkon yashin nan, ku yi iyo a cikinsa ku fita ta other side ɗin. Zazzare idanu suka yi, gabaɗaya horonsu ya canza fa, yanzu dik girman yashin nan zasu yi iyo a ciki? Kai, lallai yau gwiwowinsu zasu cire, da matsala gaskiya.Suna can suna tunanin mafita Captain ya fara kirga masu lokaci, ga shi ya ce mintina 10 kawai garesu, wanda bai fito a 10 mins ba zai faro. Cikin zafin nama suka faffaɗa, dayawansu sun ji sabon wahala, dan a tunaninsu karamin aiki ne, sai da suka faɗa suka ji lumewa ƙasa suke yi, suna ƙoƙarin ɗagowa amma ƙasar na sake yin ƙasa da su. Still Noor yana kusa da Leo. Sai dai bai fargaba ya ga Leo ɗin ya fara yi mashi nisa, hakan yasa ya kara zafin nama ya matsa kusa da shi. Da Leo ya ga haka sai ya kama hannunsa da kansa, suka fara iyo a tare, yadda kuka san a cikin teku suke…….. Note kowani horo da nufin yinsa da kuma dalilin, ba in da ba’a turasu kama masu laifi, dan haka dole gwiwar kafafu da hannu su yi kwari!.A wannan karon ma Leo, Noor, Unays, Zaynash ne suka yi farko-farkon fitowa. Ya ilahi suna fitowa, wani irin daɗi da Noor ya ji, bai san lokacin da ya daka tsalle ya rungumi Leo yana murnushi ba. Da karfi ya ce. “Thank you so much brother, I really love you”. Haka kawai Leo ya tsinci kansa da tsananin farinciki ganin yadda Noor yake murmushi saboda shi. Ganin Leo bai amsa shi bane yasa ya sake shi yana kara faɗaɗa murmushinsa. A daidai lokacin su Vash suka fito. Cike da farinciki Noor ya ce. “Brothers na shiga sahun ƴan farko”. Zuba mashi idanu Vash, Unays, Leo and Zaysh suka yi, suna ta mamaki yadda yake murya. Shi kuwa yau ya gane watau zuwa na ɗaya fa duniya ne, akwai mugun daɗi, kai kanka a farinciki na musamman zaka tsinci kanka. Shi kansa Captain farinciki ne ta lulluɓe zuciyansa, sai ya guduri niyar faɗawa Leo ya ja Noor a jiki tin da idan suna tare yana zagewa ya yi nasara, dan suna son ya yi nasara. Da wannan tunani a ransa ya haɗa kan waɗan da suka yi nasara suka nufi wata hanya, waɗan da ba su nasara ba kuma ya kyalesu tare da sauran sojojin dake wajen kan su mayar da su su sake!.Wani katafaren fili aka kaisu a yau ma, sai ya raba su team by team, bari mu ɗauki team room number 1 and room 2 mu yi bayani a kansu. Captain ya yi gyaran murya tare da cewa. “Room 1 kune a matsayin zakwakuran sojoji kun zo kama manya ƴan’taadda a filin daga, team room 2 act like gangster now, room 1 ku kama room 2 ba tare da kun kashesu ba, ku gwada dabarar yaki mu gani”. Shiru suka yi suna tunanin ai ba’a koya masu wannan horon ba. Tamkar Captain ya gane me suke tinani sai ya ce. “Ba’a yi maku practical a kan abin da ba’a koya maku ba, a cikin horon da kuka yi akwai wannan, ku fara zaku fahimta”. Shiru suka sake yi, basu taɓa sanin dik wani rarrafe ko lankwashe-lankwashe da ake sanyasu wani nau’i ne na dabarar yaki ba, su sun ɗauka kawai dan jikinsu ya yi kwari su yi karfi ne, shiyasa suke ganin ai ba’a koya masu ba. Filin yana da maɓoya sosai ta yadda gane mutun abu ne mai wahala, akwai tankuna da drones na tsofaffin bayan motocin yaki. Captain ne ya ce. “Room 2 you have two run now, room 1 ku kuma ku yi shirin kai wa gangsters farmaki”. Room 2 ne suka fara kallon juna, to su da ba ƴan ta’adda ba ya za’ayi su iya acting kamar su fisabillilahi? Basu san an koya masu salon ƴan ta’addan bama, dan wani lokaci kafin ka kama ɗan ta’adda sai ka maida kanka irinsa shiyasa ake koya masu irin salonsu.Wasu empty pistol gun Captain ya baiwa su Leo a matsayinsu na waɗan da suka zo kama gangster’s. Sauran sojojin kuma ya ce dik su koma baya, bari room 1 And 2 su gwada aiki.Baya su Leo suka juya har sai da ƴan room ɗin su Unays suka ɓuya, sannan ne Captain ya ce su juyo. A natse ya ce. “A nan wajen zaku gwada kaifin ƙwaƙwalwa mu gani, ku kama ƴan uwanku ba tare da bindiga ba, kuma kada ku bari su dakeku, sai dai ku ku dakesu, amma ban da dukan da zasu ji ciwo”. Kallon juna suka ɗan yi, Zaysh ne ya ce. “Brothers let’s walk slowly kamar yadda muke tafiya a daji yayin fitar da kanmu, muna tafiya a hankali dan kada mu bugu da itace ko wani dutse”. Kallon juna suka ɗan yi, sai Leo ya wuce gaba, bayansa suka biyo, hannu ya ɗaga masu wanda yasa suka tsaya, da hannu ya yi masu alama da su rabu ba tare da ya juyo da kallonsa a kansu ba. Baya Captain ya koma tare da rungumo hannaye a kirji, shi da sauran sojojin suka zuba masu ido. Sanɗo suka fara yi rirrike da bindigun da aka basu. Rabuwa suka yi kowa ya kama laluɓe, a yau kowa kaifin kwakwalwarsa ta kwacesa. A yayin da suke zuwa su kuma su Unays suna kara ɓoyewa ne. A hankali Leo yake tafiya har ya shiga bayan wasu matattun motocin yaki da wasu kwantaunars, a nan ya ɗan tsaya shiru tamkar mai tinanin wani abin, sai kuma ya ɗan rintse idanunsa tare da kasa kunne sosai.Lokaci guda ya waro idanunsa waje, cikin zafa ya juya gefensa tare da sanyawa Unays dake laɓe bayan wata mota bindiga a kai, da numfashin Unays ya yi amfani wajen gane yana wajen, kun tuna horon da aka basu a daji na su dogara da numfashin juna? Ashe ta shiga kansu da kyau.Yana sanyawa Unays bindiga ya yi zafin namar damkoshi ta wuya-wuya suka fito harabar wajen, daidai lokacin Zaysh ya fito da nasa ya kama shi ma. Wani irin dogon ajiyar zuciya Captain ya sauke alamar ya ji daɗi, saura Noor da Vash dake laluɓe. Kun san da cewa Noor yana da bala’in kaifin ƙwaƙwalwa, ga shi dai baya son horon, amma wlh ya naɗi komai a kansa. Dan haka shi ma da numfashinsa yai amfani wajen kama shi, yana fitowa shi ma Vash ya fito ya kama nasa. A tsakiyar wajen suka tsai tsaya kusa da Leo. Da ido Captain yai amfani wajen cewa room 2 su kwaci kansu. Ai suna gane karatun suka juya suna fuskantar su Leo gaba da gaba, kafin Leo yai wani motsi Unays ya ɗaga kafa yai ball da bindigar da Leo ya nuna shi da shi, sama bindigar ta yi, tana dawowa Unays ya caɓeta tare da nuna Leo ɗin da ita yana wani irin murmushi wai irin ya yi nasarar nan.Ɗan buɗe idanunsa Leo ya yi yana ɗan mamaki, dan shi bai zaci su Unays zasu kwaci kansu ba. Sai kuma ya ɗan fiske. Unays kuma mamaki yake yi yadda aka yi kafafunsa suka yi sama sosai, watau horon rarrafen nan tasa kafafuwansu sun kara kwari matuƙa, lallai kuwa gaskiyar Captain ne an koya masu dabarun yaki a cikin wannan horo su ne basu ankara ba.Matsar da bindigar saitin forehead ɗin Leo Unays ya yi, yana cigaba da wani irin murmushi. Cikin zafa Leo ya ɗan kauce tare da yin ƙasa kaɗan, ya kama hannun Unays mai rike da bindigar, ya murɗe hannun baya, ai bai san time da ya saki bindigar ya fasa kara ba. Kasa ta faɗi.A maimakon Leo ya ɗauka, sai ya barta a wajen, suka hau gwabzawa da hannu, while su Noor ma suna fafatawa. Cikin ƙasa da minti biyar room 1 suka lallasa room 2 suka yi laushi. Dik sun kai abokan faɗar nasu ƙasa saura Noor da suke ta fafatawa, shi gaskiya bashi da karfi, amma ya dage don ya zo na farko, ai ya ɗanɗani daɗin zuwa na farko yanzu baya wasa.Tsaitsayawa su Leo suka yi suna mayar da numfashi, while su Unays suna baje a ƙasa suna nishi sama-sama. Captain ne ya ce. “Nan fagen yaki ne, kuna iya taimakawa ɗan room naku, dan ko a daji ne zaku taimaka mashi daga abokan gaba”.Ai tin bai gama rufe maki ba Zaynash da Vash suka yi kan su Noor, take suka kai guy ɗin ƙasa. Hannu suka dunkule suka bugi na juna, amma ban da Leo dake tsaye a gefe yana rike da waist ɗinsa, tafawa suka sake yi cike da murnan sun yi nasara. Shi ma Captain murna ya yi sosai, dan bai san meyasa team nasu Leo suke mugun burgesa ba, musamman Leo and Noor, yana jinsu har cikin ransa.Hutawa ya basu dama su yi na kamar mintuna biyar, aka basu ruwan sha kafin su wuce su koma dan yin lunch and sallah, dan time ya yi. Kai tsaye masallaci musulman cikinsu suka wuce. Bayan sun yi sallah suka haɗu a dining hall ɗinsu. Kamar yadda suka saba cin abinci suka ci, suka ƙoshi nak, sannan aka basu hutun 30 mins, a nan suka yi zaman hira, shi kuma Leo ya fito da wannan book ɗin ya fara karantawa. A kusa da shi Noor ya zauna, yanzu ya daina zama kusa da su Zaysh.Dik abin da Leo yake yi yana kallonsa, so yake ya dinga kwaikwayonsa saboda rayuwar Leo ɗin tana burgesa, amma bai yi magana ba har 30 mins ta cika, a nan aka kwashesu zuwa wajen gwajin makamai. A yau handling heavy weapons aka sanyasu, manyan bindigu aka basu su rike, aka ɗeba masu lokaci, nasan dayawanku baku san cewa bindiga tana da nauyi ba ko? To nau yi gareta, musamman idan akwai bullets a cikinta, shegen nauyi ne da ita, ai ko da iya rike bindigunsu aka barku ba karamin aiki bane, amma haka suke wuni dakon kayansu bayin ALLAH.A yanzu good 30 mins suka ɗauka wajen rike bindigun nan, daga nan aka ware 30 mins again aka koya masu magana da idanu ga junansu, idan sun shiga wata matsala ga dabarun da zasu isarwa da juna saƙo ba sai sun yi magana kowa ya jisu ba, Captain ya basu kalaman sirri ga junansu, wanda dik in da suke idan suka ambaci wannan kalma an san so ne, sannan kowani room ya basu kalaman sirrin gane juna ko a cikin duhu ne.Yau sai da suka yi sallar al’asar sannan suka bufi class ɗinsu. Shi ma yau sabbin makamai za’a koya masu, sun natsu tsit suna rike da notebook and pen. Cike da tsantsar jarunta Captain ya shigo ɗauke da katuwar littafin makaman nasu. A saman table ya ajiye littafin kafin ya juya ya kallesu da kyau. Sai ya juya ya fara rubutu a board ɗin, yau ya koya masu yadda bindigun suke, wajen bullet, yadda ake goge bindigar da dik wata sirrin bindiga. Wannan ɓangaren ba zan rubuta maku shi dallah-dallah ba, dan ban san iya ina rubutuna zai tsaya ba, akwai ɓata gari, ba ta yadda za’ayi in fitar da sirrin komai! Hakan na kamar cin amanar ƙasa ne! Dan haka ita bindiga sirri ce, kawai dai yau Captain ya yi masu darasi kan dik wata sirri na bindiga, ya bage masu komai!. Awa uku tsu suka ɗauka suna karatu, dan yau babban aiki ne, kuma kasancewar sun yi wannan dogon karatun yasa karfe biyar yau suka tashi daga horo, Captain ya ce wannan abin da aka koya masu yau yana buƙatar dogon nazari da natsuwa dan ya shiga kansu, saboda a wannan gaɓa ne idan suka yi kuskure kaɗan bindigar kan iya ja masu matsala har ta yi kisan kai, dan haka su kula sosai. Dan haka karfe 5 suka koma rooms ɗinsu, basu sake fita ba sai lokacin sallah musulman cikinsu suka fito suka nufi masallaci, basu dawo ɗaki ba sai da suka yi sallar isha’i, suka ci abinci, sannan suka dawo. Wanka suka yi, kowannensu ya yi shirin kwanciya, sannan suka ciro wayoyinsu suka hau kiran gida, yau har da Zaynash, ya fito da wayansa a gabansu bai ji kunya ba, ya kira Ummie ya haɗata da su Noor suka gaisa. Still dai Leo bai yi masu magana ba, suma basu yi gigin kai mashi waya ba. Noor ya dinga murna yana faɗawa daddynsa yau ya yi kokari ya zo na ɗaya, shi ma daddy murna ya dinga yi. Sosai suka sha hira, daga nan ya kira Aunty’s ɗinsa mata su uku, Luna, Lusi, Lisa, hira suka dinga yi, ya dinga yi masu kukan ya yi kewarsu, ashe dama su suka kara shagwaɓa shi suka mai da shi na mata, suma kukan kewansa suka dinga yi, wai baya nan yanzu ba wanda suke yi wa tausa. Shagwaɓa ya dinga zuba masu suna biye mashi. Ai idanu su Zaysh suka zuba suna kallonsa cike da mamaki, wai kato da shi yana abu kamar mata, sai ma da yake magana da su Aunty Luna, wlh zaku ɗauka macece take magana, har murya, ya canza voice ya koma sak su, cike da yanga. Dik abin da suke yi Leo yana jinsu amma bai tanka ba.Wai waye NOOR. Mu ɗan ji waye shi kaɗan. Ya fito ne daga babban family, sune mamallakan STARS BODY LUSH, Companyn da ya fito na farko a duniya, mahaifinsa yana da wasu mahaukatan kuramen kuɗi, su shidda ne a family ɗinsu sai, daddynsu, Lisa, Luna, Lusi, sai Uncle ɗinsu ƙanin daddynsu wanda shi ma babban mutum ne, Noor bashi da mahaifiya, ta rasu a lokacin da take nakudansa, daga karshe aiki aka yi aka cirosa, bai sha nonon uwa ba sai madara, yana ɗaya daga cikin abin da ya kara mai da shi haka, ga cutar tsoron dake damunsa.Akwai abin da ya faru da mahaifiyarsa a lokacin da take da cikinsa ne, wanda wannan firgici yasa nakuda ya tashin mata, tashin hankalin yasa zuciyarta ta buga bata haihu ba ta mutu, shi ne abin ya taɓa Noor. Su Lusi su suka renesa har ya girma, mahaifinsa yana mutuwar son ya haifi ɗa namiji wanda zai gajesa, ko bayan ransa zai tsaya ya kula da ƴan uwansa da kuma dukiyansu, amma sai ALLAH ya bashi ƴaƴa mata, a karshe ya samu namiji, ya yi matuƙar murna na samun Noor, sun renesa cikin gata da kulawar da ko kuda basu bari ya taɓa shi in suna nan!. Magajin billions of dollars ne nan.Sai dai a lokacin da ya fara girma suka fahimci yana da tsananin tsoro, dan ko irin wasan nan da suke yi na razana mutum in suka yi mashi suma yake yi, daddynsa ya shiga tsananin tashin hankali, daga nan ya fara yawo da shi kasashe dan neman mashi lafiya, Amma ina sauki taki samuwa, daga karshe uncle ɗinsa ya bada shawarar a shigar da shi hukumar soja, idan ya kasance cikin maza zai samu jarumta. Da farko daddynsa yaki, ya ce shi ba zai iya ganin ɗansa a wahala ba, sai daga baya da suka ga yana girma abin yana kara karuwa sosai, harta maganarsa ta koma ta mata, shi da ake son ya zana tsayayyen namiji da zai kula da dukiya, shi ne ya kare a mata maza ai kunga ba zaman lafiya, nan fa daddynsa ya aminta da a kaisa gidan soja mafi horon wahala.Uncle ɗinsa ya nemo, a nan ya zaƙulo AZURE, take aka yi applying. Cikin ikon ALLAH, da yake kuma suna da abin hannu, ya samu. Ko da za’a kawosa nan ya sha kukan rabuwa da ƴan uwansa mata, suka dinga cewa babu mai yi masu parkin gashin kansu ya kitsa masu jelar, dan shi yake yi masu dama, na ce maku dik wani abin da ya shafi mata ya iya.A takaice Noor maraya ne, babu uwa, bai sha nonon uwa ba, ga ciwon tsoro, ga shi cikin mata ya girma, ai ko daga nan zaku san Noor ya yi namijin kokari ma, rana tsaka ya tsinci kansa a wannan wahala! Ya jure gaskiya. Labarinsa a taƙaice kenan, saura bayani zaku ji a gaba. Me yasami mahaifiyarsa har ta firgita nakuda ya tashin mata unexpected? Wani irin tashin hankali ne yasa zuciyarta bugawa kafin ta haihu?. ——————–🔥Sun jima suna waya da Auntys ɗinsa kafin su yi sallama, ya ajiye wayar ya kwanta shiru yana tinani, da yanzu a gida yake yana kwance tsakaninsu, suna mammatsa mashi jiki cike da so da kauna.Zuciyansa cike da wannan tinani barci ta yi awon gaba da shi. Shiru room ɗin ya yi alamar dik sun yi barci, sai Leo da ya miƙe ya nufi toilet. Alwala ya ɗauro ya dawo kan dadduma, nafilfili ya zo ya yi tare da addu’oi, sai around 1 sannan ya kwanta. Washegari kamar kullum haka ta kasance masu. In takaice maku sai da suka jera kwanaki biyar suna sake maimaicin horo, suka sake karanta sirrin bindigar nan da kyau, tin ranar Monday suna abu ɗaya har zuwa ranar Friday. Yau gajeran lokaci ne, karfe 2 suke tashi a horo su je su huta.A yau kuma Captain ya ce zasu motsa zuwa matakin horo na gaba, dan haka sai suka farka da wuri, karfe 5:30 ta yi masu a hall da suke haɗuwa kafin su fara training. Izuwa yanzu dik wata wahala ta bi jikinsu, basa gajiya sosai, kuma basa wani nauyin barci, harta Noor yanzu jikinsa dan dole ta fara karɓar horo, musamman da yana kasancewa kusa da Leo, yana samun kwarin gwiwa.A saman stage Captain ya tsaya, ya sanyasu rera taken gidan soja, bayan sun kammala ne ya kwashesu zuwa gym na barrack ɗin. Da yake yau ce ranarsu ta farko, sai ya ce.”A yau zaku yi 200 push-up, 100 sit-ups, 80 burpees, 30 squats da kaya a baya, dik wanda ya kasa kammalawa a cikin mintuna 20, sai ya sake farawa daga farko”. Sai ya rabasu team by team best on yadda suke 4-4 a ɗaki. Kun san meyasa yanzu yake rabasu team-team? Dan ya lura idan ya rabasu ya sanya masu kamar gasa suna zagewa, babu wanda yake ɗaukar last, har Noor dagewa yake yi, kun san abu da gasa takan sa mutun ya yi har over acting ma.Dan haka bayan ya rabasu team-team, sai ya ce. “Dik wanda ɗan team nasu ya yi karshen gamawa, to dinka team ɗin zasu sake farawa ne daga farko, team da suka yi karshe kuma, zasu yi frog jump 500 feets”. Babbar magana.Ai su Leo dik kai kallonsu a kan Noor suka yi, while shi ma su yake kallo, bawan ALLAH tin da yake bai taɓa push-up, ta ya za’ayi yau kawai ya fara kuma a zaci zai iya. Da sauri ya kawar da kallonsa daga kansu, dan yasan sai ya ja masu ɗaukar last.Suna can suna tinani Captain ya ce. “Ready!……. Start”………… Cikin zafin nama kowa ya fara na shi, team ɗin su Unays sun zage, su ma su Zaysh sun zage sosai. Take suka fara haɗa gumi, amma dik da haka basu tsaya ba. Noor kam yana dai yi ne kawai, amma ba daidai yake yi bama, dan ko yadda ake ajiye hannu bai iya ba.Da Captain ya ga dayawa daga cikinsu basu iya ba, sai ya ce wasu sojoji su koya masu. Cikin minti ɗaya wasu dakakkun sojoji suka yi wa wajen ƙawanya, take suka fara bankare su Noor, dan kun san koyarwa waɗan da suka sha horo kam ba a hankali zai biku ba. Tin Noor yana daurewa har ya fara kuka. Zaysh and Leo ne kawai suka iya jurewa, a wannan karon Unays ma bai iya ba, kuma bai iya jurewa ba, dan Unays ma dai renon ice cream ne, iyayensa manyan ƙusa ne a Naija, shi kuma Zaynash kun san dole zai iya, saboda wahalar da suka sha hannun Auntynsu, bawan ALLAH wuya tabi jikinsa already.Shi kuma oga Leo yana da alaƙa kakkarfa tsakaninsa da AZURE wanda a nan ba zan faɗa ba, sai mun yi gaba, baa banza Captain Onbish yake jinsa a ransa ba, bugu da kari yana da alaƙa da manyan Generals na GIDAN SOJA ɗin, musamman GAT, wannan side ɗin na bari ne saboda wani sirri na labarin gaba zaku ji me alaƙarsu, amma suma basu san alaƙar ba fa, bugu da kari tin ainahi yana gym ba yau bane farau!. Tin da Noor yake a gidan soja bai taɓa shan wahalar horo irin na yau ba, kafafunsa da hannunsa dik sun yi tsami, ya sha kuka sosai, ya kuma ci wahala, ya wahalar da team ɗinsa, dan sau uku su Leo suna maimaita wannan horo, tin suna hakuri har dikkansu idanu ya fara raina fata, yau harta Vash sai da ya yi ta kuka, Leo and Zaysh basu yi kuka ba kam, amma dai sun ɗanɗana a jikinsu, idanunsu ya yi jajir tamkar wuta, tin daga nan Leo ya kudurta a ransa cewa in dai haka ne daga yau Noor ba zai sake sanyasu faɗuwa ba, dan fa ba karya yau sun wahala, sama da 2 hours suna maimaita wannan horo, tin suna iyawa har dikkansu suka gaza, dik saura teams ɗin sun kammala horonsu sun bar wajen, amma su suna nan. A ransa Leo ya ce lokacin gyarawa Noor zama ya yi, dan ba zai lamunta ba, babu abin da ya fi kona mashi rai irin last da team nasu ta ɗauka a yau, ya ji matuƙar zafin hakan. Da Captain yaga dik sun zube a ƙasa sun kwanta sai ya ce yau zai ɗaga masu kafa, amma wlh gobe dole sai sun kammala dukkansu a kan lokaci. Vash ya yi kuka har da majina, shi kan Noor ai faɗin irin kukan da ya yi ma ba zata yiwu ba, shi kuma Zaysh tin idanu na jajir har ta ciki da kwallah. Leo ne kawai bai yi kwallan ba, an dai ji jiki.A tinanin vash za’a yafe masu sauran lokacin da ya rage ace su je ɗaki su huta tin da sun gaji, sai ya ga akasin haka, saura awa biyu lokacin sallar jumma’a ta yi, a yau in suka yi sallar jummaa shikenan horo sai gobe, na faɗa maku ranar Jummaa suna da gajeran lokaci ne. A wannan awa biyu da suka rage Captain ya ɗaukesu suka nufi filin horo, ba zai iya yafe masu wannan awa biyun ba ko da zasu mutu. Dik sauran team sun kammala nasu har sun tafi horon sake koyan magana da ido.Su kuma yanzu za su yi escape run, ɗaɗɗaure masu fuska da hankey aka yi, aka ɗaukesu a mota zuwa wani waje mai nisa da basu san ina aka nufa da su ba, kafafu da hannayensu dik zogi yake yi masu.A wani waje mai cike da yashi aka saukesu, sannan Captain ya umarcesu da su koma sansani a cikin mintuna 70. Babbar magana, zazzare idanu suka fara yi, dan bama su san a ina suke ba, kallon juna suka fara yi, Captain kuma ya nemi waje saman bayan mota ya zauna, a natse ya ce lokacinsu ya fara daga yanzu.Shiru suka yi suna ƙoƙarin ganin sun yi amfani da kwakwalwarsu……… (Dik yadda aka yi manyan sojoji suna tantama a kan kaifin kwakwalwar room 1 ne yasa suke son gwadasu, dan kuwa wannan horo sauran teams ɗin basu yi shi ba, akwai dalilin da yasa su aka masu hakan!.)Sun ɗauki a kallah mintuna 5 a tsaye, sannan suka ɗan motsa, Captain ne ya ce masu. “In dai ɗaya daga cikinku bai isa sansani a ƙasa da mintina 70 ba to tabbas zaku sake farawa dikkanku, dan a cikin team kuke har yanzu”. Da jin haka yasa suka sake kallon juna. Leo kamar ba zai yi masu magana ba, amma da ya tuna ko ya yi kokarin ya koma bai kulasu ba in suka tsaya a baya shi ma za’a sake dawo da shi ne, tina haka ne yasa ya ware tafukan hannunsa yana rarraba idanunsa a kansu. Da sauri Noor ya matso ya ɗaura nasa hannun a kan nasa, Vash and Zaysh da sauri su ma suka ɗaura. Shiru Leo ya yi for 2 mins kafin ya ce masu. “Think with your brain”. Yana kai karshe ya wuce gaba. Da sauri suka biyo bayansa.Mamaki ne ya kamasu ganin daji ne a gabansu, bayansu duwatsu, gefen da gefensu bishiyoyi, da sauri Vash ya ce. “To ta wace hanya muka zo?”…….. “Ta wannan dajin na gaban, cikin ciyayi kenan”. A cewar Noor.Da sauri Zaysh ya ce. “Kenan sai mu bi tayan mota ai”………Murmushi Noor ya yi tare da cewa. “Yes mun samo hanya, cikin sauki ma zamu koma”……. Vash ne ya amsa da. “Ashe ma ba wani wahala zasu ruɗamu”. Murna suka fara yi sun samu mafita, har da wucewa gaba suka fara neman tayar motansu.In a cool way Leo ya ce. “Before they brought us here, they kept driving around in circles to confuse us about the route, so following the tire tracks isn’t the solution!!”……. Take murnarsu ya koma ciki, watau kenan sun shirya wahalar da su. Noor ne ya ce. “Brothers me abin yi to?”…… Vash ne ya amsa da. “Gaskiya our senior are very smart, wato suka yi ta kewaye da motar dan sun san zamu ce zamu bibiyu taya”…….. Zaysh ne ya capke da cewa. “Jahili baya yin AZURE BARRACK, dik wanda ka gani a nan ɗan baiwa ne!”. Noor ne ya ce. “Mu yi ta tafiya kawai zamu samu hanya”……. Zaysh zai yi magana suka ga Leo ya juya ya koma baya in da Captain yake zaune a saman mota. A ɗan nesa ya tsaya tare da kurawa motar idanu na 1 minute kafin ya juya ya dawo in da suke, gaba ya yi, kallon juna suka ɗan yi kafin su rufa mashi baya. A bakin fita dajin gaban nasu ya tsaya, ya ɗan lumshe idanunsa yana tinanin in da gate na parking lot na barrack ɗinsu yake, da ya tina gabas take fuskanta, sai ya tina motar da kawosu tana fuskantar yamma ne, hakan na nufin da suka fito barrack daga gabas sun juyo yamma ne, in kuwa haka ne barrack ɗinsu yana ta gabas ne. Bashi da tabbaci, amma yana tsammanin haka ne.Dan haka cike da yakini da yarda da kai ya wuce gaba tare da cewa su Noor su yi sauri dan lokacinsu ya ja. Zuba mashi idanu suka ɗan yi suna mamakin hanyar da ya nufa, dan su dai iya kallonsu basu ga alamar barrack ɗinsu a wajen ba. Amma sai suka yi hakuri suka bisa. Tafiya suka fara yi tin suna hira jefi-jefi kafafunsu na yi masu zafi har suka yi shiru. Sun yi tafiyar good 40 mins kafin su isko hanyoyin sun rabe biyu, tsayuwa suka yi a wajen suna kallon Leo, shi kuma ƙoƙarin tinano yanayin hanyoyin da suka bi a lokacin zuwa ya yi, dik da cewa idanunsu a rufe, yana iya tina kwana nawa suka yi a lokacin da suke cikin mota, tabbas kwana biyar suka yi, a farkon kwanansu sun fita barrack ba jimawa ne, kuma shi kaɗai ne kwanar tsakani da ALLAH sauran kwanan dik an yi ne dan a rikitasu.Idan kuwa haka ne to kwana zasu yi, ɗayar hanyar zasu bi, kuma daga in da suke babu nisa da barrack. Dan haka sai ya bi hanyar da ta rabe ta yi kwanar. Jikinsu dik ya jigata, da kyar suke tafiya a yanzu. Sai dai duna yin kwanar basu wuce tafiyar 10 mins suka yi ba sai ga barrack ɗinsu sun hango. Ai tsabar murna Noor bai san lokacin da ya wastsake ba, cikin farinciki ya rungumi Vash, sai suka daure suka ɗaga kafafu dan karisawa.Suna isa rooms ɗinsu suka wuce, dan lokacin sallah saura ƴan mintuna. A gurguje suka yi wanka, ga shi ba ruwan zafin gasa jiki, wlh dik wanda ya gansu yasan a tsananin gajiye suke. Noor dai ko wanka bai yi ba, gado ya haye, ya kwanta abinsa, tin da bani horo a gaba ai sai barcin huce gajiya.Su kuma suka shirya suka tafi masallaci, Leo ya shirya cikin wasu tsadaddun ripped jeans blue mai bala’in kyau, daga sama ya sanya polo shirt fari tas, still ya sanya army p-cap, amma ya juya p-cap ɗin dan ya iya yin sallah. Ya tara kitson kansa ya ɗaure a baya, ya tura jelar cikin p-cap ɗin, sai tashin daddaɗar kamshi perfume na kamfaninsu Noor yake yi. Watau yau Leo ya fito a ainahin ɗan duniyarsa, ripped jeans ɗin nan ta kara mai da shi irin shahararrun ƴan iskan nan ne, irin jeans ɗin nan ne masu zubin crazy, but ripped ba’a yayyage take skint a waje ba, tana yayyagen amma daga ciki an sanya wani tadin jeans ɗin, yagi-yagin ya zama kamar kwalliya ce kawai.Dadduma ya ɗauka ya fita zuwa masallacin, su kansu Zaysh da suke maza sai da suka kallesa suka kara, daga karshe ma zuba mashi idanu suka yi har ya fita. Sannan suka karisa nasu shirin, Zaysh kayanmu na hausawa ya sanya, kyakkyawar jumpa milk color da ta sha guga sosai. Vash ya sanya three-pieces suit. Ya yi matuƙar kyau, amma sai santin kayan Zaysh yake yi, wai shadda tai mashi kyau, Zaysh ya ce su je masallaci su dawo zai bashi kyautar kala biyu, ya zaɓi wanda yake so, sai murna yake yi. ——————- After 40 mins.Bayan sun yi sallah sun fito, za su nufi dining hall, a kan hanyarsu na zuwa suka ci karo da GAT da ya fito daga office ɗinsa, sai sauri yake yi, ai take kowa ya kame suka hau sara mashi. Har ya wucesu kuma sai ya dawo, a gaban Leo ya tsaya, dama tin ɗasun da ya kalli yadda suka yi suka dawo gida yake ta faman kallon Leo a video ɗin, dan yaga shi yai masu jagora.Key ɗin hannunsa ya miƙawa Leo, a natse ya ce. “Ka je sashin horar da jami’ai na musamman ka ɗauko mun yarana ka kaisu gida”. Yana gama faɗar haka ya wuce bai kara wata magana ba. Mamaki ne ya kama Leo, to shi a yaushe ya san yaransa fisabilillahi? Bai san hakan ma dik gwada shi yake son yi dan ya tabbatar da cewa da gaske da ƙwaƙwalwa Leo yake aiki ne ko kuwa! Watau ya gano yaran da kansa, ya yi tinani da brain ɗinsa.Ya ɗan jima a tsaye kafin ya juya ya nufi harabar office na Seniors ɗin nasu. A hanya ya haɗu da Captain, sara mashi ya yi, har zai wuce Captain ya miƙa mashi hannu kan su gaisa, ya ɗan yi mamaki. Katse mashi mamakin Captain ya yi da cewa. “A lokacin da ba lokacin horo ba ka ɗaukeni matsayin brother”……. Watau a lokacin horo kuma ba sani ba sabo.Jinjina kai ya yi tare da bashi hannu suka gaisa…….. “Ina zaka je?”. Captain ya sake faɗa…… Sai da ya ɗan yi shiru na ƴan sakani kafin ya ce. “GAT sent me to pick up his children from school and take them home”……. Jinjina kai Captain ya yi, shi ma zuciyarsa cike da mamakin yadda aka yi su Leo suka dawo, a tarihin AZURE team biyu ne suka taɓa haye waɗan nan gwaji dik da akwai wasu masu zafi a gaba, amma tin a farko babu wata wahala sun fara wucewa, gaskiya su ɗin ƴan baiwa ne.Wucewa Leo ya yi ya nufi wajen motocin. Duba key dake hannunsa ya yi, ta Pagani huayra lmola ce, yasan mota sosai shiyasa ya gane key ɗin wacce ce. Kai tsaye ya nufi motar, bai ɓata lokaci wajen shiga ba, ya ajiye daddymarsa a saman seat na motar, a natse ya tada ta ya nufi barin wajen.Sai da ya tafi kaɗai ya fara tinanin ina nema school ɗin kwararrun jami’an yake? Kwararru ma ta wani ɓangare ne? Dan kwarewar ai kala-kala ce. Hakan yasa ya tsaya tare da tambayar wasu zaratan sojoji dake ta faman sarawa motar a tinaninsu GAT ne a ciki. Sauke glasa ya yi tare da sara masu, sannan ya yi masu sallama. A mutunce suka amsa, a natse ya tambayi ina ne school na yaran GAT. Ba ɓata lokaci suka sanar da shi ai suna ɓangaren computer ne, su kwararrun jami’ai ne ta ɓangaren computer. Godiya ya yi masu tare da jan motar ya wuce, da kallo suka bisa suna manakin irin tsantsar kyan da yake da shi, basu taɓa kallonsa a barrack ɗin ba sai yau. Kai tsaye gate na school ɗin ya nufa, ya yi mamakin ganin babu students. Yau jummaa tin 1 suka tashi, yanzu kuma 2:30 ta yi, students dik sun watse, GAT ya shiga meeting ne ya makara zuwa ɗaukar yaran nasa, ga shi kuma bai basu driver ba saboda tsananin son da yake yi masu, komai da ya shafesu da kansa yake zuwa ya yi, dan in yasa ayi masu sai ya ga ba’ayi masu yadda ya dace. Rarraba idanunsa ya fara yi tin da ya shiga school ɗin, makarantar tana da girma sosai, zaka ce ba’a cikin barrack ɗin ma take ba saboda girma. Yawo ya fara yi a ciki yana neman ta ina zai gansu ne wai. Can ya hango wata studens sanye da uniform ɗinsu, tana duke a kusa da filin wasanninsu, jan motar ya yi ya karisa wajen. Jin motsin mota yasa ta ɗago kai slowly. Ya subhanallah, ALLAH ya yi halitta a wannan waje, ƴar yarinya ce da bata wuci 13 years ba, tana sanya da mini sket zuwa santala-santala cinyoyinta, black color ne sket ɗin, sai top daga sama white color, haka uniform ɗin nasu, tana da gashi mai tsananin kyau, bakinkirin, ta ɗaure shi kashi biyu, ta zubo jekar ta gaba gar kasan kirjinsa, ga jekar gashin an ɗaure da ribon kalar uniform ɗin, kafafunta sanye da boot fari tas, tana goye da jaka black color.Ganin motar yasa ta ɗaure fuska sosai, tamkar bata taɓa sanin menene dariya ba, da ta haɗe ran ma ta fi kyau. Da sauri ta bar wajen ta shiga wajen wasannin. Kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kansa, kuma ya gane ita ce ƴar GAT, dan ga kama nan a kan fuskansu. Jan motar ya yi ya bi bayanta har zuwa wajen wasanin cike da mamakin meyasa ta ga motar gidansu kuma bata tsaya ba? Bai san yaran nan sun fi ubansu murɗaɗɗen hali ba.A ɗan nesa da su ya faka motar tare da fitowa, ya jingina da jikin motar a ransa yana jin ba zai iya juwa ya yi masu magana ba, ɗan ɗagowa ya yi ya kalli yarinyar, sai ya ga ashe su biyu ne a wajen, ɗaya tana ƙoƙarin ɗaure igiyar boot dake kafafunta, ɗayar kuma hannunta rike da basket ball.Da sauri ya ɗauke kallonsa a kansu, amma ya sha mamakin ganin kamar kamanninsu ɗaya su biyun. Dan ya tabbatar kallon gefen ido ya sake binsu da shi, nan fa ya kara shiga mamaki ganin da gaske ne a kan fuskokinsu babu wani banbanci, sun yi mugun kama na wuce misali. Like seriously! Wow, abin da mamaki. Jingina sosai yai da jikin motar yana mai da kallonsa ƙasa, babu alamar zai yi masu magana. Wasu ƴan’mata guda biyu ne da suka shigo wajen basket ball ɗin a yanzu suka sanya yai gaggawar ɗan raba jikinsa da jikin motar, dan ta witsiyar ido ya gansu, sai yaga tamkar almara ce ko inuwarsu Arya ya gani. Nan fa ya ji kamar kwakwalwansa ta ɗan juya, a cikin ransa ya ce kenan ƴaƴan GAT Quadruple ne? Kuma dikka mata masu tsananin kama da juna? Kai bai taɓa ganin haka a zahiri ba. Amma sai ya fiske tare da mai da kallonsa ƙasa.Wacce ke rike da basketball ɗin ce ta ce. “Arya time is going let’s finish this game before that ya kariso”. Kalamanta ya nuna basu san da Leo a tsaye a wajen ba. Arya dake faman ɗaure igiyar boot na kafafunta ne ta ɗago da kai. “Angelina dad can’t come now, because he has a meeting, so we have a lot of time da zamu buga game ɗin nan slowly”. Uhm Angelie, Arya, Manassa and Vanisha, ƴaƴa ne ga GAT namu, ƴaƴan da kenan ya mallaka a rayuwansa, ƴan huɗu ne watau quadruples, sun taso ne cikin tsananin kula da soyayyar mahaifi, bai taɓa bari sun yi kuka ko sau ɗaya na rashin wani abu ba a rayuwarsu, yana sonsu fiye da yadda yake son kansa, basu da mahaifiya, daga su sai uban masu aiki dake kula da su, ma’aikatan gidan GAT sun haura 15, kuma dik saboda farincikin su Arya ya zuba su. Sun taso sangartattun yara waɗan da basa ji kuma basa ragawa kowa, ranon soja ne su ɗin, basu ɗaukar rainin hankali, musamman Arya, asalin sunanta DINEARIS, suna ce mata Arya ne kawai saboda wani dalili na daddynsu da yasa ya ɓoye ainahin sunansa. Yaran nan sun gado madarar kyau ne daga mahaifiyarsu, tamkar ku sacesu ku gudu ku je ku ajiye ku yi ta kallo, komai nasu iri ɗaya ne sak, sai banbancin halaye, dan Arya ita ce babba, kuma tafi kowa jiji da kai a ganin jama’a, amma a zahirin gaskiya tsantsar kamun kai ne da gudun rainin wayau, shiyasa bata kula kowa, ko ɗaga ido ta kalli mutane bata yi, ƴan uwanta sai daddynta kawai take kulawa. Sai mai bi bata Manassa, ita ma tana da halin shariya, amma ita kuma akwai son gulma sosai, dik wani news na gulma to a zo wajenta amma akwai shegen tsoro. Ta ukunsu Angelina, ita ƴar baruwana ne, kowa nata ne, sai zafin ran balai idan ta ga ana zaluntar wasu, wani lokaci bata da hakuri kuma bata da daɗin sha’ani, dan bata barin ko ta kwana, na karshensu kuma autarsu ita ce Vanisha, suna ce mata V, yarinya son kowa kin wanda ya rasa, shagwaɓaɓɓiya number ɗaya, ga zallar iya soyayya, akwaita da son karanta labaran soyayya, ga son kallon film da ake mutuwa kan soyayya, kullum maganarta ɗaya yaushe masoyinta zai bayyana, tana da fara’a sosai, dik cikin Quadruple ɗin ita kaɗai ce mai fara’a, sannan ita kaɗai ce mai saukin kai da kaunar ƴan aikinsu, sai Angelina ita ma time to time tana da mutunci.Dikkansu suna da mugun tsabta, dan wlh ko mai ƙanƙantar datti basa accepting a arear da suke. Dikkansu ba musulmai bane kamar yadda kuka san GAT mahaifinsu ba musulmi bane. In maku yadda zaku gane, idan kuma gansu yadda kuka san irin fashion model ɗin nan, watau irin shahararrun mata masu tallan kaya ko wani abin, suna da tsawo da kyakkyawan jiki, kuma just 13 years suke da shi fa.Dikkansu gashin kansu dark ash ne haka, mai balain kyau wanda har wani sheki yake yi idan ya ji gyara. Ga idanunsu dara-dara fararen sol, kuma abin dake kara rikita mutane da su irin tiger brown eyes ɗin nan ne da su kamar na daddynsu, idan suka zare maka ido tamkar idanun tiger, jikinsu tamkar madara, da yake suna da tsawo sosai zaka iya basu 15 years in ka gansu.Dikkansu suna da zane a wajen wuya wanda daddynsu yai masu tin suna ƙanana dan mutane su rinƙa rabesu, tsananin kamar tai yawa ne. Kowacce a gefen wuyanta an rubuta mata harafin farko na runanta, Arya and Angelina da suke da A a farkon suna sai daddynsu ya sanyawa Arya sunanta ARYA, Angelina kuma A kawai dan banbanci, to da wannan zanen ake banbancesu.Su ɗin ba kamar sauran yaran da kuka sani ba ne. Kwararrun jami’an bincike daddynsu yake da burin su zama, kuma ALLAH ya zuba masu baiwar, yanzu haka suna da 13 years, amma idan suka rike computer sai kun sara masu, suna karatu ne a nan A-C-S dake nan cikin Barrack ɗin, makaranta ce da ake kwankwasan kwararrun jami’an da suka san computer, wanda dik wani aiki da za’ayi sai da su, cikin ƴan mintuna ƙalilan suke iya binciko abu dik nisansa, basu da wasa kuma basa ɗaukar wasa, yanzu trainin suke karɓar a kan computer, sannan suna karɓar horo irin na su Leo, sai dai ba kamar nasu kai tsaye ba, sese-sese dai, su ana basu horon ne dan kare kansu idan suka shiga wajen haɗari. Bari in yi maku misalin jami’an zaku fi ganewa, su idan za’a je kama riƙaƙƙun ƴan ta’adda ana tafiya dasu ne a motarsu daban da Computers ɗinsu a cikin motar, zasu tsaya ɗan nesa da in da ƴan ta’addan suke, zasu tura drone mai ɗauke da Camera da suke controlling ɗinsa daga in da suke, idan ya isa wajen ƴan ta’addan zasu dinga ganin dik abin da suke aikatawa, daga nan su samu connection da sojoji suna faɗa masu dik wani motsi na ƴan ta’addan tin da suna ganinsu. Nasan yanzu kun gane irin jami’an da nike nufi, masu kaifin ƙwaƙwalwa da basira, kina basu number kika ce su nemo maki mai ita cikin ƴan sakanni zasu faɗa maku a in da yake, to su ana basu horo ne dan su kare kansu idan yaki ta ɓarke ta ritsa da su a wajen kama ƴan ta’addan……………. To abin da su Arya ke karanta kenan, kuma su dikkansu uku da, ita kuma Manassa tana ɓangaren Surgeon Generals, watau likitan sojoji, sun mai da hankali sosai, dan suna burin zaman manyan jami’ai. Aikin soja suka so, amma daddynsu baya son su sha wahala shi ne ya sanyasu waɗan nan matsayi.Uhm yanzu muka fara tafiyar, wasan kwakwalwace zallah a book ɗin nan, ilimi za’a gwada da kwarewa, ga soyayya mai zafi! me kuke tinani? ku biyoni dan samun ilimi kuma!. ————————🔥”Woooow”. Angelina ta faɗa tare da miƙewa tsaye gabaɗaya, ta kara zaro tiger eyes ɗinta a kan Leo dake tsaye yana kallon ƙasa. Da sauri ta taɓo Arya tana faɗin. “Bloody, look at this handsome guy, heroic man”. …. Kusan a tare dikkansu huɗu suka ɗago kai da kallonsu a kan Leo. V mayyar soyayya da shauki ce ta fara cewa. “Kai anya wannan ba Angel bane? Dik yadda aka yi mala’ika ne”. Ta faɗa cikin ruɗu tattare da shauƙi tana wani ɗan rintse ido ta sake warowa. “This is unbelievable V, this is seraph, look at his body, like wow”. Cewar Manassa… Angelina ce ta capki zancen da cewa. “Laaa motan daddynmu ne, mu ya zo ɗauka, daddy ba zaizo ba dama”. Waro idanunsu gabaɗaya suka yi a kan motar da ya jingina, lokaci guda suka hau sauke ajiyar zuciya. Arya ce ta ɗan ja siririn tsaki kafin ta ce. “Seraph bai kamata ace yaron daddy bane! Disgusting!”. Ta faɗa tare da nuna yatsarta na tsakiya alamar ƙasƙanci.Manassa ce ta amsa da. “All though wani guru ne! Look at his body, his soft skin, all though ɗan wani shegen ne, but it’s very disgusting ace boy ɗin daddy ne, I feel very shameful for him”. Cikin sigar rainin wayau tai maganar.Arya ce ta sake cewa. “Leave all your bags here bari mu sakashi ya zo ya ɗauka mana tin da boy ɗin daddy ne”. ………. Su fa daga ganin ya zo ɗaukarsu kenan ɗan aikinsu ne tin da a karkashin daddynsu yake!.Nufar in da yake suka yi, cikin takun class da yanga, Arya ce a gaba hannunta rike da basketball ɗin nasu. Shi dai tamkar babu shi a wajen. A gabansa suka tsaya, cikin bada umarni Arya ta ce. “You don’t know your work, right? Ko dai door ɗin ma mu zamu buɗewa kanmu ne?”. Da yake yana kallon ƙasa ne sai ya kalli Boot dake kafafunsu, a nan ya gane sun iso in da yake, ko kaɗan bai motsa ba, babu alamar ma zai tanka masu. Dikkansu da suka matso kusa da shi babu wacce kirjinta bai buga ba, sunga madarar kyau ga kwarjini, dik sun kasa magana, Arya ce ma da yake akwaita da karfin hali da tsiwa shiyasa ta iya yi mashi magana.Ganin bai amsa masu bane yasa suka kalli juna, sai kuma suka mai da kallonsu a kansa. V sarkin saukin kai sai ta nufi wajen motar, buɗe kofar tai tare da cewa. “You people should come in”. Wani irin tsaki haɗe da kallo mai wuyar fassaruwa Arya ta dallawa Leo da bai san tana yi ba, a cikin ranta ta ce dole ta faɗawa daddy ya hukunta shi, dan ya ɓata mata rai. Manassa da Angelina da suka kasa yi mashi magana ne suka yi saurin shigewa cikin motar, sai kallonsa suke yi tamkar zasu cinyesa da ido. Ita kuma Arya gyara tsayuwarta tai tare da riki waist ɗinta da hannayenta dikka biyu, cike da gadara ta ce. “Ka kwaso bags ɗinmu mu je”. Still Leo bai motsa ba, yana tsaye. Motsawa tai tamkar zata shiga motar, ganin bashi da alamar zuwa ɗauko bags ɗin nasu ne yasa ta dakata, matsawa kusa da shi tai, dik da mugun kwarjinin da ya yi mata, ga shakka da tsoronsa amma ta daure ta tsaya dab da shi, zuciyarta na bugawa da karfi, amma saboda karfin hali irin nata sai ta miƙa hannu ta ɗago haɓarsa tana faɗin. “Kai kurma ne? Ko baka san aikinka ba……”.Gagara karisar da maganar ta yi saboda sharp eyes ɗinsa da ya sauke a kanta. Wani irin rikicewa ta yi, a miliyan ta ja da baya har kamar zata faɗi tai zafin namar rike kanta, zazzare idanunta a kansa ta yi, tamkar kwayar zasu faɗo ƙasa. Shi kuwa kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa, gentle ya raba jikinsa da jikin motar, ya buɗe from seat ya zauna, ba tare da ɓata lokaci ba ya yi wa motar key.Ganin tsab zai iya tafiya ya bar Arya ne yasa Angelina tai saurin leƙowa ta jawo hannunta, dama basu rufe door ɗinsu ba. Kuma tsabar girman kai irin na Arya taki zuwa ta kwaso masu jakunkunan, watau sai da shi ya zo ya ɗauko ko a barsu a wajen.Shi kuwa reverse yai, ya juya kan motar, ko a jikinsa, bai ɗago ko sau ɗaya ya kalli in da suke a ciki ba, da sauri Angelina ta rufo kofar. Da gudun gaske ya ka motar suka bar school ɗin.A shagwaɓe V ta ce. “Daddy’s boy mu idan an ɗauko mu a mota ba’a gudu saboda ina tsoro, please go slowly”.
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥


